Da Wani matsiyacin lugude a kirji Sameer yake nufar falon Haj da Bello da Aisha suna biye a bayan shi har ya tura kofar falon ya shiga Yana baza idanu da son ya hango Blessing sai Kuma Bai ga kowa ba a falon wata Kil dai ADDU AR shi ce Allah ya karba mishi.
Ya Sauke AJIYAR ZUCIYA Yana Fadin, “Haj muje ga D’aki ki cire kayan jikin ki.
Haj ta juyo tana Duban Aisha tana Fadin
“Taho muje ki cire kayan jikin ki Aisha kar sanyi ya kamaki.
Suna Shirin wucewa Zuwa kofar da ke da D’akin saukar Bak’i sai kawai ga Blessing ta fito da kayan Abincin da ta shiryo Dama k’arar motar Sameer da taji ne yasa ta nufi kitchen dauko Abincin.
Wani irin matsiyacin Jiri da yake Neman kayar da shi ganin Haj da Bello suna kallon Blessing wacce itama tayi turus tana kallon su cike da shakka da tsoro.
“Wacece wannan?
Cewar Haj wacce ta nuna Blessing da Hannu Baki Yana kyarma.
“No wonder Abinda ya Hana ka zuwa gida dama kenan? Ni na San karya kake ka Rungume hannuwa Baki alaikum in baka nemi Mata ba kuwa kayi me? .
Bakin shi ya Soma kokarin magana Amma ya kasa cewa komai inda Aisha Kuma take Raba musu kallo.
“Ka Gani ko Bello? Kaga Abinda yake aikatawa shiyasa ya barni da Yar baiwar Allah yarinyar Nan tsayin watanni UKU? Ka Gani ko?.
Haj ta fad’a a Rude kafin ta fashe da kuka tana Fadin.
“Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un.
Sameer ya Kasa motsawa inda blessing ta aje kayan Abincin da take Rik’e da su ta sulale ta bar Gidan don duk da Bata Jin Hausa Sosai ta fahimci Abinda Ake magana Akai .
Haj ta juya tana Duban bello tana Fadin
“Muje Bello mu Nemi Tasha ce mu kwana kafin safe mu juya gida tunda Kuma munzo Allah ya bankada Mini Asirin shi ai shikenan in yaso in ya ga Damar zuwa sai ya kawowa mana takardar sakin Auren Aisha.
Sameer yayi k’arfin Halin motsawa yana fad’in
“Tasha Haj? Don Allah kuyi Hak’uri.
“Inyi Hak’uri in Zauna mazauni Daya da Kai kana aikata wannan alfashar? Allah ya sauwake mini Sameer na kwana gidan ka.
“Wannan matar Haj haya fa take ba nine na kawo ta ba.
“Eh ai Da yake Bani da Hankali gara ka Nemi maida ni k’aramar yarinya. In ma kace tsuntsuwa ce ai daidai da Kaine.
Aisha dai ta kasa cewa komai sai Bak’in ciki take ji a zuciyar ta na Ganin wannan takaicin.
“Kai Bello muje na gaji da Magana in Kuma kana Nan ne ni na tafi.
Sameer yayi maza ya Rik’e hijabin Haj Wanda yake digar Ruwa.
“Haj shaidar Zina fa tana da Nauyi ban zaci wannan shaidar daga gareki ba har ki kasa fahimta ta. Baki ga ta tafi ba? A Nan gidan take su ba wani Abu bane don sun yiwa mijin wata girki ko da Kuwa Yana da Mata ne su ba irin Rayuwat mu suke ba. Da ni na kawo ta ai ba zata tafi ba sai na sallame ta Amma tunda ta ga Abinda yake faruwa.
“Kai kar kayi zaton zaka iya yaudara ta . Kai din ne ban sani ba? Ko da yake kana zaton ban San Rayuwar da kake ba ko? To kar ka fusata ni Wallahi Allah yasa had’akar Auren ta kukayi Amma ni Yar iska na Gani a gidan ka Kuma Kai ka Kawo ta.
Ta fincike hijabin ta zata wuce tana Duban Aisha tana Fadin
“Wuce muje nayi nadamar gabatar da na nuna akan Asiya har ta yarda ta bani Auren da nake zaton na Isa Ashe ban Isa ba .
