“Kai yanzun ko kunya baka ji? Kazo cikin mata kayi tsaye, sai giringidishi kake kamar wanda za’ayi wa haihuwar fari?”
Wani irin kallo Habibu ya watsawa kanwar mahaifiyar tashi da suke kira da Innani. Tunda yaga shigowarta asibitin tare da Hajiya, ranshi yayi masa bakikirin, yana da tabbacin babu abinda ya kawota sai gulma da son kara tunzura Hajiya, ko rantsuwa yayi ba zai kaffara ba, ita ta tuso Hajiyar ma gabaki daya suka zo asibitin
“Wallahi Innani na rasa wannan lamari, in dai akan Abida ne to yaron nan bayaji baya gani. In ba wani salo nata ba, nakuda kwana daya ace an kwaso an taho asibiti? Kawai neman dora masa dawainiyar da tafi karfin shi, inace haihuwar Nabila kwananta hudu a gida kafin ta sauka, me ya sameta?”
Wani abu Habibu yake kokarin hadiyewa da yayi masa tsaye a wuya
“Kuma duk wannan wahalar karshe dai mace ce…”
Cewar Anty Talatu
“Idan haihuwar ta waiwayeki saiki fara da maza biyu ko uku tunda littafi ake mikowa ka zaba da kanka”
Habibu ya fadi rai a bace
“Gorin haihuwa zakayi mun Habibu? Ni zaka yiwa gorin haihuwa?”
Kai ya kauda, ko Innani darajar Hajiya na kusa dashi takeci
“Kifa kyale shi Talatu, akan yarinyar nan ai babu abinda ma ba zaiyi ba, ya sa kafa yayi fatali da maganata ma balle kuma ya goranta miki?”
Wani nishi kawai Anty Talatu ta sauke, saboda maganganun shi sun daki zuciyarta, duk a cikin halayenta marassa kyau da akanyi kasonsu akan faranti a cikin dangi, babu wanda yake damunta irin ayi mata gorin haihuwa, aurenta uku, na farko shekaru biyar, ta kife kai ta rantse ta kuma mijin ne baya haihuwa ba zata zauna dashi ba, saboda zuri’arsu ai kwanika ma matan sukeyi, ko ita gidansu su goma sha dayane a wajen Hajiya, biyar suka rasu, su shida suka rage, haka bangaren mahaifinta, duk da rashin zumuncin dangin nashi tun kafin ya rasu, balle da kasa ta rufe masa ido. Haka baiso ba ya saketa, dan yana kaunarta, duk kuwa da rigima, tsegumi da kuma fada irin nata. Bata rufa shekara ba ta sake wani auren, shi matar shi ce ta rasu, sai ya jima bai sake wani auren ba, shi kuma tun kafin a shekara biyu, dangin shi da suka fara maganar haihuwa ta dinga bi tana nuna musu halinta na babu wanda ya isa ya takata bata rama ba.
Karshe rashin kunya da maganganu ta fada inda tasan abin zai komawa mahaifiyar shi, yar shi tazo neman ba’asi suka fara cacar baki, Anty Talatu ta daga hannu ta shara mata marin da yayi sanadin guntulewar auren nata. Wannan na ukkun a ta biyu ta shiga. Kuma mijin nata yaran shi hudu a lokacin, tana gidan matar ta kara hudu, da kowanne a ciki da yanda take kara tabbatarwa da kowa Talatu ce bata haihuwa. Wani abu da har yanzun ta kasa dangana dashi, bai kuma sa ta saduda ba, halinta kuwa sai abinda yayi gaba. Kawai dan daga mijin nata har dangin shi mutanene masu tsananin hakuri da kawaici, haka abokiyar zaman nata, bata cika biye mata ba sai ta kaita bango.
“Amman Habibu baka da mutunci….’yar uwar taka?”
