Goggo ta Zubawa Bakin murja ido tana kallo da sauraren Bayanin da take Mata.
"Babu fa lafiya Goggo. Yanzu wasila ta Kira ni shine nake fada Mata irin mafarkan da kika fara da ita Nima Kuma nayi sau biyu na ganin biran Nan a kewaye da ita to Wallahi Goggo yanzu take tabbatar mini da Cewa gidan da aka Kai ta cike yake da barai manya da k'anana Anya kuwa Goggo ba Wani babban Al Amarin bane ba kuwa? Wallahi na tsorata matuka Gaya musamman da tace mini na Roka Mata ke gafara na kuma Rok'a Mata ISHAQ. . .