Skip to content
Part 2 of 75 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Sai yamma Farida ta farko sakamakon Wani matsiyacin Ciwon ciki Wanda shine ya farkar da ita ta Kuma farka a wahale tana dafe kici duk da jikin ta Babu Abinda yake mata sai ciwo da zogin ciwukan da ke jikin ta Wanda Suke manne da bandeji.

Haj da take goye da Hanan ta matso ga Farida tana Mata Sannu.

Ta Dubi Haj idon ta Yana ganin Hajiyar dishi dishi.

“Haj ciki na ! Ta fada cike da gajiya da Wahala. “Subuhanallahi Farida ciwo yake cikin ?

Ta Kara dafe cikin da Hannun ta inda Saddam ya ke tsaye Yana kallon yadda Uwar tasa take motse fuska.

“Mami cikin ki Yana ciwo ne?

Saddam din ya jefa Mata tambayar yayin da Haj ta tafi Kiran likita.

Farida ta Bude idon ta tana kallon Saddam Wanda ta mikawa hannun ta Wanda yake sakale da Robar drift.

Cike da tsoron Robar ya Mika Mata nashi hannun Wanda aka nade da bandeji.

“Mami ina tsoron wannan abin na hannun ki Allura ce ? Akwai zafi?
Duka ya jera Mata tambayoyin…

Ganin hannun shi nade da bandeji yasa ta motsa tana Fadin

“Me ya samu Hannun ka Saddam?

Ya motse fuska Yana fadin

“Ba daddy bane ya taka min Hannu da takalmin sa Mai zafi ba.

Sai a Nan ta tuna lokacin da Sameer yake finciko ta a Nan Ta tuna da kukan da yaron ya kwalla.

Duk da nata ciwon da halin SHIGA UKU da take ciki sai taji tafi tausayin Halin da Saddam din yake ciki.

“Kayi hak’uri bari nayi maka ADDU A zai warke gobe ko jibi.

Wata irin murdawa da Cikin nata yayi shi ya katse Mata sauran maganar ta dafe cikin nata da karfi tana runtse ido kafin taji Wani Abu ya tsinke a cikin nata.

Haj da likitan suka shigo inda zufa ke fesowa Farida tuni likitan ya shiga Aikin shi da son ya samo bakin Zaren Amma Ina ! Kan kace me? Jini ya Soma bin kafafun ta kafin ta fidda tayin da ke kwance a marar ta.

Aka Yi Mata wankin ciki kafin aka fito da ita likitan Yana Mata Bayanin cikin nata ne ya fita sakamakon Wahala da tasha wacce take ko dai duka ko Kuma hatsarin mota Dole akwai daya Wanda shine Silar zubewar cikin Allah ya kiyaye Gaba.

Haj tayi shiru tana Zubawa Farida ido Dake baccin Wahala tana tunanin Abu Biyu tsakanin duka da hatsarin da ya faru da Farida. Maman Umar dai tace Mata taji kukan yaran ne tazo ta samu Farida a Haka. Gashi Kuma Sameer Bata sani ba ko Yana gari ko baya gari bare Taji Wani Abu daga gareshi. Taki Kiran sa ne don Kar ta tayar mishi da Hankali Farida ce kawai take son ji daga gareta.

Saddam Yana tsaye gaban gadon Farida Yana kifta idanu kuka yake son yi Amma ya kasa samun Dalilin kukan.

Dauda ya shigo Asibitin Yana Kiran wayar Haj ta fada mishi inda suke ya K’araso ya samu Haj ta Zuba Uban tagumi ga Kuma Farida ta fyade tayi Wani fari Alamar ta Zubar da jini.

Ya zube gaban Haj Yana gaishe ta ta Amsa tana tambayar yaushe ya iso? Yace yanzu yazo muntari Kuma yake sanar dashi suna Asibiti.

“Wallahi kuwa zuwa Babu shiri Nima Ina gida makociyar ta ta kira ni na taho afujajan.

“Me ya same ta ne Haj?

Ya fada Yana mikewa Yana kallon Farida Dake Kwance. Ya kama Hannun Saddam Yana fadin

“Shima Saddam din bashi da lafiya ne?

Saddam ya bare Baki Yana kuka Yana fadin

“Ba daddy na bane ya taka min Hannu da takalmin sa Mai zafi Kuma ya Doki Mami da belt din sa har tayi kuka.

Haj tabi bakin yaron da kallo tana son ta gaskata shi tana Kuma tsoron kama maganar yaro.

Yaya dauda ya sunkuya ya daidaita tsayin sa da na Saddam din Yana shafa kanshi Yana Fadin.

“Shi Daddyn naka ne ya taka Maka hannu Kuma ya Doki Mamin taka?

“Eh Mana shine har Yana ce mata zagi.

Yaya dauda ya juyo ya Dubi haj Yana Fadin

“Har yanzu gayen Nan Haj Bai Daina Halin sa bane?

“To bana zaton yaron Nan zaiyi karya dauda Amma Kuma akwai wauta a kama zancen sa.

