Al’Amarin mutuwar Abdullahi sai ya Dawowa Farida sabo gal musamman wannan Rashin kirkin da tayiwa su Baba isuhu da Yaya lami Saboda Gadon da Babu tabbacin amfana daga gareshi tunda Wanda ya Tara Dukiyar ma yau Ina yake? Ya barta duk da shi yafi kowa Sanin Wahalar da yayi kafin ya same ta Amma gata ya barta Babu shawara Babu SANARWA.
Hawaye ya Soma wanke Mata fuska tana hango Nisan tazarar da DUNIYA ta shata tsakanin ta da Abdullahi.
Kukan Sulaiman ne ya sa ta juyowa inda taga yaron Yana kokarin dauko Katon hoton Abdullahi da yake KUSURWAR D’akin.
Kuka yake Yana son jawo hoton Yana Fadin
“Mami Daddy zanje . Ni daddy zanje.
Ta Mike ta nufe shi don taga yana Shirin Figo hoton duk da yafi k’arfin sa Amma bege irin na yaro ga Uban sa Uban da ya Rasa Wanda sai fa a kiyama shi da Uban Amma gashi Yana Jan taswirar sa tamkar in ya dauko hoton zaiyi nasarar taso shi daga makwancin da ba ma a Nigeria yake ba.
Ta kama Hannun shi da nufin ta mayar da hoton shi Kuma tayi mishi Hikima Amma ya Soma kokarin kwacewa Yana fadin.
“Daddy zanje ni Daddy zanje.
Hawayen ta ya Kuma tsinkewa ta mayar da hoton ta kife don in ta tabbata idan Yana ganin fuskar Uban sa ba zai taba mantawa da shi ba.
Ta Rungume yaron Wanda yake kuka da gaske tana Rarrashi.
“Yi Hak’uri Sulaiman mutuwa batayi Maka wannan hanzarin ba ta shata muku layi da Daddy sai dai ka kalli hoton sa irin haka ko Kuma ka kama Wani nashi a matsayin Daddy.
Tamkar Yana fahimtar abinda take fad’a ya kasa Yin shuru sai kuka yake Yana kankame da ita tana Zubar da nata hawayen Wanda ya zama biyu ko ma uku don a Yanzu kam tausayin yaron take don ma Dan Uwan shi na debe mishi kewa da wasanni shiyasa Bata so Salman yayi bacci ya barta da Sulaiman shine kawai ke dauke mishi kewa da bege.
Basma ta Ratso sashin na Farida inda take Jin kukan Sulaiman Wanda ya koma cewa indomi yake so.
Farida ta Mike da nufin shiga kitchen dafawa Sulaiman indomi sai ga Basma ta shigo fuskar ta a hade tamkar Zata kama da wuta.
“Mami Nima zanci indomi.
Ta tsinci muryar Salman Wanda ya tashi daga bacci yaji Sulaiman Yana kukan indomi.
Basma ta zauna a kan kujera tana Wani shakar hanci tamkar wacce ke jiyo wari.
Salman ya kama Hannun Sulaiman Suka fice waje ya Rage daga Farida sai Basma a falon. .
“Farida kina zaton kudin da su baba isuhu suka dauka suka Baki a cikin Dukiyar marayun Nan kika Saka Hannu kika karba saboda Rashin tsoron Allah kina zaton zan yarda ne? To Wallahi ko ita Yaya lamin sai ta mayar min da kud’in Nan. Idan fa da can na yarda na zuba ido anyi min danne hakki a yanzu baga Uban da ya Isa yayi Hakan ba. Don haka shawara ce Nazo Baki ba Wai Umarni ba Ina so mu fahimci juna ni da ke Ina fatan Zaki Saka nutsuwa ki fahimce ni? Yanzu saboda Rashin tsoron Allah an Dauki kudi an Baki wai kyauta ce yayi tun Yana Raye Basu Daga cikin Kayan gado nawa kud’in kujera ne a jirgin yawo? Ina ce sun Kai milyon biyar an Baki na mutum Biyu ke daya sai Kuma an zo kason gado Kuma ace Ya’yan ki Maza ne kason su ya linka nawa ni Ya’ya na Miata ne ke zaki yarda ayi Hakan ne idan kece? Tun a yanzu ba a zo kan Rabo na kin tashi da da milyon kusan goma ga Yaya lami itama wai an Bata milyon Biyar? To ita kuma a Uban wa aka Bata su? To duk ma ba wannan ba Ya’ya Biyu gareki Ya’ya Biyu gareni har an fara cewa ke Mai Ya’ya Maza kece da Gida ni Kuma da nake da Mata an soma cuta ta to ban shirya yarda ba Wallahi da Baba isuhu da Yaya lami Dole na Kai Yan iska kotu kema sai kin fiddo kudin da aka Baki Kuma Ina son ki sani matukar kina son rufuwar Asirin ki to dole sai dai ki Zaba Daya tsakanin Sulaiman da Salman don Dole ne ma ya zamo ni da ke Kai Daya ba zan bari a Raba gadon Nan da duka Ya’yan ki Biyu ba sai dai ki San yadda Zakiyi da Daya don k’in yarda da hakan shine zai Saka ni na tona Sirrin boye don haka zabi Daya tsakanin Sulaiman da Salman In yaso ni Ina da Hikima wacce zata shafe Komai.
