Skip to content
Part 63 of 66 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Basma tayi taga taga zata kife saboda ganin Bak’on nata Wanda firgici da tsoro suka diro Mata a lokaci Daya Amma tayi jarumtar dafe bango ta tsaya kyam akan kafafun ta Amma Kam Bata Daina karkarwa ba.

“Mamman?

Ta Fadi sunan can a k’asan makoshin ta shi Kuma Yayi murmushi Yana shafa fuskar shi da ya Tara gashi biya biya wacce ba a Samu zarafin gyarawa ba.

“Mu SHIGA daga ciki Mana ni fa gaisuwar mijin ki Nazo Yi Miki can nake samun LABARIN Rasuwar sa shine na taho Yi Miki gaisuwa.

Taja baya don yadda ya taho Kai tsaye ya kuma shige ciki Dole ta mara Mishi Baya tamkar ya San sashin sai gashi turyan turyan ya zurce har falon inda Najwa da Nabeela suke zaune Amma Najwa na ganin ya shigo ta kwala ihu tana runtumawa a guje don har ga Allah tsoro yake Bata ita Kam mahaukaci ta Gani.

Mamman ya juyo Yana Duban Basma wacce da jikin ta yake a Sanyaye.

“Wai wannan ba Najwa bace ba Basma ? .

“Itace Mana.

“Kuma take tsoro na? Ce min tayi fa mahaukaci Amma dubi yadda Nabeela ta girmama ni har da kawo mini Abinci da Ruwa? Kai Allah ya tsinewa talauci Wallahi har na zama Abinda za a Kira ni da mahaukaci saboda kawai Babu ta same ni ?.

Ya zauna akan kujera Nabeela tana kallon shi ita Kam Bata ji tana tsoron shi ba sai ma Wani Abu da ya zama na mamaki Wani irin kallo take mishi irin na Wanda ta Sani ko Wanda ta tab’a mu amula Dashi.

Nabeela ta tashi ta nufi Uwar D’akin da Najwa ta shige tana boye kanta inda suka jiyo Nabeela na Cewa Najwa.

“Ke Wallahi ba mahaukaci bane Najwa bakiji Yana magana lafiya Lau ba? Kawai dai Kila ba shi da kudi ne Shiyasa baya wanka da gayu.

Basma ta dubi mamman tana kare mishi kallo kafin tace

“Yaushe ka dawo garin Nan mamman?.

Ya dauki kular da take Kam dining table Yana Budewa yaga abinci har da Naman kaji ya Soma danna Naman a Baki har Yana taune K’ashin ya hadiye kafin ya jawo Wani Naman Yana Fadin.

“Yaushe Rabo na da katsina ai Wani jagwal na bari Wanda katsina tafi k’arfin shigowa ta ko zan shigo sai da badda sawu ai har da kamar da yarinyar Nan ta Gani a tare Dani ne na Rufe fuska da takunkumin Baki ne yasa take Min kallon mahaukaci Bata san Cewa sai da Hakan zan iya yawo a garin Nan ba ana Gane na shigo Yanzu ne LABARIN zai sauya.

Yana fada Yana danna Naman kaza a Baki har sai da ya lashe shi tas har da alkubus din ciki ya koma sud’e yatsun tamkar zai fince su saboda sud’ar da yake musu.

“Ya muka ji da Hak’uri Kuma ? To Allah ya sa ya huta ya jikan dukkan musulmi.

Basma ta Amsa da Ameen Ameen.

“Kin San Halin da nake ciki kuwa Yanzu Basma ? An fa Kore ni Daga Aikin Dan sandan Nan Saboda hada Kai da akayi Dani na yin wata safarar miyagun kwayoyi ana bani Wani Abu to Allah da ikon shi Asiri ya Tonu shine aka sallame ni Aiki tun daga wannan kora da Akayi Mini sai Rayuwa ta sauya mini sai Kuma ga Wani ibtila I ya fada min Dole dai na bar garin katsina nayi hijira Zuwa shagamu daga can ne Kuma nayi ilesha to a yanzu fa ilesha nake da zama kafin Nan din ma na kasaye ta na Kara Gaba.

“Amma banji Dadin Hakan ba mamman Ashe har Yanzu ba zaka nemi zaman lafiya ba?.

Ya Dube ta Yana kara sud’e yatsun shi Yana Fadin

“Yo wannan Duniyar akwai zama lafiya ne a cikin ta? Ai zaman lafiya Kam sai ka tserewa talauci Amma matukar baka tserewa talauci ba ai Kuma kunyi Hannun Riga da shi sai dai kame kame. Dan bani lemu Mai sanyi na kora .

Ta Mike ta nufi fridge din falon ya bita da kallo irin kallon Nan na mayata da son tankawa .

