Yana rungume da Farida wacce ta kasa tantance reality da kuma imagination.
Yana sumbatar Bakin ta taji a Ranta Bata yarda da wannan siddabarun ba ta Zame daga Rungumar da yayi Mata ya bita da ido ta fice da sauri daga sashin nata tana mayar da numfashi tamkar wacce tayi Gudun fanfalaki.
Ya shafi gashin gemun shi Yana Raya matar tashi ta tsorata da shi fa kar taje ta cutu.
Ya bi bayan ta inda yaga ta shuga sashin Basma sai ya juyo Salman da Sulaiman suna ta mishi tambayoyi Yana Duban Gadon jariran da yake Rufe da net ya Kuma tabbatar da identical twins din ne a ciki
Ya Isa ga Gadon ya yaye net din Yana dauko Abdurrahaman kyakkyawan yaron Wanda Babu Abinda ya baro nashi tun daga hasken fata Zuwa tsarin jikin shi
Ya Sumbaci bakin yaron Wanda yake baccin sa sadidan cikin cute face baby din sa yayi matukar burge Uban sa Wanda yake Jin Bai kyautawa Uwar sa ba da ya yarda aka ajiye shi a wakafin nan har tayi laulayin ta ita kadai ta gama ta Kuma Sha Wahalar nakudar ta ta Haihu cikin kewa da Alhini.
Ya ajiye Abdurrahaman ya dauko Abdullahi Shima dai sai kayi da gaske ka iya banbance su shi dai Bai iya banbance su ba wannan Kam sai Uwar su.
Yana Rungume da yaran Salman da Sulaiman suna zagaye dashi shi Kuma Yana Rungume da Yan Biyu Yana Raba musu kallo tsakanin Salman da Sulaiman da Kuma Yan Biyun Wanda sunan su kawai ya sani Abdullahi da Abdurrahaman Amma ba zai iya Raba musu sunan su ba.
Da Wani irin firgici Farida ta fada sashin Basma tana Rik’o Yaya lami tana mayar da numfashi.
“Yaya ne Farida? Cewar Yaya lami da tagan ta a firgice.
“Yaya lami zo ki ganshi don Allah Wallahi na haukace Yaya lami don Allah taho ki tab’a min shi kiga shine ko kuwa dai gizon da yake Mini ne?
“Waye Kuma Farida? Yaya lami ta tambaya itama a tsorace.
“Taho Muje Yaya lami don Allah ki taho muje ki ganshi idona ya Soma Nuna min invalid. Ko Kuma na haukace.
Ta figi Hannun Yaya lami wacce ta Kuma Rudewa tana biye da ita tamkar Rakumi da Akala
Suka nufi sashin nata inda Yaya lami taga Wani Abu Mai kama da mafarkin sanyi.
Da sauri Yaya lami taja baya tana Fadin.
“Ya hayyu ya qayyum innahu min Sulaimana wa innahu.
Sai tayi Baya tana ciri tana lahewa Bakin kofa tana leko Abdullahi Wanda yake Rik’e da Abdurrahaman da Abdullahi ga Sulaiman sai surutu yake Mishi Yana Hawa jikin shi Alamar shi Kam Daddy ya Gani ba abin tsoro ba.
“Ke Farida karbe Ya’yan ki kar a Rikita Miki su wannan Kam ba mutum bane.
Abdullahi yayi murmushi Yana Fad’in
“Yaya lami in tsoro kukaji me zai Hana ku ambaci sunan ALLAH ai zai Kore muku Dukkan wata shakka Kuma zai tsare ku daga shaidan da jaye jayen sa.
Sai a Nan Yaya lami ta Soma ADDU AR Neman tsarin ALLAH.
Farida kam sai ta dubi Yaya lami ta Kuma Dube shi Yana Rik’e da twins itama sai ta Soma Jan nata ADDU OIN kafin ta Mika hannu zata Ciro Sulaiman da yake bayan Abdullahi Yana sakala hannun shi a wuyan shi Yana ta surutu.
