Kukan Yusra ya tab’awa ishaq ZUCIYA ya Dube ta tana zube a Gaban shi tana Fadin.
“Don Allah don ANNABI Abba ka yafewa mamar mu tace na Rok’a Mata gafara wurin ka ka yafe Mata don Allah don ANNABI ka yafe Mata Wallahi Bata da lafiya Abba har tana ce min mutuwa Zatayi Abba in ta mutu Yaya Zanyi? Ta fada cike da tabbaccin Abinda ta fada tana tsananta kukan ta.
Tausayin ta yayi matukar kama ISHAQ ya kama ta Yana Fadin
“Daina kukan Nan Yusra ADDU A Zakiyi Mata ba zata mutu ba kuka Baya maganin komai Allah ya Bata lafiya.”
“Ameen Abba ka yafe Mata din ?
Ta fada tana Jiran Amsar shi Dole ya amsa Mata Yana Fadin
“Na yafe Mata Yusra Allah ya yafe Mana Baki Daya ya Kuma Bata lafiya..
“Ameen Abba ka bani kud’i na sai na Kai Mata ko magani sai ta Siya .
“Nawa ne ma kud’in ki a wuri na?.
Ya tambaye ta Yana zura Hannu cikin aljihu ya fito da kud’i tana Fadin
“Dubu biyu Babu d’ari Biyu..
Ya Mika Mata Dubu Biyar Yana Fadin
“Gashi na Kara Miki Dubu UKU sai ki Bata ki gaishe ta ..
Ta Amsa tana Kara share HAWAYE tana Fadin
“Nagode Abba Allah ya jikan magabata.
Zan siya Mata diapers tunda Bata iya Rik’e tutu Kuma ko kudin diapers din Bata da su ..
“Kai Kai Mata kudin duka zata San yadda Zatayi da si tunda Baki San Yaya diaper din yake ba can sai ta Siya..
Ta Mike tana Fadin
“To bari na Kai Mata yanzu Abba..
Yabi ta da kallo har ta fice yaji hawayen tausayin yusra ya cika idon shi . Wato ita Uwa karshen Magana ce ko da tafi lalacewa lalacewa Bata da Abinda zai Bata sunan ta ga Ya’yan ta. Ko ya bacin ma zai wanke Kuma da an ganta cikin Wani yanayi Dole ZUCIYA ta motsa. Shima yaji Wani Abu musamman akan Halin da yusra ta karanta mishi mahaifiyar tata take ciki duk da maimuna ma ta Soma labarta mishi Amma ya katse ta cike da fusata Abinda Bai tab’a shiga tsakanin su na Sabani ba shi da maimuna sai da ta Soma labarta mishi Halin da Wasila take ciki.Bata tab’a ganin bacin Ranshi ba sai a wannan Rana ta Kuma Yi nadamar Hakan don har gobe Bata San musababbin Dalilin Da ya Raba su ba Abinda kawai ta Sani Wani Abu na bacin Rai ne ya faru a tsakanin su don haka ta bashi hak’uri yace ya wuce Kuma har yau din ya wuce ne basu kuma Samun matsala a tsakanin su ba .
Ya sauke AJIYAR ZUCIYA Yana Jin baiyiwa Goggo halacci ba ai ko don ita zai tausayawa wasila bare Kuma ga Sagir da yusra da Zainab. Bare Kuma Goggo wacce yake Mata kallon Uwa mahaifiya don haka yaji Dole ne yaje yaga irin taimakon da zai iya Bata abin Duniya in baya wucewa kuwa ai SHIGA UKU ta samu mutane Kuma da Babu yafiya a DUNIYA da yanzu Labarin Ya’yan Adamu ya jima da shafewa don Ubangiji zai kife Duniya ne ya sake sabuwar Halittar wata Al Ummar..
Yusra tana Shirin fita ne sagir ya kafe mashin din sa ya Dubi yusra wacce ido yayiwa jajir shi Kuma idan Akwai Abinda yake so a Duniya to sune don Yana Ganin su kamar marayu ..
“Ya akayi ne yusra ?
Ya fada Yana Ruko ta ta Soma kuka tana Fadin
“Yaya Sagir mamar mu Bata lafiya tace na Rok’e ka ka yafe Mata tace baka zuwa inda take Yaya Sagir har tace min mutuwa Zatayi .