Bello ya Rik’e Hannun Haj Yana Fadin
“Haj kar ku munana zato tunda yarinyar Nan ko a shaidar Zina muka zo a mu uku sai an Nemo cikon na Hudu Kuma ba mu ga Wani Abu da ya nuna Yana Neman ta ba don Haka kiyi mishi uzuri Ina Mai tabbatar Miki da idan har Aikin sa ne Wallahi sai Allah ya bankada Miki Asirin sa.
“Banda Wanda Allah ya bankada Mini yanzu? Kana son Cewa Kai ka yarda da Abinda ya fada? Arniya a block din sa Amma ya mayar Dani yarinya k’arama yana fadin haya take? Ina ce shi kadai ne a gidan in ma hayar take Akwai wata bak’ar kasuwa a tsakanin su Kuma shi ne Wanda ya gayyato ta?.
“Yanzu Haj idan muka koma gida da yarinyar Nan ai Kuma kunya kawai zamu Sha Wanda Bai san Abinda akayi ba ma in Magana ta fito Kinga sai kowa ya Sani.
Haj ta Yi Shiru tana sauraren Bello har ya dire zancen shi Sameer kuwa ya Dora da tsara ta da karya da makirci har ya shawo kanta ta shiga D’akin ta sauya kayan ta Amma Bata yarda taci Abincin da blessing ta girka ba Dole ya fita restaurant ya Nemo musu abinci.
Da ke a Gajiye suke salla sukayi sukaci Abincin suka kwanta sai bacci.
Washe gari Haj ta Soma Shirin komawa tana cewa bello ya shirya su juya dama kawo Aisha sukayi Gata Nan Kuma in yaso ya yi Mata duk Abinda ya ga Dama zai zo ne ya same ta Kuma Dukkan Abinda Aisha ta Gani Wanda baiyi mata ba ta Kira ta ta fada Mata.
Da kyar ya samu ya Rarrashi Haj ta k’ara kwana zuwa jibi sai su wuce Don zaman motar ma Aiki ne.
A Ranar da su Haj zasu wuce Aisha taji kamar tabi su su koma don tuni taji ta tsani Sameer da irin Rayuwar da ta tabbatar Yana Yi don ita din ta San shi ya San ta .
A haka ya cika Haj da Bello da kayan tsaraba suka wuce su ka bar Aisha cike da damuwa. Inda tashi damuwar ta zarce tata don yadda yaga Haj ta fusata idan yace zaiyiwa Aisha Wani wulakanci Ranshi ne zai Baci ko da Kuwa Ran nashi ya Kai guda Dubu
Tunda Aisha tazo ya sallami blessing wacce ta nace ta kasa yarda ta Rabu da shi
Iyakar shi da Aisha tayi girki yaci Amma maganar ya Dubi d’akin ta baiji Hakan a Ranshi ba don ya San Aishar tun kafin ma tayi Aure bare yanzu da yake cikin Wani garnakakin.
Dukkan Aiken da Basma take yiwa Farida har yanzu Shiru take ji. Ga shi Kuma duk Bayan wata Biyu suka Zuwa duba Cikin a lass Vergarn Abinda yake Kona Mata Rai kenan
Ta Kira lawisa tana fada Mata Halin da Ake ciki da Kuma irin Rawar jikin da Abdullahi yakeyi.
“Ki Rabu da su Basma ke dai kiyi Abinda malamin nan ya fada Miki kin San fa ba tashi Daya magani yake ci ba sai a Sannu a Hankali.
Sun dawo daga lass Vergarn ne a Zuwa na uku da sukayi don yanzu cikin Farida Yana cikin watan Haihuwa inda Kuma ta matsu da son Ganin Saddam da Hanan ta fada mishi ya kuwa je ya kwaso Mata yaran ya zube Mata su tana kallon su da wayon da suka Kara .
Saddam Yana kwance jikin Farida tana shafa Sumar kanshi tana Fadin
“Saddam Ina kuka baro Haj?.
Ya tashi zaune Yana Fadin
“Tana gida Mami meye a cikin ki Nan?
Ya fada Yana tab’a cikin ta da yaga yayi girma.
“Kanin ka ne Saddam ai Zaka so baby boy ko?