Ya ji Innani, zata cigaba da cin arzikin Hajiya ne yau. Kuma yasan ba Abida kawai ta tsana ba, har dashi. Dalilinta a wajen shi ba mai karfi bane ba. Su biyar suka rage a wajen mahaifiyar su, yayyen shi uku, Anty Umma da take aure a garin Katsina, Anty Talatu da take nan Kano, sai Anty Larai tana aure a kauyen Badume da yake nan Kano, shi, sai kanwar shi Maimuna. Ya sani, babu fadi tashin da mahaifiyarsu batayi ba wajen ganin basu tagayyara ba tunda mahaifin nasu banda dan gidan da suke ciki, ba wani abu ya bar musu ba. Hajiyar da ake kiranta ba don ta keta hazo bane, haihuwarta akayi ranar aikin hajji, sai lakanin ya bita a dangi harma da su yaranta. Haka duk surutu irin na lokacin baisa tayi wani auren ba, kuruciyarta, da karfinta duka ta tattara ne ta sadaukar musu kamar kowacce uwa da bata da fatan daya wuce na ganin rayuwar yaranta ta inganta.
Sai dai da an tambayi Habibu, da an bashi zabi, ba zai taba zabar ya zamana tilon da namiji daya rage a gidansu ba. Saboda burin kowa daya tashi ya gani jingine da nasarar shi. Yanda ‘yan uwan shi mata da basu auri masu arziqi ba suke jiran ya zama mai kudi suma su ci daga kudin nashi. Da mahaifiyar shi da yake hangen kyallin burin nata yafi nasu haskawa a cikin idanuwanta. Ba kudi kawai take jira yayi dan ta huta ba, duka zabinta take so ya zama nashi. Habibu ya san ko ya kasance yanda take son shi ba zai taba biyanta ba, tabbas abinda duk zai samu idan ya mikawa Hajiya baiyi asara ba. Sai da ta tabbatar ya samu kwalin sakandire, ta hanyar yin wankau da duk wata karamar sana’a da zata kawo mata kudi koya suke.
Takardun da suka bashi damar samun dan karamin aiki a kamfanin leda. Aikin daya zame masa rufin asiri, ya hana Hajiya duk wani aiki da takeyi, sai sana’arta ta siyar da mai da bata bari ba har yau. A lokacin ne ya hadu da Abida, wake da shinkafa suke siyarwa ana gefen kamfanin su, kannenta zasu kawo mata bokatan da kwanonin, wani lokaci kafin ma tazo har an gama siyarwa, hada kudaden kawai zatayi su tafi. Tun farko-farkon zuwan shi ta karyata duk wani tambari da ake yiwa ‘yan talla, ta kuma nuna masa kowacce sana’a fa in dai halak dinka kake nema, zaka iya yinta batare da ka zubar da mutunci ko kimarka ba. Ko fuskar Abida ka kalla zaka ga sanyin halinta, idan magana ta hadaku kuma za kaji natsuwa a yanda take sauke kowacce kalma da zata furta.
Ya sha wahala kafin ya samu ta sake dashi, saboda tana tsoron maza da zata hadu dasu a wajen sana’arta, kudin goron da ake yiwa ‘yan talla na rashin kamun kai, haka su masu kamun kan sukeyiwa mazan da zasu sake musu da kallon cewar suna da wata manufa ta daban. Abida, marainiya kamar shi, sai dai ita duka uwa da uban ne babu, a hannun ‘yayarta take da kuma mijinta da suke rike da ita, suna duk wani kokari na ganin batayi kukan maraici ba. Abida da bata dauki lokaci wajen siye zuciyar shi ba. Barumaya da tsagenta uku-uku a kowanne kunci da ya kara mata kyau. Sai dai bata da hasken fata, ba kamar Habibu ba, bafullatani da ya biyo hasken fata irin na mahaifin shi, dogon hanci da idanuwa irin na Hajiya. Kyakkyawan matashi dan gaye irin na zamanin shi, kullum tsaf-tsaf dashi, matashin da ‘yan mata in suka kalla zasu kara.