Dauda ya Mike Yana zaro wayar shi ya Soma Kiran Sameer Wanda yake dab da shigowa Asibitin ya Kuma dauka Yana Fadin,”Yes Sir.

“Sameer meye Dalilin Zuwan Farida gadon Asibitin Nan? Da gaske ne Abinda Saddam ya fada mini?

In inar da ya kwaso ce tasa dauda ya katse wayar Yana huci inda likitan ya dawo da magunguna Yana. Duban dauda ya Kuma sake Rattaba mishi kiyaye tab’a lafiyar Farida wacce tayi b’arin cikin ta.

Dauda ya Soma duban Farida Yana numfarfashi inda a dole ya yarda da maganar Saddam ta Cewa dukan ta Sameer yayi hat tayi b’arin cikin.

Farida ta Bude idon ta daidai da shigowar Sameer Wanda yayi bala in Shan jinin jikin shi.

Ya zube gaban Haj wacce Bata nuna mishi komai ba ta karbe shi Suka Gaisa inda dauda yake kallon shi da wata irin fusata Mai Jin tamkar ya Saka bindiga ya dauke.

Ya gama gaishe da Haj kanshi a k’asa ya kasa tashi bare ya motsa. Yayin da dauda ya kasa kunnuwa yaji Abinda zaice da Haj. Ita Kam almunya Bata iya ce mishi uffan ba sukayi shiru su Duka tamkar Babu kowa a wurin hatta da Saddam da yake Kallon Daddyn nashi Bai iya matsowa inda yake ba.

Haj ta Gaji da Shirun ta dubi Saddam tana fadin.

“Baka ga Uban ka ba ne Saddam? Yaron ya Kuma bare Baki Yana Fadin.

“Ni ban son Daddy yanzu tunda ya doki Mami da belt ya taka min Hannu da takalmin sa Mai zafi ban son shi ban zuwa wurin shi.

Wata irin kunya ta lullube Sameer yaji tamkar ya nutse in ma ba a San Abinda yayi ba Saddam ya fasa mishi Aiki.

Wurin ya Kuma daukar shiru yayin da Farida take ballawa Saddam din harara don Bata so yaron ya Fadi Abinda ya fada ba don Bata son Yaya dauda ya San wannan Al Amarin don shi ba afuwa bare sassauci a Lamarin sa komai sai ya nuna son iyawa da iko da kasaita.

“Haj ayi min Afuwa Dukkan Abinda ya faru kuskure ne ban so Hakan ba don Allah ayi Hak’uri. Cewar Sameer Wanda yayi maganar kanshi Yana k’asa.

Haj ta sauke AJIYAR ZUCIYA tana fadin. “Kai Babu komai Sameer Allah ya kyauta na Gaba.

Yaya dauda ya Mike Yana Fadin. “Haj bari na Kira likitan Nan ya Bata sallama sai na wuce da ita can Kaduna na sauya Mata Asibiti.

Haj ta Dube shi don ta San Akwai magana a bakin shi Amma Kuma sai tace.

“Kamar Yaya ka wuce da ita Kaduna? Nan ma in ka barta ai zata samu Sauki ko.

“Kiyi Hak’uri Haj Kaduna zata koma can tayi jinyar kafin naga yadda jikin nata zai zama.

Ya fice Bai tsaya jiran cewar Haj ba inda zufa ta Soma karyowa Sameer don ya Gane nufin dauda Amma Kuma Haj ce kadai yake da tabbas akan ta na takawa daudan burki. Amma Kuma idon shi da kunya tunda har Saddam ya bare mishi Aiki me zai iya Cewa.

“Farida ta dubi Haj tana fadin.

“Nifa Haj ba wata Kaduna da zanje tunda naji sauki a sallame ni na koma gida na.

Shigowar dauda da likitan ne yasa tayi shiru inda Haj ta ke fad’in.

“To Kai kaji fa Bata son Zuwa Kaduna ka kyale ta ta koma gidan mijin ta tunda ya bayar da hakuri Kuma waye baya kuskure a Rayuwa?

Dauda ya watsawa Farida Wani matsiyacin kallo yace

“To ni ta fada min da Bakin ta Haj tunda ta zama Dabba stupid in ta Isa marar mutunci….

“To shi mijin ta Kuma da yawun shi zakayi Hakan ? Ai banji ka tuntube shi da maganar ba.

“Haj Dubi yarinyar Nan a Hakan ta. Anya kuwa Saddam zai Fadi wannan maganar ko da Yana karys zai iya shirya irin wannan? Ga hannun shi nade da bandeji yace Uban sa ne ya taka shi Kuma yace ya daki Uwar sa da belt dukkan Abinda ya fada ya tabbata to bance Farida ta koma Kaduna da zama ba Amma a nemi lafiyar ta kafin ya sake sabon dukan ko zata koma ai ta warke daga wannan Halin dubi jikin ta fa?