Ya Soma share mata hawayen Yana Fadin
“Ya Isa ya Isa ai babu Abinda mama tayi min yusra nine dai nayi Mata laifi yanzu Ina zakije?
Ta Kuma Saka kuka tana Fadin
“Tace min mutuwa Zatayi in ta mutu Yaya Sagir yaya Zanyi? Bata lafiya Sosai Bata iya zama Kuma fa diapers Ake Saka Mata Kuma gashi Bata kudi shine na Karbi kudi na wurin Abba zan Kai Mata har ya Kara mini Dubu UKU..
Ya fito kudi daga aljihun shi sun Kai Dubu goma ya Mika Mata Yana Fadin
“Ki Kai Mata wannan Yusra zanzo na Duba ta kice Ina Gaishe ta..
Ta karbi kudin tana murna ta Kuma fice da sauri zuwa gidan Goggo..
Wasila ta Zubawa kud’in ido tana Zubar da hawaye tana sauraron yusra da take Mata Bayanin yadda kudin suka zo da cikon da ishaq yayi Mata akan nata kud’in da Abinda yace na ya yafe sai Kuma Abinda sagir yace da Kuma nashi kud’in da ya Bata..
“Allah ta ala ya tsare kuruciyar ku da Rayuwar ku Yusra sai a yanzu na Gane baiwar da Ubangiji yayi min Amma na gama Bata komai na ..
Tana kuka take Fadin Hakan yayin da Yusra take Fadin
“Wai mama me kikayi wa Abba da Yaya Sagir ne?
Ta juyo tana Duban yusra wace Amsa zata Bata?
Sai ta shiga kad’a kanta tana jin nauyin Fadawa yusra don wannan Kam shine BABBAN SIRRI .
“Nayi musu laifi ne Yusra don Allah Kar ki tambaye ni wane irin laifi nayi musu ? Don Allah Kar ki tambaye ni ..
Da dare sai ga ISHAQ ya Sallama a kofar Goggo wacce ta fito tagan shi tana Fadin
“ISHAQ Sannu da Zuwa
Ta shimfida mishi tabarma ya zauna yayin da wasila taji muryar tashi sai Wani firgici ya saukar mata ..
Tana ji suna gaisawa da Goggo Yana Fadi
“Goggo ya Mai jiki? Allah ya Kara lafiya ban San haka jikin yayi tsanani ba sai da Yusra taje tana kuka nace to abin yayi tsanani kenan?.
“Uhum ai ISHAQ Abu Kam Mai tsanani ne ..
Sai Goggo ta shiga Rattabawa ISHAQ yadda Al Amarin ya faru tamkar wasila ta Mika hannu ta Rufe bakin Goggo ta Hana ta wannan zayyanar Amma Ina tuni Goggo ta Kora mishi bayani filla filla har zuwa Aikin da Akayi har Sau UKU baiyi ba Kuma ga Halin Rayuwa Babu kudi ko kud’in diaper Babu sai dai tayi k’unzugu..
Ya tausaya kwarai Yana Fadin
“Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un Ubangiji Allah yasa hakan ya zama kaffarar ta Goggo Allah ya yaye ..
Ya fito da kudi Yana ajiyewa Goggo Yana fadin
“Goggo ga wannan ki siyi Goro ace Mata Ina duba ta Allah ya Bada lafiya..
“Baka gajiya ISHAQ? Allah ya Kara daukaka ka ya Kara yauk’ak’a Arzikin ka. Na Gode Nagode bari na ga idan idon ta Biyu sai ku Gaisa.
Da sauri wasila ta Rufe idon ta wai tayi BACCI Dole Goggo ta fito tana Fadin
“Tayi bacci in Sha Allah zataji Allah ya biya..
Sukayi sallama ya fice Goggo kuma tana ta mishi ADDU AR fatan Alheri..
Wasila ta fito bayan ISHAQ ya jima da tafiya Goggo ta dauko kudin Nan tana Fadin
“ISHAQ ya shigo na shiga naga kina BACCI duk da Raina ya bani ba BACCI kike ba Amma sai ban matsa Miki ba Kinga kudin da ya bayar Nan Rik’e su kiyi hidimar jinyar ki da su ALLAH ya sa kaffarar ki kenan..