Yaran sun debe Mata kewa matuka Gaya.
Kwanan su UKU tace a mayar da su Amma Abdullahi yace ba yanzu ba
Haka kuwa aka bar Mata yaran har sai da Haj tace a maido su saboda makaranta.
Ranar wata asabar Farida ta tashi da nakuda bayan fitar Abdullahi Wanda a kullum idan zai fita tunda ta shiga watan Haihuwa yake cewa da taji ba daidai ba ta Kira shi don ance satin da zai kama zata shiga Lokacin haihuwa Wanda ya Shirya musu tafiya Can lass Vergarn don ta Haihu sai ga haihuwa a Ranar asabar
Kafin ma ta Kira shi Allah ya kawo Mata Mai sauki ta haihu lafiya da katon yaron ta Wanda tana kallon shi taga Saddam sak sai farar fata irin ta uban sa haka ma gashin yaron irin na abdullahi be amma kama yake da Saddam Babu ko canjin kamanni . Saddam Kam yana kama da ita ta wata fiskar amma a tssye tantama da ka ganshi kaga Uban sa Sameer.
Tayi kokarin kimtsa Kanta ta kuma kira abdullahi Wanda ya ajiye tarin aikin dake gaban shi ya nufo gida aguje
Kan kace me? Abdullahi ya dawo gida Yana Rungume da yaron Wanda yake ta Sumbata Yana murna har yayi mishi huduba da sunan salmanun farisi .
Ya rungume farida yana bata kyakkyawar Sumba yana Fadin .
Baki kyauta min ba farida kikayi nakudar ki ke daya ba tare da na rarrashe ki na fada miki kalamai masu dadi ba .
Allah ya Raba mu lfy derlin ai bana son na tayar maka da hankali ne.
Muje asibiti ko da wata mstsala su duba min ke don nan da Dan lokaci fa zamu mayar da mahaifa ki sama min wani boy ko baby girls farida auren ki ya zame min alheri ta ko ina ya Raba ni da wata rayuwa ya kuma sakani a wata sabuwar rayuwa ya Kama bani baby boy Wanda nake ta fadawa Allah ya bani gsshi kuma ya bani salman sauran Suleiman farida in sha Allah shima yana tafe ai ni kam nayiwa mijin ki addu a sau fin Dubu Dari da ashirin da ya sake ki har na samu auren ki da dykkan alherin da auren ki ya Samar min .
Tayi murmushi tana rungume da shi tana fadin.
Nice nagode mishi da ya sake ni derlin har Nazo gareka ina son na tabbatar. Maka da INA son ka INA kaunar ka.
Ya hade bakin su yana kissing yana rungume da yaron suka nufi asibiti aka duba ta lafiya lau sai magunguna da aka bata tare da cewa ta nemi lomon coca cola tasha saboda ciwon ciki.
Basma ta dafe kirji tana Shirin faduwa kasa ta Suma Jin wai Farida ta Haihu Kuma Namiji.
Haka taja kafa ta Isa sashin Farida tana ganin jariri wanda jar fstar shi take irin ta Uban sa tayi Mata barka ta juyo tana ganin jiri da fadawa tashin hsnkali.
Haka Abdullahi yayi ta Hidima tamkar Bai San ciwon kudi ba har Akayi suna yaro ya amsa sunan salmanun farisi Amma suna Kiran shi da Salman ko suce farisi
Hajiyar Sameer tazo taga jariri Wanda take ta kambama kamar shi da Saddam tana ta Fadin
“Ikon Allah Rabon wannan ne ya Raba Auren Farida da Sameer.
Basma Kam tana hadiyar Bak’in ciki Domin kuwa ko Ranar Aikin ta ne haka Abdullahi zai shigo mata Rungume da Salman yazo Kuma ya yi ta yiwa Najwa da Nabeela bita Yana Dora musu yaron suna dauka Yana fadin
“Dan Uwan ku ne Nabeela ku so shi ku tausaya mishi kuyi zumunci ku so juna kunji ko? Yaran su amsa mishi da to Daddy
Haka Kuma idan ya tafi maida Salman din zai share Lokaci Bai dawo ba wani Lokacin ma sai tayi bacci zai Dawo duk Yana can wurin yaron wai baya son Rabuwa da shi sai yayi bacci ne zai shigo mata in kuwa a sashin Farida yake to kwana yake da yaron a kirjin shi Yana faman tarairaya
Tuni Farida ta Daina daukar Kiran wayar Sameer in zai shekara Kiran ta ba zata dauka ba don tace ta gama da shi tun Yana nacin Kiran har ya Hak’ura da kiran ta sai dai in ta Saka status Yana Gani ko yayi mata magana a WhatsApp din ma bata maido mishi Amsa.
