Skip to content
Part 70 of 74 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Jin wannan FALLASAR da mamman ya dauko Yi wa Basma ne yasa ta Figo kwalbar turaren motar da yake Saman dash bon din motar Abdullahi a fusace ta makawa mamman da yake bayan motar a goshi sai ga shi kuwa ta Darewa mamman goshi jini ya Soma sauka Saman Rigar shi ya Kuma kame Bakin shi daga son ya fadawa Abdullahi gaskiyar kowaye shi a wurin Basma ba kamar yadda ta fadawa Abdullahin ba na Cewa mamman Dan Uwan ta ne daga can Ahalin mahaifiyar ta tun lokacin da mamman din ya zo gidan Sukayi arangama da Abdullahi shiyasa ta boye kowaye mamman don hakikatan saurayin ta tun Yana cikin Aikin Dan sandan Kuma a tare suke har tayi Aure ta kuma gayyato shi.

Ya dafe goshi Yana kwartsa ihu saboda yadda ta kwantsama mishi kwalbar da karfi tayi hakan don ya gama kaita wuya Jin Yana Shirin kwanar Mata Aiki don Bai San Halin da take ciki ba a yanzu na Ganin Abdullahi akan kafafun shi a lokacin da Bata zaci Hakan ba .

Da sauri Abdullahi ya sauka gefen hanya Yana fadin

“Subuhanallahi Basma wane irin Rashin Imani ne haka kike kokarin halakar da mutumin Nan.

Da sauri Basma ta Kuma fitowa a fusace tana wani murfin tukunya da ta Gani dab da wata Mai abinci ta nufi mamman zata sake kwantara mishi don a Ranta Babu Abinda take so irin ta ga gawar mamman don ya gama kashe ta ko a iya Nan da ya Soma fadawa Abdullahi shi ba Dan Uwan ta bane saurayin ta ne .

Da sauri Abdullahi ya tare ta Yana Fadin

“Kina hauka ne ? Me kike zato idan kika kashe shi? Hukuma zata kama ki dama kin dawo Cikin hayyacin ki Kun fahimci juna ke da shi .

Basma ta Saka kukan da Bata San ko na meye ba Amma dai ta San koma na meye ba zai Wuce na Bak’in cikin kasa cikar Buri ba sai gashi nata Asirin Yana kokarin tonuwa.

Kan kace me?

Farar Rigar da ke jikin mamman tayi kaca kaca da jini har ya Soma layi Yana dafe da goshi yana shirin faduwa Saboda yadda jinin ya zuba da yawa .

Da sauri Abdullahi ya mayar da shi motar ya nufi Asibiti da mamman Wanda yayi matukar sanyi Yana dafe da goshi har suka iso Asibitin aka karbe shi yayin da Basma Kuma ta sulale daga Asibitin ta nufi gidan su da Neman hanyar bullewa don ta Soma tunanin ta Gudu kawai ta bar garin Nan tunda Asiri dai har na boye ya fito har Wanda Bata zaci zai fito ba ma gashi ya fito.

Aka karbi mamman aka bashi taimakon gaggawa ya Kuma Samu relief Amma gishi a sumtume ya Sha bandeji ga Ciwon Kai da ya tsananta mishi Amma Kuma Yana cike da kunyar Abdullahi Wanda yayi tsaye akayi mishi komai aka gama ya Kuma biya kud’in ya kuma nufi gida don kawo mishi Abinci.

Yayi mamaki da Bai iske Basma a motar ba yaja ta Zuwa gida ya Kuma nufi sashin Basma Amma Bai Tara’s da ita ba sai Yaya lami wacce ta Dawo tana tare da Yara.

“Basma Bata shigo bane Yaya lami?

Ya tambaya Amma Yaya lami tace Bata shigo ba.

Ya fita ya samu tarba daga Sulaiman Yana ta jera mishi tambayoyin Ina ya tafi ya barshi? Don ya fita me Lokacin da bacci ya dauke Sulaiman.

Ya Dauki Sulaiman Yana fadin

“Gani na dawo Sulaiman yanzu fa ai duk inda zanje tare zamu tafi don Kar na sake guduwa ko kuwa?

Ya gyada kanshi Alamar haka ne

Ya ce Farida ta zuba mishi Abinci zai Kai Asibiti. Ta Kuma zuba har da lemuka ta hada ya dauki Sulaiman Suka nufi Asibiti aka kaiwa mamman Abinci ya tashi Yana Godewa karimcin Abdullahi yayin da Sulaiman ya Zubawa mamman ido Yana Kallon shi ya Kalli Daddy Yana Fadin

“Daddy wanene wannan? Me ya same shi ? Anyi mishi Allura ne ? Yayi kuka?