Hawaye ya kawo fuskar wasila tana Fadin
“Ki Rik’e kudin ki Goggo ke ya bawa bani ba. Naji ke ya bawa ISHAQ ba zai iya bani kudin sa ba ko zai bani ni da kaina kunya ce zata Hana na karba..
“Ke karbi Nan kinji . Ko ni ya bawa ai kece Silar da ya Sanni har yake girmama ni wasila Kuma ma da ya bani ai ni ke na bawa saboda Ina tausayawa Halin da kike ciki .
Ta Mika hannu ta karba tana sharbe hawaye .
Washe gari da safe sai ga sagir ya iso Gidan Goggo suka gaisa da Goggo Yana shiga D’akin wasila wacce taji kamar ta nutse kasa saboda kunya ..
Ya zube a Gaban ta Yana Fadin
“Mama Ina kwana ya jikin? Ban San haka jikin ya zama ba Allah ya Kara Sauki.
Ta amsa idon ta cike da hawaye tana Fadin
“Sagir na San nayi maka laifi Wanda na cancanci fiye da haka. Ba zan iya duban idon ka ba wallahi musamman akan Abinda ka gani da idon ka na San Kuma har ka komawa Ubangiji ba zaka manta shi ba bare ka yafe mini ..
“Mama mu Rufe babin wannan maganar don Allah Allah ya Baki lafiya. yanzu me kike bukata?..
“Yafiyar ka kawai ta wadace ni sagir don na San Ina da hakkin ka Akaina..
“Na yafe Miki Wallahi na yafe Miki ki Daina Tino komai sai Alheri don shi nake zato Miki a yanzu..
“Nagode Allah ya daukaka Rayuwar ka ya tsare kuskure irin nawa yaci gaba da Rik’e Hannuwan ka ya Kai ka ga Alheri yasa Rayuwar ka Alheri yasa koman ka ya zama Alheri ko bayan Raina. Kuma don Allah don ANNABI ko bayan na mutu kar ka kalli kuskure na kayi min ADDU AR Ubangiji ya yafe mini ..
“Ba Zaki mutu ba mama kowa zai cimma lokacin sa Ina fatan Ubangiji ya Amintar da ke Alherin da yake cikin DUNIYA da LAHIRA..
Ta Amsa da Ameen Ameen tana share HAWAYE ya Mike Yana aje Mata kud’i sukayi sallama inda take kuka kashirban. Lallai kuskure kuskure ne Sagir kadai Alfarma ce a gareta ko a lafazin Bakin sa zaka gane baiwar Allah a tare da shi..
Cikin kwanaki biyu da Zuwan ISHAQ gidan Goggo sai gashi ya sake Dawowa Yana yiwa Goggo Bayanin Asibitin da ya binciko a Zaria wacce suke Aiki akan irin lalurar wasila don haka ya biya komai na kud’in Aikin da magani Gobe Idan ALLAH ya Kaimu motar Asibitin zata zo har kofar gida ta dauki wasila Zuwa Asibitin in yaso ko Anty murja sai ta Raka ta kwana biyu ne za ayi aikin a gama motar Asibitin zata maido su Gida..
Goggo ta kame Baki tana Fadin
“Kai ISHAQ? Ikon Allah Allah ta ala yayi maka Rahama da gidan ALJANNAH an Gode Allah ya Kara sutura.
Ya Mike Yana fadin Babu
“Babu komai Goggo Babu Abinda ba zan iya Yi Miki shi ba Allah ya Bata lafiya.
Bai Jira komai ba ya fice don ma kar ace wasila ta fito tayi mishi Godiya.
Wasila tana Jin su shi da Goggo har Goggon ta tura kofar ta shiga tana fada Mata Abinda ISHAQ yayi musu..
“Mun Gode Goggo Amma ba zanje Aikin Nan ba Goggo..
“Yo saboda me ?
“Goggo har yanzu ishaq fushi yake Dani Kuma Dukkan Abinda yakeyi Saboda ke yake yin su Goggo Amma na San bashi da laifi tunda banyi mishi Abinda zai yafe mini ba Amma don Allah don ANNABI Goggo kice yafiyar sa kawai nake so Domin kuwa wannan Ciwon ba na tashi bane na tafiya ne kar ya Wahalar da kud’in sa..
