Tudun fulani Wani k’aramin kauye ne a Cikin k’aramar Hukumar b’atagarawa. A Nan Wani malami Mai suna malam zulk’e yake da zama wanda Aikin Nashi ba na malamta bane an dai fake ne da malamta Amma boka boka Dan tsubbu tsubbu haka yake Aikin Nashi Kuma abin Mamaki zakayi mamaki idan kaga yadda Mata suke sunturi wurin shi musamman Wanda Suka siyar da Imanin su wa wulakantacciyar Riba Kuma abin haushi da takaici shine wai saboda kishiya suke wannan sunturin .
Kuma kowace da irin Abinda take so ayiwa kishiyar daga Kan wacce ta shigo ta iske ta da wacce ke Shirin shigowa . Wata ma Bata Kai ga shiga gidan mijin ba bare taga kamun ludayin kishiyar Amma tun a waje tana Neman yadda za ayi ta salwanta ta . Idan Mai Hankali ya Dubi yadda Mata ke sunturi a wurin malamin Wanda yafi kyau a Kira shi da boka Kai tsaye zai tuna fad’ar manzon Allah S A W da yaje isra I ya dawo Yana bamu labarin ya leka wutar jahannama ya Gano Mafi yawan Yan wuta Mata ne . Ta Nan zaka hada UKU da Biyar su baka takwas idan kaga yadda Mata kewa mutumin can zarya Kuma Babu wacce ke zuwa da sunan Neman taimakon su zauna lafiya ita da kishiyar ta sai dai yadda za a halaka kishiyar koma yadda za a mallake mijin sai yadda akayi da shi..
Basma ta faka motar ta a gefen gidan malam zulk’e ta fito Zuwa cikin gidan
Ya Dube ta Yana kallon ta tamkar Yana kallo yan hanjin ta da kwanyar kanta..
“Malam matar Nan tayi ciki jiya kwana Nayi Ina zarya kitchen Ina faman dorawa da saukew har nayi kaicon Rashin karbar maganin da zan Zuba Mata a abinci Amma yanzu Kuma malam ba maganin tsanar juna nake so ba na Wanda cikin can zai zube nake so don in ta fara haihuwa SHIGA UKU ta same ni..
Yayi murmushi Yana Fadin
“Kar kiyi garaje gara dai kiyi Wanda na Baki don in Suka tsani juna har Ya’yan nasu abin zai shafa . Amma in aka zubar da cikin ai suna iya samun Wani..
“Ba zata same shi ba malam don wannan ma Ina kokonto akan sa ..
“To yanzu dai kinfi bukatar a zubar da cikin kenan?.
“Eh haka nake so Malam Kuma idan Akwai maganin da zan Bata a cikin Abincin Wanda zataji ta tsane shi a bani kaga idan cikkn ya zube Kuma taji ta tsane shi Dole su Rabu tunda ba gware suke wurin zuwa Duniya ba ..
Ya kulla maganin ya Bata har guda Biyu ya Kuma ce tayi na Hayakin da ya bata dayan Kuma ta zuba a Ruwan shayi ko lemu ta Bata in Tasha ko awa ba za a Rufe ba cikin zai fice har da mahaifar
Kwanan da Farida tayi tana Amai shiyasa me Gemu yayi musu Shirin tafiya.
Kafin karfe Sha Daya na safe ya gama komai duk da yaso Basma ta Dawo kafin su tafi Amma karfe Sha Biyun Rana Zasu Daga zuwa lass Vergarn na k’asar amurka a Asibitin Nan Mai shahara a Duniya don duba mishi Farida
Dole sai dai Kiran wayar Basma yayi ya fada Mata sun wuce lass Vergarn kome kenan suyi magana.
Tana tafe a mota tana shirin dawowa ya Kira ta don haka taji gwiwar ta tayi Sanyi tana Nan tana fafutukar Neman yadda za ayi su Rabu shi Kuma Yana can Yana Neman yadda zai tura Mata Bak’in ciki..
Wasa wasa sai da sukayi wata Biyu a lass Vergarn duk da sunan Rainon ciki kafin suka Dawo Nigeria Farida kam tayi Wani irin fresh fatar ta ta wankan tarwada ta zama so fresh tana glowing ga Kuma Cikin ta da ya tura Riga yayi Mata kyau matuka Gaya..
Basma kam cike take da dakon Zuwan su duk da ta so ta Yi wulakanci Mai kalar Ruwan Omo Amma sai ta tuna makaman da ta mallaka.
Ta Shaka Sosai da taga irin kudin da yake kashewa Farida duk akan Cikin ta..
