A Ranar da Haj tazo Asibiti Ganin Aisha a Ranar Kuma ta Kira wayar Sameer tace komai yakeyi ya ajiye shi Gobe Goben Nan tana son Ganin shi.
Haka ya dauko hanya daga pertercout zuwa katsina saboda a yanzu Kam Neman Gamawa lafiya da Haj yake tun da tace zata sallamawa DUNIYA shi ya saduda.
Can gidan Asiya ta nufa don a Daren aka sallami Aisha da safe da Haj ta tafi Ganin jikin nata tana can ya Kira ta yake fada Mata ya iso tace yazo nan gidan Asiya ya same ta
Aisha Kam ta Rikice da Ganin Sameer Wanda ya zube a Gaban Haj da Anty Asiya Yana Gaishe su .
“Me kake nufi da Abinda kayi? Shin ka zabi Rabuwa da Aisha ne don na sallamawa DUNIYA Kai ko kuwa kana son nuna mini ni ba wata tsiya nake a wurin ka ba? .
“Kiyi Hak’uri Haj ba haka nake nufi ba Wallahi . Nufi na ku tambaye ta ai ta San Abinda tayi min.
“Bana bukatar jin Komai da ya faru ka dauki matar ka kawai ku wuce Baki alaikum tunda Kai kaki fada itama Taki fad’a zamu lalace ne akan ku? Kuje can koma meye ta matsse muku a tsakanin ku tunda kunki ku fad’a to kuje can damuwar ku ce bana bukatar Jin Komai Kuma bari kaji ba hauka kake takama dashi ba? To zaka ga Aikin hauka kuma Wallahi ahir din ka Duk irin laifin da Aisha tayi Maka idan ka Kuma gigin harbinta Wallahi nice zan Rama Mata ba da bindiga ba sai dai na sheme ka da tab’arya Wallahi.
“A a Yaya Amina Adalci fa ya kamata kiyi a maganar Nan ba b’angaranci ba Kai Sameer fad’a mini Abinda Yar iskar yarinyar Nan tayi Maka na San banza ba zata Kai zomo kasuwa ba Kuma Akwai Dalili .
Yayi k’asa da kanshi Yana share gumi yana fad’in
“Anty Asiya Naso ace ta Fadi Abinda nayi Mata Wanda inda ya zamo laifi na na tabbata ba zata Rufe ba zata fada Amma da yake laifi ne Kuma ita tayi gashi ta Rufe Bata fada ba.
“Ni na San Hakan fada min don in har akwai damuwa nice Mai tsaya Maka Wallahi kar kaji komai Sameer don na san halin yarinyar Nan.
Yayi k’asa da Kai Yana Jin nauyin Fadawa Anty Asiya maganar Nan Amma Dole ya fade ta Yana Fadin
“Anty Asiya kwarto na kama ta dashi a lokacin da Basu zaci Gani na ba . Yaron da na yarda dashi nake aikowa Gida shine na same su a cikin Wani irin hali na tsoro da mamaki ni Kuma ZUCIYA ta ciwo ni na sakar musu harsashi don ma sun gudu wata Kil da anyi danyen Aiki shine fa ta taho Babu Shiri.
“Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un ni Asiya Aisha ? Ta fada tana dafe kirji cike da Mamaki da tsoro tana Duban Aisha wacce ta Rufe fuska tana kuka.
“To kinji Yaya Amina kina ta Sababi kina masifa ni na San Sameer ba Zaiyi Hakan da gangan ba tun yaushe suke tare baiyi Hakan ba?. Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un hasbunallahu Wani imal wakeel Wala haula Wala kuwwa ta illah billah.
“Kwarto fa Aisha a gidan Aure? Sai Kuma ta rushe da kuka tana kankame Yar Uwar ta cike da Tashin hankali.
“Hakan yayi maka daidai ko? Ka tonawa yarinyar Nan Asiri a gabana a gaban Yar Uwa ta ? Kai duk naka sharrin da aibin baka Gani ba kazo Nan kana fadin ga zance ga magana? Ka manta da ita Aishar ce ta Soma Rufa Maka Asiri tunda a Ranar da muka kaita taga dadaron da ka ajiye Amma shine Kai ka iya bayyanawa Duniya Aikin ta ? Kai din baka iya Rufa mata Asiri ba waye zaiyi Hakan ? .