“Kar kiyi haka . In ma Abinda yakeyi don ni yakeyi ai kina da Damar wanke laifin ki ko Neman tafiyar sa da kanki Amma ni ai ba zan shiga tsakanin ku ba Kuma in kikayi haka ai kin tozarta baiwa kuje wata Kil kiga ta Nan din an dace Mai imani baya cire Rai da Rahamar Ubangiji kar ma ki Soma Allah yasa zuwa Asibitin ne karshen Wahalar Nan Taki.
Ta amsa da Ameen
Washe gari kuwa Anty murja Da wasila suka nufi Zaria don motar Asibitin tun da safe ta iso tuni kuwa suka dauki hanyar Zaria.
Kwanaki Biyu kuwa Akayi Aiki cike da nasara tare da abubuwan da akace ta kiyaye.aka Hado ta da magunguna Wanda mafi yawan su Wanda zata zuba a Ruwan zafi ne take shiga da Wanda Zai wanko Mata Abinda aka zuba Mata ya zama tsutsa da Wanda zai mayar Mata da fatar da ta saki ta kame Kam ta yadda Zata iya Rik’e tutu
Cikin kwanaki Sha Hudu Kuma ta Soma Gane Aikin yayi kyau Domin kuwa ta Daina Saka diaper Kuma sai ta Kai abin ta makewayi kamar dai yadda kowa Mai lafiya yakeyi..
ISHAQ yazo duba ta ya Kuma Samu lafiya ta Samu .tana Gaban shi tana tsiyayar hawaye ta Rasa Abinda zata ce mishi kalma daya take nanatawa..
“Ban cancanci yafiya daga gareka ba. Ban cancanci afuwa daga gareka ba ishaq Amma a yau Ina Neman Alfarmar su . Ni da kaina Al Amari Na baya burge ni . na gudu don talauci Amma sai Gani a karshe dai Kaine Mai taimako na Ina amfanin Badi ba Rai?..
Ya Mike Yana Fadin
“Na yafe Miki Allah ya tsare mu Aikin kuskure komai ya faru ga bawa zanen kaddara ne Babu Mai zanawa Kansa Rayuwa ko Ka zana ma Kai da kanka zaka dawo ka Goge don tsarin tun Ran Gini tun Ran Zane ne yadda Allah ya zana Maka haka zata kasance.
Yayiwa Goggo sallama ya wuce ita Kuma ta kasa tashi daga inda itake sai faman lissafa Rayuwa take tana Yi Mata Hukunci da Duk yadda ka ke zaton ta ta wuce Nan Shiyasa Ake cewa tafi bagaruwa iya jima..
Tun daga wannan Rana ta samu lafiya inda Kuma mijin Aure yaki bayyana . Bama wannan ne abin haushin ba sai yadda ta kasa yin Daraja a idon mutanen da suka neme ta da fasikanci ba sa ma son ta nuna ta San su bare wata harka.
Ta tab’a haduwa da honorable Gona Abokin Yan Doma Wanda yayi mamaki da ganin ta har Yana Fadin
“Ai nayi zaton kina daga Cikin Wanda aka Kone gidan Yan Doma da ke don an fiddo wasu Mata Biyu a lokacin da Ake kone gidan Saboda Allah ya bankada Asirin shi ya Kuma gudu ance ya na Nijar sai biran da aka Kone Ashe Kema kin tsira..
Tayi murmushi tana fadin
Tun kafin Azo Hakan ma ita suka gudo .
Anan take bashi Damar ya fito suyi Aure Amma yace shi ba ya Auren macen da ya gama watsewa da ita don zuciyar shi ba zata Aminta da ita ba ya fito da kudi dai ya Bata aka ja shi a motar sa suka wuce..
