Skip to content
Part 44 of 75 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

A Rikice Farida ta Isa Asibitin federal medical center inda ta wuce A@E Accident and Emergency inda ta tabbatar can ne zata samu Abdullahi.

Ilai kuwa can ta hango Rigar shi yayin da wasu mutane suke tsaye akan shi yayin da Hannun shi yake nad’e da bandeji.

Da sauri ta iso inda yake tana dauke kwallar idon ta .

Idon shi Biyu ya kalle ta Yana mata murmushi har ya tashi Zaune.

Ta Soma Fadin

“Sannu derling a Hannu kawai Raunin yake ? Allah na Gode Maka .

Ta zauna tana shafa hannun Wanda aka nade da bandeji tana mishi ADDU AR Allahu yashfeeka.

“Ai an auna Arziki Wallahi ban San Hawa ba ban San sauka ba sai ji nayi Abu ya wuce ta gefen wuya na Wani Kuma ya wuce ta gilas din motar wai Ashe harsashi ne . Wannan tsautsayin ne dai Wanda ya wuni Bai kwana ba shine ya samu Hannun Shima Allah ya kawo da sauki tunda iyakar shi a fatan hannun Amma Bai Kai ga wata jijiya ko K’ashi ba Kinga mutanen da suka kula da mota ta tana Rawa suka kawo min agaji ni Lokacin ma ban San Wanda yake kaina ba saboda na Suma a lokacin .

Sai a lokacin Farida ta waiga taga mutanen su UKU tayi maza tace musu

“Sannun Ku fa bayin Allah mun Gode Allah ta ala ya biya ku da Alheri.

“Babu komai Haj Allah ya Kara kiyaye Gaba ai taimako yiwa Kaine duk da lokacin da Abin ya faru wasu sunbi bayan Wanda yayi abin Amma Basu iya kama shi ba .

“Babu komai Allah zai kama shi in ya tsere wa mutum ba zai kasa kamun Allah.

Daya Daga cikin su ne ya mikawa Abdullahi key din motar sa Yana Fadin

“Ga key din motar Nan Alh Allah ya tsare gaba .

Zasu tafi ne Mai gemu yace da su tsaya

Ya Dubi Farida Yana fadin

“Akwai kudi Cikin motar Bude cikin dash bon ki Basu Dubu d’ari na Gode.

Farida ta Bude jakar ta tana fadin

“Akwai kudi a wuri na bari na Basu .

Ta zuge jakar ta ta fito da kudin da ta Ruko don biyan kudin da za ayi cajin ta ta Basu tana musu Godiya

Kafin karfe Sha Biyun Rana an sallame shi.

Yana Rungume da Salman da Hannun shi Mai lafiya Farida tana kama shi Suka fito inda motar shi take

Ta Dubi motar wacce harsashi ya Huda kofar Direba da Kuwa gilashin baya sai Kuma wata hudar a Dayan sashin na Mai Zaman Banza.

Ta Bude mishi kofar Motar ya shiga ta mayar ta Rufe ta dawo kujerar Direba ta tashi motar suka nufi gida Yana Rungume da Salman Yana sumbatar shi yaron Yana Dariya don watan shi uku Amma yayi girma kamar ya wuce watannin sa

Sai da Suka zo Gida ne Farida ta shiga kofar Basma tana fada Mata an sallami Abdullahi duk da tayi Mamakin Abinda ya Hana Basma zuwa Asibiti ita da tace gata Nan Zuwa.

Basma ta biyo bayan Farida taga hannun Abdullahi nade da bandeji ta Soma tab’a hannun tana mishi Sannu tare da ADDU AR Allah ya kiyaye Gaba ya Kuma Saka mishi.

“Wallahi yanzu nake shirin zuwa Asibitin sai ga ku .

Ta jima a sashin Farida tana Magana ita da Abdullahi Wanda yake fada Mata Al Amarin da ya faru a motar shi na Wanda ya sakar mishi harsashin Wanda ba zai iya Cewa ga kowaye ba .