Kamar yanda Asabe, ‘ya a wajen Innani ta kyasa, musamman ganin ya samu aikin a kamfanin leda, saita daina boyewa ta fito fili, har a dangi kowa yasan cewa Asabe fa tana son shi. Innani da kanta tazo ta samu Hajiya da tace mata ai aure tsakanin Habibu da Asabe kamar an daura ne. Ina zata bari wata can ta aure mata da taci moriyar wahalar shi da ta sha, ai ko da Innani bata zo mata da zancen ba, ita zataje mata dashi. Sai dai a karo na farko Habibu ya daga idanuwan shi ya sauke shi cikin na Hajiya ya kuma yi mata maganar da tayi kama da yana so ya saba ra’ayinta
“Bana son Asabe Hajiya, na rigada na samu matar aure, daman cikin satin nan nake so inyi miki zancen”
Cike da mamaki take kallon shi, akan maganar auren ne kuma ta fara ganin wannan taurin kan da kafiya da ‘yan uwan shi suke cewa yana da ita, zuciyar nan ta Habibu da ake kawo mata magana akai tana turewa. An kai ruwa rana, rayuwaka kuma sun baci, musamman na Innani da Asabe ta saka a gaba tana risga mata kukan da tun tana lallashi har saida ta mangareta tana zagi
“Tunda bashi bane autan maza saiki hakura ai, ga Alhazawa na sonki, wanda suka fishi arziki. Da kyanki da komai zaki likewa Habibu ana masa magana yana mayarwa mutane”
Kuma zancen Innani ba na uwa bane da idanuwanta basa tana ganin munin yaranta. Gaskiya ta fada, Asabe fara ce kal, wani irin fari daya fi na Habibu, ga idanuwa dara-dara yalwace da gashin da yayi musu ado, dan bakin nan ya zauna a fuskarta kamar ita ta zaba. Asabe macece da in ba zuciya da abinda take so ba, bai kamata Habibu ya kita ba. Ita ma kuma tasan a manemanta akwai wanda suka fishi arziki, amman tana masa kallon dan boko, kuma mai zuwa ofis, ba kamar sauran yan kasuwa ba. Gashi dan gayu da yake saka kananun kaya, ita kuma abinda take so kenan a tare da namiji, shisa ya haska a zuciyarta.
Sai dai yakita, ya kuma bama Hajiya da dangin shi dalili na farko na tsanar Abida, ta samu dalili na biyu dana uku a gari bayan anzo mata da maganar Abida ‘yar talla ce, kuma barumaya da sukayi kaurin suna wajen neman asiri. Nan fa Anty Talatu da Innani suka kara yi mata famfo cewar an ma rigada an fara kama hanyar asirin, tun ba’a daura auren ba, gashi Habibu ya fara yi mata musu. Su duka ukun suka saka shi a daki da dalilan su da suke fatan ya zama hujja wajen saka shi hakura da Abida. Ya ba Hajiya hakuri, ya kuma sille Anty Talatu tas, hakama Innani da ta saka kukan cewa yayi mata rashin kunya kamar ba ciki daya ta fito da mahaifiyar shi ba. Hajiya kuma tace in dai da yawunta ne bata amince ya auri Abida ba.
Magana tayi girman da sai da Habibu ya dinga dauko mata duk wani wanda ya isa ya fada ta saurara yana hadata dasu, karshe Gwaggonta tayi mata maganar data sakata rissinina.
“Ina gudun kar rabo ya kasheki akan batun auren nan Hajiya, tunda kika ga ya kafe gara ki kyale shi yayi abinda yake so, watakila rabone yake fisgar shi, kina ganin Mariya haka ta kafe kan auren Masa’udu, sai gashi kasa ta rufe mata ido, kuma anyi auren har ga matar nan da yara hudu, ina guje miki jayayya kan abinda kaddara ta rantse akan shi.”
Ba dan ranta yaso ba haka akayi auren, shima duka kayan lefen shi a wajen Maimuna ya tara, ita kadai ce take murna da auren da zaiyi take kuma yi masa fatan alkhairi. Tun daga lefen, gidan daya kama mai dakuna uku da kuma kayan da aka kawo Abida dasu, babu wanda bai zama abin magana a wajen Hajiya da yake ganin gabaki daya halayenta sun sauya tun daya kawo zancen Abida ba.
“Ni na rasa abinda Habibu ya gani a jikin wannan bakar yarinyar, fuska duk tsage, yaki Asabe.”
