Wasila ta Dubi Zubaida cike da tausayawa ganin hannun ta da kafarta da Basa iya mora Mata tamkar wacce Inna ta shanye ko Kuma mutuwar b'arin jiki.
"Zubaida su waye ku a gidan Nan? Me yasa kuke boye bakwa fita inda za a ganku? Ta Yaya kuka shigo Gidan Nan ko Kuma irin Mai gidan ne ?.
Duka wasila ta jerawa Zubaida wannan tambayoyin tana Jiran Amsar ta.
Zubaida tayi murmushi tana Duban Wasila.
"To zan iya Cewa kaddara ce ta shigo Dani don ma Allah ya taimake ni Ina ADDU A Amma da yanzu tarihi na ya jima da. . .