Skip to content
Part 47 of 75 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Haj ta Zauna akan kujerar cike da wani irin Bak’in ciki Wanda take Jin Sameer ya Zame mata babban kalubale a cikin ZURIAr ta.

Ya zube a Gaban Haj Yana Gaishe ta tayi maza ta dakatar da shi tana Fadin.

“Ban wanko kafata daga katsina zuwa Nan don ka Gaishe ni ba. Meye alakar ka da Farida da har ka ke taka gidan mijin ta? .

“Haj ni tace naje gidan ta?.

Fasss ! Haj ta wanka mishi Mari a fuskar.

“Ina tambayar ka kana tambaya ta don Uban ka? Kana son karyata ni ne ko kuwa zaka ce min baka je katsina ba? To an ganka Kuma na tabbatar da Abinda Farida ta fada min ba shikenan ba tunda baka tsoron Allah komai ma zaka iya Yi don haka fada min alakar ka da ita da har kake gadarar taka gidan ta. Wallahi kukan Farida ya Alamta min Wani Abu na fin karfi da kayi Mata Amma Ina Jin ka.

“Sharri tayi min Haj . Me zai kaini gidan ta ni saboda Allah?.

Aisha ta fito ta Kayan Abincin da ta hadowa Haj tana dire Mata a gaban ta yayin da bello yake waje don ya bawa su Haj wuri suyi magana.

Haj ta dubi Aisha tana Fadin

“Ke Aisha jiya Sameer Yana garin nan ? Kuma gida yake ko fita Yayi?.

Aisha ta dago tana fadin

“Jiya baya gida gaskiya sai tsakiyar dare ya Dawo Kuma na ganku a yanzu haj har hankali na ma ya tashi.

Haj ta Dube shi tana jan kwata kafin tace

“A jiyan da Farida ta Kira ni tana kuka na kira Wayar ka a kashe don ka San Dole zan neme ka. Naje gidan maman Umar ta tabbatar mini da taji motsin ka Kuma taji fitar motar ka . To Naji Farida tayi Maka Sharri Amma me yasa tun wancan Lokacin Bata Yi maka Sharri ba sai yanzu ? To Bude kunnuwan ka Sameer. Wallahi tallahi kaji na Rantse Maka da ALLAH ko? Akan wannan maganar zan iya Yi maka ALLAH ya Isa na Kuma LA ance ka don na tabbatar ba Alheri ya kaika gidan Farida ba Akwai wani BOYAYYEN MAKIRCI da ka shirya tunda kake Neman makasar mijin ta . Kar ka Kuma taka inda Farida take . Idan kuwa kayi Hakan zan nemi kadin NoNo na da ka Sha in Kuma bi da Allah ya Isa kafin na tsine Maka Albarka tunda ka zama shaidani Banga amfanin ka a tare da ni ba Kuma Wallahi har Wallahi idan Wata tab’argaza ta fito nice wacce zan fara bankada Asirin ka in kafa shaida don zan Saka mijin ta ya Rubuta ya ajiye dukkan Abinda ya biyo baya tsohon mijin ta ne yake bibiyar ta ni dama Raina Bai gamsu da Kai ba Wallahi akan Farida Kuma zanje na samu Farida naji komai har Abinda yake lullube zan jiyo shi Allah ya sa na Gane Akwai Abinda nake zargi kaga yadda zan watse ka Sameer. shiyasa dama kake wulakanta yarinyar Nan don Kana son zama shaidani? Kana nufin da Auren Farida zaka bibiye ta? Kai kam tur da irin Halin ka Wallahi . Kuma idan dai kana a haka Wallahi ko a LAHIRA bana fatan haduwa da Kai kar ma kace ka Sanni .

Haj ta wanke shi tas da masifa tana ta antaka mishi Ashar.

Ta Mike suka juyo gida ita da bello .

Tun a jirgi take kuka bello Yana Bata hak’uri.

“Yaya zanyi bello tunda Allah ya jarrabe ni da wannan kaddarar? Yaya zakaji idan Ubangiji ya baka Dan da baya tsoron yaja Maka abin kunya abin magana ? Wallahi tallahi Farida ta Rufe Wani Abu Amma ni na San Halin yaron can Ina tsoron kar ya nuna Mata karfi yace zai zalunce ta tunda ta Kira mishi kalmar zalunci na San Abinda yayi mata ya munana.

