Abdullahi ya Soma Fadin.
“Allah ya Saka min Kaunar Yara a Rayuwa ta. k’ananan Yara suna Debe min kewa shiyasa ban iya boye soyayyar Ya’ya na ba a ko Ina ba nawa kawai ba duk inda zanga yaro musamman Mai shirmen kuruciya ko Mai k’iriniya ko Mai yawan tambaya Ina Jin son sa da Kaunar Sa a Raina. Tun Lokacin kuruciyar Najwa da Nabeela idan Basma Zata Fadi gaskiya ta Kuma Yi min Adalci ta San yadda nake son kasancewa tare da yaran . Ko na Saka su mota Nayi ta zaga gari da su duk inda zanje Muna tare. Allah ya sani ban tab’a Nuna wariya ga jinsin Mazantaka ko matantaka ba ni dai duk Wanda Ubangiji ya bani Ina so Ina Kuma Godiya
Dukkan Wanda ya Sanni zai iya Sanin shak’uwa ta da Ya’ya na . Amma sai Basma ta manta komai kishi kuma ya Rufe Mata ido har take ganin na fifita su Salman da su Najwa don su suna Maza su Kuma suna Mata to Allah ya San Abinda nake fada shine a zuciya ta .
A lokacin da Farida ta Haifi Salman Basma Bata boye adawar ta ga Farida da Salman ba ni Kuma Dukkan su na San yadda nake tafiyar da Kaya na Kuma na San kishi kaikayi ne a zukatan Mata Amma kishin Basma ya wuce hankali tunda kishin ta har Salman Bai bari ba tunda Tasha fad’ar cewa kishiyoyin nata sun zama biyu kenan Salman da Uwar sa tunda Ko a Ranar girkin ta Ina shigo Mata da Salman Wanda Uwar sa Bata barta ba bare shi da Bai San Abinda take ba. Ni Kuma munyi sabo da shi matukar dai na dawo to ko a Ina nake Ina Rungume dashi Abinda Basma ta manta kafin Salman Najwa da Nabeela ne Suka samu haka Amma shi Bata yarda ayi Mishi Hakan ba .
Sau tari ta kan kawo min maganganun Farida Wanda na Gane ita Farida kamar tana mantawa da Basma na Raye don Wallahi Bata tab’a kawo min zancen ta ba. Wasu abubuwan ma idan inayi itace ke nuna min kar na SHIGA hakkin matata Kuma Zanyi wa Salman Wani Abu ma sai tace sai dai na hada su tare da su Najwa duk da ban tab’a Sha awar ware su Najwa a komai da zanyiwa su Salman ba.
Wannan tafiyar da Zanyi Saudi Arabia ne naji zan iya biyawa Farida jirgin yawo ta taho min da Salman da Sulaiman Wanda na Gane tashi kalar kuruciyar Tasha banban da ta Yan uwan shi don Yana da k’iriniya Yana Kuma da Rigima ga magana da son komai ya Gani sai ya tambaya. Sai ya zama duk motsin shi zai ce Daddy sai naga zanyi kewar shi sai na yanke biyan kudin jirgin yawo Farida ta taho min da su . Amma Abinda Farida ta fada min shine ba su ya kamata su fara bina ba sai su Najwa Alhalin mun tab’a zuwa Umrah tare da su. Amma ban fada Mata Hakan ba nace in ba zata yi Abinda nace ba ta Sha zaman ta na Saka Yaya lami gata Nan itama Abinda ta fada min shine nake yin Adalci Amma ban fasa Mata komai ba nace haka na tsara don Babu macen da zata Hana ni abinda nayi Niya
Babu Abinda Basma Bata ce ba mun Kuma Sami Sab’ani da ita Duk akan tafiyar Nan Amma dai batayi nasara ba a karshe ma Cewa tayi idan Akwai gaba da Saudi Arabia muyi ta tafiya in ma mun tafi kar mu Dawo
A Ranar da zamu tashi Ina Nan wurin ta nace ayi min Dambun Naman kaza da yaji don Ina son tafiya da yaji don sai da shi ko Abinci Zaiyi Maka Dadi don na tab’a zuwa na samu Abincin Babu gishiri Babu yaji shiyasa nace duk in zanzo kuwa da yaji na zanzo don zaka samu kaza har kaza Amma salam Amma idan da yaji ba zaka Gane Halin da Naman yake ciki ba
Garba ya Kira ni ya iso don zamu tashi ne da wuri. Ina ta shiri har na fito Allah ya Nuna min Wani Abu da Naga Basma tana zazzagawa a cikin dambun Naman da ta gama Amma zuciya ta Bata bani wani mugun Abu ba don banyi Mata wannan hasashen ba .