Aisha da taga kukan da Uwar ta keyi ta Kuma Rude wa tana kuka inda Haj ma ta Soma nata kukan tana Fadin
“Sameer ka Gallabe ni a Rayuwa Kai ne matsala ta a cikin ZURIA ta . Ni ka tonawa Asiri ba Aisha ko Asiya ba don Abinda ya samu Asiya ni ya sama Abinda ya samu Aisha Kuma yadda nake ji in akan ku ne itama Hakan . Don haka Nagode maka da wannan wulakancin da kayi min ba zan ce Maka Allah yayi maka yadda kayi mini ba sai dai zance Maka Nagode zaka Kuma Gani Idan Rufawa dan Uwa Asiri Yana da tasiri zaka Gani don duk Wanda ya Rufa Asirin Dan Uwan sa Allah NE zai Rufa NASA kamar yadda in ya tona Mishi ma Allah NE zai tona Mishi NASA duka dai abin yiwa Kaine Kuma bana ko shakka Abinda Aisha tayi Kaine ka Bata Damar yin sa bana ko musu bare in Karin Hakan .
“Wallahi ta dai ga Damar Hakan ne Kuma ta Saka wa Ranta Amma gata Nan ki tambaye ta Akwai Abinda ta Rasa? Da tana da yunwa ko kishin Ruwa da itace wacce zata fara tona min Asiri tace na barta da yunwa.
Aisha ta yaye Rufin da tayiwa kanta tana fadin.
“Dama Abinda ka zano Abinci shine kawai hakkkin Aure? To Haj Dukkan Abinda nayi Wallahi shine ya bani kofar yin Hakan. Hakika haj ya na bani komai na bukatar Rayuwa Amma har yau din Nan Haj gashi ki tambaye shi Bai tab’a duban hanyar daki na da sunan bani hakkin Aure ba .
Haj ta dauki salati da Aminci tana Fadin
“Muhammadur RASULULLAHi sallalahu alaihi wassalam ni Amina na SHIGA ALJANNAH.
“To Asiya kina Ji ko? Kinji Abinda yayi ? To ka Gani tun bamu tashi a Nan ba Allah ya Nuna Maka iyakar ka . To Kuma ma me kake nufi da ka Saka bindiga ka harbe ta? Ina ce haka kake nufin tayi dama? To me kake so ayi kenan? Kai baka tuna da naka abin Kunyar ba na Nemo arniya sai ita don ta nemawa kanta mafita Kai karshen hukuma kake son Yi Mata Hukunci? To ai Kuma shikenan wai an kama Uwar Amarya da Ango Kun Raba ma kowa ya Kalli inda yake so tunda Kai dai ka zama azzalumi. Kai kam kana tsoron Allah? Duk tsawon Lokacin Nan kana zuluntar yarinyar Nan? Amma Kai ai ka Nemi mafita tunda kana da arniya a gefe Amma sai ita ce kake da dogon bakin cewa ta kawo maka kwarto?.
Aisha ta Soma share Hawayen ta tana fadin.
“Haj Wanda yake fad’ar ya kama mu a tare yaron shi ne Kuma shi ya fada min wai Sameer yace mishi shi fa ba wani Sona yake ba tunda Babu inda Bai sani ba a jiki na . Haj tun kafin nayi Aure a siyayyar da kuka San munyi da bawan Allah Nan Haj Wallahi Babu Abinda baiyi Dani ba tamkar ya Aure ni don kawai ya Gane Ina son sa shine yake fallasa ni haka . Ni Kuma shaidan Yaja ni tare da wannan shaidanin Wanda shine ya fara nema na Yana fada min Sameer Yana da wacce yake tab’awa ni ma na nemi Wanda zai taba ni shine ya yaudare ni har mukayi Abinda mukayi inda Kuma na Gane Cewa Dole ni da Sameer mu kasance cikin matsala tunda muka kasance mazinata Muna ha intar juna don haka ni Kam da dai Nayi ta cutuwa Ina keta haddin Ubangiji Wallahi Haj na Hak’ura a Raba Auren Nan.
“Karya kenan Aisha ai ke shi kune daidai juna tashi ma Maza Wallahi a yau Zaku koma kar Allah ya baku ikon Daina wa in ma Baku bari ba gaku ga ALLAH!.
Sameer da ya ke ta share gumi ya kasa motsi yayin da Anty Asiya ta zuba tagumi tana Kallon ikon Allah Wanda ya girma ya daukaka Jin abubuwan take tamkar A MAFARKI.
Taji a Ranta hakikatan Yar Uwar ta mutum ce Mai tsayawa kan gaskiya wacce ke iya yiwa kowa Adalci akan gaskiyar ta .
Dole kuwa Aisha ta Mike Shima Sameer ya Mike inda Haj ta Mika mishi takardar kudin maganin da akayiwa Aisha tana Fadin
“Biya Asiya kudin ta don kasan Kaci Uwar karya ka kwana da yunwa ta Yi maka wannan Wahalar Kai ka kaja Kuma Dole ka biya ta kudin ta in yaso kaje ka kashe Aisha ka kawo Mana gawar ga. Ke Kuma idan kika sake aikata shigen irin Abinda kika aikata zan gurfanar da ku a gaban kotun musulunci don tayi muku haddi Shima haka duk Shegen da yake Jin shi Dan iska ne mu zuba mu Gani Shege ya fasa.