Cewar Anty Talatu, da duk dangin nasu ma. Innani kanta sai da ta rage kishin da take taya ‘yarta bayan ta ga Abida, saboda taga babu wani abu da zata nunawa Asabe da za’ace don shine ya aurota yaki Asabe. Kamar yanda Hajiya ta canza haka duk wani motsi nashi akan matar shi ya zama abin saka ido a wajenta. Ta zame mishi irin iyayen nan da yake ji a labari suna kishi da matan yaransu, suke kuma kyashin ganin yaran nasu sun morawa matan nasu. Sai dai uwa uwa ce, kuma yayi dace da mace tagari, macen da ta fahimci Hajiya fitila ce a rayuwar shi, aljannar shi na tare da ita, ita kuma tata tana tare dashi. Tana masa kaunar da ba zata so ta ga ya halaka ba.
Duk idan yayi nufin bata hakuri akan halin Hajiya, ko wani abu da tayi bayan tazo gidan nasu ta tafi, saita tare shi da murmushi.
“Hajiya fa ta gama mun komai tunda ta haifeka harka ganni ka auro, babu wani abu da zatayi da zai zauna mun a rai, ko da raina ya sosu idan naganka ya kan wuce mun.”
Amman ya san yau da gobe bata bar komai ba, hakan kuma ya faru, lokacin da Abida ta jera haihuwa uku duka mata. Su Hajiya suka sakota a gaba akan ta cika masa gida da mata da babu komai a haihuwarsu sai wahala, shi ba zai samu magaji ba. Hajiya ta kara daga hankalinta na cewa tana son ganin jikanta na bangaren shi tunda shi kadaine namiji da take dashi. A karo na farko kuma da yaga zubar hawayen Abida akan Hajiyar shi. Sai dai duk da haka, hakurin na nata bai canza ba. Data samu cikin nan baccinta ragagge ne, bayan laulayin shi da yazo mata da zafi fiye da sauran, haka Habibu zai tashi ya ganta tana raya da yawan dararen nata da sallah, har saida yace mata.
“Nifa ban damu da haihuwar wani namiji ba Abida, Allah ya sani ina murna da kuma kaunar yaran nan da ya bani, idan duka matane ya rubuta mun ina maraba da su, ina kuma addu’ar Allah ya rayamun cikin aminci yayi musu albarka”
Murmushi kawai tayi batare da ta iya amsa shi ba. Ita ma bawai tana kin matan bane ba, ko yanzun tana rokon Allah ya bata namiji ne in dai zai zame mata alkhairi, kawai tana kwadayin zaman lafiya ne da Hajiya, tana kwadayin samun waje komin kankantar shi a zuciyar Hajiya da take cike da kiyayyarta. Kamar komai tare da cikin, haka ta tashi da ciwon nakudar da ya fara mata da zubar jini, ya kuma saka da taimakon makociyar su Larai ya samo mota suka nufi asibiti, duka haihuwarta a gida takeyinta. Ya sha masifa wajen likita kamar ma ba zasu karbeta ba, sai dai a ranshi yake alkawari yana karawa idan ta samu wani cikin, daga farkon shi zata fara zuwa asibiti ana dubata, sunayin awon da suketa yi masa masifa akan rashin zuwanta shi.
“Ina ‘yan uwan Abida Bello?”
Jikin shi har bari yakeyi sanda Nas din ta fito tana neman shi, yana jin Hajiya na fadin.
“Oh ni jikar dan azumi.”
Lokacin da yayi tuntube ya kusan kifewa saboda sauri.
“Ta sauka lafiya, ta samu ‘ya mace, sai dai kamar yanda muka nemi ku siyi jini, shi ake kara mata yanzun, ta galabaita ba kadan ba, ba zaka iya ganinta ba sai zuwa anjima, yarinyar dai ana gyarata ne, da an karasa zan fito maka da ita.”
