Babu Abinda kake ji sai sautin kuka Wanda akeyi k’asa k’asa tare da share HAWAYE har da fyace majina da tissue paper.
Kowace tana tana Rik’e da carbi tana ja inda Mata ke ta ta fadar
“Allah yayi mishi Rahama yasa ya huta sai Hak’uri Rayuwar kenan yau Kai ne Gobe Kuma sai Labarin ka Allah ya jikan Wanda Suka Rigaye mu mu kuma ya azurta mu da kyakkyawan karshe.
Yaya lami ma da take ta fyace majina da habar zanin ta tana fadin
“Shikenan ni Kam Ina Ganin Rayuwa duk na bunne iyaye da dangi har da Yan Uwa nu kuwa Dadin me wannan Duniya zatayi min? Dama daga ni sai Abdullahi muka Rage to ya tafi ya barni ni Kuma ko ga wa ya barni? Sai Yaya lami ta rushe da kuka tana Fadin
“Kaicon DUNIYA da Bak’in cikin ta baya karewa Mai Rai Yana ganin Rayuwa.
Basma da take Hararen Yaya lami ta Dube tana Fadin
“Haba Yaya lami Babu kyau fa kukan mutuwa don Allah ki Daina kukan Nan kuyi ADDU A Mana?
Yaya lami ta dubi Basma idon ta tar Babu ko dis na hawaye tayi mamaki matuka Gaya Domin kuwa ko kwararaton ihun da Basma tayi Babu digon hawaye a idon ta sai kawai tayi Mata zaton juriya da Kuma shanye damuwa.
“Ta Yaya zan iya Daina kuka Basma? Ni fa kad’ai nayi saura a wannan kuntatacciyar Duniyar yau Gani Babu Uwa Babu Uba Babu Yan Uwa sai Ya’ya. Kukan mutuwa ma mutum Yana sanin lokacin da yake Yin sa ne?.
“To komai ba Hak’uri Ake ba? Ni ba gashi na Hak’ura ba tunda na San ya tafi ba Kuma zai dawo ba? Ai kukan da ba zai Dawo Maka da mutum ba banga amfanin yin sa ba.
Farida da ta zube tagumi tana Jin Basma da Yaya lami inda ta tabbatar da gaske Basma take nayi nufin Yin wulakanci Mai Daraja.
Sai taji Wani kuka Yana kwace mata Wanda Bata San manufar Basma akan su ba musamman da ta tab’a ce mata ta saurari zuwan ta don zata wulakanta ta sai Kuma ga wannan Al Amarin.
Salman ya Soma kuka don Bai Saba ganin taro a gidan nasu ba sai gashi yanzu yaga gida a cike har da kukan Uwar sa sai Shima ya Soma kuka Yana Fadin.
“Mami a kaini wurin Daddy.
Basma ta wurgawa yaron harara tana Fadin
“Uban ka fa ai Yana can a kushewa gara ma ka sakawa Ranka hak’uri Yan iskan Yara masu Nacin tsiya da binbini in ba zai Yi Mana shiru ba don Allah ja su ku koma sashin ku ni wannan koke koken ya Soma Isa ta kaina ya Fara Ciwo.
Yaya lami ta dubi Basma tana Fad’in
“Me kike Yi ne haka Basma? Yanzu yaron Nan Bai zama Abun tausayi a wurin ki ba har kike mishi wannan zagin irin na tsamar Nama? Uban shi fa yake nema Neman da kika tabbatar da Babu inda zasu kuma haduwa sai dai ya ganshi a mafarki ko Kuma taswira Amma Bai zama Abun tausayi a gareki ba kike Mishi wannan zagin? Kar ki ki Kuma zagin shi in ba Zaki tausaya mishi ba to ki barshi.
“A a Yaya lami barni na fada mishi don Uwar sa ta Gane yaren da nake magana da shi .
Matan da suke cike a sashin suka Soma Fadin
“Haba Basma ke da akayiwa mutuwa Amma kike wannan Abu haka? Meye haka sai kace wata jahila? Kishi hauka ne wai?.
Farida dai Bata ce mata ko uffan ba tana Rungume da Sulaiman Wanda yayi bacci a jikin ta Shima Salman din Da yaji irin zagin da Basma Basma take mishi sai ya lafe a jikin Farida don ya San Basma Bata musu da kyau.
Matashin ya shigo sashin Yana Sanye da Rigar t shirt da wando tree qwater kanshi dauke da Suma Mai kama da shekar ungulu sai Kuma katon gilashin idon shi wanda ya Kuma mamaye fiye da Rabin fuskar shi.
Ya duka Yana gaishe da Matan da suke cikin falon Yana gaisuwa suka amsa inda Basma ta Dube shi tana Fadin
“Kwairo Yaya Aiki ya kammala Kuwa?.
