Skip to content
Part 25 of 67 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Duk tsokanar da suka saka shi a gaba sunayi dan yace suje su kwashe dangin amarya su mayar dasu gida, ya gaji, so yake da yaje ya kwanta bai dame shi ba, asalima baiko daga kai ya kalle su ba, sai da Mukhtar yace,

“Ban fa ga laifin shi ba, baku ga yarinyar ba? Koni aka kaiwa wannan zanyi rawar kafa fiye da yanda yakeyi”

Yana da kishi ya sani, kishi ba dan kadan ba, dan ko a gidansu ma sunsan wannan kishin nashi, ko abune yafi son ya kasance shi kadai yake da irin shi, yanda duk Hajiya Hasina take nuna wariya akan shi, idan yaga ta nunawa wani kulawa alhalin yana wajen sai zuciyar shi ta sosu. Ko ‘yan uwan nashi yana kishin yaga sun nuna kulawarsu akan juna fiye da yanda zasu nuna akan shi, ko fuskar shi ka kalla zakaga yanda baya son hakan, a ranakun daya daure baiyi magana ba kenan. Balle ma Ibrahim da yayi abokai a lokacin fiye da kowa na gidan, dan haka zakaga in dai yana kasar ya kuma zabi ya zauna a gida anzo neman shi, akwai wani abokin shi Yazid, da JB ya kafa masa tsana ganin yanda Ibrahim ya shaku dashi saida ya rage zuwa gidan sosai, karshe ma sanadin wannan tsanar abokantar tasu ta zama tarihi, sai dalili yayi dalili ne suke haduwa

“Wai shikenan ba zamuyi abokai ba JB?”

Mus’ab ya taba tambayar shi

“Ni bance ba, amman me yasa zasu dinga shige muku kamar sune ‘yan uwanku?”

Shima ya fadi, balle kuma Aisha, tun kafin ya gane sonta yake bayason ganin kowa a kusa da ita, har da kawayenta mata, balle kuma mazan ajinsu. Saida ya rabata da duk wata kawa da suna Sakandiri, kuma bayajin ko bayan ya fita sun cigaba da kawance, saboda yanda suka kullaceta kan biye masa da tayi ta daina zama a cikinsu. Ko yanzun inya daga hannun shi zai kirga mutanen da suke cikin rayuwar Aisha da yatsun shi, basu da yawa, suma fadan Farhana yaji ya kyaleta take kawance dasu, kuma tana kaffa-kaffa wajen ganin bata nuna ta wani damu dasu a gabanshi ba

“Kasan abinda kake nunawa obsession ake kiranshi a turance? Abune kuma da idan ka cigaba zan fadawa Hajja kana bukatar ganin likitan kwakwalwa, saboda disorder ne, babu yanda za’ayi ace kana kishi da duk wani da zamu nunawa kulawa, matarka ka hanata mu’amala da kowa, bayan kai kanayi da mutane. Ba kuma zai yiwu da kaga mun kula wani ka fara dora ayar tambaya akan kaunar da mukeyi maka ba”

Shisa ya fara danne zuciyar shi, amman bawai yana so ba, me yasa shi kadai ba zai ishesu ba? Me yasa sai sun kula wasu? Sun damu da wasu? Sai sun raba damuwar da sukayi dashi da wasu can daban? Ko mijin Farhana yaga yana rirrike mata hannu sai ranshi ya baci, yaran dake tsakaninsu baya nufin ya fishi kusanci da ita. Duk kuma yanda zai dinga rirriketa haka, yana da yakinin idan akace ta zaba a tsakaninsu shi zata zaba. Idan ya tuna hakan sai ya dan samu natsuwa. Sai dai baiyi zaton zaiga wani jan abu ya gilma ta cikin idanuwanshi dan Mukhtar ya fadi maganar nan akan Sa’adatu ba. Kallonta ya tsaya yayi kenan? Baisan ya akayi hotunan taron nan ya zagaya yanar gizo sosai ba, dan har wasu shafukan ma sun wallafa a manhajar Instagram. Har wani zafi-zafi yaji kirjinshi nayi, musamman da sauran sukayi dariya, alhalin shi baiga abin dariya ba.