Bello yayi shiru yana Mamakin Al Amarin Dan Uwan shi Sameer .

A Ranar da suka Dawo ne daga pertercout Haj ta so Zuwa gidan Farida Amma ta barwa safiya kasancewar sun dawo da yammaci don ma tafiyar jirgi Sukayi

Bayan fitar Abdullahi Wanda aka cirewa bandeji Yana ta harkokin shi Babu matsala dama ko kafin a cire Yana fita office din sa sai dai baya jimawa yake Dawowa.

Bayan fitar shi ne Haj ta iso gidan farida wacce ta karbe ta cike da mutuntawa.

Haj ta Zauna tana daukar Salman Wanda yake rarrafe har Yana kama Abu ya Mike tsaye .

Ta Zubawa yaron ido tana kallon shi da suffar shi irin ta Saddam Wani Abu Yana Mata yawo a zuciyar ta amma ta kawar da shi .

Farida tayi ta kawowa Haj Kayan tab’awa suka shiga Gaisawa. Bayan sun gama Gaisawa ne Haj ta dubi Farida tana Rik’e da Salman Yana Kai Hannu bakin ta da hancin ta da yake son kamawa .

“Farida Nazo ne don muyi magana Dake akan Sameer. Don Allah Kar ki boye min komai ni Kuma zan fahimce ki don naji a Raina ni da kaina Ina son tuhumar Sameer tun da a ka ce an harbi mijin ki naji a Raina shine Wallahi duk da zato zunubi ne . don na San Abinda zai iya ne . Haka Kuma tinda kika Kira ni kina kuka na San Abun ya wuce hankalin ki to zan fahimce ki fada min komai don Allah.

Hawaye ya kawowa Farida ta Soma share su tana fadin

“Hakika haj Sameer ne ya har bi Abdullahi da niyar zai kashe shi tunda nace ba zan koma gareshi ba. Sai da ya Kira ni ya fada min Hakan da Bakin shi Amma ban zaci da gaske yake ba sai da yace naje wuri kaza na dauki GAWAR Miji na sai gashi Kuma inda ya fada din Nan aka Yi Al Amarin. Ba wannan ne Abinda yafi daga min Hankali ba Haj irin yadda yake so yaxo Gidan Nan ya nemi keta min haddin Aure da Kuma yadda yake son ya kashe min miji na wai a dole sai na koma gareshi.

Haj ta dafe kanta tana Ambatar Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un .

Tashin hankali ya bayyana a fuskar Haj wacce ta Zubawa Farida ido Kafin ta sauke AJIYAR ZUCIYA tana fadin

“Tun yaushe ya Fara Yi Miki Hakan Farida?.

“Wannan Zuwa na Biyu ne yayi Haj shine na Sanar da ke .

“Gara da kika Sanar Dani dama Raina ya bani Kuma Ubangiji ya haska min Al Amarin tun lokacin da ya gigice da son Komen Auren ku naji a Raina ba zai barki zama lafiya ba Amma kuwa kinyi Kyan Kai da Baki bar Abin a Rufe ba. Don Allah ki Rufe maganar Nan Farida don Ina Jin kunyar iyayen ki Shima mijin ki Ina Jin kunyar shi ace nice Uwar Wanda ke Neman keta haddin iyalan sa Farida ki taimake ni don Allah ki Rufe maganar Nan.

Sai Haj ta fashe da kuka kukan da ya tayar da hankalin Farida.

“Don Allah Haj kiyi Hak’uri Wallahi nayi miki alkawarin Hakan don Nima Ina Jin kunyar mutane da yawa idan maganar ta fita . Abinda yasa na fada Miki don kiyi mishi magana Amma ko Mai gidan na dai fad’a mishi yana min barazana ne .

“Nagode Farida in Sha Allah kuwa idan dai ya yarda Nice Uwar sa zai manta da ke bare yayi Miki barazana.