Numfashi ya sauke yana godewa Allah. Ko da aka fito masa da yarinyar, katuwa da ita, riketa yayi a jikin shi yana jin kaunarta kamar sauran, yana kuma toshe kunnuwan shi daga surutun da su Hajiya suke tayi na haihuwar macen da Abida ta sakeyi, da kuma kudin daya kashe a asibiti. Ko bayan an sallameta sun koma gida, kayan barkar daya siyo sai da ya zama abin magana, ragon shi daman ya siya tuntuni ya bawa Maimuna ta hada a cikin dabbobin da take kiwo batare da kowa ya sani ba. Wani abu daya kara bakantawa Hajiya rai, gani takeyi kamar duk wani samu na Habibu akan Abida da yaranta yake karewa. Da dangin Abida ba masu kawaici bane da an dibi yan kallo washegarin suna wajen rabon naman da aka soya. Sai suka kyale su Anty Talatu suka raba da kansu, sukayi son rai babu wanda ya tanka. Sune ma suka tafi suna tsegumi.
Sai dai Abida ta shiga daki tayi kukan wannan kiyayyar da alamu suka nuna babu ranar karewarta. Da gaske ne, duk yanda namiji yake sonka, duk yanda ya kai makura a wajen kyautata maka, akwai abinda zakaji ka rasa a auren in har dangin shi basa so, wanann kwanciyar hankalin ta gidan aure tana samun nakasa idan akwai kiyayya daga bangaren dangin miji. Gashi da alama kiyayyar da suke yi mata har yaran nata abin ya shafa. Ko kyalle Hajiya bata taba kawowa da sunan a sakawa yaran a matsayinsu na jikokinta ba. Tana son Habibu, wani irin so da take jin inama zata iya budewa Hajiya zuciyarta ta leka ko zata tausaya mata, idan bata tausaya mata ba to ga cewa son yayi girman da ba zata iya rabuwa da Habibu ba.
Ko arba’in din yarinyar da ta ci suna Hafsatu ba’ayi ba Hajiya tace sai Habibu ya kara aure.
“Hajiya samuna bai kai na rike mata biyu ba, ina zan sakata idan na aureta?”Maganar shi akan gaskiya take, uzuri ne kuma ya bayar da badon idanuwan Hajiya sun rufe ba ya kamata ta duba. Kamar ma bata san Abida tana siyar da gawayi a cikin gida ba, haka kuma ta fara wainar filawa, da yake gidan nasu a tsakiyar Bachirawa ne, zagaye suke da makarantun Islamiya da kuma na boko masu zaman kansu, sai sana’ar ta samu karbuwa fiye da zaton su. Da ribar ne suke karawa suna toshe wata kafar batare da kowa yaji sirrin su ba. Yasan idan ya fada Hajiya zatace a jikin shi Abida ta samu jarin, tunda babu wani abu da zatayi da Hajiya zata kalla da haske.
“Ina ce gidan naka dakuna ukune? Ko duka hamshakiyar zata hada ita kadai? Habibu wallahi ka kiyaye ni, ka tasamma hanyar da zaka sa inyi maka baki akan wannan yar dangin asirin, kai baka kwadayin ganin ka samu magaji? Akanta da yaranta zaka kare rayuwarka su girma suyi aure kai ka tashi a tutar babu kenan? Wanda zai taimaka maka ma baka samu ba.”
Shiru yayi, baya son yin wata magana da zata tunzura ta, sai dai da tace.
“Ai ba lallai sai budurwa ba, ga Asabe nan tunda kishiyoyi sun sakkota a gaba sun hanata zaman gidan aurenta, ba sai kaje ku dai-daita kanku ba, daman kai kaqita da fari.”
Yaja numfashi ya fitar yafi a kirga, tunda yaji labarin Asabe ta fito daga gidan aurenta da haihuwa biyu duka maza, na biyun kuma ta yaye harya karbe abin shi, jinin shi yake akan farce kar Hajiya ta nemi kakaba masa ita. Gashi nan kuwa an dauko hanya.