“JB na gab da shakeka Mukhtar.”

Abbas ya fadi yana dariya, ganin irin kallon da JB din yake jifan Mukhtar daya daga hannuwan shi duka biyun cikin nuna alamun sallamawa yana cewa,

“Yi hakuri Angon Sa’adatu…nayi shiru”

Bai daice komai ba, amman har suka fita daga gidan ranshi a bace yake jinshi, tsayawa sukayi sukayi masa siye-siyen kazar da ta zama al’ada, ledoji ne manya guda hudu, Abbas ya ajiye a bayan motar da suke ciki, yana fada masa, kai kawai ya iya dagawa Abbas din. Haka suka karasa gidan da yanzun yake ganin kamar yayi karami da yawa, harabar gidan baifi ta dauki motoci biyu ba, daga ciki kuma dakuna ukune bayan falo, kowanne da bandaki a ciki, falon ma akwai bandaki, kicin sai kuma store. Daga harabar kuma akwai dakin maigadi da kuma bandaki, su Farhana ne kuma suka zuba duk wani kayan bukata daya kamata a gidan, yanzun dai yake tuna sai yayi magana an samo maigadi, ya manta kwata-kwata. Sai dai da suka kira Farhana sai tace musu,

“Karku damu, yanzun zamu fito, gasu nan zamu mayar dasu, ba wani yawa gare su ba, kuma babu kawayen Sa’adatu ko daya ma, daman yanzun zan kiraka ince ka taho kar a barta ita kadai”

Anan waje suka tsaya da motocinsu, su Farhanan suka fito, sai da suka kara gaggaisawa da ‘yan uwan Sa’adatu, suna ma juna godiya da bangajiya tukunna, sosai suka kara saka shi gaba saboda yace su tafi, ba sai sun rakashi ciki ba, tunda dai babu kawayenta ko daya balle suce wani abu, haka yayi musu sallama, yaja motar shi zuwa cikin gidan, ya fito yaje ya rufe gate din gidan. Ya kwashi ledojin a bayan mota yana nufar kofar da zata hadashi da cikin gidan. Sai ya tsinci kanshi da sauke ajiyar zuciya, anyi mai wahalar an gama, yanzun duk wani abu da zai biyo baya tsakanin su ukune kawai. A hankali ya murda hannun kofar yana shiga cikin gidan bakin shi dauke da sallama, kamshin turaren wuta da wani kamshi na daban ya daki hancin shi, wani kamshi mai cike da bakunta a wajen shi.

Sosai ya shiga cikin gidan zuwa daya daga cikin dakunan baccin ya tura, kayan dakin ba masu hayaniya bane ba, sunyi mishi kyau, ya janyo ya rufe ganin bata ciki, na biyun daya tura kamshin shi ya bambanta da sauran, kamshine mai sanyin gaske, irin kamshin nan mai saukar da kasala, tana zaune kan gadon ta sauko da kafafuwanta da take lilawa a hankali, da alama tunaninta yayi nisa shisa bataji tura kofar da yayi ba, har saida ya shiga cikin dakin, rufe kofar taji, ta kuwa dago idanuwanta dauke da tsoro, da wani abu daban, sun rine sun sauya kala cikin yanayin da bai taba ganinsu ba, ga wani kwantaccen maiko da ya rasa hawaye ne kawai ko akwai wani abin daban, da akwai kwalliya mai sauki a fuskarta, baisan leshi bane ko meye a jikinta, ya daiyi mata kyau, haka mayafin da ta dan daga ya zauna a saman kanta kawai. Wani irin shiru ne ya ratsa dakin, kafin cikin rauni tace masa,

“Ina wuni”