A wannan lokacin ne Kuma yaga ta Dora hoton Salman Wanda yake cikin wata na biyu yayi girma yayi wayo kamar shi da Saddam sai Kara fitowa take.
Yana ganin fuskar yaron ya danna status din Nata yaga yaron da kyau Wanda yake sak da Saddam.
Yayi Maza yayi save din hoton ya koma Yana Kiran ta don zuciyar shi na fada mishi farida haihuwa tayi?.
Ya Kira ta Yafi a kirga Amma Bata dauka ba don dama Abinda ya ke Hana ta Dora hoton Salman kenan ta San In ta Dora sai ya gani koma yace zai tambaye ta . Don haka wannan Kiran ma ta San akan Salman ne tunda taga ya Duba hoton .
Yayi ta jera Mata Kira Amma ta watsar da shi Bata dauka ba .
Ya gaji ya kyale ta sai Kuma ya kira Haj tana dauka ya soma gaishe ta Yana Fadin
“Wai Haj Farida ta Haihu ne Naga ta Dora Wani yaro Mai kama da Saddam?.
“Eh Sameer ai ta Kwan Biyu ma da Haihuwar Nan don wannan yaron a kwana Saba in kadan ya Rage. Yaro fa Masha Allah Salman kenan ance Rabo in Bai kashe ba yayi da sauki kaga wannan dai Bai kishe ba sai dai Rabuwa Yaya matar ka tana lafiya?.
“Lafiya Lau take.
Ya Amsa tamkar zai fasawa Haj kuka Yana Mata sallama ko su Saddam Bai tambaya ba ya katse wayar ya bar Haj da tsegumi tana Fadin.
“Ni wannan bin bini ya ishe ni haka . Sai kace dai masu Auren zobe? Kowa ya kama Abokin Rayuwar sa Amma Baku Hak’ura da kishin Aure ba? Haba wannan fitinar ta Isa haka Wallahi.
Ya wuni Kiran wayar Farida Amma Taki dauka Dole ya Nemo Wani layin ya gwada Kiran ta ta Kuma dauka ba tare da ta San shine ba.
“Don ki nuna min kinci Amana ta shine kika yarda shegen mutumin Nan yayi Miki ciki Farida? Shine har shegen danki yayi kama da Saddam don ki nuna min kin Yi nufin wulakanta ni ? To Wallahi tallahi sai na Rama wannan wulakancin da kukayi min ba haihuwar ki ce damuwa ta ba yadda kika saki jiki da mutumin Nan har yayi Miki ciki Wallahi tallahi ki Yi gaggawar kashe wannan Auren kafin karshen wata na Rantse Miki da Allah idan na Nazo garin katsina sai na kashe Mijin ki don na Gane Hakan kawai zanyi na kashe shi kiyi takaba na dawo da ke Hannu na tinda nayi Miki kawaici da alkunya duk Baki kula ba har kika bari ya kwanta ki yayi Miki ciki wannan abun ya kusa k’arar min da numfashi Wallahi .
“Kai a WA kake min wannan maganar? Idan Uba na ne kai ka tsine min sau yawan Haihuwar da kayi min. Kai bari fa na Gaya Maka in kace ciki na da Haihuwa ta ne damuwar ka kana Dab da mutuwa Wallahi don ni sai yanzu ma na Gane Kai Babu abinda ka iya a mu amalar Aure sai zargi Amma mace taji Dadi a Aure ni Kam Abdullahi ya bude min ido soyayya kawai Yana iya aje Aikin shi don ya nuna min ita Kai kuwa fa? In Banda zargi me ka iya ? Baka ga ko kiran ka na Daina dauka ba? To Allah ya baka Sa a Wallahi tallahi idan ka sake ko harara kayiwa derling na Rantse Maka da Allah sai kayi kuka da idon ka Allah ya sa yace min ko MAFARKI yayi da Kai Wallahi zaka Gane na gama da Kai na gama da Wanda yake yin ka .