Ta dauko mishi lemun Roba na coca cola ta kawo mishi ya karba ya fige murfin ya kafa Baki Bai aje ba sai da yaji Babu Komai ya dire Yana sakin gyatsa gwahhh.

Ya zauna ya Mike kafa wacce ya dora akan center table Yana Kara kallon falon Yana Fadin.

“Kai gaskiya Mai gidan Nan Yana da kud’i Kinga Wanda ya zauna lafiya nan Domin kuwa yayi Hannun Riga da talauci Naga Duk yayi Gyaran da ban San su a da can ba. Wai meye ma sana ar shi?

Ya fada Yana kallon Basma ta bashi amsa da Cewa

“Canji yakeyi .

“Kai Eh lallai Dole ya samu kudi ai Yan canjin Nan suna samun kud’i kamar hakin daji Nima ai na dan tab’a harkar Nan a Legos can WAFA na samu kudi Wallahi Amma da yake garin banza a farau faraun banza yake karewa duk Mata Suka cinye kudin sai yanzu nake Jin haushin da na Adana kudi na da yanzu talauci Bai Isa yayi min barazanar k’are dangi ba koma yayi min barazanar Rayuwa da barin Duniya ko Babu Shiri ai ALLAH ya tsinewa talauci sau D’ari da Hamsin.

Basma da ta k’agara ya tashi Amma ya tsaya sai zayyana yake Mata.

“Har yanzu ke kadai ce ko Kuwa ya Auro wata Matar?.

“Yayi Aure itama har ta Haihu.

“Yaya an Raba muku gado ne ko kuwa ba ayi Rabon ba?.

“Ba ayi ba Saboda matar shi ta ce tana da ciki Dole sai ta Haihu za ayi Rabon.

“Masha Allah Amma kinyi Yar wata Hikima dai ko ? Don in ba Hikima kikayi ba za a fiki samun gado Mai yawa Amma kafin Azo kan Tara Dukiyar kiyi Hikimar kwashe fiye da Rabi na dukiyar ta yadda ko Bata fiki Samun kaso ba ki zamo babbar da kika Riga ta zuwa sai da hikima ai Abun.

“Ai ta ma fini samun kaso mamman Domin kuwa Ya’yan ta Biyu itama Kuma duk Maza kaga kaso takwas take da shi ni kuma Ina da Biyu bare kuma ga ciki tana da shi ko mace ta Haifa dai a sama take nice a k’asa bare Kuma ta haifi Namiji.

“To yanzu ke Baki San komai akan Dukiyar tashi bane?.

“Tana can dangin shi sun kammale komai suna Jiran sai ta haihu ayi kasafin gadon.

“To ke Kuma Baki nemi yin sama da fad’in wasu abubuwan daga cikin kayan da ya mallaka ba tunda ma har kin Gane ba wata tsiya Zaki tashi dashi ba sai kaso Biyu a cikin goma? Wata Hikima Zakiyi ki kwaci Abinda kika kwata tunda har kin Gane kece a k’asa Abinda Zakiyi kawai ki samu wasu kaddarorin sa ki kad’a shegu kasuwa tun kafin a zo Rabon gadon ko Kuma Bayan an gama sai kawai ki Dafe kud’in ki ki samfe can ki bar su da Allah ne yayi abin in ma kin shirya ni zan Nemo Miki Wanda za ayi black market din har a gama don ni na duk na San Yan Rigimar da zasu iya Shiga ayi kasuwar a gama tunda abin duk dauki Dora ne .

Basma ta Dube shi tana Fadin

“Kaga kuwa Wallahi ka bani shawara mamman kaga dama sashi UKU ne a gidan kaga sai na sayar da su na karbe kudi na Kuma na San wasu kaddarorin Nashi duk da dai takardun suna banki in ba yaron shi na shago ba Dan gidan Dan Uwan Uban shi shine kawai yake da ikon dauko su a Banki .

“Kar wannan ya Dame ki ke dai kawai ki bari zan Nemo Wanda zai siya ko Babu takardu ai wannan tsohon yayi ne ace ba za a siyi Abu ba sai da takarda duk karya ce ko kuma Rashin Sanin ta kan tsiyar .

“An gama Dama tun ba ayi Nisa ba an fara danne mini hakki da bawa Yara wasu kudi wai kyauta ce kaga Nima na samu hanyar da zan Rama.

“Wai tsaya yanzu anyi wata nawa da Rasuwar?

Ya tambaye Basma wacce tace wata uku Babu kad’an.

