Rana Ta Takwas
Tun cikin dare Wazirai ke ta tattaunawa a tsakaninsu game da al'amarin wannan yaro. Babbansu ya ce, "kun ga dai wannan yaron na son ya faskare mu a wajen Sarki da surutunsa. To kuwa muddin muka yi sakaci ya samu kansa to mu kashinmu ya bushe. Don haka ku tashi mu tafi gaba ɗaya mu yi wa Sarki magana da murya ɗaya domin ya kawo ƙarshensa mu huta."
Da gari ya waye gaba ɗaya Wazirai suka faɗi gaban Sarki suka ce, "Allah ya ja zamaninka, ka tuna cewa ka ɗauke mu aiki. . .