“A a kyale shi shi Kam ya nuna akwai Jini na a jikin shi Kinga Bai ji Yana shakka ta ba sai ma kusancin da Ubangiji ya Saka Mana Wanda na tabbatar da ko da ya Ganni da farin alawayyo ba zaiji shakka ba zai nufo ni Amma ke da Yaya lami Naga shakka a fuskar Ku Amma Kuma banyi mamaki ba don abin tsoron ne Ni.
Da sauri Yaya lami ta fice Zuwa gidan baba isuhu sai gasu tare sun dawo Farida kam ta Soma kallon Abdullahi da tabbaccin shine ba Wai yadda tunanin ta yake Bata ba don ta auna a mizanin hankalin ta tunda dai ba su Suka wanki GAWAR sa ba bare tace tana da tabbaccin mutuwarsa.
Yaya lami ta shigo ita da baba isuhu inda Abdullahi ya ajiye twins a kan kujera Ya Mike da sauri Yana Fadin.
“Baba sai da Yaya lami ta taso ka ? Ya jawo kujerar Roba ya aje mishi.
“Ai ko ba a taso ni ba Abdullahi Dole zan taso wannan ai abin a duba ne.
Ya zube a Gaban Baba isuhu yana gaishe shi ya Amsa Yana tambayar.
“Kaine kuwa Abdullahi? Kai abin fa da shakka da Kuma tsoro ai lami da Farida ma sunyi jarumta da Basu Tara maka mutane ba.
Yayi murmushi Yana Fadin, “Ai saura kad’an Baba don Yaya lami ma ai Bata yarda ta matso dab dani ba nesa nesa take min.
“Nima fa Nan karfin Hali kawai nake Abdullahi don ban fidda tsammanin zanji kayi WUF da wuya na Nayi maka Rakiyar da ban samu zarafin Yi Maka ita ba Amma dai in har Kai din ne da gaske sai Nace muyiwa juna barka.
Akayi Dariya har da Yaya lami da take dardarce ita da Farida wacce ta koma yiwa Abdullahi kallon Yaya Abin yake?
Abdullahi Yana murmushi yake Fadin
“Ayi Mana Afuwa Baba garba ne da wannan tsarin duk da naga Hikimar sa kwarai Amma fa da gaske Baba Nasha jinya Allah NE ya kaddara Ina da sauran numfashi Amma fa da an jima da share makoki kamar yadda na ji anyi don Ina samun labarin komai ta Hannun Garba.
“To Alhamdulillah Abdullahi Koda ma ace mutuwar kayi ka Dawo sai muce ka dawo a daidai Lokacin da Muke matukar bukatar son ganin ko da fatalwar ka ce kamar yadda Yar Uwar ka lami tace gaka kayi fatalwa ka dawo . Domin kuwa Al Amura sun tasarwa lalacewa Abdullahi Amma ni Kam na Soma hada biyar da uku suna Shirin bani takwas.
“Duk na samu Labarin komai a Bakin garba Amma gaskiya ba wannan Al Amarin ne ya sa na zabi na fito daga boyon da nake ba sai don hotunan Abdullahi da Abdurrahaman da garba ya tura mini sune suka sa na fito don ko garba Bai San na iso Nigeria ba saboda na Gane banyiwa Uwar yaran Nan Adalci ba na San tana da ciki hakikatan Amma na barta tayi laulayin ta ita kadai Tasha Wahalar nakudar ta ita kadai hakika banyi Mata Adalci ba shine na taho Amma baba duk abinda Ake ciki ayi tayi kar zuwa na ya sa a fasa komai ni zan iya bayar da Dukkan Abinda na mallaka ma tunda shine sanadin da Ake tozarta min Yara ana Kiran su shegu Ake Kuma Neman Rayuwa ta don a Gaji Abinda ni a wuri na ba komai bane face Bak’o Wanda zan bari wata Rana ko Kuma shi ya barni.