Saboda batasan abinda ya kamata tayi ba, ana cewa an daura auren, zuciyarta tayi wata irin bugawa, bawai Tahir baya fado mata bane, akwai abubuwa da yawa a kowacce rana da ko taso ko bataso ba cin karo dasu na tuna mata dashi, ta dai dauka ta warkene daga ciwon da yayi mata sanadi, sai yau da komai ya dawo mata sabo. Lokaci daya wasu hawaye suka dinga saukar mata, su kansu ‘yan uwanta sai aka koma lallashi maimakon tsokanar da suka fara suna mata wakar ta zama ta zama, ganin irin kukan da takeyi, abinci kuwa kasa ci tayi, sai yoghurt aka samo mata, shima dakyar ta sha rabin roba, lokacin da akazo daukarta kuwa, Abdallah da kanshi ya kamata zai sakata a mota, saita rike shi tana wani irin kuka daya karyawa kowa zuciya, shima saida yayi gefe da kanshi kar taga hawayen shi ta sake rikicewa. Saboda har lokacin zuciyar shi ta kasa natsuwa da auren.

Yanda zuciyarta take a cunkushe ya hana mata ganin kyawun gidan da tunda su Nabila sukaje suka gani suketa zuzutawa, kuma maganganun su kan gidan ne yasata jin tana so ta ganshi itama, ranar dan karsu tsokaneta shisa bata tambayesu ko sun dauko hotunan gidan ba. Da suka zo tafiya ma suna karayi mata nasiha sai da tayi wani sabon kukan, da sunsan wanne irin aure tayi ma da sun daina wahalar da kansu wajen yi mata addu’ar Allaah Yasa mutuwa ce zata rabata da Jabir. Na Tahir ma da aka kulla shi da wannan fatan babu inda yaje, sun kaita ne ko gajiyar bikin bata gama sakinsu ba auren ya kare.

“Sannunki da gajiya”

Ya amsa can kasan makoshi a madadin amsa gaisuwar da tayi masa, yanajin wani abu na fisgar shi da yanayin rauninta, ledojin ya ajiye a kasa, ya dan danna wayar da take dayan hannun shi, karfe takwas harda rabi.

“Ki taso ki rufe gidan, dare nayi.”

Ya fadi yana juyawa ya fara tafiya kamar bai fadi abinda taji yayi mata wani irin duka ba, batasan me tayi tsammani ba, watakila shisa maganar shi ta daketa da yawa haka. Yana kuma tuna mata dan taji kanta a matsayin matar aure, amarya a yau din baya nufin komai, aure gareta, amman bata da miji, ta amsa sunan matar aure a yau badan tana da kwana ba. Sosai take kokarin mayar da hawayen da suke neman zubo mata, saboda haka kawai taji batason Jabir ya gansu, batason ta bashi dalilin da zaisa ya dauka ta manta ya matsayin aurensu yake, aurene na yarjejeniya kawai. Dakyar ta iya mikewa, batama kula gyalenta ya zame ya fadi ba, bata kuma damu da bata da ko takalmi ba, riga da skirt ne a jikinta na wani leshi mai matukar laushi kar sararin samaniya mai haske sosai, dinkin rigane da skirt, wani irin skirt da sai take shi takeyi tana neman faduwa saboda tsayin shi, da kuma yanda yayi wata irin budewa daga kasa, kamar bai zauna a kugunta daga sama ba, zaka rantse a jikinta aka dinka shi saboda yanda ya kamata. Hakama rigar da take da wani irin budadden hannu, saukaken daurin dankwaline akayi mata, an dai saka masa pins yanda in ba hannu tasa ta ture ba, ba zai zame ba.

Ta dauka iya kofar falon zata rufe, shisa da ya fita daga ciki ta nemi mayar da kofar ta rufe.

“Sai kin fito kin rufe har gate din.”

Daga idanuwan ta dake kasa tayi tana kallon shi, saboda da gaske zuciyarta ta buga, cike da tsoro, tunda take a duniya bata taba kwana wani waje ita kadai ba, batama taba hasashen hakan zai faru da ita ba, shisa bata taba sanin firgici da tsoron dake ciki ba sai haka. Kowanne gida irin wannan ba akwai maigadi ba? Itace bata dashi? Saboda bai daukar mata ba? Ko saboda me? Ita kadai zata kwana a wannan bakon gidan? Idan wani yaga babu maigadi ya diro ya shaketa fa? Kanta ta mayar kasa tana daga mishi kai a hankali, kafin ta cigaba da binshi a baya, hawayenta na hana mata ganin hanya sosai, sai dai da yazo shiga motar shi, ta kuma tabbatar da tafiya zaiyi ya barta da gaske, ita kadai, sai taji ta riko rigar shi ta baya, cikin mamaki ya juyo, hawayen da taketa kokarin tarbewa suka zubo mata.