“Ni dai kiyi hakuri Hajiya, amman bani da karfin kara wani aure”
Ya karasa yana mikewa, zata sake magana yace
“Ana kiran sallar isha’i”
Daya fita bai koma gidan ba. Amman Hajiya bata dauko maganar dan ta hakura ba. Da ta fara sintiri gidan shi tana ma Abida dibar albarkar cewar ko da bakar doguwa take tsafi sai Habibu ya kara aure, kuka sosai Abida ta saka shi a gaba tanayi tana rokon shi da ya kara auren ko zasu samu salama. Ganin ta bangaren Hajiya ba sauki, ga Abida ma taki kwantar da hankalinta, harta kwashe takarcenta daga daki daya tana bar masa filin dakin, duk kuwa da bakin da yake ta kokarin bata
“Abban su kasan son da nake maka? Kasan ya zuciyata take kuna da tunaninka tare da wata? Kasan dararen da sallah ce kawai take sama mun salama daga numfashina da yake barazanar tsayawa saboda kishinka da yake nukurkusata? Da nake rokonka ka karo aure ka dauka dan ina so ne? Abinda nake fuskanta daga wajen Hajiya inajin idan aka rufa wata babu wani canji zuciyata ba zata iya dauka ba wallahi, gara in rayu ina ganinka da wata da ace Hajiya na gidan nan kullum tana mun zagin da jikokinta suke tsaye suna kallo, bana son mutuncinta ya raunana a zukatan su harya hada da naka, don zasu zuba idon ganin ka hana ne, ba suyi girman da zasu fahimci ba komai ne kake da ikon kare mun ba.”
Wannan maganganun nata, sune tsanin daya hau ya tarar da burin Hajiya, ya kuma auri Asabe kamar yanda taso. Auren daya faranta mata rai, ya kuma kara zama wata hanya da zasu cusgunawa Abida. Ko wata shida Asabe batayi ba a gidan shi ya fara saka ayar tambaya akan cewa kishiyoyi ne suka fito da ita daga gidan aurenta ba mugayen halayenta ba. Kyawunta iya fuska ta tsaya, zuciyarta cike take da hassada ta gaske, ga bakin kishi da takeyi da Abida, duk wanu salo na neman fada tayi, tana kanyi. Kauda kai kawai Abida takeyi, haka ita da yaranta in sun dawo makaranta suke wuni zaman daki, saboda jibgar da suke sha a wajen Asabe, tsoronta ma sukeyi. Ko aiken su tayi sai Abida ta jiyo kukan su, a gabanta ta taba dauke Nabila da wani irin mari sai da ta fadi.
Har ranta taji zafin marin, duk a cikin yaran nata, Asma’u da taci sunan Hajiya suna kiranta Amira, Maryam, Nabila ta uku sai kuma Hafsatu, babu mai sanyin hali da gudun bacin ran mutane irin Nabila, komai na yarinyar da sanyi take yin shi, ko kwarin kirki ma bata dashi. Ita da kanta bata taba dukan Nabila ba, batajin ko a makaranta yarinyar ta taba wani laifin da za’a dake ta. Haka ta kauda kai, saima ta tashi ta koma daki dan kar zuciya ta tunzura ta. Habibu ne daya dawo yaga shatin yatsu a kuncin Nabilar ya nemi jin dalili, Amira ta fada masa Mama ce ta mareta, kamar yanda suke kiran Asaben. Yaje ya sameta duk kuwa da Abida ta hana shi, ya sauke mata fadan shi kamar zai ramaw Nabila marin, inda wani ta daka a cikin yaran ba zai tanka ba, amman yasan ko rantsuwa yayi ba zai kaffara ba, Nabila ba abinda tayi mata.
Wajen karfe tara ne na dare, haka Asabe ta zari mayafi ta tafi gidan Hajiya tana risgar kuka. Shikuma yace ba zai bi bayanta ba, in ta gaji da kanta saita dawo. Yayi biris da aiken da Hajiya ta dinga yi masa na yaje tana neman shi. Sai da Asabe tayi sati biyu cir, ta fara amai a gidan Hajiya da duk wata alama da take nuna cewar tana da ciki, sannan Hajiya ta sakota a gaba, tana cika tana batsewa, ta kuma saukewa Abida rashin arziki har sai da tayi kuka. Da Habibu ya dawo ya samu Asabe ta dawo, dakin Abida ya nufa, duk da bata fada masa Hajiya tayi mata wani abu ba, yaga alamar tayi kuka. Ta tarbe shi da hakurinta, da kawaicinta da kuma murmushinta har ya rasa bakin da zai bata hakuri. Kaunarta da kimarta ce ta dinga ninkuwa a ranshi har yanajin ko a aljanna shi kam zai zabi zama da ita kadai ne, baya neman komai a tare da mace kuma.