Sai a Nan Yaya lami ta saduda ta yarda Dan Uwan ta ne wannan.
“Alhamdulillah Abdullahi matar ka tayi Mana abubuwa da yawa Amma a yanzu itace a ciki tunda yanzu haka tana Hannun Hukuma tunda har ta iya Siyar da gidan Nan ta kulle kudin ta wai duk don Kar Yaran su gaji Uban su har tana dauko Mai gwada Jini wai Bata yarda Ya’yan ka bane sai Kuma reshe zai juye da mujiya Domin kuwa nata Ya’yan ne Suka fita daban da jinin ka da na Yan Uwan su.
“Wannan duk bani da matsala da shi Yaya lami Ya’yana ne bana Wani Neman sanin meye jinin su ita Kuma a yanzu zanje na fito da ita in ma ta ci kud’in da ta siyar da gidan duk zan mayar wa Wanda ta Siyarwa.
“Ai Kuma tunda ta biyo ta wannan hanyar cewa sai an banbance Ya’yan ka da wanda ba naka ba Dole ne abi kadin yadda aka Haihu a Ragaya tunda in da ta yarda da kanta da Bata so shegenta Ya’yan wata ba.
“Yaya lami mu Rufe wannan babin don Allah Rayuwa tana Hannun Allah Ina ce da kuka samu Labarin Rasa ni Kun Yi Imani? To a yanzu ma Wanda duk Allah yakewa fada to Bai kamata yayi fad’a ba . Basma dai kin San ko wacece a wurina tunda Uban ta mahaifi Abokin mahaifin mu ne Kuma ya bani Auren ta a lokacin da na Rasa Auren Farida. Ina tuna wannan halaccin nashi har gobe Wanda muka Rasa a yanzu . Ba zan iya ja da Basma ba ba zan iya daukar kowane irin mataki akan ta ba Kuma Ina Mai tabbatar Miki dukkan Abinda tayi zata Sha ne daga gareni Domin kuwa na YARDA DA ALLAH gashi Kuma ya tabbatar muku da shi din Yana Nan Kuma Baya BACCI.
“Wannab haka yake Abdullahi Kuma da Babu yafiya a DUNIYA da yanzu Ubangiji ya Dade da kife Duniya kuma duk Wanda aka zalunta idan yayi Hak’uri KARSHEN zaluncin sai ya zama Riba Amma duk da haka sai kaja kunnen matar ka don zata iya daukar WUKA ta Soka Maka da sunan kisa.
“Sai dai kar a Kuma baba Amma ai Hakan ta so sai Allah Bai nufa ba.
“Ni kuwa wai ta Yaya ma akayi wannan Al Amarin Abdullahi? Shin ta Yaya kayi jinya Kuma baka dawo ba sai garba ne ya Dawo Mana da kayan ka Yana sanar damu ka cika?
Yayi murmushi Yana Fadin, “Baba bari na kashe wannan case din na Basma sai na Sanar daku komai ya zamo itama da tayi abin tana wurin zan fad’a kowa yaji Amma yanzu zanje na kashe case din Nasu.
“To Amma dai ka tsaya ka huta tukuna Kuma garba da Kabir suna tsaye akan komai ni yanzu Babu Abinda zancewa Allah sai Godiya ko Babu komai Yan yaran ka Basu zama marayun da na Soma tausayawa goben su ba Kuma ko Babu komai ka kawo karshen wannan fitinar ta Basma wacce har da alkali ta gayyato Mana a gidan bayan ta gama zage yaran Nan tamkar Bata tab’a hada hanya da su ba don kawai sunyi kukan begen ka.
“Babu komai baba ai duk Abinda mutum yayi Kansa yayiwa Basma ta gama shayar Dani Mamaki Amma ba zance Mata komai ba bare na bari Wani yace Mata a bar mutum da Aikin sa ma kadai ya ishe shi yanzu Kunyar ta kadai ta isa ta Dame ta.