Ta datse wayar ta bar shi cike da Mamaki Yana Shirin mutuwa don yadda take Fadin Bai iya komai ba sai zargi .
Zufa ta Soma keto mishi Yana faman taunar lebe Bak’in ciki na dafa zuciyar shi Yana Jin tamkar ya Rasu
Babu Abinda yake hangowa a idon shi sai haduwar Farida da Mai gemu Wanda har ya bayar da cikin wancan yaron.
Ya Mike Yana Jin idon shi Yana fidda kwalla jijiyoyin kan shi Suka fito idanu sun rune ya fita da wani irin sauri ya hada kayan tafiya katsina ko Aisha Bai SANARWA ba.
Yadda yake falla Uban Gudu shine zai bawa Mai kallon shi Mamaki har ya yanke mishi Hukuncin ba a hayyacin sa yake ba.
Ya iso garin cikin tsakiyar dare wanda Bai so Hakan ba . Yaso ace da sauran haske yazo don ya farauci Abdullahi Mai Gemu amma lokacin da ya shigo garin duk gidaje ma sun kulle don haka a zaune ya kwana Bai iya ko kwanciya ba bare ya Runtsa. Babu Abinda ke yawo a zuciyar shi irin kalaman da Farida ta fada mishi mijin ta ne ya iya soyayya shi kuma Bai iya komai ba sai zargi .
Wannan shine Abinda yake ji fiye da ace an Saka mishi kaifi da tsini .
Har gari ya waye Yana hadiyar zuciya inda Kuma ya Mike ya fita daga Gidan ya shiga motar shi ya nufi gidan Mai gemu ya faka a Derk side Yana pesin din kofar da dole ta Nan zai fito
Zaman awa Biyu da Rabi ya fito daga gidan cikin motar shi GLK fara tas ya Karya kwana .
Sameer ma ya tashin motar shi ya bi bayan Mai gemu cikin Sirri ba tare da ya San ana bin bayan sa ba har suka shiga wajen gari inda Sameer ya jawo bingidar shi Yana saita motar me Gemu ya Kuma sakar Mata harsashin har sau UKU a Jere inda motar ta Soma Rawa a tsakiyar titi kafin shi kuma mugun dan masara ya juya kan tashi motar ya juya a guje ya sauya hanya.
Ya dauko wayar shi Yana Kiran wayar Farida wacce tayi banza da shi Amma sai ya tura Mata gajeren Sakon text message.
Tana zaune taji shigowar sakon daga wayar Sameer da har zatayi delete sai Kuma wata zuciyar tace Mata duba ki Gani meye yake fad’a?
Ta Bude sakon inda taci karo da sakon Mai layi Biyu kadai Yana cewa
“Kizo Ring road ki dauki GAWAR mijin ki ko Kuma ki saurari Kiran waya don ni da kaina ne na kashe shi tunda ya iya Yi Miki ciki Farida ya tab’o Ajalin sa.
Ta danna Mishi Kira Amma kafin ta shiga sai ga Kira a wayar Abdullahi tayi maza ta dauka inda taji muryar Wani mutum Yana Fadin
“Don Allah waye Kai ko ke? Mai wannan wayar ne Wani mutum ya harba da bindiga Kuma ya tsere shine muke neman Wani Abu akan Mai wayar sai muka ga wannan Lambar a KARSHEN Kiran shi don haka Muna Nan federal medical center mun dauko shi zuwa Asibiti duk da Bai San Wanda yake kanshi ba.
“Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un.
Farida ta fada sai Kuma ta fashe da kuka ta Mike da sauri tana goya Salman tana kuka .
Basma ta shigo a Rikice tana fadin
“Farida yanzu aka Kira ni da wayar Daddyn su Najwa wai Wani mutum ya harbe shi da bindiga ya gudu shi Kuma Yana Asibiti.
“Yanzu aka Kira ni Kuma can zanje Yanzu.
Basma tace gata nan tafe itama .
Farida ta fice da sauri Bata iya tafiya da motar ta ba don Bata da nutsuwar yin tuk’i da kanta.,.