Farida ta Dube ta a watse tana Fadin
“Ban Gane in zabi Daya tsakanin Sulaiman da Salman ba? Wai Basma a me kike daukar DUNIYA? Saboda Gadon Abdullahi ne ya sa kike zagin Baba isuhu da Yaya lami? To fada min yadda kike nufi tsakanin Salman da Sulaiman na kasa Gane zabin da kike magana.
Basma ta fito da maganin Bera Dan china ta farke tana zazzagawa Saman farar shinkafar da tazo da ita wacce taji kayan lambu ga Miya Mai Rai da motsi har da kifi . Sai ga guba Basma ta bad’e Abincin Nan da shi ta ajiye a gaban Farida wacce take kallon ta irin kallon da akeyiwa TV lokacin da suke nuna abin Mamaki.
“Abunda nake nufi shine Salman ko Sulaiman Wani yaci Abincin Nan Kinga da ya mutu gadon yaran Nan ya Kara yawa za ace danki Daya ne Kinga ni da ke Kai Daya za a Raba tunda kunce Namiji Daya kason mace Biyu yake dauka. Kinga in ya Rage Daya kwal Babu sauran Wani fin da Zakiyi mini.
Farida ta dagawa Basma hannu tana Fadin
“Amma Basma a wace makaranta kikayi karatu ne in ma kinyi din? Baki San Cewa a yanzu ko su Duka Suka mutu sai an bani kason su ba tunda Uban su ya Riga su mutuwa ba? To kalas ki hutar da kanki tunda har kika iya zuba gubar Nan da nufin bawa Salman ko Sulaiman Wallahi tallahi na Rantse Miki da Allah ko Ciwon Yaran nan Sukayi sai na tuhume ki . A kan ido na kike wannan ikirarin na kashe min yaro saboda daudar Duniya? To ba kotu ba Basma ki tafi k’oli ki Kai k’arar mu kowace irin kotu ce mun Isa mu karbi haddin Shari a .
“To Alhamdulillah tunda ma Kun Isa ku karbi haddin Shari a ai ta kwana gidan sauki Kuma kin fahimta ta da kikayi Ina ganin kamar kece Baki sani ba Amma ni Asirin ki nayi nufin Rufawa don haka Karbi hotunan Nan ki duba wata Kil ki samu Wani makamin Rik’ewa.
Ta dorawa Farida hotunan Wanda ta yi Maza ta cabe tana Kai idon ta akan hotunan.
Ta waro ido jiki na Mata b’ari ta Soma Duba su Daya bayan Daya har ta k’are kallon su ta mayar da Kallon ta ga Basma wacce take murmushin mugunta kafin ta ce.
“Ai na San kin Tuna ko? To in ma akwai Abinda ya shige Miki Duhu ki tambaye ni zan haska Miki shi Kuma ki saurari Kira.
Basma ta Mike ta fice Rike da Abincin da ta bardawa guba tana murmushi.
Zufa ta Soma wanke fuskar Farida tana Rik’e da hotunan ta kasa motsi bata taba nadamar sanin sameer ba sai a yau.
Ta Mike da sauri Saboda Jin k’arar kukan Salman ta fita da sauri inda ta ganshi shi kad’ai .
“Ina Sulaiman din yake Salman?
Yaron ya juyo da gudu Yana Fadin
“Maman su Najwa ce ta tafi dashi zata bashi indomi.
Da Wani irin matsiyacin firgici ta nufi shashin Basma ta afka Babu ko sallama inda ta hango Sulaiman akan kujera Basma na Rik’e da flat wanda ta aje a gaban shi Wanda yake dauke da taliyar Indomi har da dafaffen kwai a sama yayin da Basma ke zazzaga sauran gubar nan ta gawa Dubu.
Da Wani irin sauri tayi tafiyar Ruwa Ganin Sulaiman Yana Shirin Kai taliyar da ya Debo da Hannun sa Yana Shirin kaiwa Baki .
Gaba Daya taliyar da plat din suka dire akan jikin Basma wacce Bata San Farida ta shigo ba sai ji tayi anyi tafiyar Ruwa da ita.
Sulaiman ya fasa kuka Jin an tankade hannun sa da taliyar da yake mayata .
Farida ta Cabo Sulaiman ta Rik’e tana Duban Basma fuskar ta murtuk .