“Ba zai Wuce nagauta ba Allah dai ya shiga tsakanin mu da azzalumai cewar Basma.

Farida kuwa mamakin Sameer take da ya fada ya Kuma cika . Bata tab’a zaton zai cika Baki wannan mugun Aikin gareta ba Kuma har ya cika. Amma ya dauki Bashi Wallahi don Wallahi ba zata kyale jinin Abdullahi ya tafi a Banza ba.

Sameer a Ranar da ya harbi me Gemu a Ranar Bai tsaya komai ba ya dauki hanyar pertercout don ya San Harbin da yayiwa me Gemun ko Bai mutu ba to Yana dab da mutuwa don Yana da saiti a harbi Kuma ya saita shi ya Kuma tabbatar da ya same shi don yaji k’arar da me Gemun ya Saka.

Don haka ya bude kunnuwan sa da son yaji ance Mijin Farida ya mutu

Har dare dai baiji komai ba don Haka sai ya yanke shawarar Kiran Hajiyar Farida ya Kuma Kira ta Yana Gaishe ta har Yana cewa ta hada shi da Saddam da Hanan ta Kuma bawa Saddam din wayar ya karba Yana Fadin

“Daddy yaushe zaka zo ka kawo Mana sweet?

Ya biyewa yaran suna ta masa shurme Amma Bai ji Wani Abu da yake son ji ba don yayi zaton Haj zata ce mishi anyi Rasuwa Amma baiji tace komai ba sai ya tambayi Saddam Yana fadin

“Saddam ka je wurin mamin ka kuwa?.

“Eh munje da Haj har da Hanan uncle din can gidan yayi ta Siya Mana ice cream.

Zancen yaron ya ishe shi ya kashe wayar shi Yana cizon lebe don ya tabbatar da me gemun Bai mutu ba shi Kuma a yanzu Babu wani buri a Ranshi da ya wuce mutuwar Mijin Farida don haka sai ya shiga laluben mafitar da zai samo .

Ya danna Kiran layin Farida tayi k’arar ta ta gama Bata dauka ba. Ya sake Kira Nan ma Taki dauka har yayi Mata missed call fiye da Sha Biyar Amma Taki dauka Dole ya kyale ta

Ganin Kiran da yake Mata ne yasa ta tunanin me yake nufi da Kiran ta? Ko kuwa Yana son Jin Halin da mijin ta yake tunda baiji ance mishi ta fara takaba ba?

Ta fito Abdullahi Yana zaune Rungume da Salman Yana mishi wasa .

Ta aje mishi kayan break din Yana Sanye da Rigar t shirt da wandon tree qwater ita Kuma tana sanye da doguwar Riga wacce aka fidda Mata kirji ta kama ta Sosai ta fidda mata tsarin Halittar ta.

Ta zauna tana hada mishi abin break din ta bashi ta karbi Salman ya Soma kurbar Ruwan shayin Yana kallon ta Yana murmushi.

Ta matsa kusa da shi tana Bashi Ruwan shayin a Baki tana daukar su a wayar ta shi Kuma Yana Kara Rungume ta har Yana hada tsinin hancin shi da nata suna kissing din juna.

Farida ta Dora wannan Vedio na sakan talatin Wanda tayi Rubutu a k’asan Vedio tana Fadin

“Derlig duk Wanda yake son Ganin bayan ka shi zai fara mutuwa”.

Ta Dora Vedio a status.

Tamkar tayi mishi Rad’a kuwa ko ya San don shi tayi wannan Arashin. Ya kuwa duba status din nasu ita da Mai gemu Wanda ya kusa sumar da shi musamman Da yaga yadda Mai gemu yake hada fuskar shi da tata tana Rik’e da gashin kasumbar shi har suna sumbatar Bakin juna .