Abdullahi ya Dora shi akan cinyar shi Yana bawa mamman amsa da Cewa Babu komai ita Rayuwa yiwa kaice Allah ya bashi lafiya

Ya jima a Asibitin kafin yayiwa mamman sallama ya wuce

Suka shiga sashin Basma har yanzu Bata Dawo ba Yaya lami tace Bata fa shigo ba

Ya San ba zata wuce gidan su ba don haka ya barta har zuwa safe idan Bata Dawo ba.

Gari ya dauka da yekuwar bayyanar Abdullahi Abinda yayi matukar bawa dubun dubatat Al Umma mamaki wasu Suka Soma zaryar zuwa duba Abdullahi da Jin Yaya akayi wannan haihuwar Ragayar? Wasu kuwa da Basu da hanyar zuwa gareshi sai dai suyi ya jita jitar su .

Sameer Yana daga Cikin masu mamakin yadda akayi Hakan ya Kuma Kara tabbatar da Farida tayi mishi Nisan da ba zai Kuma Tara’s da ita ba

Basma Kam da ta Isa gida a furgice mahaifiyar ta ta Soma tambayar ta Abinda taji ana ta yawo da shi na dawowar Abdullahi. Basma tace haka ne Amma Daga haka Bata Kuma tankawa ba taja bakin ta ta tsuke Amma Kuma kallo Daya Zakayi Mata kaga wacce take cike da tashin hankali

Washe gari tun da sassafe Basma ta gama yanke shawarar ficewa ta bar garin Nan Amma Kuma tana son Zuwa Asibiti wurin mamman don ta karbi key din motar ta da Kuma kudaden da ya karba hannun ta.

Don haka ta fice Zuwa Asibiti wurin mamman.

Fitar ta Babu jimawa sai ga Abdullahi ya iso Gidan su Basma Yana gaba Sulaiman Yana take mishi sawu Suka SHIGA gidan hajiya baraka mahaifiyar Basma ta tarbe su suka gaisa tana Duban Sulaiman tana fad’in

“Wanene wannan ?

Da sauri Sulaiman ya cabe da Cewa

“Sulaiman ne .

Haj tayi murmushi tana kamo shi tana fadin

“Madallah da Kai Sulaiman Rabo na da Kai tun kana zanin goyo Masha gashi kazo da kafar ka.

Yayi Maza yace

“Ai yanzu an Daina Goya ni sai su twins Ake goyawa Mami tace na girma.

“Masha Allah Sulaiman ka girma Allah ya k’arawa Rayuwa Albarka kaji .

Yayi Maza ya Amsa da Ameen ya hayyu ya qayyum Allah ka Amsa

Suka Dube shi da Mamakin shi .

Haj ta dubi Abdullahi tana Fadin

“Abdullahi sai gaka Kuma Saman Duniya abin da mamaki jiya Basma tazo Amma Bata ce komai ba har ta kwana yanzu ma naga ta figi mayafi ta fice Wani Abu ya faru ne Halan?.

“Eh to Haj Wani Abu ya faru Amma da ta tsaya ai ba tafiyar ce abinda ya kamata ba tunda ni Bata ji ta Baki na ba .

“Bata da gaskiya yarinyar Nan Abdullahi son zuciya yayi Mata yawa ne duk kuwa Wanda ya Saka son zuciya a Al Amuran sa zai Hadu da Abinda ZUCIYA Bata so . Da tana da gaskiya ai da tace min kinji kinji Haj Amma mursisi abinta ba sai na kawo ido na zuba Mata ba? Ai ba nice Mai Binta ta Fadi Abinda ke faruwa ba Kuma ba yarinya ce k’arama ba bare tace sai an Rarrashe ta Zatayi Bayani .

“Haka ne Haj Wani Abu ne ya faru ta siyar da gidan da suke ciki ne ba tare da kowa ya Sani ba shine fa maganar ta tashi Kunya ta kamata ni Kuma ba wannan ne Abinda ya tab’a min zuciya da Basma ma irin yadda ta nemi shegan ta min yaran Nan Haj har tana Hana a Basu kason gadon su na mutuwa ta shine Kuma na zo gagab sai Al Amarin ya ishe ta Amma Yaya Zanyi da Basma ? Har gobe da Babu Ran malam ba zan iya cin mutuncin Basma ba ko da Kuwa me tayi min Albarkacin malam Wanda ya bani ita a lokacin da nake cike da Alhini Rashin samun Farida. ALLAH yayiwa malam Rahama da gafara Basma taci har ta cinye Wallahi Albarkacin malam Amma me yasa ta kasa fada Miki Hakan Haj?.

