Skip to content
Part 10 of 14 in the Series Ba'indiya by Haiman Raees

Tiger Shroff

Ga baitin tiger nan 

Jarumin fightern nan 

Matashin jarumin nan 

Na Bollywood ɗin nan 

Gwanin rawa ɗin nan. 

Matashi kake mai ƙwanji

Ga farin jini ka iya mazga

Gwanin rawa kuma ga tsalle

Kai ne na gidan Hrithik Roshan

Sabon jini masanin ehe. 

Ka shigo da ƙafar dama

Kuma ka tsaya da ƙafafunka

Ga ka da sa’a ɗan yaro

Mata na son ka fa na gane. 

Mai murmushin sule goma 

A kwana a tashi ka harba 

Rukunin farko na taka rawa 

Tabbas dai ka wuce wawa. 

Cin ƙarfe da motsa jiki

Gwanin caskale da gyaran gashi

Ah! Ga na Shraddha

Oh! Ga na Kriti

Toh! Zance ya kwana.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.6 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ba’indiya 9Ba’indiya 11 >>

2 thoughts on “Ba’indiya 10”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.