Ya saki wayar ta kife a k’as Yana Jin wani irin Jiri Yana Shirin wurwura shi ya antaka a k’asa.

Babu Abinda yake Gani a idon shi sai sumbatar Bakin juna da Farida da Abdullahi suke har tana shafa Sumar fuskar shi cike da wata irin kauna da soyayyar Da ya yarda da gaske Farida take tana son Abdullahi ya Kuma iya nuna Mata soyayya.

A wannan ya wuni a haukace don mutane ma sun Gane haukan soja ya motsa mini bare Kuma Aisha baiwar Allah wacce ta zama tamkar ita ta kashe zomon. Taga tijara da JANHURUN masifa har tayi nadamar yarda da Auren shi . Tayi ta kuka tana Jin Lallai ta hada Kayan ta ta bar mishi gidan shi ta koma katsina

Sai dai ta tuna da haj tace duk abinda yayi Mata ta Kira ta ta sanar da ita don haka sai kawai ta Kira wayar haj tana kuka

Yana Zaune a falon tana Jin kukan da Aisha take tana Fadin.

“Wallahi Haj na Gaji da Auren Nan zan hada Kaya na na dawo gida dama biyayya ta Saka ni Auren shi tunda nazo gidan nan nake hadiyar Bak’in cikin bawan Allah Nan yanzu haka kawai Haj ban San hawa ba ban San sauka ba taka Haye ya mare ni banyi mishi komai ba? To zan taho Haj don Allah ki sauwake min Auren nan don Allah.

Ta fada da Amon sautin kuka.

“Duka Kuma Aisha? Har lamarin nashi ya Kai lalacewar haka? To ki barni dashi kar ki taho don Allah ko Asiya kar ki fadawa maganar Nan Aisha in Taji ai ni na kunya ta tunda Yana son nuna min yafi k’arfin na Amma ki bari zanyi mishi magana in ina da wani girma ko Kima a idon shi Yana Gidan ne?

Haj ta fada ta kare da tambayar Aisha

Yana Ji tace Yana Nan .

“Ki Kai mishi Wayar Maza Yanzu.

Aisha ta fito daga D’akin ta ya bita da wani matsiyacin kallo ta Mika mishi wayar tana Fad’in

“Haj na Magana.

Ya karba Yana mata sallama.

“Kar ka Kuma Yi min sallama tunda Banga kana nema na da Aminci ba . Dama irin wulakancin da kakeyiwa yarinyar Nan kenan har iskancin naka ya Kai da Duka? To bari kaji na fada maka Wallahi har Wallahi idan kana son zaman ka lafiya Dani ka zauna lafiya da yarinyar Nan idan Kuma ka shiryawa fushi na don Allah ta sake Kira na tace ka Dake ta ko kayi Mata Wani Abun wallahi tallahi zan yafewa Duniya Kai don na Gane kafi k’arfi na. Idan ka Shirya sai mu zuba da Kai dan iska marar mutunci. In shiga gaba a baka matar ko ban shiga gaba ba Aisha ba zata ci Darajar Uwar ta da take Yar Uwa ta a wurin ka ba? Kuma Wallahi tallahi bari na fada maka kar ka yarda na Gane da Hannun ka a cikin Abinda ya samu mijin Farida don Raina ya gama Sanar Dani da Hannun ka a cikin Abinda akayi Mishi don an ce min anga motar ka a garin Nan Shekaran jiya Wallahi ko na Rantse ba Zanyi kaffara ba Kaine kayi mishi Abinda akayi Mishi Amma in Sha Allah zanyi tsayuwar Dare a yau in ma Kaine sai Allah ya tona Maka Asiri Kuma ka Rik’e wannan a Ranka ko Mijin Farida ya bar Duniya to Farida ta zama haramiyar ka Kuma mutuwar shi ma zata jawo Maka JANHURUN masifa don ni da kaina zargin ka nake Wallahi tunda ZUCIYAR ka ta gama mutuwa Bata da Rayuwa . To ka fita idona Wallahi Dan iska marar mutunci wato kaga Taki yarda tayi Auren da zata fito shine kake Neman makasar mijin ta in ka kashe shi ai zata dawo gareka to kar ka yarda Wallahi Gane da Hannun ka a cikin Abinda ya samu bawan Allah Nan don Wallahi zan nuna maka bayan gaskiya nake ba bayan kowa ba . Aisha Kuma gata nan in ka Raga Mata kar Allah ya Raga Maka ni da Kaine ne.

