Skip to content
Part 25 of 75 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Mutum uku Sameer ya kawowa Farida Amma Dukkan su tace basuyi Mata don Babu ta yadda Zata iya kwatanta su da kanta a matsayin Mazan Auren ta . Bata Jin zata iya tana Jin tamkar Zata mutu idan ta tuna ta tab’a hada kanta da su da sunan Mazan Aure. Sameer kadai take so da sunan wannan Rayuwar ta Aure Amma duk Mazan Duniya Basu Kai ta Daga Kai ta kalle su ba matukar Sameer Yana Raye bare tace sun burge ta har tana tunanin wata Rayuwa dasu irin wacce ta shafe babin ta sai ga Sameer kad’ai Kuma da gaske take wannan maganar ba daga Bakin ta Kalaman suke fitowa ba A a sai daga k’asan ZUCIYAR ta…

A Rikice Sameer yazo don yaji ko mutumin da ya turo Mata Wanda ya kure gayu da turare yayi Mata ? Amma yasha mamaki da ta Sanar da shi baiyi Mata ba…

Ya zuba Mata ido cike da Tashin hankali ya Rasa Abinda zai ce mata Amma sai yaga gara ya bude Mata kalubalen Da yake Gida Yana jiran shi na Auren Aisha da Haj take Neman k’ak’aba mishi ita da kanwar ta Anty Asiya suke Shirin auno mishi ya San idan taji Hakan zatayi saurin yarda…

Ganin ya shiga tashin hankali yasa ta Rik’e Hannunwan shi kafin ta Rungume shi cike da bege da kewa tana kuka tana Fadin

“Ka gafarce ni Sameer bana iya jure Jin ance Wani na ke Aure ba Kai ba. Wallahi ba zan iya bane shiyasa duk Wanda ka turo da sunan yazo mu daidai ta da Kai nake hada shi sai Naga Bai Kai ko Rabin ka ba bare ya kamo ka ko ya fika sai Naji baiyi min ba duk da na San manufar Auren ta KISAN WUTA ne…

“Na Sani Farida na Sani Amma kiyi mana gata don Allah ki Hak’ura da kallon dacewa ko Rashin ta ki fidda mu daga wannan kangin kin kuwa San Haj ta Soma maganar hada ni Aure da Aisha ta Anty Asiya? Bana son Al Amarin nan Farida ki daure kawai duk Wanda na kawo Miki a yanzu kice yayi a gabatar da shi ga su Haj da Yaya dauda ayi a gama ko ma koma tunda har Haj ta Soma min Arashi da fadin ko Ina jiran mijin da Zaki Aura ya mutu ko ya Sako min ke shine ba zanyi Aure ba . Idan suka Aura min Yar su Farida ba zan iya Yi Mata Adalci ba saboda bana son ta ba Kuma zan so ta ba. Don haka don Allah don ANNABI Farida ki Amince da Duk Wanda zan kawo a yanzu Saboda Babu wani Abu da zai faru a tsakanin ku kina katsina Yana Daura za ayi Auren Nan bare Wani Abu ya shiga tsakanin ku wata Kil ma har Auren ya kare ba Zaki kuma Ganin fuskar shi ba…

Wani irin tsoro da firgici suka lullube ta Domin kuwa ta san yadda Aisha taso Auren Sameer tun suna soyayya haka ma da tayi Auren Bata fasa Kiran shi a waya ba bare Kuma tazo garin kamar wahayi akayi Mata sai tazo Gidan shi sai Kuma ta ganshi ko zata koma don haka sai kawai ta dubi Sameer da suke Rungume da juna tana fadin…

“Na yarda koma waye ka turo Sameer ai ban San Aisha ta na Neman shigowa tsakanin mu ba wallahi da tun na farkon da ka kawo yanzu da an kusa gamawa Amma har Abada ba zan taba yafewa kaina ba idan har Aisha ta SHIGA gidan ka Sameer Wallahi zan mutu ne…

“In Sha Allah ba za ayi Hakan ba tunda kin yarda Nima kuwa ai zan mutu ne don Baki da mahadi a zuciya ta bari na koma kar Kuma a Saka Mana Ido kin San fa Babu Wanda ya San da zaryar da nake daga pertercout zuwa katsina bana son su Haj su fahimci Wani Abu idan suka Gane zasu kawo Mana matsala don haka in na Samu yadda nake so Satin sama Zaki ganmu Nazo da wanda za ayi Hakan da shi koma kawai na sake Nemo yaron Nan Nazir nafi Aminta da shi Farida ba zai kawo Mana matsala ba…

“Ko shi din ma ka maido ai bana Jiran Wani Abu Kuma yanzu sai ta yadda zan Raba ka da Aishar can Sameer don Allah Kar ka yarda su lika Maka ita Wallahi zan Rasa Rayuwa ta idan ta Aure ka…