“To ki nuna min inda kaddarorin Nashi suke ni zan shiga gaba ayi komai tunda dama da wata Magana Nazo na San Kuma zata faranta Miki idan gaisuwa nazo Miki da Kuma Albishir din na dawo a yanzu idan kika fita ta takaba muyi Aure don ki Saka ni a layin manema tunda dama akwai tsohon alkawari.

Basma ta Dube shi tana Fadin

“Mu bar wannan maganar mamman don nasan Abinda ya Saka ka yin ta saboda kana ganin zan samu kudin gado . Yanzu fa kake fada min katsina Bata shiguwa gareka sai ka badda sawu.

“A a ki dai ce saboda Kinga yanzu bana kama kudi to har gobe Ina Nan a yadda kika Sanni wurin yiwa mace asara Kuma zan SHIGA na fita na Samu kudin bawa mace matukar dai Ina son ta don haka kwantar da hankalin ki ki Kuma Rik’e gadon ki ni ke din kawai nake so Kuma bance kiyi min komai ko ki bani Komai ba don Haka in kika Aure ni ai na zama jigon ki na Kuma zama bangon da Zaki jingina ko Babu komai ga Najwa da Nabeela da Dole na na tsaya musu inda duk Ake tsayawa Uba.

“To Naji Amma kana da wurin ajiye ni idan munyi Auren? .

“Ga Nan Gidan Kuma Ina zamuje?.

“Ai nan din Yana daga Cikin Abinda zan Siyar .

“Sai mu Zauna a cikin kason su Najwa da Nabeela talke tana yiwa Audi Gori ne? .

“Na fa sanka mamman irin sanin da nayiwa yunwar ciki na Amma dai yanzu mu bari matar shi ta haihu in yaso da anyi Rabon sai mu San Abinda zamuyi.

“Kinji Kuma wata wautar in akayi Rabon Kuma ai kin mayar da Aiki baya ai ni tun yanzu nake so kiyi komai ki gama Babu Wanda ya San anyi na ma Fi son ki nuna min inda kaddarorin nasa suke in Akwai gidaje da filaye tun yanzu na fara Nemo Wanda zasu shiga cikin cinikin.

“A a mamman ai ba k’aramin kuskure zan tafka ba idan na nuna maka kaddarorin Nashi tunda kace ba zaka koma ilesha ba to ni da Kaina zan kira ka ka shige min gaba .

“Ke ai Sanin da kikayi min da ba shine a yanzu ba Duniya ta hora ni baki ga duk nayi sanyi ba? Ai Ruwan ya daki babban Zakara Maza sunyi Sanyi.

“Kar ka Damu yanzu ka bani Lokaci ai Dole na neme ka .

“Ok to Yanzu Abinda za ayi na kawowa Wani Dan kasuwar ZINARE Wani tagulla da na Hak’o a ilesha Ban ko tsaya na karbi kudin ba na zarto nan Ara min ko Dubu Hamsin ce naje na aske gashin Nan na sauya Kaya na fito mutum a Sosai don ki Kara Ganin kyau na don nasan yanzu har da wannan biya biyan gashin ne ya sa Bakiyi min marabar kirki ba duk da na San maitar ki akan gashin Nan in na dawo ba Zaki Gane ni ba.

Tamkar wacce ya daurewa Baki ta jawo jakar ta ta fito da Dubu Hamsin ta Mika mishi ya karba Yana kirgawa ya Saka aljihu Yana fad’in.

“Kiyi Abincin dare da ni don zan dawo Nan naci Abinci mu kuma Kara zantawa akan maganar Nan don ma kina cikin zanin takaba ai da har firar soyayya mun Dan tab’a Amma dai time is coming.

Da haka ya fice bayan ya nad’e fuskar shi da rawani tamkar Wani buzu ko marar gaskiya.

Ya bar Basma cike da tunanin hanyar da ya Dora ta ta Kuma gamsu da Hakan shine kawai mafita Abinda dai Bata yarda da shi ba shine ta nunawa mamman muhallin kaddarorin Abdullahi Domin kuwa ta San shi fiye da sanin da tayiwa yunwar cikin ta . Ba k’aramin kuskure zata tafka ba idan mamman ya San mazaunin kaddarar Nan . Kamar yadda ya fada abubuwa da yawa ne akan sa Wanda ko za a kasafta Naman jikin shi ba zai iya Biyan Abinda yake kanshi ba.