Haj ta datse wayar ta barshi Yana fidda kwalla. Babu Abinda ya tayar mishi da Hankali a cikin tarin fadan Haj sai yafewa Duniya shi da Kuma yadda ta farke mishi layar shine Wanda yayiwa Abdullahi wannan ta addancin. Ta Ina ya kuskure da har Asirin shi ya tonu.

Ya jima Yana share kwalla Abinda Kuma ya tayar da hankalin Aisha wacce taji da ta Sani Bata fadawa Haj ba .

Ta Duka a gaban shi tana Fadin

“Don Allah kayi hak’uri wallahi ban San haka Haj zatayi ba da ban fada Mata ba. In Sha Allah ba zan Kuma fada Mata Wani Abu da ya shafe mu ba

Bai tanka ta ba ya Mike ya fice

DUNIYA tayi mishi zafi Al Amarin ya Zamo mishi gaba kura baya siyaki. Ga damuwar da Farida ta Saka shi ga Kuma tashin hankalin da Haj ta saka shi

Ya Kuma shiga Wani tashin hankalin a duk lokacin da ya duba status din da Farida take dorawa Wanda ya Gane da gayya take yin Hakan . Sai suyi Vedio ita da Abdullahi suna Rungume da juna koma suna sumbatar Bakin juna ko ya Dora kanshi akan kirjin ta ko ita tana kwance a jikin shi haka zai gani tashin hankali ya ishe shi yaji kamar ya Rasu. Ga shi a yanzu duk Lokacin da yaga Farida zai ga ta cije shi irin cizon da yake wuyar shanyewa musamman akan bukatun gangar jiki don haka kwanaki da yawa suka shude har zuwa watanni inda Aisha ta samu yancin baya dukan ta Baya kyarar ta kamar yadda Babu Ruwan shi da ita bare ya nemi Wani Abu daga gareta.

Tsayin watanni UKU ya wayi gari baya muradin komai sai Farida musamman da ya duba hoton da ta Dora a status ita danra Salman Wanda yayi girma Sosai kamar shi da Saddam ta na ta fitowa.

Ya zuba Mata ido Yana ganin yadda ta sauya ta zama mace ta Sosai .

Ya Mike Yana nufar mota ya kuwa Yi Mata key ya dauki hanya don Yana Jin yau idan Bai tab’a Farida ba Akwai matsala don haka a bakin Rai bakin fama koma me zai faru a yau sai ya kashewa Farida Auren ta .

Bai iso garin katsina da Rana ba sai dare don haka gidan shi ya zarce ya Kwana da safe ya fito Bai dauko mota ba ya hawo Napep ta kawo shi Gidan Mai gemu ya Kuma tsaya nesa da gidan Yana kallon Mai shiga da Mai fita har yaga fitar Abdullahi ya Kuma tunkari gidan Babu tsoro Babu shakka ya shige ya Kuma wuce sashin Farida

Tana zaune tana sakawa Salman Kayan sanyi tana mishi wasa Yana Dariya sai Ganin inuwar mutum tayi a kanta .

Da sauri tace

“Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un. Ta dago kanta sai ganin shi tayi tsaye kyam akan kafafun shi Hannuwa zube a aljihun wandon shi.

<< Tana Kasa Tana Dabo 43Tana Kasa Tana Dabo 44 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×