“Kwarai kuwa Haj ai har an gama tunda kika ce da sauri kike son a Gama ai ba a jima na Rubuta Kuma Babu laifi an saki kid’an yadda kike so ga shi ma a kunna aji idan wannan kid’an baiyi ba za a sake Wani don piano ne yayi daidai da tone din.
Matashin da Basma ta Kira da suna kwairo ya fito da plate na CD ya na mikawa Basma ta karba inda hoton Abdullahi ya bayyana a bayan plate din CD aka Kuma Rubuta sunan shi R l P Abdullahi yakubu.
Basma ta karba tana Ganin hoton CD ta ta aje CD din a Gaban Yaya lami tana Fadin .
“Yaya lami ga plate din wakar da na Saka akayiwa Abdullahi ta mutuwa gashi har an gama Yanzu zan kira gidajen radio Azo a karba a Saka Nan din ma in akayi ADDU AR uku sai a Saka don kowa ya San anyi Rasuwa Wanda Bai sani ba ma zai sani.
Yaya lami ta dubi Basma tana Fad’in.
“Banji me kike fada ba Basma? .
“Waka ce na Cewa kwairo ya rerawa Abdullahi ta mutuwa to gata an kawo in zan Bada ita ne gidajen radio a ke Sakawa Kuma idan anyi ADDU AR UKU nan kofar gida ma sai a Saka.
“Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un wace irin masifa ce wannan ni jaku? Cewar Goggo Amu wacce take Zaune cikin Matan da suke zaman ta aziyya.
Haj kulu wacce take kanwar Uwar su Yaya lami ce itama ta karbe da fad’in.
“Yau mun SHIGA UKU mutuwar ce akewa waka ? Amma kuwa wanna yarinya kin cika tattaciya . Tun da Ake Duniya mamaci da yake Neman ADDU A ke shine kika Saka akayi mishi Waka? To wai tsaya ma ganga aka buga rangal rangal ko kuwa karatun Dala ilu ne ko ishiriniya akeyi acikin wakar?.
“Haba Haj ai koma me Ake fad’a Waka fa tace ba karatu ko ADDU A ba . Shi Wanda ya Riga mu Gidan gaskiya Yana bukatar Wani Abu bayan ADDU A ne da har shaidancin ya Kai da ayiwa mutum wakar mutuwa? Wannan Kam Banga kauna a Nan ba sai ma Raini da matar Abdullahi ke Shirin kawo Mana Waka fa jama a? Muna Nan muna kukan Rashin bawan Allah Nan sai kawai a tayar Mana da kida gidan makoki ya koma gidan Biki ko? Wata Kil ma ita da ta bayar da kwangilar wakar har ta taka Rawa tunda an fara Siyar da imani wa wulakantacciyar Riba ai Kuma shikenan mutuwa ta koma bidi a.
Yaya lami ta share tawagar wasu hawaye a fuskar ta tana Duban Basma .
“To madallah da wannan kokarin an Gode Amma a Ina kike nufin a saka wakar ? Kuma su waye zasu kunna ta? Me ye ma Hikimar fada mini da kikayi? Basma na gama Gane Akwai Wani Abu a Ranki to don Allah hutar da kanki ki Kuma hutar da kowa kawai kiyi Magana zamu fahimce ki. Ke yanzu don Allah in kina da kunya ma har Zaki Dube ni kice kin Saka anyiwa marigayi wakar mutuwa? Me ya Hana da Uban ki ya mutu ki Saka ayi Mishi tashi wakar? An banji Jin Saka anyiwa Uban ki ba bare kice bajintar da kikayiwa Uban ki irin ta ce kika karanta wa Mijin ki Wallahi Basma ki kiyaye ni don Wallahi na Soma fahimtar akwai wani Abu a Ranki da kike rara gefen fada. In ba kin mayar Damu yan iska ba ayi Mana mutuwa Amma kina fadin kin Saka ayiwa mamaci Waka? To ki bari Uwar ki tw mutu ba Waka ba in kika tayar da gad’a ma duka Daya wannan lalurar ki ce.
“A a Yaya lami daga magana sai cibi ya zama K’ari k’ari Kuma ya zama K’ababa? Mutuwa dai anyi ta Wanda ya mutu Kuma ba Dawowa zaiyi ba Duniya zata tashi ne don Wani mutum guda ya barta ? Ina ce iyayen wasu ne da yawa suka mutu kafin shi? Ai in kinji mutum ma Yana tsoron mutuwa to Bai aikata Alheri ba bare Abdullahi da ba wani Adalci yayi min ba ai ku da kanku Dole kuyi kukan mutuwar sa tunda Kun san Yana can b’arin jiki a shanye tunda ke da kanki kin San mutumin Nan Baiyi mini Wani Adalci da zai samu sassauci a kiyama ba. To Kuma don na Saka anyi mishi Waka shine Wani JANHURU? Ai in mutum ya aikata Alheri ADDU AR mutane da Cece kucen su Daya yake da irin Aikin da ya aika . Don Abun iya kudin ka ne iya shagalin ka.