Ya Sumbaci bakin ta yana shafa fuskar ta sukayi sallama ya wuce ita Kuma ta shiga Gida

Haj ta kalle ta kamar Mai karanto Al Amarin da take ciki sai Kuma ta ce

“Da wannan Zaman da Zakiyi da makarantar Nan ta islamiya kika koma zai Fi Miki Wannan Zaman Shirun ko ba komai dai kin Rage lokaci kin Kuma samu Karin Haske akan ilimi Kafin Allah ya Kuma fiddo Miki Wani Mijin…

Sai Kuma taji Zancen Haj shine gaskiya don haka ta shiga Neman shiga makarantar ta tanbihul Islam da ke nan bayan su tuni kuma ta kama karatu ka in da in inda taji kaso mafi yawa na damuwar ta ya yaye.

Ta Hadu da Abokan karatu masu kirki da mutunci irin su hadiza balarabe da Kuma Maryam Ibrahim Wanda ta Gane suna da Sani akan Rayuwa sai gashi Kuma haduwar su ta Kara Mata Wani ilimin

An tashi makaranta ne Suka nufi gidan wata Yar Uwar su daliba wacce ta Haihu don Yi Mata barka a kofar guga don haka suka je su uku Sukayi barka suka fito kowace ta kama hanyar tafiya Gida Farida ta taho zuwa gida inda motar Tasha gaban ta tana Mai shirin fitowa sai kawai taga Abdullahi Yana fitowa Yana Fad’in

“Kai Farida nake Gani ko kuwa dai Mai kama da ita ce?Y a fada cike da zolaya Yana Kuma Kare Mata kallo tun daga sama har k’asa Abinda Kuma ke Bata HAUSHI da shi kenan akwai barikanci a harkarsa.

Tayi murmushi tana Fadin, “To duba dai da kyau wata Kil ka cinka daidai…

Ya yi Dariya Yana Sosa gashin gemun shi Yana tsura Mata ido har ta tsargu don shi Kam akwai kallo har na tashin hankali ..

“In ce dai dauda ya Kai sakon gaisuwar da na bashi Farida? Satin da zan tafi America muka hadu da dauda har Yana fada min Auren ki ya mutu shine nace ya Mika sakon gaisuwa Kuma in na dawo zan shigo wata Kil dai Allah ya tsaga da Rabon kura a takobi sai na shigo da karfi na mu shiga daga ciki ko Yaya masoyiya?..

Wani Abu ya tsirga mata tayi murmushi tana fadin
“Wai shi Yaya daudan ne ya fada Maka mutuwar Aure na?

“Wallahi shine na Kuma San Sharar hanya yayi min Kuma sai ya duba a daidai tamkar ya San Ina kan hanyar Kara Aure Kinga ga tsohuwar Zuma Farida ke kin sani Rashin ki ne ya Saka ni Auren Basma sai Kuma ga Rabo ya Rantse…

“Kai Haba dai Kai yanzu in nace ka fito sai ka fito Abdul? Na zama cus fa.

“Ni a wuri na babu Abinda Zaki zama na kasa son ki Farida Wallahi har gobe Ina mafarkin Auren ki Kuma Idan kin bani Dama Wallahi Babu Bata Lokaci zamu shige daga ciki uhum? Wannan Bakin har gobe ban bar mafarkin Ina tsotsar sa ba.

Kalaman shi Suka Bata kunya ta juya tana Fadin.

“To in dai da gaske kake mu Hadu gida yanzu daga makaranta nake Kuma Ina sauri.

“Yo ni Aikin me nake da zan barki ki tafi? Meye amfanin mota ta my Farida? Yau din Nan na dawo daga America Kuma Wallahi tunda dauda yace min Auren ki ya mutu naji a Raina da Rabon sai na shimfidar da ke Farida a kirji na har nayi.

Ya bude mata kofar Motar ta shiga ya zagayo ya shiga suka dauki hanya har kofar Gida ya fito Yana Bude mata ta fito ya bi bayan ta har cikin gida inda Haj ta gansu tare da Abdul din.

“Kai Abdullahi wai Dama kana Nan? Kwana biyu an Daina ganin ka.

“Ayi Mana Afuwa Haj karkoki ne Sukayi yawa.

“Ai kuwa Amma yanzu ma na Gane Abinda ya kawo ka Farida ce ta kawo ka.

Yayi dariya Yana Fadin, “Wallahi Haj Babu karya a maganar Nan Domin kuwa dauda ya fada min Rabuwar Auren su shine nace ta wata kil fa akwai Rabon kura a takobi yanzu ma na dawo Haj.