“Haj ke kadai zan iya fadawa Sirri na shiyasa har na fada Miki Hakan Amma ko mahaifiya ta ba zan iya wannan maganar da ita ba. Haj a yau zan fada Miki Wani Abu Wanda Baki San da shi ba Amma na San a k’asan ZUCIYAR ki kina tunanin meye Dalilin da yasa Sameer ya Dora min zargi? To Haj ni na bashi Damar ya zarge ni tunda nayi kuskuren da Dole haka ta kasance. Nayi nadamar Abinda nayi Wanda nake jin Ina ma Ina da Amon sautin da zan fada don yan Mata su kiyayewa Abinda na kasa kiyayewa ?.

“Wallahi Farida har gobe har gobe Ina tambayar kaina meye Sameer ya Gani a tare da ke da ya Dora Miki wannan zargin? Kunyar ki tasa ban Miki wannan tambayar ba Farida.

“To Haj yau zan fada Miki. Saboda Nima Abin ya dame ni har na Gane sau tari damuwar da ta zama damuwa ga bawa Zaki iske kuskuren kuruciya ne Wanda za ayi ta da na sani banyi ba kamar dai ni yadda ta faru gareni Haj Ina son Sameer Yana Sona Amma zargi ne jigon Abinda ya Raba Mana Aure har yake neman Saka mu Cikin hadari.

“Haj a Ranar da na Fara ganin Sameer a gidan Yaya dauda Wanda shine yayi mishi hanyar samun Aikin SOJA a Ranar na karyata kaina da nake cewa so karya ne saboda kallo Daya nayiwa Sameer na yarda Ina son shi Kuma son Bai zama karya ba. Kamar yadda nake fada idan Naga masoya. Amma akan Sameer na karyata kaina.

Allah da ikon shi sai aka hada zukatan mu Domin kuwa sati Daya ba a Rufa ba Sameer ya kuma dawowa jaji garin kaduna inda ya samu Yaya dauda da maganar ya ganni Yana so Yana Neman izinin magana Dani.

Kafin satin Allah kadai ya San yadda na kasance Haj don Ina Jin tamkar zan zautu idan ya kasance Sameer Bai kula da Halin da nake ciki ba. Babu irin shawarar da ban yanke ba akan na samu Yaya dauda na nemi lambar Sameer Amma sai na tuna mutuncin mace Yana Nan a tafin Hannun ta itace Mai kiyaye Abinta kuma itace Mai watsarwa don haka sai na kame kaina nace Allah idan haduwar mu da bawan ka Alheri ne to ka tabbatar Dashi a ZUCIYA ta idan Kuma Babu Alheri Allah ka fidda min shi kamar yadda ka kimsa min shi ba tare da Sani ko tsammani ba.

Sai dai maimakon naji ya fita a Raina kullum sai Kara Jin son shi da begen shi nake har ta Kai mafarkai na suna k’arewa ne ga Sameer

Ban fasa ADDU A ba sai gashi cikar sati da Zuwan sa Ubangiji mishi fiye da Abinda aka Saka min

Yaya dauda baiji magana ba yace shine Mai Bada Aure na ya Kuma bawa Sameer Saboda ya San shi ya San waye shi

Yaya dauda ya Kira ni nazo sai kawai naga Sameer Wanda yake Zaune a kujera Yaya dauda yace na kawo mishi Ruwa Bako na ne

Na kawo mishi Ruwan yayi min bayanin da Gani na ya haifar mishi irin Wanda nashi ganin ta haifar min

Haj tun a Ranar muka kulla wata irin soyayya wacce ban yarda akwai ta a Duniya ba. Sai dai tun tafiyar tamu batayi Nisa ba na Gane Sameer irin soyayyar da yake so muyi itace wacce Babu shamaki a tsakanin mu tamkar dai irin Rayuwar ma aurata

Ban yarda da hakan ba Amma sai ya nuna min shi Kam baya iya irin wannan soyayya ta mace tana katsina miji Yana Daura.

Da dai ya Gane bana muradin irin yadda yake muyi sai ya SHIGA barazanar zai fasa aure na tunda ba son shi nake ba. Wannan Abu shine ya tayar min da Hankali wata Kil ya Gane yadda nake son sa ne shiyasa yayi min wannan barazanar.

Haka na Amince mishi Yana Runguma ta Yana kissing dina duk da sunan soyayya.