Haj ta kame Baki tana Fadin

“Ikon Allah ta Ina kuwa zata iya tsayawa har ta hada ido da Kai Abdullahi? Ai kowa yayi tutun inuwa Dole ya Barta. Kuma Mutumin da yake fada akan gado har kisa zai iya Yi don ya samu gadon Nan to bana ko shakka wannan yarinyar ba zata Rasa fitilar haskawa akan Al Amarin ka ba Abdullahi Dole kuwa ta gudu wane ita da tsayawa ? Ai ko ni Nan ta San Babu Hali wai SATA LAHIRA a kawo Duniya a siyar oh ni baraka har ta iya Saka gidan kasuwa ta Siyar Saboda tsabar mugunta?.

Yayi murmushi Yana Fadin

“Babu komai Haj in dai ta dawo ace Mata Nazo Kuma Ina jiran ta a Gida.

Ya Mike Yana ajiyewa Haj kud’i tana ta Godiya inda take duban Sulaiman tana fad’in

“Taho Sulaiman na baka Tantabara kayi kiwo kaima ka gwada Rabon ka.

Ya kuwa daka tsalle Yana Fadin

“Ina so Haj Guda nawa Zaki Bani?

Ta dauko su gurbi Daya mace da namiji ta Saka kwali ta bashi ya kankame abin sa Yana Duban Abdullahi Yana Fadin

“Daddy haj ta bani Tantabara tunda Bata bani sweet ba .

Sukayi Dariya Abdullahi yayiwa Haj Godiya itama tayi ta Godiya har mota Sukayi sallama.

Basma Kam a Gadon Asibiti ta iske mamman Wanda ya samu da kyar bacci ya fige shi don jiya Kam Bai iya Runtsawa ba saboda ciwon Kai Amma dab Asuba ya samu bacci Amma Yana cikin baccin yaji Basma tana tayar da shi .

“Tashi Bak’in munafuki tashi muyi ta ta Kare .

Tayi wuf da wayar shi ta dauka tana Fadin

“Ina mota ta da ka yaudare ni ? Me kake nufi da fad’in Kai ba Dan Uwana bane? To Wallahi Nima zan juya maganar Nan ta yadda zaka kare Rayuwar ka a gidan sarka.

“Ba zanji Komai ba in dai na tona Asirin ki ga Mijin ki Wanda zan FALLASA ko su waye Najwa da Nabeela a wurin sa in Kuma dauki Ya’ya na mu bar k’asar nan ke Kuma duk Abinda Zakiyi kiyi ko Babu komai dai yanzu ai na Fara yada Miki Kari Kuma in Sha Allah zan k’arasa mishi sauran Bayanin da Bai San komai akan sa ba.

“Sai dai ko kayi wannan Bayanin a kiyama mamman Amma yanzu zan kashe ka da Hannu na tunda ka zamo min JANHURUN masifa in yaso kayi komai ma a can kiyama Amma nan dai karya kake Wallahi.

Ta fad’a tana zaro WUKA daga Jakarta.

Abdullahi da ya iso kawowa mamman Karin kumallon safe Yana dab da kofar ya Soma jiyo Abinda suke fada Dole ya dakata Yana Jin su Babu Abinda ya daga mishi hankali sai Jin cewa zai dauke Najwa da Nabeela su bar garin Kuma Yana Kiran su da Ya’yan shi .

Ya shigo daidai Lokacin da Basma take nufin sokawa mamman wukar Nan a ciki Amma Ganin shigowar shi yasa tayi sak ta kasa aikata Abunda take niyar aikatawa ga mamman wata kunyar ta Kuma lullube ta .

“Me yasa kike son Kashe mutumin Nan Basma? Kina ganin kisan shine mafita a gareki? To kashe shi don Allah sai kiga inda ke Kuma Zaki kare wata Kil akashe ki ko Kuma ki kare Rayuwar ki a sarka kinga Aikin ki yayi Riba.

Mamman da ya bawa mutuwa amanna don ya tabbatar da kashe shi Basma take nufin Yi sai Kuma yaji Maganar Abdullahi wacce take sauka akan kunnen shi duk da ya Rufe ido Yana sauraren shigar wukar Basma a sashi sashi na jikin shi.

Abdullahi ya juya Yana Rik’e da Hannun Sulaiman Yana Kiran waya.

Kan kace me ? Sai ga gangami ya taru a D’akin da mamman yake.

Haj baraka da Yaya lami sai baba isuhu da Kuma Haj kulu .