“Auho In na fahimce ki Saboda Abdullahi baiyi Miki Adalci ba shine kike mishi wannan bak’ar fatan ta sakawa ayi Mishi kida bayan mutuwa? Anya kuwa Basma Lamarin ki akwai gaskiya? Ni fa har yanzu Wallahi Banga alhini ko jimami a Lamarin ki ba tunda har kika samu zarafin zagin yaron Nan Salman don kawai ya yi begen Uban da ya Rasa Wanda Mai Imani ne kawai zai tausaya mishi saboda sanin Nisan tazarar da suka Samu. .
“Nifa Yaya lami koma me Zaki fassara ni ai na Isa zama komai ma tunda ni Allah ya Saka min imanin sanin samu da Rashi duka na Allah NE Kuma ba zanyi wannan jahilcin ba Kuma shi Wanda yayi Waka ai Dole a sallame shi tunda yayi Aikin shi .
“Sai ki biya shi tunda ke kika Saka shi jahilci Kuma da kika kira Mana Basma ai kin San inda jahilci yayi Aure ya tare mu .
“Lami Rabu da yarinyar Nan kar ki sake tanka Mata tunda ta fito ta nuna Mana kowacece ita Allah yayiwa Abdullahi Rahama da gafara dama ance mutuwa Mai tonon Asiri gashi kuwa yau saboda Babu idon Abdullahi yarinyar Nan tana wulakanci Mai kalar Ruwan Omo ni kulu. Sai Haj kulu ta Kuma Saka kuka tana Fadin
“Wallahi ban tana zaton yarinyar Nan da wannan mugun Halin ba Amma Babu komai Duniya ce Wanda Bai shigo cikin ta ba ma tana Jiran shi Allah ya shafe k’asa goshin ka Abdullahi .
“To Haj Baku son gaskiya dai Amma ni a magana ta Ina aibu saboda Allah? In Baku son wakar Nan Haj sai a Hak’ura dama ni na Saka shi in ma ba za a biya shi kudin wakar shi ba a bashi cikin tumunin takaba ta ai Ina da hakkin Hakan.
Goggo Amu ce ta fusata tana Fadin
“Ni Kam tashi Zanyi na tafi gidan su yarinyar Nan na kiro Uwar ta wannan Rashin Darajar ya Isa Nan fa gidan makoki ne ba gidan Biki ba. Dubi yadda ta watsar da carbin hannun ta tana Rashin kirki Mai takaba da ba a son Jin Komai a bakin sa Banda Ambaton sunan ALLAH Amma dubi yarinyar Nan idon ta tarrr tana zayyana to Banga za a kwashe da marar Arziki da yarinyar Nan ba gara kawai na kiro Uwar ta in ta Isa da ita tazo ta fada Mata .
“To Goggo ayi Hakan kawai tunda dama ana jiran a mutu a bankada ni mutum Bai Isa ya Fadi gaskiya a yarda ba?.
Goggo ta Mike tana Duban matashin Nan mai suna kwairo tana Fadin.
“Kai yaro tashi ka kama gaban ka Bama bukatar wata Waka Kai in Uwar ka ko Uban ka ne ya kwanta dama zaka Yi mishi wakar mutuwa? Ko da yake ba laifin ka bane Saka ka Akayi.
“Yi Zaman ki Amu tayi duk irin Rashin mutuncin da taga dama Waka Kuma ta sallami yaro ko Kuma ta ajiye idan Uwar ta kwanta Dama sai a rera Mata.
Cewar Haj kulu.
Farida dai tana kallon ikon Allah Bata iya tofawa ba inda Basma tace da kwairo ya Bata account din sa zata Saka mishi kud’in shi don in Amarya Bata hau Doki ba to fa Babu Mai Dora Mata Kaya Dole ne a bashi kudin shi wakar shi.
Kwairo yayi musu sallama ya wuce Matan da suke zaman makoki sukayi ta maganganu akan Basma da Bata iya kame Bakin ta tayi Shiru ba. Banda Yaya lami tayi ta kawar da Kai wata Kil da sai an dambace Amma su Haj kulu da Goggo Amu suna tausar Yaya lami ta Kuma kawar da kanta ta kyale Basma.
Kukan Sulaiman kam akan Kira Mishi Daddy yaki Jin Rarrashi inda su Haj da Yaya lami suke ta Rarrashi Amma yaki Shiru Abinda ya Kuma fusata Basma wacce tace.