Jikin Haj yayi sanyi Bata Kuma cewa uffan ba yayin da Sameer ya Soma bawa Yaya dauda hak’uri Amma Bai ko nuna ya san da zaman mutum a wurin ba . Haka itama Farida Mai cewa ba zata je kaduna ba Bata sake ko tari ba har Yaya dauda ya karbi takardar sallama ya Dube ta Yana Fadin zata iya tashi ko sai an kamata?

Bata tanka shi ba tana daure fuska ta Mike duk da iska na Neman daukar ta don jinta take sawat Babu nauyi Amma a haka ta Mike yayin da Sameer ya kamata ta kuwa kwanta a jikin shi har motar Yaya dauda inda Haj ta Saka mishi su Hanan da Saddam ….

“Haj a baiwa Uban su su in taji sauki ta dawo Amma tana a wannan Halin zata tafi da Yara ? A baiwa Uban su su.

“Kai bana son tashin hankali in shi Saddam ya yarda ita wannan kana ga zata yarda ne?

A guje Saddam ya shige motar Yana fadin. “Ni ba zan bi Daddy ba wurin Mami zanje tunda Yana taka min Hannu ya Kuma Doki Mami ba zanje wurin shi ba. Tamkar Farida ta buge bakin Saddam don Bata tab’a Jin surutun shi ya dame ta irin yau ba. Dole Haj ta Saka mishi Hanan a motar tana fadin sati Daya tak da taji sauki ka maido ta Gida kaji na fada maka.

Sameer Kam Yana kallo Yaya dauda yaja motar a guje ya fice daga Asibitin Haj ta juyo tana bashi hak’uri tace yayi Hak’uri yayi yake wai Dariya yayi ya Budewa Haj motar ta shiga ya mayar da ita Gida ya wuce Yana hango Abinda dauda yake nufi da dauke Farida ya mayar ta kaduna har Yana fadin a bashi Ya’yan shi ya tafi dasu. Abinda ba zai taba yarda ba kenan yace zai Raba su.

Ya dawo gida Al Amarin yayi mishi zafi gashi mutum ne da Allah ya zabawa son a kula dashi bare Farida da ya tabbatar itace Duniyar sa gashi an dauke ta Bai Kuma San Ranar dawowa da ita ba. Da ya tuna Hajiyar shi na can tana jinyar bello akan Abinda muguwar zuciyar shi ta ingixa shi yayi sai yaji ya tsani kanshi ya tsani Abinda yayi.

Ya Mike Yana fita don ya Gane in ya bar Haj da jinyar bello to ya Kuma Wani Rashin Hankalin.
Ya iso Asibitin inda ya samu salmanu Abokin bellon Wanda shine ya zo yace da Haj ta koma gida ta huta jinyar namiji sai namiji Dole haj ta yarda ta bar Salmanu ta koma Gida.

Yaji Dadi da ya samu jikin bellon yayi sauki Sosai don haka ya wuce gida wurin Hajiyar su inda ya Kuma Bata hak’uri tace ai shi za a bawa hakuri Amma Kuma motar da ya tankada din ta Salmanu ce Kuma anyi kushi ta adi Mai yawa don haka sai ya biya Salmanu motar shi . Dole ya yarda da biyan motar Salmanu inda Haj Kuma tace gobe ma ya Kuma Abinda yayi Wanda in bai bi a Hankali ba to zai jawowa kanshi JANHURUN masifa ne matukar dai yace zargi da muguwar zuciyar shi tana Nan a yadda take to zai tabbata a cikin nadama.

Kwanaki UKU kacal ga tafiyar Farida ya shiga kunci da takura matuka Gaya yayin da wayar ta ma tana gida Babu wayar da zai Kira ta ya same ta in ba ta dauda ba. Yaushe Kuma zaiyi Hakan ?

Bai Kara Gane muhimancin Farida a tare da shi ba sai da tayi Kwanaki bakwai ba tare da yaga zuwan ta ba duk kuwa da Cewa k’uda ne baka Haram akwai Leke Leke Amma dukkan wacce zai tab’o Bata Kai mishi matar tashi Farida Al Amarin da ya kaishi tsaka Mai wuyar fita .

Ya Soma Kiran lambar wayar wasila da ya karba don yanzu Kam Yana son Rage zafi da wasilar Amma Kuma wayar tata a Rufe don haka ya Mike ya nufi inda zai samo Labarin wasila koma ya samo ganin ta su yaho gidan nashi ayi Bak’ar kasuwar da a wannan Zamanin itace ke tsaka da ci da Kuma tashe . Keta iyakokin Ubangiji ko? Kutsa a gari ka Gano yadda Al Umma suka Zamo Al Amarin da yake zama TANA K’ASA TANA DABO ne don Dukkan Sharrin da mutum zai aika to Yana Nan dawowa gareshi Allah ta ALA ka Amintar damu ka Hana shaidan shiga cikin ayyukan mu da zukatan mu..

<< Tana Kasa Tana Dabo 1Tana Kasa Tana Dabo 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×