Dukkan Hidimar da Ake musu wacce take fitowa daga office din kabir tun Ranar da Abdullahi ya bar Duniya har yau din Babu wacce aka fasa. Komai na bukatar Rayuwa Kabir kam ya zama Dan alkawari duk safiya zai zo ya duba su ya Kuma tambayi Abinda suke bukata Kuma ya kawo musu. Haka ma su Basma da su Salman da Sulaiman hatta da sweet din da Uban su yake Siya musu Kabir ya Rik’e wannan alkawarin don haka ne Kuma kayan bukatun Farida na laulayi suka tsone idon Basma ta ce ana bawa Farida Abinda ya zarce Wanda Ake Basu inda Kabir Kuma ya fada Mata ko ba a cikin kudin Abdullahi ba zai iya yiwa matar Abdullahi Alfarma da kayan Laulayi dai itama ta fadi Abinda take so yake kawo Mata.

Bata kuma tankawa ba Amma dai ba Haka taso ba .

Da dare kuwa sai ga mamman ya dawo cikin wata dakakkiyar shadda yayin da ya gyara fuskar shi ya fito Wani mutum na musamman bare Kuma idon shi da Basma ta duba Wanda ya rambad’a kwalli Al Amarin da ya tilasa Basma Gigicewa akan mamman Wanda yaga yadda Basma ta Soma tarairayar shi tare da kawo mishi Abinci da lemu. Yayi murmushi Yana ayyana Basma tazo Hannu tun Bai furta ba ta bayar da Kai bori ya hau.

Najwa ma da ta ganshi sai ta zuba mishi ido Bata gudu kamar Dazu ba har tana Gaishe shi .

Yayi murmushi Yana Fadin

“Najwa yanzu na zama Mai Hankali ko? Ai Allah ya tsinewa talauci dama Lokacin da kika Ganni ZINARE na kawo na siyar shiyasa kika Ganni dukun dukun amma yanzu har kudi na karba kuzo ga wannan ku siyi Wani Abu don banzo da komai ba.

Ya waro Dubu Ashirin ya bawa Nabeela Yana Fadin

“Ai Nabeela Dole kifi Najwa kaso tunda kin tarbe da mutunci ga Dubu Ashirin ki suyi sweet ke Kuma Najwa ga Dubu goma.

Suka karba Najwa na Fadin

“Wallahi ban Gane ka ba uncle kayi Hak’uri .

“Nifa ba uncle bane Najwa Daddyn ku ne kinji?.

Ta Amsa tana tashi daga gaban shi .

Basma Kam ta zuba mishi ido tana kallon shi cikin Wani irin bege da so tamkar wacce aka tsafe .

Ya juyo yaga yadda ta zuba mishi ido tana kallo yayi murmushi Yana zaro Dubun ta Hamsin Yana Mika Mata.

“Ga kudin ki Yan Mata Nagode ga kuma wannan tunda ban Riko tsara ba ga sauran Kuma ki ajiye min su nan wurin ki don bani da account Kuma ba zanyi ta yawo da su ba Akwai ma sauran da zan karba don tagulla biyar na kawo wannan kudin Daya ne aka bani nace a Rik’e min sauran sai in zan tafi Amma dai yanzu ni Maganar Auren mu ce a Gaba na shiyasa ba zan koma ilesha ba har sai kin fita takaba naga magana tayi karfi tukuna.

“Basma ta karbi rafofin kudin tana zuba su a Jaka har Dubu d’ari UKU da Hamsin inda Kuma taji ta yarda da Abinda ya fada mata na tagullar Gold din da ya zo da su daga ilesha.

Ya Soma auna Abincin a bakin shi Yana tausa Naman Wanda ya jima Basu hadu ba sai da ya share Abincin Nan tas kafin ya Dauki lemun yana kafa Kai ya tuttule ya dire Robar inda ya saki gyatsa Yana Duban Basma wacce ta zuba mishi ido cike da mayata ta yadda akayi Bata iya Gano kwarjinin mamman ba duk da ta San shi fiye da hakan Amma a yanzu Kam yazo Mata da wani irin sauyi na ban mamaki.

Yayi murmushi saboda ya Gane kallon don haka ta cire hular shi yana fad’in

“Kalle ni da kyau more ni na San har gobe Ina Nan da kwarjini na da furgita Mata ni da ke ai 5 ce take dukan 6 me Zaki bani my baby? Ya fad’a Yana kama fuskar ta Suka Zubawa juna ido Yana Mata Wani yaudararen kallo .

Basma Kam ta gama zuwa hannu don haka Yana Kai Bakin shi a nata ta Rik’e fuskar shi suna kissing din juna tamkar wasu mayu haka mamman ya Soma yamutsa Basma wacce tuni Kuma tayi giving up mamman Kuma ya Dora ta sama duk da takabar da take Amma an keta haddin Ubangiji ALLAH Muna neman gafarar ka da yafiyar ka akan Sharrin kawunan mu da wawayen cikin mu ya hayyu ya qayyum.

<< Tana Kasa Tana Dabo 62Tana Kasa Tana Dabo 64 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×