“Ni Kam kukan Nan ya ishe ni Wallahi don Allah ko Uwar yaron Nan zata koma sashin ta ni dai bana son kuka Yaya lami dama ke kika ce ta zo to don Allah ta koma wurin ta taji da Ya’yan ta .
“Ai Basma wannan yaron da kike Gani Yana iya cin kason Nan sashin naki da na Uwar sa shi kadai gara ki koyi sakawa bakin ki linzami don shine Mai fidda ki a gidan Nan ba ke ba so be careful ki ke lallaba su kina Basu girman su don kaso takwas suke da shi ke kina da Biyu Kinga kuwa kece Mai fita a nan ki bar musu Gidan su .
“Heeeey Kai subuhanallahi sannu Yaya lami a Ina za ayi Hakan? Ai da dai bamu San Asalin ungulu ba sai tace Mana daga masar ta fito . To ayi Hakan ma kawai .
Farida ta Mike tana Fadin
“Yaya lami kuyi Hak’uri zan koma sashi na idan babu damuwa don ni Kam ba ta Wani Abu nake ba Wallahi sai ta Rashin Abdullahi idan Basma taso ma don Allah ta hada har da su Salman da Sulaiman ta gaje ni Mai Abun nake so ba Dukiyar da ya tara ya bari ba . Shima da ya Tara Dukiyar yanzu Yana Ina bare magadan ta? Wallahi Yaya lami ban yarda da matar Nan ba matukar dai ba haukacewa mutuwar Abdullahi ta ja Mata ba to Akwai Wani Abu da In an bi sawu za a Gani gidan makoki Amma tana cika wannan bakin?.
Basma ta Mike a fusace .
“Ni kike cewa mahaukaciyar? To Naji na haukace Zaki Kuma tabbatar wa kanki da na haukace. Kin Kuma Yi dabara Wallahi idan kika ce kin barwa Najwa da Nabeela Dukiyar su Dama tasu ce in kikayi Hakan Kam kin Zauna lafiya Amma ba Zaki taba tabbatar da hauka na ba sai kin ce gadon Ya’yan ki kike so a Nan kam Zaki yarda hauka nake Amma a yanzu ai sharar fage nake Farida muci gaba da istigifari Kawai.
“Farida kar ki Kuma biye Mata koma kiyi zaman ki ai kinyi Mai Wahalar ma tunda kika gane tabu’war kanta Babu mamaki zafin mutuwar nan ne ya fidda ita a saiti. Cewar Goggo Amu.
Lawisa da ta samu Labarin mutuwar Abdullahi Hankalin ta yayi matukar tashi ta iso gidan makokin inda ta iske Basma Sanye da hijabi da doguwar carbi Amma reaction din ta kawai ya Isa bayar da ita sai ma Rashin kirki da take ta tatawa tsakanin ta da su Yaya lami inda take Ganin kokarin Basma na yin wannan abun.
A Ranar da akayi ADDU AR uku a Ranar ne Kuma Basma tace tana son a tattaro Dukkan Dukiyar Abdullahi Kuma kowa ya kawo Abinda yake wurin sa. Baba isuhu ne take fadawa hakan a lokacin da ya shigo cikin Gidan Yana Rungume da yaran Abdullahi Najwa da Nabeela sai Salman da Sulaiman ita Kuma tace a tattare komai nashi don a kwai takardun wasu kaddarorin a wurin ta Kuma ta San Akwai wasu wurin Farida.
“To Hakan yayi Amma saurin me Ake ne Basma ? Ina ganin a bari wannan Abokin nashi garba Abubakar da yake can Saudi Arabia ya dawo shi ya San wasu abubuwan da yawa daga taskar Abdullahi Kuma Akwai Yaran shi na shago Suma duk za a hada su su bayar da komai ne sai a Kasa muku ko Babu komai an sauke mishi Nauyi tunda barin Dukiyar mamaci ba a rabawa magadan sa ba nauyi ne Mai yawa Ake barin sa da shi a makwancin sa .
“A a Baba isuhu gara kawai a tattara komai mu San Abinda yake Akwai k’asa Ina tsoron a kwashe komai tunda Babu tsoron Allah sai Abinda aka ga Damar bayar wa ni Kam zanso a tattara komai ta haka ne zamu San da zaman komai.
.
“To haka ne Amma ayi Hak’uri har garba Abubakar ya dawo Basma in Kuma Kuna da matsala ki sanar dani In Sha Allah zanyi muku maganin ta.
Yaya lami ta zuba Uban tagumi yayin da Goggo Amu da Haj kulu suka Yi jugun jugum suna Mamakin Basma da Bak’in Halin ta tamkar Mai Jiran mutuwar Abdullahi ta fito da Halin ta sarari.