Baba isuhu ya tashi Yana Fadin, “Allah ya kyauta Amma don Allah Kar kaje ko Ina tukun ka bari ka huta don Kar bakin mutane ma ya ishe ka.
Da haka Baba isuhu ya fice Yaya lami Kam Bata tafi ba sai ta koma sashin Basma tana fadawa su Najwa ga Uban Nasu ya zo.
Aguje suka shigo suna Rungume shi Yana shafa fuskar su cike da kauna da soyayya a gare su Suma Hakan.
Ya fito da sauran kayan kwalam din da ya taho Dasu daga Saudi Yana Basu yayin da Sulaiman ya Haye jikin Abdullahi Yana Fad’in
“Daddy baka bani irin wannan ba da wannan da wannan.
Ya tara musu kayan kwalam din masu tarin yawa suna ta murna da FARIN CIKI Yana kallon su Yana Jin Dadi.
Farida ta Soma sauke mishi kayan da tayi nufin tarbar shi da su Yana kallon ta Yana Fadin
“Kinyi giving up ne madam tun da wuri haka?
Tayi murmushi Bata tanka mishi ba sai fama shiga kitchen take tana dorawa da saukewa shi Kuma Yana Rik’e da Yan Biyun Yana ta jera Mata tambayoyin suna Rigima ko suna kukan Dare? Amma Bata bashi Amsa ba sai da ta gama komai tazo tana service din sa.
Ya Dube ta Yana Fadin, “Dauko kin dan Goyon yaran nan na Goya su kafin Kaya na su zo don na siyo har da jakar Goyon su irin ta turawa wacce zan Rik’a Saka su a Gaba Ina Rataya Kaya na.
“To kayi hak’uri dai har Kayan su iso Amma Mai gida da goyo ai Zaka ja ace ka zama MIJIN TACE
“Ai ni kafin tace ma na zama ba tace ba kafin tace ne ni Farida ke Daya kikayi Rainon yaran Nan ban Taya ki da komai ba Hakan kinyi Amai Sosai irin Wanda na San kina Yi?
Tayi murmushi tana Fadin, “Kaci Abinci don Allah zamuyi Magana.
Sulaiman ya bude womars din Yana jawo cinyar kaza wacce ta dahu Yana Fadin
“Daddy’ zanci wannan.
Da sauri Farida ta karbe tana Fadin
“Dawo Nan bari na dauko Maka Kai ko fiffike Amma Ina Kai Ina wannan.
Abdullahi yayi Maza ya jawo Naman da ta karba ta mayar Yana jawo Sulaiman ya bashi Yana Fadin.
“Dauki duk Wanda kake so in ma zaka iya cinyewa duk na bar Maka
Sulaiman ya Saka tsale Yana Fadin, “Daddy bana iya cinyewa duka sai dai muci ni da Yaya wato Salman.
“To ku taho muci tare Mai Yaya har sunan shi ya zama Yaya?
Ya tambayi Sulaiman Wanda ya kada kanshi Yana Kai cinyar kaza Baki Yana Jan Naman ya cika baki Yana tauna Salman Shima Ya dauki kirji suna ja inda Sulaiman ke fadin
“Daddy ko zan kaiwa su Najwa wannan ?
Ya fada Yana nuna Naman da yake Hannun shi.
“Ci naka gashi can za a Kai musu kaji
Farida tana Zaune tana kallon su ya dago Yana kallon ta Yana Fadin
“Kizo muci Mana madam? Ta kada kanta tana fadin
“Ni Kam ai ba zan yarda naci Abu da GAWA Taki Rami ba Kai dai da Ahalin ka kuyi tayi.
Yayi murmushi Yana Fadin, “Zakiyi bayani ne yanzu da yaren larabci don wanka kawai zanyi na tambaye ki ki bani Ams
Ta Mike tana Fadin
“Dole yaran Nan su tafi can gidan Haj don zasu Hana ka hutawa.