Na kammala komai mukayi sallama da ita tana ta cin magani Amma ko bakin mota Basma Bata Rako ni ba hatta da Kaya na Najwa da Nabeela ne Suka kawo min wurin mota sai da Farida ta fito ne tace it’s zata kaini sai garba yace a Kira Basma suyi Rakiya Amma da ta fito sai tace ba a gayyace ta ba Kuma ita Bata shiga Abinda ba a Saka da ita ba.
Da haka dai mukayi sallama Ina jaddada wa Farida nan da sati Biyu su Yaya lami zasu taho
Mun Isa Saudi Arabia lafiya ni Kira don na Sanar musu na sauka lafiya Amma Basma na Kira ta Bata dauka ba na Tura Mata text message Babu reply haka nayi ta faman jera Mata Kira Amma ko sau Daya Bata dauka ba na Kira Farida nace Mata Basma Kam lafiya take ? Tace lafiya Lau take sai na Gane Basma ta Shaka akan Abinda mukayi sai na kyale ta Naga idan zata Kira ni tunda nayi Mata missed call Yafi goma Sha Biyu ..
A kwana na Biyu ne na tuna da yaji na da Kuma dambun da nazo Dashi na Kuma dauko Dambun bayan mun dawo masallaci na Fara ci Amma tun tafiya batayi Nisa ba naji ciki na Yana kartawa..
Kan kace me? Ciwon ciki ya sark’e ni yayin da Garba da Muke fira da shi sama sama ya Soma bacci Bai San Abinda ke faruwa ba .
Ina kwance Ina Jin yadda ciki na yake Ciwo sai Kuma Amai ya taho Babu kakkautawa Kuma abin tsoron shine Aman Bak’i kirin tamkar Naci gawayi..
Kakarin Aman ne ya tayar da Garba Wanda muka nufi Asibiti a lokacin da ni na gama fita hayyaci na ban San Abinda yake faruwa ba sai da na kwana Biyu kafin na farfado likita Yana Bayanin Abinda Naci wato guba inda garba ne ya koma Gida Lokacin da aka bukaci a kawo abinda naci sai ya kawo dambun Naman Wanda aka auna aka kuma Gano daga cikin shi ne naci gubar..
Na samu Sauki garba Yana tsaye kaina har na farfado a kwana UKU aka sallamo ni Daga Asibiti.
Washe garin dawowa ta Asibitin ne Ina ta mamakin Abinda ya kawo Guba a cikin Naman har dai ZUCIYA ta ta tsayar min da Cewa karya ne ba guba naci ba Allah dai ya kawo Kawai.
Wallahi a lokacin ban dorawa kowa ba bare Basma sai da azal ta Sa na kuma cin yajin Nan Shima Ashe akwai gubar a ciki sai Gani na Kuma komawa Asibiti Hajaran majaran Nan aka sake auna ni aka ce guba ce Amma a wannan karon kam Nasha wuya don ni kaina ban zaci zan tashi ba Saboda dama ban warware ba na koma Ruwa.
A lokacin ne garba yake fada min lallai akwai wani Abu a boye nima Kuma na yarda akwai wani Abu sai Kuma na hada uku da Biyar suka bani takwas da na tuna irin sallamar da mukayi da Basma da Kuma irin yadda mukayi da ita akan Biyan kud’in su Salman . Amma Kuma sai na ga kamar ba Zata iya aikata Hakan a gareni ba inda nace da Garba ya Kira ya sanar bani da lafiya kafin kuma Nace idan har Basma Bata da Hannu a ciki zata damu Amma sai na Kuma Shan mamaki don Farida kawai ke Kira na Garba ma da ya Kira ta Bata dauka ba sai dai text Wanda muka zaci zata Kira ta nuna Alhini Amma shiru har dai aka Sanar da mutuwar..
Hakan ne yasa na aka dakatar da tafiyar su Yaya lami da su Sulaiman. Inda har wannan lokacin da garba ya Kira ya Fadi mutuwar Basma Bata sallama ba bare ta Kira shi Abinda Kuma ya nuna ta kenan Amma ni duk Ina ta imagine din ba dai Basma ba.