“A me kike nufin Yi min haka na kashe mini yaro? Wai Basma Dole sai kin shiga Rayuwa ta ne da karfin tsiya? To ko kin shiga sai kin fita wallahi don nayi miki nisa a komai babu kuma ranar da zaki taddo ni bare ki zama kamar ni. Ki kashe mun yaro saboda kin maida ni yar iska? Ba zan yarda da wannan wulakancin ba Wallahi Basma baki Isa ki Saka ni barin Gidan Nan ban shirya ba Kuma idan ke Sharri kika iya to don Allah ki Jira ki Gani.
Ta fice sashin tana Rik’e da Sulaiman Wanda yake kuka shi indomi zaici.
Suna SHIGA sashin ta ta Kira garba da baba isuhu ta fada masu Abinda Basma tayiwa Sulaiman.
Baba isuhu ne ya Fara isowa suka nufi sashin Basma inda Farida ta nuna Mishi taliyar da Abinda ta Gani tana Zubawa na maganin Bera Dan china Shima duk baba isuhu ya Gani.
Ya Dubi Basma Yana Fadin
“Yanzu Basma har Zaki iya bawa wannan Dan yaron guba Saboda kawai ki gaji Abinda Babu tabbas akan shi ? Kisa? Lamarin ya zama ta addanci kuma To wannan maganar ba wacce za a kyale bace Dole hukuma ta shiga ciki tayi muku iyaka don ko ni naji wani Abu ya samu yaran nan kece wallahi.
Garba ya iso ya samu Labarin Abinda Basma tayi Wanda Bata karyata ba Shima yace Dole hukuma ta Sani don ko Gaba idan Wani Abu ya samu yaron itace abin tuhuma .
Tuni kuwa Kabir Dan gidan baba isuhu ya Kai rahoton wannan maganar a hukuma aka zo har Gida Kuma aka Samu taliyar da aka Zubawa guba tare da takardar gubar aka dauki komai aka bawa Farida copying takarda Daya akayi musu iyaka da basma aka wuce Nan
Ranar wata juma a bayan an sauko masallacin juma baba isuhu ya samu bakuncin dan Aiken kotu Wanda aka Aiko kawo sammaci ya Kuma fadawa baba isuhu cewa Ranar litinin Ake son Ganin shi a kotu tare da lami da Farida.
Baba isuhu ya fadawa lami an kawo mishi takardar sammaci ya Kuma San daga basma take don haka Ranar litinin zai je yaji Abinda take nufi .
Yaya lami tace
“Ni Kam da ka kyale yarinyar Nan tayi ta karar gado dai Allah NE da Kansa ya Raba shi duk hauka take Abinda Bata so ne zai faru .
“Barta lami Allah ya Kaimu Ranar ni zanje naji Abinda kenan in bukatar ganin Wanin ku ke da Farida ya taso zanyi muku magana.
Amadu ne Yayan Farida ya iso gidan nata Saboda Jin Abinda Basma tayiwa Sulaiman na bashi gawa Dubu. Amadu shine yake biwa Gali sannan Farida sai mukhtar. Mutum ne Dan te kife da son ayi ta balaki shiyasa ya iso Gidan Kai tsaye ya zarce sashin Basma wacce take Zaune taga Gali ya shigo.
“Kai lafiya ka shigo min Gida ko sata kazo Yi min?.
Ya Dube ta Yana Fadin
“Kinga nayi Miki kama da barawo ne? Kashe di nazo Yi Miki ai kin San wannan Abun ko?.
Ya fada Yana aje Mata askar zabira tayi maza taja Baya a tsorace.
“Sunana amadu Yayan Farida ne wacce kika so kashewa yaro. Ashe ke da sauran Imani a tare da ke ma tunda har Baki iya kisan WUKA ba sai na guba. ? To ni ne Zanyi Miki kisan Rashin Daraja Wallahi Idan Baki fidda kanki daga sabgar Farida ba Allah yasa na Kara Jin kince Wani Abu Yasin ta Katanga zan hauro sai dai a wayi gari da GAWAR ki a Rasa Uban da ya kashe ki.
Ya fada Yana ficewa tabi shi da Kallon tsoro.
Ranar litinin da aka shiga kotu baba isuhu ne da Kabir sai garba inda aka karanto k’arar da basma ta shigar ta Cewa an cuce ta an Yi kasafin kudin gadon Ya’yan ta ga yayar mijin ta da Kuma Ya’yan mijin da son ayi musu Rabon gadon a gaban kotu.
Basma da ta dauki lauya lauyan ta ya fito Yana ta zayyana inda alkali ya nemi lauyan Wanda Ake Kara wato baba isuhu yace Bashi da lauya tunda Abinda take Kara ai Akan Dukiyar da mijin ta ya bari ne. Baba isuhu ya Soma karanto biyawa su Salman da Yaya lami kujera da yayi Wanda Farida tace Bata yarda ba hakkin marayu aka shiga sai kuma duka Rabon na da take so ayi shi a Gaban kotu.