“Kai Amma kuwa nayi murna Abdullahi Allah ta ala ya Sanya Alheri ya sa Kuma Alherin ne s tsakanin ku.

Ya amsa da Ameen Ameen ya dauko kudi Yana ajewa Haj kafin ya Mike Yana cewa Farida
“To Amarya fito na ganki Mana minti Biyar.

Ya fita zuwa soro Farida ta fito itama suka zauna a kujerun Roba Yana kallon ta da zalama Yana fadin

“To Farida har ga Allah banzo a karo na Biyu da wasa ba tun a lokacin budurci naso na dauka allah Bai nufa ba Amma a yanzu kam Ina jin Akwai Rabo na a nan Don haka kar ki boye min komai idan kinji kinyi na am Dani Ina fatan hakan idan Kuma ba Kya Ra ayi na zan matsa Miki ba tunda Shari a ma ta Baki zabin mijin da kike so a yanzu ba zanga laifin ki ba Saboda shi Aure na mutum Biyu ne idan daya baya Yi to Dole Daya yayi Hak’uri.

Ta Sauke AJIYAR ZUCIYA tana fadin, “Babu komai Abdul ni ba zan iya Cewa komai ba ka samu Yaya dauda shine madadin Uba na duk yadda ya yanke a Kaina yayi daidai Kuma ba zan ja da shi ba tunda a matsayin Uba na yake.

“Nagode Farida Amma duk da Hakan na San dauda zai yanke Hukunci ne bisa zabin ki da Ra ayin ki idan har Baki muradi na zai Miki Adalci nafi son naji daga Bakin ki kice kin yarda Dani kin Amince Dani sai na san har yanzu Ina Nan a Mai gemu na da nake firgita Mata Kuma ba a Isa a ce ba a Sona ba har gobe fa Ina Razana Mata Farida ban sani ba ko har da ke ko Babu ke?

Tayi kasa da kanta tana fadin, “To ai Mata kace ni kuwa ai ban Kai macen da zan daki kirjin cewa Nima mace bace.

“Wallahi kin Kai Farida har kin wuce kin kuwa duba madubi Kinga kanki ? Har gobe ban daina Mafarkin ki ba fa . Rashin ki ya kaini Auren Basma ita da kanta ta San ke nake so tunda yarta ta fari sunan ki na Saka Mata Amma tace Bata yarda ba ba sunan tarta Farida ba sunan ta Najwa.

Farida tayi murmushi tana fadin, “Kaji Halin ku maza ba? Meye zaka Saka Ma yarta sunan budurwar ka Kai yanzu zaka so ta sakawa Danka sunan saurayin ta?

“Kai ita ta isa ma? Ai kuwa da ta kwana Gidan su Wallahi duk da ta San Bana daukar wargi musamman da ta Gane bata mallaki Abu Daya da nake so ba . Farida Bata da diri irin naki . Bata da kirji irin naki Kuma ni din Ina son mace Mai cikar kirji Kuma ba fara ba Kuma ba baka ba Akasin ita da take fara tas Kuma Mai tsawo haba mace Mai tsawo sai kace dai Daren sallah? Kawai dai Wanda ya bani Auren nata ba Wanda zanyiwa gardama bane don Abokin mahaifi na ne Ganin ba zan iya fito da wata ba bayan ba Rasa ki shine ya Yi min madadi da ita Kuma har Gobe bata Daina adawa da Mai sunan ki ba sai gashi Kuma Zaki Aure Mata ni Farida bayan fargabar da kika Saka ta ta mallakar Abinda Bata da shi kina Wani gidan ma kenan Ina ga Kuma kin zo Kun Zauna?.

“Duk da haka Kuma Maza Kuna da laifi ka San in Kai tayiwa Abinda kayi Mata ba zaka ji Dadi ba itama sai kayi Mata Adalci. Babu Mai samun Abinda yake so d’ari bisa d’ari sai ka boye Abinda kake so a zuciyar ka ka Kuma karbe ta a yadda take don kaima baka cika cif irin yadda take so ba. Amma Kuma in nice ita Wallahi ba zan tashi hankali na akan namiji ba har na damu da sai na zama yadda ya Zana Yana son mace ta zama idan kuwa har ta zama yadda kake so in Sha Allah Wahala Bata kare Mata ba a lokacin ne zata Gane akan ka sai dai ta zama wahainiya Mai sauya launi don daga yadda take zata sake komawa wata kalar don zaka ce ba haka kake son ta ba sai wata kalar da ba zata iya komawa ba.

“Mu Rufe babin Basma farida ni yanzu a me kika aje ni ?

“A zuciya ta na aje ka Abdul.

“Kice dai yau in kwana Ina mafarkin I love you Farida.

Sukayi Dariya ya Mike Hannun shi cikin aljihun Rigar shi ya fito da kudi Yana Mika Mata..