Lokacin da aka fara daukar alhazai zuwa gida Nigeria Garba ya tafi ni Kuma na tsaya a Saudi Arabia na kama hotel don Akwai wasu Yan Nigeria da suka Sanni inda kuma Garba ya Isa gida ya Kuma Kira ni Yana fada min Halin da Ake ciki Wanda Basma ke ta yin Abinda taso akan Gadon Abinda ya tabbatar mini da Basma tayi Abinda tayi ne ba kuskure ba sai don ta huce fushin ta Akaina. Banyi niyar dawowa a wannan Lokacin ba sai sun gama Raba komai nawa saboda ni Babu Wani Rabo nawa da nake musun zai same ni sai dai in Allan Bai nufi nawa bane Amma banji haushin su Raba komai ba Amma bisa tsarin Shari a ita da Farida ni da wata Kil ma ba zan dawo ba sai nayi zamana a can Saudi Arabia na kafa wata Rayuwar tunda Ubangiji ya sa da sauran numfashi in Kuma da Rai da Rabo to Amma hoton Abdullahi da Abdurrahaman da garba ya tura min shi ya Hana ni na ci gaba da boye kaina wakafin da nake sai naji ba zan iya daukar lokaci Banga yaran ba shine Dalilin da kuka ganni Amma baba da wata Kil sai dai Nazo gaishe ku na koma na Kuma Roki kuyi ta Rufa Sirri na akan mutanen da suka yarda na bar Duniya sai fa Saudi suka zo suka ganni sai Kuma ga Abdullahi da Abdurrahaman. na dawo Kuma Dawo na iske harkallar mamman da Basma ..
Wurin yayi tsit baka jin Komai sai tasbihin Baba isuhu da Haj Baraka mahaifiyar Basma da Haj kulu.
Ita Kam Yaya lamin sai tace
“Ni Kam fasaha ta dauke Wallahi abin Nan ganin shi nake KAMAR A MAFARKI Wallahi Basma Kam tayi bazata..
Mamman Kam sai ya juya Yana kallon Basma Yana mamakin Abinda ta aika ..
“Ni Kam na Shirya karbar kowane irin Hukunci ne daga gareka Alh tunda na yarda na ci Amanar ka Kuma zan dauki Ya’ya na Najwa da Nabeela mu wuce Nijar..
“Karya kake mamman ka Raba ni da yaran Nan ko Shari a ba zata baka su ba tunda ka San matar Aure ce dole Aure ya bani Ya’yan Nan ba zan baka ko Daya Daga cikin su ba don in na bar Maka su wulakanta ta same su zan Rik’e Najwa da Nabeela Ya’ya na har karshen numfashi na ko Babu komai Babu Mai kiran su da wani suna bayan Gani .
“A a Alh kar muyi haka da Kai don Allah. Wallahi yaran Nan Ya’ya na ne Kuma ni idan na komawa mahaifiya ta Babu yaran Nan zamu samu matsala..
“Sai dai ku samu matsalar Nan Amma kayi karya ka dauki Ya’yan Nan idan Ya’yan ka kake so to kaje wurin matar makocin ka da kayiwa ciki ka karbi Dan ka ko yarka Amma ban Shirya bari Najwa da Nabeela su tozarta ba in yaso Kai da Uwar su sai ku tanadi Amsar bawa Ubangiji Wanda shine ya kamata ace kun damu da son samu Cikin Aminci Amma ni in kace sai ka karbi Najwa da Nabeela to a Nan ne zaka Gane Ina da yadda zanyi da Kai don duk inda ka San ka kasaye sai na Saka an kaika don kwatar hakkin su .
Basma Kam da take Zubar hawaye tun lokacin da Ake batun Kai tsaye ta fice daga Asibitin ta wuce tana Jin nadamar ta batayi mata Rana ba tunda haka taso Ganin Farida sai ita ta zama madadi..
Babu Wanda yace Mata ko uffan har ta fice .
“Ido Kam ai ba mudu ba ya Sam Kima. Basma Kam ai Dole kike barin wannan inuwar don kowa yayi tutun inuwa ai Dolen shi ya barta Kuma macen da take iya kashe Miji Anya akwai Imani a kirjin ta?
Cewar Haj kulu..
“Babu Kam Haj Amma Gata ga Duniyar Nan..
Cewar Haj baraka mahaifiyar Basma wacce take kuka ..
“Kiyi Hak’uri Haj don Allah Kar ki damu ni Kam Basma zatayi ta cin Albarkacin malam in taga zata iya tazo mu Zauna Amma Aminci kam na san babu Shi a tsakanin mu.
“Ba dai ita ba Abdullahi. Wallahi ba dai ita ba ko ni ba zan Kuma barin ka da Basma ba ..
“Kiyi Hak’uri Haj saboda malam..
“Wallahi Basma ta zama haramiyar ka Abdullahi in don malam ne ko Kuma kana son ka cika umurnin sa kazo ga Amina Nan Labuda na baka ita Halin su da banbanci Amma Basma Kam ko Wanda zan fadawa yaji ba zan bashi shawarar Neman ta ba tunda har imanin ta yayi fitar burtun da take iya yin kisan Kai ..