Lauyan Basma ya karbe da fad’in
“Ai anyi zalunci ta Yaya za a biyawa wasu Ya’ya ba a biyawa wasu ba? Kuma ita yayar shi tunda ya mutu ai ta San kudi na marayu ne Dole ta mayar Musu da Abinsu.
Alkali ya Dubi Baba isuhu Yana Fadin
“Wasiyya yayi na in ya mutu a biya musu ko kuwa ya biya musu ne Yana Raye?.
Baba isuhu ya fada mishi tun Yana Raye ya biya ba wasiyya yayi ba.
“To wannan kudin tamkar Sadakar da yayi ce ga Wanda Baku sani ba Babu Mai tayar da kyauta sai in ta wasiyya ce wacce zata haddasa husuma irin wannan to ba a cika ta Amma in kyauta ce yayi to ko da Kuwa da Rabin Dukiyar sa ne ya bayu.
Basma bata so hakan Amma tana Ji tana Gani Yaya lami ta Sha da kudin ta haka Salman da Sulaiman ma suka tashi da nasu kason inda a take Kuma sai Basma ta kitsa Wani MAKIRCI na Cewa ai Abdullahi ya ce ya barwa Najwa da Nabeela duka Gidan shi Mai sashi uku wai don kasancewar su mata Wanda za a zarta gado itama don Gudun husuma ne Bata furta ba Amma tunda an tabbatar wa su Salman da Nasu kyauta Suma su Najwa alkali ya tabbatar musu da tasu.
“Akwai Rubutacciyar takardar da kukayi haka? Ko kuwa akwai shaidu Wanda Suka tabbatar da Hakan? Tayi Maza tace akwai takarda har ma da shaida.
“To ki kawo ta Ranar Sha takwas ga wata Kuma Rabon gadon Ya’yan ku sai kowa ya hallara kina iya kawo wakilin ki itama abokiyar zaman ki ta kasance da Nata wakilin in yaso sai kuzo da komai a Raba muku In Kuma Kun yarda da wannan dattijon Shima Yana iya kasafa muku tunda shi gado Allah da Kansa ya Raba shi Abinda ke kawo shi kotu dama Gudun husuma.
“A a Allah ya gafarta malam shi wannan ba Zaiyi min Adalci bane don suna maganar Ya’yan ta Alhalin Kuma Ya’yan kishiya ta ba na marigayi bane shiyasa nake so a zo kotu tumunin takaba kawai take da hakkkin samu .
Baba isuhu ya Dubi Basma Yana Fadin
“Sharrin Kuma da zakiyiwa yaran Nan ki shegen ta su? Idan ba Ya’yan ta bane na waye?.
“Ai kuma baba wannnan ba zancen ka bane ka bari sai Ranar da muka hallara ni da ita zan Fadi hakan don ta karyata ni in ta Isa.
Kabir da garba suka cika da Mamakin Basma na furucin ta akan wai Ya’yan Farida ba na marigayi bane .
Da haka kotu ta tashi sai Rana irin ta yau da aka ce basma ta kawo takardar da Abdullahi ya ce ya barwa su Najwa da Nabeela gidan shi Abinda yake ta bawa baba isuhu mamaki na zalamar Basma da son shegen ta su Salman da Sulaiman.
Lauyan da Basma ta dauka suka kebe Yana Fadin
“Sai fa munyi da gaske don Alamun sun Nuna ba zamu Kai yadda muke so ba tunda sun fimu hujja .
“Ko da hujjar su barrister sai sun Fadi Wallahi Kai dai ka jajirce ka lauya min magana don Wallahi sai na keta Mutanen Nan Kuma sai su Najwa sunci gidan can Dolen Farida ta bar Gidan Nan.
“Yanzu tsaya Maganar gidan Nan da gaske ne ko kuwa itama tana bukatar mu Zauna ayi Mata gyara?.
“Babu ita manuba ce kawai sai ka Rubuta min In ya so na samo shaidu .
Ai kuwa aka Soma Rubutu wanda Barrister yayi da Hikimar shi inda a shaidu Basma ta Bada sunan lawisa da kuma Wani tsohon Mai gadin da suka taba Yi Wanda ya aje Aikin gadi ya koma buga buga mai suna jafaru sai Kuma kanwar ta labuda.
Akayi Rubutu aka gama tare da kwanan wata har da Saka hannun shaidu aka linke aka bawa Basma Saka jaka Sukayi sallama da barrister ta wuce gida tana Kiran labuda da Kuma Neman layin jafaru don ta gayyace su kotu zuwa bayar da shaidar zurr Amma Kuma Abinda Bata sani ba shine TANA K’ASA TANA K’ASA