Laulayi sosai Asabe takeyi, sai gashi Abidar da take tunanin a duniya bata da wani abu da zatayi mata, itace mai taimakonta. Cikin banda wainar filawar Abida duk wani abu da taci saiya dawo, haka bata taba gajiya da soya mata ba. Har ta fita watannin laulayin ta murje idonta, ta hanyar da idan wani yaga abinda Abida tayi mata, ya kuma ga rashin mutuncin da ta koma tatawa zai dora ayar tambaya akan halaccin haihuwarta, tunda hausa sunce dan halak baya mance alheri. Abida kuma bata kula ba sam, daman batayi dan ta yaba mata ba, ko kuma wata rana ta rama mata, tayi ne saboda Allah da zaman tare.
Sai ga Hajiya tana washe baki duk idan Asabe taje awo ta biya ta gidanta, tana kuma murna da duk wani abu da Habibu zai yiwa Asabe da sunan kyautatawa, daga ita har Innani da take zugata kan ya lalace a wajen Abida da yaranta. Ashe kyautatawa in dai bataci karo da son kai ba abin yabawa ce a wajen su Hajiya. Da ta fara nakuda ma Abida na tsaye akanta, da su Hajiya suka zo sai ta koma daki tunda aka fara gasa mata magana. Habibu ya tafi ya nemo mota saboda bayan Magriba ne, kafin ya dawo har Allah ya yanke mata, ta sullubo yaronta a hannun Hajiya da tayi hamdalar da ta rangade gidan tana dorawa da.
“Allah ya nuna mun, Asabe kin ci gida kin haifi magaji”
Wannan ranar da wadanda suka biyo bayanta zuwa ranar suna, babu salo da Abida bata gani ba. Sai dai wannan karin abin dariya ya bata maimakon haushi, tunda ba da ita suke ba, da Asabe ta haifi namiji ba rawa tayi ba Allah ya bata. Amman izgilin da suke tayi sai ka zata hannu ta mika ta zabo namijin. Yaro ya ci suna Abdallah, Hajiya ta daga shi tayi shewa tana mikawa Talatu da adduo’i kala-kala da maganganun da zallar habaici ne take yiwa Abida data shige daki tana juyo suna cewa bakin cikine ta turnuqe zuciyarta. Asabe kuwa ta rike yaron a hannunta tana jin wani farin ciki yana ratsa ta. Zatayi karya idan tace zuciyarta bata tare da yaranta guda biyu data baro a gidan Alhaji Hashimu, wato Aminu da kuma Tahir, amman ta yarda da maganar nan da akace ba’a raba da da uwar shi, ko ba jima tasan zasu nemo ta.
Yanzun dai ta rungumi Abdallah, tana kuma jin zai zame mata fitilar da zata haskata a zuciyar Habibu da kaunar shi ta kara sabunta a tata zuciyar, maganganun su Hajiya da Innaninta kuma na kara kumbura mata kai, tana jin cewa duk wani abu da Habibu yake dashi a yanzun, da wanda zai samu a gaba nata danta ne, nata ne. Babu wani sauran feleqe kuma da Abida zata yi mata a wajen miji.
Sai dai wa yake hasashe a cikin rashin tabbaci na yau da gobe?
Wa yake da ikon leko gobe balle kuma yaga me zata haifar?
Ina Asabe take da sanin cewa kaddara ta rantse tsakanin gudan jininta da Abida.
Masha Allah. A very good start
Thank you
Wanan tafiya da alama zatayi dadi💃🏻
Fatan da tafiyar ta mika tayi miki dadi
Dakyau. Muna biye.
Godiya nake Haiman
Wow gwara a fara da ni gwanata.
Allah ya kara basira,taku ba irin tasu bace, Ni’ima dai ta Allah yayi muku, Alhamdulillah
Masha Allah,a journey worthy to emberk on
Allah ya sa mun fara a sa’a
Sannu Lubnah
Good.
Yayi kyau maana mai girma Allah y kara basira
Masha Allahu
Allah yakara basira
Ina bala,in kaunar rubutunki Allah ya Kara basira