Da haka ya direwa Anty Asiya kudin da tayi Maganin Aisha Amma tace ba zata karba ba Haj ta warce kudin daga Hannun shi ta aje Mata su Kuma suka fice kowa ZUCIYA tamkar zai Rasu .
Haka Suka dauki hanyar pertercout kowa na Jin tamkar yayi aman ZUCIYAR shi har suka Isa Babu Mai kula Wani don su Duka wai talle ce da natayiwa Audi Gori kowa Yana da abin Kunyar Nan to daga hanci na me Kuma?
Tunda ya dawo ya shiga farautar Mustafa Wanda ya samu Labarin Yana Asibiti Yana jinya . Babu Abinda zuciyar shi take fada mishi illa ya bishi har can Asibitin ya kashe shi don in Bai kashe Mustafa ba to Bak’in cikin Abinda yake hangowa Wanda idon shi ya Gano mishi shine Ajalin shi sai Kuma yaga Mustafa Bashi da laifi musamman yadda ya fallasa mishi Sirrin Gidan shi da matar shi in dai za a Fadi gaskiya mustafa bashi da laifi sai dai in anso zalunci kamar yadda yayiwa Aisha itama in har ya so gaskiya Bata da laifi shine BABBAN Mai laifi. Ta Yaya yake zaton ba za ayi Mishi Abinda yayi ba? Meye baiyi da Farida ba? Sai shine ba za ayi wa ba? Anya kuwa yadda yayi in Akayi Mishi zai iya shakar numfashi? Hakan da ya tuna yasa ya fasa iske Mustafa Asibiti don ya tabbatar da maganar manzon Allah ce take tabbata akan sa Bata ma gama sauka ba tunda ga can Hanan mace ce wacce yake tsoron ayi Mata Abinda yayiwa Uwar ta da Kuma Aisha har ma da sauran Matan da ya nema a waje.
Mustafa kuwa tun Yana Gadon Asibiti yake request din sauyin wurin Aiki daga pertercout zuwa Wani wurin ba don komai ba kuwa sai don Kar ya Kuma haduwa da Sameer ya Kuma samu Hakan ba tare da Ogan ya San Akwai Wani Abu ba.
Tuni kuwa Mustafa ya wuce Legos inda aka sauya shi ba tare da ya gama warkewa ba duk don Kar ya Hadu da Sameer Saboda ya San haduwar tasu ba zata haifar da D’a Mai ido ba tunda aka fara da Harbin kafada.
Duk wata ana fiddawa blessing kudin ta Daga cikin albashin Sameer suna karba ana Hidima har tsayin wata Tara blessing ta haife cikin ta sai ga ta da yarta a Hannu aka Kuma shaidawa Sameer haihuwa Dole Kuma aka Saka shi yin Kayan Haihuwa da Duk wata Hidima inda Kuma yarinya ta Raba gardama tayo kamar Hajiyar Sameer Kai zaka Rantse da Allah Hajiyar Sameer ce ta haife ta.
Ana yin kwanaki talatin madam gora tace lallai ya fito a Daura Auren su Amma Sameer yace Sam ba zai Auri blessing ba tunda basuyi wannan alkawarin ba .
Madam gora tace to In dai ba zai Aure ta ba sai ya Karbi yarsa. Kuma ya mayar Mata da yarta yadda take kafin a tab’a ta ta koma budurwar ta gal don su a kabilar su Wanda yayiwa yarinya ciki shine mijin ta
Duk yadda aka turza Sameer yace ba zai Auri blessing ba sai dai koma me za ayi ayi inda Ogan Sameer yace da Madam gora tunda dai Sameer ya Yi musu hidimar ciki da Haihuwa to tunda yace baya son Auren suyi Hak’uri tunda shi ba kabilar su yake ba shi ba haushe ne Kuma Daga yau ya kashe Maganar Nan kar a Kuma yin ta .
Kuka madam gora ta fasa har tana faduwa a k’asa tana hade Hannuwan Roko wai In Sameer Bai Auri blessing ba zasu kunyata a gari Kuma ace yarta Bata kirki tunda Wanda yayi Mata ciki yaki Auren ta .
Hak’uri ya Bata yace
“Kiyi Hak’uri madam da yarki taji magana da Bata biyewa Hausa ba kinga laifin nata ne shi Dama ba Auren ta zaiyi ba da ta Gane Hakan da Bata jawowa kanta Aiki ba .
Haka madam gora ta taho tana Shan Alwashi Wallahi ba zata yarda ayi Mata wulakanci ba a tab’a Mata yarinya Kuma ace ba za a Aure ta ba to zata Rama Abinda Akayi Mata Kuma wannan jaririyar Dole zata gano iyayen Sameer a arewa ta Kai musu abin su don itama Hausa girl zata zama gara ta mayar Musu da kayan su in yaso an Rabu kenan har Abada.