Ledoji ne manya guda biyu ta shigo dasu, yanayin yanda take rike dasu zaka san kayan ciki ba 'yan kadan bane ba, kallonta Abida takeyi tana karajin tsanar tashin da sukayi. Duka a cikin Bachirawa ne, sai dai nan din wani yanki ne da bata takowa ba duk shekarun data shafe a cikin a unguwar kuwa, sun sha kuka ita da makota da aka saba dasu, har nan din da yawa suka rakato, wanda basu samu yin rakiyar ba duk sunzo daga baya, suna kara jaddada mata tazarar da aka samu ba zata taba yanke zumuncin daya kullu shekara da. . .
Masha Allah Allah ya kara basira
Allah ya Kara basira