Ta taho tana Kara Gane Duniya da mutanen cikin ta da kome kace kaji ka Gani in aka barka da shi ya ishe ka JANHURUN masifa. Don haka sai ta kama hanyar islamiya tana zuwa makaranta inda duk Wani da zai fito da sunan yazo Yana son ta sai tafiya ta Mika zai nuna Mata shi fa ba Aure ne ya kawo shi ba sai shakatawa don haka ta dinke kofar kula Maza taci Gaba da Zuwa makaranta inda a wannan Shekarar ne Kuma ISHAQ ya biyawa Goggo da Inna suwaiba kujera don shi a Shekarar da ta wuce ne yaje ya sauke nashi faralin don haka Goggo sai murna take tana Fadin
“Ikon Allah Ashe dai Nima da Rabon zamu gaisa da manxon Allah a shabbaki .
Tuni wasila ta jingine maganar Aure gefe ta kama koyarwa a makarantar. Yayin da Sagir Kuma yake ta samun daukaka a kan harkar gyaran shi Kuma komai ya samo zai tuna da wasila da Haj Goggo har zuwa Ranar da ALLAH ya kawowa wasila mijin Aure Wani dan kasuwa ne da ya tab’a son ta tun lokacin kuruciya da tayi Aure Kuma Shima yayi nashi Auren sai aka shafe babin komai Amma Allah da ikon shi matar tashi da Allah yayiwa cikawa wurin haihuwa ta bar mishi Yara Hudu shine Kuma ya Dawo akayi Maja . Wasila Bata ja ba ta sallama Domin kuwa badamasi Yana da mutunci Kuma Yana Daya Daga cikin Yan kasuwar garin katsina ta fannin kayan Ruwa wato lemun Roba dila ne ba lemun Roba kowane iri kuwa don haka Goggo tace in yayi Mata su Rufawa juna Asiri Kuma ta tuna Ya’yan shi marayu ne in har ta San ba zata iya tausaya musu ba to kar a Soma Amma tace Babu komai zata iya.
Haka kuwa akayi wasila ta shiga gidan badamasi da ZUCIYA Daya Amma kuma Wani irin kalubale da ta Tara’s shine komai tayi zai Rik’a kallon tana cutar Yan yaran shi don baya gamsuwa da kulawar ta musamman da yaran suka zama matasa ne Wanda Suka San ita ba Uwar su bace sai Rashin kirki da Rashin Daraja in Kuma Uban su ya dawo zasu fada mishi karya da gaskiya ya Kuma Haye ya zauna Yana cika Yana batsewa har zuwa Ranar da Allah ya gwada mishi Rashin kirkin da suke Mata ya Kuma Gane ba cutar su take ba . Da ya nutsu Sosai ma sai ya Gane yaran sunyi wayewar da Bai sani ba inda Kuma ya Bata Damar hora su matukar sunyi laifi..
Tace A a in dai Allah yasa ka Gani ka tsawatar Amma ni ai ko Duniya sai ta zage ni idan aka kula Ina dukan su Kuma ban doke su ba sun iya tsari Ina Kuma ga na doke su? Na godewa ALLAH da ya nuna Maka ba cutar su nake ba .
Tun daga Ranar kuwa ya Saka ido a gidan shi har zuwa Lokacin da wasila ta Soma aje nata Ya’yan kafin Al Amarin ya tafi daidai sai dai kalubalen da ba za a Rasa ba..
Ta karbi bakuncin Zubaida wacce ta ganta ta koma lafiyar ta ba kamar yadda ta San ta da shanyewar jiki ba. Inda suka Rungume juna suna murnar ganin juna inda taga Zubaida da Yara har uku take tambayar ta bayan Rabuwa ta fada Mata yadda Tasha da kyar har ta Samu lafiya tayi Auren ta har da Yaran ta UKU . Sun jima kafin Sukayi Mata sallama wasila na karbar lambar Zubaida tana Fadin sai tazo Gidan ta kawo Mata ziyara.
A Ranar da wasila ta isa Asibiti saboda ciki na uku da take dauke da shi a Ranar ne Kuma ta Hadu da Shama cikin almajirai tana bara Al Amarin da ya tab’a zuciyar ta matuka Gaya.
Ta Bude Jakarta ta dauko Dubu Biyar ta sakawa Shama wacce Bata kula da ita ba sai da warware kudin ne taga wasila ce. Da sauri kuwa tabi bayan wasila tana Fadin
“Wasila ce don Allah ko kuwa Mai kama da ita?