Baba isuhu ne ya Fara tashi Yana Fadin
“Kai wannan Al Amarin kamar tatsuniya? Mata sun Siyar da imanin su wa wulakantacciyar Riba in dai akan KISHIYA ne Babu Abinda ba zasu iya aikatawa ba? ALLAH ya sauwake Mana wannan makahon Zamani..
Yaya lami ma ta Mike Haj kulu ma ta tashi Garba ma ya tashi suna ta maganganu akan Basma inda suka bar Garba kwance a gadon Asibiti Yana tunanin wannan karimcin na Abdullahi da Gane Rayuwa da bin ta a Sannu..
Farida Bata San komai Akai ba don Abdullahi Bai fada Mata komai ba don Yana Ganin Sirrin Basma ne Kuma ya barta da kayan ta Amma Kuma yaji Wani Abu Yana dibar shi musamman da aka ambata mishi Amina Labuda har yaji Lallai Yana bukatar Hakan musamman da labuda ta kasance wankan tarwada Kuma ba doguwar da take irin Basma ba . Sai kuma tsarin Halittar ta Tasha banban da basma Sai yaji Yana bukatar Hakan Amma Kuma ya San yadda Basma ta mutu akan shi kamar in ya karbi kanwar tata Bai Adalci ba ..
Don haka ya Roki Haj da ta bar maganar labuda Amma tace Wallahi ta Haramta mishi Basma don itace ba zata yafewa kanta ba idan ta bar shi ya ci gaba da zama da Basma Kuma Bata fidda tsammanin wata Rana zata kashe shi ba tunda akwai burin Hakan a Ranta don haka ta gama magana ga labuda Nan ko Bai shirya ba ita zata biya mishi sadakin..
Basma da take Gida abin Duniya ya Dame ta don Haj Bata nemi jin Komai daga gareta ba sai banza da bawa AJIYAR ta Amma sai kawai taji an Dora sanwar Bikin labuda tare da mijin nata Abdullahi. Abinda ya kusa k’arar mata da numfashi don sai taji tafi kishin labuda akan Farida . Kuka take Riris Amma Babu Wanda ya kula ta Haj sai hidimar ta take.
Farida kam Bata San komai ba ta ga dai ya dawo da su Najwa wurin ta ya Kuma fad’a Mata maganar auren shi da mahaifiyar Basma ta bashi na Labuda ya nuna Mata iyayen Basma iyayen sa ne da kad’an ya Rage ace Nan Gidan ya tashi Kuma sun karrama shi irin karramawar da iyaye sukewa Ya’yan su don haka za a Daura Auren shi da labuda wacce aka bashi Auren ta ..
Duk da irin tashin hankalin da taji Hakan Bai sa ta nuna mishi komai ba tace Allah ya Sanya Alheri yasa Aminci a tsakanin su.
Kan kace me? Ya SHIGA hidimar Auren labuda wacce yaji ya Gani don shi Kam nace wankan tarwada Mai kirji tana yakar sa don a Cewar sa sune kyawawa Wanda ba kowa ya Gane Sirrin kyan Yana garesu ba. Akasin farare da ko sauro ya sauka akan fatar su sai ya Nuna..
A wurin lami Farida taji Dukkan Abinda ya faru inda farida ta Gane ya Rufawa matar sa Asirine kum hakan ys Dace Amma Kuma Bata zaci zataji Abinda take ji akan Auren da ta San ba shine ya nema ba bashi akayi koma tace madadi..
Ta damu kwarai Amma da ta Gane ita fa KISHIYA kamar wayar android ce a gidjen mal Bahau she sai ta maze tana kissim kouece ts fidds Kants . hidimar ta inda Kuma ya cika ta da Kaya har Da sauya Mata kayan d’aki da na sutura ya Kuma Siyawa yaran ta Kaya na kece Raini Dole ta Kuma mazewa taji a Ranta ba kishiya ce ya kamata ta Zama damuwar ta ba sai alakar ta da mijin ta wacce in ta bari wata ta kama to ta saki layi ta Rik’e mijin da Duk bukatar shi tayi Abinda ya Saka ta ta Kuma bar Wanda ya Hana ta kalas ta gama nata..
Abu kamar wasa sai ga Gud’a Auren Abdullahi da Labuda ya dauru har ana lullubo ta a kawo gidan Abdullahi Abinda yayi matukar tayar da hankalin Farida taji cikin ta Yana kartawa Babu shiri ta shige toilet tana fesa zawayin da Bata San ko na meye ba. Shin na cuta ne ko kuwa na firgici da tsoron gud’ar da take tabbatar Mata da Abdullahi zai angonce da Labuda wacce take amsa sunan kishiyar ta a yanzu?