Ta iso sashin na Farida tana yak’e tana Fadin
“Kai Sannu Amarya wannan baby Kam ya Wahalar da ke da yawa Allah ya Kara lafiya ya Raba lafiya.
Farida ta Dube ta tana Amsawa don tun Ranar da Basma tazo Mata tsegumin Nan ta fice mata a Rai duk da Dama can ba wani yin ta take ba . Kuma a yanzun ta Gane Akwai Wani Abu a k’asan ZUCIYAR Basma shiyasa ma ta Daura aniyar gaisuwa ce kawai Abinda zai hada su Amma bayan Hakan kowa yayi harkar sa.
Irin karbar da taga Farida tayi Mata ne a shek’e yasa ta Mike tana Fadin..
“Allah ya Kara lafiya Amarya idan kina bukatar Wani Abu na girki kiyi min Magana..
Farida Bata tanka Mata ba har ta fice
Da Rana Basma ta yanke shawarar ba sai ta Aiko ta ce tana son Abu kaza ba Kawai tayi Wani Abu irin na kwalam Wanda ta tabbatar Farida zata so sai ta zuba maganin ta Mika Mata kawai
“Haka kuwa ta Shirya miyar ughu Wanda taji bisasshen kifi ta Kuma hada shayin citta da Karanfani Wanda ta zuba maganin malam zulk’e itama miyar ughu din sai da ta ambama Mata magani ta kwasa ta nufi sashin Farida tana Fadin..
“Amarya ga Dan makulashen da nayi na kawo Miki na San zaiyi Miki Dadi..
Farida ta Dube ta ta karba tana fadin
“Na kuwa Gode Sosai Amma maman Najwa ki bar Wahalar da kanki Domin kuwa yanzu ba komai ma nake ci ba wani Lokacin ma hollandia nake Sha Kuma Ina jimawa ban ci komai ba idan Ina bukata zan girka tunda yanzu na samu Sauki Sosai..
Ta karba tana mata wannan Bayanin..
“Kai yo meye don nayi Miki girki? Ai lalura ce Kuma irin wannan lalurar yau gareka ne Gobe ga dan Uwa Nima in tawa ta same ni ai nasan Zaki Yi min..
Suka sallama Basma ta wuce tana fatan in bata Sha miyar ba to ta Sha shayin Amma Haka Nan Taji Dukkan abubuwan Basu kwanta Mata ba don Haka ta Zubar da su ta wanke kayan ta ajiye Mata don ko sashin nata Bata son Zuwa
Haka Basma tayi ta dakon taji ance ga Abinda ya samu Farida Amma shiru har kwana biyu Kuma bataji Farida ko shi me Gemun yazo yace tayiwa Farida girki ba . Sai ta koma kan Hayakin ta Wanda take ta gumbudawa kullum dare da safiya Wanda har sashin Farida take kawo Mata Amma shiru wai an Aiki bawa garin su ..
Wata Biyu da Mika Aisha gidan Sameer Amma har wannan lokacin Babu shi Babu labarin shi don haka Haj da kanta tacewa Bello ya shirya karshen watan Nan idan Sameer Bai zo ba zai Raka ta har can pertercout din ta Kai Mishi Aisha..
Sameer Kam Yana can ya gigice akan Rashin samun wayar Farida wacce ya tabbatar da gaskiyar Abinda ta fada shiyasa ma ta kashe wayar ta don ma kar ya neme ta. Yana son Zuwa katsina don yaga Farida Amma Yana tsoron iske Aisha a matsayin matar sa Dole tasa ya kwashe wannan Lokacin Bai zo ba Amma Kuma ya kasa zama lafiya don bai san halin da Farida take ciki ba .
Aisha ta Soma Kiran wayar shi kiran da yayi matukar Bashi haushi tun Yana sharewa har ya Gane sai ya dauke ko zata saurara mishi
Ai kuwa ya dauka Yana balbale ta da masifa akan Kiran da tayi Mishi.
Ta Saka mishi kuka tana Fadin
“To ni wai me nayi maka ne da zafi haka har kake k’in zuwa saboda ni? ..
Ya tsinke wayar ya barta da kukan ta don da gaske kuka Yana tayar mishi da Hankali musamman kukan mace . Macen ma Farida..
Wannan wulakancin da yayiwa Aisha ne ita Kuma ta fadawa Haj har tace zata kulle Aisha ta bishi da ita can pertercout din in yaso ya huta Gudun ta
Blessing itace yarinyar Da ta mutu akan Sameer tun Ranar da ya dauko ta ya Kwana da ita ta tafi da tuntube da son shi ta Kuma kasa zama lafiya.