Samun wannan Damar Kuma sai ya koma cewa lallai sai ya Sanni a mace ni Kuma nace ban San maganar ba . Shine fa yayi min yaji har tsayin watanni Kafin yace ya fasa Aure na. Sanin da yayi wannan kalmar tana tayar min da Hankali yasa ni Nemo shi na yarda na bashi Kaina yayi yanda yake so Dani. Tun daga wannan Rana sai dai in Bai zo garin ba Amma da yazo zai zo ya dauke ni muje gidan shi har Allah ya kaddara dauruwar Auren mu. Abinda ban Sani ba shine duk Namijin da kika bawa kanki ya sanki a mace ko ya Aure ki Kuma ko shine ya fara sanin ki a mace to zargi zai darsu a zuciyar shi har ma yake ganin ba shine FARKON Wanda ya Fara sanin ki ba wani ma ya Taya kin sallama.

Tunda na SHIGA gidan Sameer da sunan Aure Haj na Soma dandanar Bak’in ciki Domin kuwa duk inda naje na dawo abin zargi nake gareshi Kuma sai ya tuhume ni. Babu ta inda na barranta da zargin Sameer Koda kuwa daga family din mu ne sai yace yaga Ina yiwa Wani Namiji fari ko Muna magwna Ina kashe murya. Duk da wannan zargin Nashi Haj Bai taba kamani da laifi Daya na irin mu Amala da Maza ba Amma shi na Sha Ganin hotunan da Mata ke tura mishi na tsiraici Amma ban zarge shi ba saboda na san Babu macen da ta Isa ta Hana mijin ta mu Amala da Mata sai dai in bai ga Damar Hakan ba.

Tun daga wannan Rana Haj muke Samun matsala da shi tun munayi a tsakanin mu har kuka sani kawo Rabuwar mu ta karshe wacce Dukkan Abinda zaiyi sakin akan sa da sunan zargi Idan ya bincika sai ya samu Sabanin zaton sa ne Amma Bai saduda ba har dai na Gane shine Bai kulla gaskiya ba yake zaton Nima Ina yin Abinda ya Gani duk na dorawa kaina dukkan laifin tunda na kame kaina Haj da Ban kasace a haka ba Kuma da nayi kima a idon sa.

Haj ta sauke AJIYAR ZUCIYA tana dauke kwallar idon ta tana fadin

“Lallai kuwa kuskuren kuruciya Farida kin Kuma Yi shi. Fadar Allah ce Hakan mazinaci sai mazinaciya da kin kame kanki Wallahi ke ba tsarar Auren shi bace sai dai ya Nemo Yar Uwar sa mazinaciya. Amma na yarda da maganar ki kuskuren kuruciya ne Amma shi din haka yake tunda ni da ido na naga arniya a muhallin sa Kuma iskancin ya hada su. To Babu komai zan yi Wani Abu in Sha Allah Farida . Nagode da kika zabe ni kika fada min Sirrin ki Kuma in sha Allah yadda kika San Sirrin ki Yana cikin ki haka na barwa nawa cikin Kuma idan zan Baki shawarar sai hace Miki duk Ranar da Sameer ya Kuma Zuwa gidan Nan kiyi mishi ihu ki Tara mishi mutane. Ke ko wayar ki ya kuma Kira ki sanar min.

Da haka Haj ta wuce tana yiwa Salman wasa Farida Kuma taji gara da ta sanar da haj ko ba komai taji tamkar ta sauke Wani Abu Mai nauyi a kirjin ta.

Tun daga wannan lokacin kuwa sai dai taga Sameer ya duba Mata status Amma Kira Kam ya Daina bare Kuma wata magana ta biyo baya.

A yau Kam ta wayi gari da amai Wanda take ta kwarawa tamkar Zata Amayar da kayan cikin har zuwa yamma ta Wahala Sosai ko Ruwa ta Sha sai ya dawo har Abdullahi ya dawo ya samu tana faman aman hankali a tashe ya tarairayo ta jikin shi Yana shafa fuskar ta Yana tambayar ta Abinda yake damun ta ta fada mishi amai ne kawai yake Wahalar da ita.

Da sauri ya Rungume ta a kafadar shi Yana Kuma Rik’e da Salman Wanda yake ta gwarancin sa suka nufi Asibiti Yana fadin

“Allah yasa new baby ne my Darling.

<< Tana Kasa Tana Dabo 46Tana Kasa Tana Dabo 48 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×