“Ga kudin tad’i na bayar Amma Kuma haka zamu Rabu Babu gaisuwa?

Ta Mike tana Fadin, “Wace irin gaisuwa ce banyi Maka ba to ?

Ya matso Yana kallon ta Yana kamo Hannun ta ya Rik’e ya na Zuba Mata ido sai taji ya Rungume ta Yana Goga Mata gashin sajen shi Yana fadin,

“Irin wannan gaisuwar nake nufi ki fa shirya gyaran gemu Farida tunda kin Auri Mai gemu bana yarda Namiji ya tab’a min gemu matata ke gyara mun.

“Ni Kam ban iya gyara Wani gemu ba Amma tunda matar ka ta iya sai tayi ta gyara maka.

“Ai duk yadda zan so nata ba kamar naki ba don kece Duniya ta Farida Babu Abinda Zakiyi min Naga laifin ki kiyi komai ba komai Yan Mata na.

Ta Zame daga Rungumar da yayi Mata don sai goga Mata gashin gemun shi yake a fuska har Yana Neman fidda ta a saiti Abinda dama yake so kenan.

Ya nufi hanyar ficewa Yana Fadin, “Ai Kuma tunda na dawo sai dai ki cewa Haj tayi ta Hak’uri Dani don kullum Ina Nan.

Ta Tako mishi har mota ya zuba Mata ido Yana Fadin, “Ni kuwa Farida ya akayi sai yanzu nake Ganin kyan ki kama Wanda akayiwa Rufa ido? Ki duba madubi don Allah ki Kalli baiwar da akayi min .Kai Lallai Allah yayi mini baiwa in Sha Allah ba zan bari a Kara wata Guda Nan gaba ba tunda dauda yace min kin gama idda kinga sai mu shiga daga ciki mu mayar da kofar.

“Allah yasa kar wannan Dan iskan dauda ya kawo min kauli bare yaga na matsu Ina son kawo ki ai sai ya ja ni.

“To ai tsakanin ku ne ni zan SHIGA ciki Allah ya tsare hanya a Gaida min Anty Basma.

“Kuma kuwa Yasin sai na fad’a Mata in tace wace Farida ke zan fada Mata kice yau Akwai bori in ta San kina hanyar shigowar gidan ta.

Sukayi sallama ya wuce Yana kallon Farida Yana shafa fuskar shi.

Ta shiga gida tana tunanin Anya kuwa Bata zura jiki da yawa ba? Anya kuwa Abdul Mai Gemu zai iya sakin ta idan ya aure ta? Ta Yi saurin jawo wayar ta tana Danna Kiran wayar Sameer Wanda ya dauka ta tare shi tana fadin.

“Albishirin ka derling? Bata bari ya amsa da Goro ba ta zarce da Cewa.

“Allah ma ya kawo Mana Wanda zamuyi Hakan mu gama ba tare da wata matsala ba.

“Waye kika samu haka Farida?

“Wani tsohon saurayi na ne da ya tab’a Sona tun Ina budurwa shine yazo yau ya Kuma ce yaji ta Gani kaga tsuntsu daga sama kenan.

“Anya kuwa Farida Babu kuskure a cikin wannan Hikimar? Ta Yaya Wanda ya taba son ki zai yarda ya Aure ki Kuma ya Sako ki? Gaskiya ban yarda da Hakan ba gara Wanda Bai San ki ba ma yafi akan Wanda ya San ki har ya taba son ki yaushe kike Ganin Zaiyi Hakan? In ma Baki bashi dama ba kar ki bashi ki bari kawai na zo da Nazir ayi komai Asiri a Rufe Amma ko kallon Sha awa tsohon saurayin ki yayi Miki Farida ai ya cuce ni.

“Kar ka Damu Babu wata matsala Wallahi Kai dai ka bari

“Farida ban gamsu da wannan zabin ba waye wannan da kika zabi yin Hakan Dashi? Ya sunan shi ? Kuma a Ina yake?

“Sunan shi Abdullahi yakubu Wani Dan canji Kuma a garin katsina yake.

Wani irin matsiyacin tari ya sark’e shi ya Soma Yi tamkar Wanda ya shaki barkonon tsohuwa ya samu ya hadiye tarin Yana fad’in.

“Kika ce Abdullahi yakubu dan canji? Ta amsa da Eh.

“Wai wanda Ake Cewa Gemu Farida? Ta Amsa da sauri tana fadin

“Shine fa Ashe ka San shi? To shine Kuma tsohon saurayi na ne Babu wata matsala idan na Aure shi cikin Sauki zai sake ni ko don son da yake mini.

<< Tana Kasa Tana Dabo 24Tana Kasa Tana Dabo 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×