“Babu inda zasu je tura su wurin Yaya lami ai ta San Akwai Dalilin tura su ba ba zata bari su Dame ki ba don ni ba zasu ishe ni na wata nawa Rabo na da su? Kin kuwa San Yaya naji a kewar yaran Nan?
Tuni kuwa ya tashi ya barsu Nan suna faman jan nama ya SHIGA ciki Farida ta hada mishi Ruwan wanka ya SHIGA itama Kuma ta Zubawa Yaya lami Naman da Abinci tace Salman da Sulaiman su kaiwa mama lami can wurin su Najwa.
Suka dauka suka fice ta mayar da kofar ta kulle don ma kar su Dawo.
Yana kwance a kan gadon Yana Rik’e da Abdullahi a kirjin shi yayin da Farida take shafa har ta k’are ta dawo dab da shi ya Bata Abdullahi Yana Fad’in
“Kai shi ki shimfide ki dawo muyi fira
Ta dawo Yana kallon tsakiyar idon ta Wanda yake Tara hawaye Saboda tuna Abinda ya faru tsakanin ta da Sameer Wanda take son sanar da shi don ba zata Rufe shi gara ta fada mishi kawai ko da Kuwa zaiji Wani Abu da dai ace tana dauke da hakkin sa don Yana daga Cikin babbar nadamar ta akan zuwan sameer gidan shi da abinda yaso nuna mata .da suka zaci ya Riga mu Gidan gaskiya shine Bata fada mishi Abinda ya faru tsakanin ta da Sameer ba . Don haka a yanzu take nadamar sanin sameer a rayuwar sai ma karfi da ya so nuna Mata banda Allah ya tsare ta ta gudu da ta tafka abin kunya ace da auren ka an haike maka da kuwa har abada ba zata daina bakin ciki ba bare kuma girman zunubin.
Ya Soma dauke Mata kwallar idon ta Yana Fadin
“In dai kukan FARIN CIKI kike to murmushi ya kamata na Gani a fuskar ki kina min welcoming ba hawaye ba
“Nayi maka laifi ne Wanda nake nadamar sa
“Na yafe Miki Farida . Na yafewa Basma ma bare ke da ZUCIYA ta Bata da gurbin ajiye laifin ki duk girman sa? Yanzu fada min sau nawa kikayi kewa ta ko Kika ganni nazo Miki a mafarki? Don Ina son na tabbatar Miki da ganin da kika Yi min a MAFARKI zan tabbatar da shi a zahiri.
“Baka fa ji laifin ba kake fadar ka yafe,
“Bana kuma son Naji shi kar ki Kuma tayar min da Zancen bani abinda Zaki bani muyi fira dear Darling
Bata bari ya dure ba ta soma fadin,
Dole na sanar da kai derlin irin zaluncin da sameer ya so yi mana don kar wata rana kaji zuciyar ka ta raya wani. A nan ta soma zayyana mishi zuwan da sameer ya rika yi da irin ta addancin da ya so yi mata na fyade har sai da ta sanar da hajiyar sa . Abu daya ne bata sanar dashi ba shine Harbin da sameer din yayi mishi.
Na yarda da ke ne derlin na kuma gamsu da kaunar ki gareni don haka manta komai shima sameer din na yafe mishi na San so ne amma sai dai yayi hakuri abdullahi ya kwace mishi farida sai dai ya dubi Saddam da hanan su tuna mishi farida don haka bani labarin soyayyar.
Bai Bata Damar sake magana ba taji Yana Jan zif din Rigar ta ya zuge shi Yana Rad’a Mata a kunne Shima ya zama Abdurrahaman ko Abdullahi a bashi Abincin sa.
Ga mamakin ta sai taji ya Kai bakin shi a kirjin ta baya ko jin karni cike da kauna da soyayya ya kash Mata jiki har tayi giving up shi Kuma ya nuna Mata yadda yayi kewar ta ta Kuma gamsu da soyayyar sa gareta Domin kuwa duk abinda ya fada to Yana nufin Hakan Babu Rufa Rufa a Al Amarin sa.