Don haka a yau tayi wanka na daukar hankali ta iso gidan nashi ta Kuma Yi sa ar samun shi
Ya bude Mata kofar Yana kallon ta inda ta fada a jikin shi tana Rungume shi Shima ya Rungume ta don da gaske yaji Wani Abu akan ta Amma ba wau so ba. Wani Abun ma da yaji don ya jima Bai nemi wata mace ba don Haka sai Blessing ta zama Ruwan kashe gobara.
Ya Kara siye ZUCIYAR blessing da kyakkyawar soyayyar shi da kulawa wacce ta Saka ta Jin zata iya sadaukarwa a gareshi.
Tun daga wannan Rana blessing take Jan zaren ta wurin Sameer irin zaren Nan na ba yabo ba fallasa. Yana Mata Hidima da kudi ya Kuma kula ta a shimfidar sa duk da ba wani Abun kirki yake tsinta ba don ma abin ya zama tamkar ibada
A yau Kam da suke karshen mako a Nan blessing tayi week End din ta tun Ranar Friday take sai Monday zata koma Gida.
Tana kitchen tana Aikin girka mishi Abinci Wanda blessing ta Soma daukar hankalin Sameer da girkin ta Mai daukar hankali ta Kuma Yi sa ar samun shi
A Ranar Lahadi Haj da bello tare da Aisha suka dauki hanyar pertercout don Mika Aisha ga Sameer.
Tafiya yankin azaba sai dab da magaruba suka Isa pertercout gidan Sameer a cikin barikin SOJA na garin pertercout inda Sukayi nocking din kofar suna tsaye a bakin kofar ga gadari ya gamgamo ana ta sakin walkiya har da kananun yayyafi .
Blessing Da take Zaune a falon tana kallon Wani film nasu na ibgo saboda fitar da Sameer yayi zai siyo Kayan bukata da Basu da shi a gidan don ya jima Bsi fita siyen abinci ba tunda blessing ta zo mishi weekend Shiyasa ba ya Jin Wahalar siyen komai..
Jin ana buga kofar yasa ta ki motsawa don ta San dai Sameer Yana da key din gidan in shine Budewa kawai zaiyi ya shiga ita Kuma sai tayi banza da Mai buga kofar tayi ta kallon ta..
“Ko dai ba gidan bane Bello?.
Haj ta tambaye Bello..
“Nan ne Haj ai kowane da Lambar sa da sunan Mai shi duba kiga ga sunan shi Nan.
Haj ta Daga kanta ita da Aisha suka ga sunan shi Rad’au..
Ya Kuma doka kofar da k’arfi Amma blessing tayi kunnen Uwar shegu sai ma tsaki da taja..
Ruwan sama ya Soma Saukowa gashi Babu wurin fakewa a jerin gidajen sai dai ka lafe a bango..
Ruwa Mai karfi ya yi sallama kamar da Bakin kwarya ya Soma sauka a jikin su Yana jika su .
Jin dukan yayi yawa ne yasa blessing ta leko taga su Bello Wanda kamar shi da Sameer Bata boyu ba ta tabbatar brother sa ne Amma sai taja tsaki ta koma don matan da ta Gani taji Wani Abu na son Jin me Kuma suka zo Yi? Abinda ya Bata HAUSHI shine ta San zuwan su zai Rage Mata Jin Dadi da Sameer din tunda su hausawa sun cika Fi ili da yawa..
Ta koma abinta ta zauna taci Gaba da Kallon ta..
Sameer da saukar Ruwan ya maido shi gida tun daga nesa yake hango mutane a kofar gidan nashi..
Ya Tako motar a guje ya K’araso sai kawai yayi Arba da mahaifiyar sa Ruwa na dukan ta ta jik’e sharkaf ga Kuma Bello Shima suna ta Shan dukan Ruwa. Sai Kuma Aisha wacce take ta kyarmar Sanyi..
Wani Abu ya daki ZUCIYAR sa da ya tuna Dalilin Zuwan su da Kuma Blessing Da take cikin Gidan ya Kuma tabbatar da taji dukan kofar Amma don tsohon wulakanci ta bar mishi mahaifiyar shi da Dan uwan shi suna Shan dukan Ruwa..
Ya fito motar da sauri murya na kyarma yake Fadin.
“Haj kece a garin Nan?
Bata tanka mishi ba ya zura key Yana Budewa kofar ya yi Maza ya cire Rigar ledar Yana Rufawa Haj suka shiga ciki Yana faman Yi musu sannu da Zuwa.
Gaban shi yayi wata matsiyaciyar sarawa saboda Blessing. Shin idan Haj ko Bello suka ganta suka Kuma tambaye shi wace ce ya ce musu me?.sai yayi fatan ace blessing din Bata a falon tana can D’akin a kwance ko Kuma tana toilet.