Abdullahi ya Dube su Yana Fadin

“Haj ban so sauraren Wani Abu da ga bakin Basma ko Abdullahi ba Amma yanzu nazo na samu Basma tana Shirin sokawa mamman wuka tana ikirarin kashe shi to a yanzu Kam Ina son sanin Abinda ke tsakanin Basma da mamman Wanda tace min Dan Uwan ta ne shin Haj kin San mamman Kuma da gaske Ahalin ku ne?.

Ya tambayi Haj baraka Uwar Basma wacce ta kame Baki tana Duban mamman kafn tace

“Ban ma tab’a ganin shi ba Kai yaro daga gidan wa kake? Ni dai ko Mai kama da shi ban taba Gani ba Amma ta yuwu ko a dangin dangira ko Kuma ita tayi Mana shi taga kamatar ya zama dangin mu Amma ni dai ban San shi ba.

Mamman ya tashi zaune Yana kallon Ahalin Mutanen da suke cikin D’akin kafin ya Dubi Basma sukayi kallon kallo kafin ya Dubi Abdullahi Yana Fadin

“Na cancanci a kashe ni Amma ba daga Basma ba sai daga gareka Domin kuwa na cutar da kaina na Kuma cutar da Kai duk da ban shigo Gidan ka da kaina ba sai da Basma tayi min jagora.

“Sunana mamman Kuma ni mutumin Nijar ne karatu ne ya shigo Dani katsina. Har na samu Aikin Dan sanda Wanda ya zama cuwa cuwa ce kawai ta Samar da Aikin. A Ranar da ka fara Gani na na jima da tafka Maka barna da ta asa Amma Lokacin da ka shigo Basma tayi maza ta sanar da Kai cewa ni Dan Uwan su ne to ba haka bane Asali ni din saurayin ta ne Wanda muke soyayya Amma dare daya tace min mahaifin ta ya bayar da Auren ta ga Wani Dan Abokin shi duk da naso Auren ta Amma sai na Hak’ura.

Akayi Auren ta babu jimawa Amma Kuma sai ta Soma Kira na a waya Muna zantukan soyayya har dai Ranar ta gayyato ni tace min mijin ta Yana yin tafiya idan ya tafi Yana jimawa Bai dawo ba kuma ita ta Gane idan ya fita Shima Yana shanawa da Matan waje .

Ni Kam ganin da nayi Mata tana cikin daula Abinda nake iya yin Komai akan su kenan wato kudi don Rayuwa ta ni Kam Babu Abinda yafi kudi a gareni sai Kuma Basma ta Soma Yi min yayyafin su na Kuma karbi Basma da bukatar ta muka Soma Rayuwa tamkar dai ace nine mijin ta .

Kullum muna tare da ita har tsayin watanni UKU mijin ta Bai dawo ba sai kwatsam ta wayi gari tana Amai Wanda ni da kaina na Gane ciki ne da ita ko da muka je Asibiti akace ciki ne na sati shida.

Abunda ya firgita ni kenan Amma Basma tace kar naji tsoro mace Mai Miji waye zai tsaya bibiyar cikin ta? Sai tsoro yayi matukar kama ni har a zuwa Ranar da Abdullahi ya dawo ya Kuma Dawo ne ya same mu a D’akin ta Amma da sauri ta sanar da shi ni Dan Uwan ta ne ni Kuma tun daga wannan Ranar na Daina Zuwa gidan Amma sai ta isheni da waya har dai ta Kuma Ce min baya nan ya Yi tafiya. Na Kuma Dawowa muka Dora daga inda muka tsaya har Zuwa Ranar da ta haihu ta haifi Najwa wacce na ganta sak da fuskar mahaifiya ta. Al Amarin da ya bani tsoro don Gani nake kowa ya San Abinda Nayi .

Tun Ina zaton Al Amarin Basma Mai karewa ne har na Gane tana da wani Abu a k’asan Ranta Domin kuwa ta sanar dani mijin ta Yana son mace Mai cikar kirji Kuma wankan tarwada Kuma ba doguwa irin ta ba gashi Kuma ita Allah ya jarrabe ta da kaunar shi Amma duk yadda Zata so ta burge shi da ta tuna ita fara ce Kuma bata da cikar kirji sai taji kamar ta mutu har sai da ta shiga Neman magungunan da zasu ciko mata da kirji tare da shaye Shayen magungunan Mata don duk ta jawo Hankalin shi Amma sai ya nuna Mata komai fa kamar Dole yake yin sa tare da ita ita Kuma tana cutuwa musamman idan Tasha magungunan Matan Nan Dole sai ta Nemo Wanda zai dawo da ita saiti inda Kuma na Soma karbar kudi daga hannun ta Muna Masha a har ta Kuma haifar Nabeela.

<< Tana Kasa Tana Dabo 69Tana Kasa Tana Dabo 71 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×