“Ni…ni kadai”

Ta fadi a tsakanin shesshekar kukan data taso mata, yarintarta na fito masa a fili da wani abin daban.

“Ba zan iya ba, tsoro nake ji.”

Ta fadi tana saka bayan hannunta tana goge hawayenta, wasu na sake zubowa, haka kawai sai murmushi ya kwace masa.

“Akwai tsaro sosai a unguwar, kuma gobe za’a samo maigadi, mantawa nayi, zanwa Adda magana a samo miki mai aiki da zata dinga kwana, na yaune kawai.”

Kai Sa’adatu ta girgiza masa, na yau din kadai, ba zata iya ba, idan ma tace zata daure tayi jarumta to karya takeyi, bata taba kwana ita kadai ba, bata jin zata fara yau.

Ka tafi dani to, gobe saika dawo dani.”

Zuciyar shi ta buga, ya tafi da ita? Ina? Gidan shi? Gidan da jiyan nan ya samu ya lallaba Aisha data fara rikice masa, yau kuma batayi wata magana ba, amman bayason wannan sanyi-sanyin da takeyi masa, yanzun ma hankalin shi gabaki daya yayi gidane dan karta saka wani tunanin a ranta. Kuka takeyi, hawaye wani na bin wani, gyara tsayuwar shi yayi.

“Babu abinda zai sameki Sa’adatu, da kin rufe gate din, saiki koma ki rufe gidan ko’ina. Ungo wayata…”

Yace yana mika mata wayar.

“Ki saka lambarki a ciki, zamu dinga magana, babu komai fa.”

Wayar ta karba, amman bata daina hawaye ba, ta saka masa lambarta, tana mika masa, ya danna ya kira.

“Da kin koma ciki zaki ga number dina, babu abinda zai faru, baki yarda dani ba? Ki kalleni, kinsan ba zanyi miki karya ba.”

Kallon nashi tayi da wani yanayi a fuskarta, tana saka shi mika hannu ya goge mata hawayen daya zubo mata a gefe daya.

“Good girl, kizo ki rufe.”

Ya fadi yana saka gwiwoyinta yin sanyi, yana kuma kashe mata duk wata wutar musu da take shirin yi masa, ba wai dan tsoron da takeji ya barta ba, tana kallo ya karasa ya bude gate din, ya dawo ya shiga motar shi ya rufe, ya kuma jata yana fita daga gidan, sai dai fitowa ya sakeyi, yaja mata gate din yana rufewa ta waje, sai da yaji ta saka duka sakatar daya kamata.

“Ki koma ciki to, ina nan sai kin shiga zan tafi.”

Cewar Jabir yana mamakin kanshi, da kuma damuwar da yaji yayi sosai da kuka da takeyi da kuma tsoron da yagani bayyane a tare da ita. Ya kusan mintina biyar a tsaye, iya mintunan da yake tunanin ya kamata ace Sa’adatu ta shiga gidan ta rufe, tukunna ya koma motar shi ya zauna, sai kuma yaga hannun shi na danna wayar shi yana kiran lambar da ta saka masa, bugu daya ta dauka.

“Hello…”

Ta fadi muryarta a shake da alamar kuka takeyi.

“Bana ce ki yarda dani ba?”

Shiru tayi, yanajin saukar numfashinta da ajiyar zuciyar da ta yamutsa wani abu cikin kanshi har saida ya runtsa idanuwan shi.

“Ki daina kukan nan, kije ki wanke fuskarki, akwai abinda zaki samu kici a ledojin dana ajiye…in kinci ki kwanta, kar in kira inji baki daina kuka ba.”

Haka kawai yaji alamun kai ta daga masa

“Good…”

Ya furta ya sauke wayar daga kunnen shi, ya katse kiran yana kunna mota ya nufi hanyar gida, zuciyar shi dauke da wani bakon yanayi. A gefe daya kuma yana addu’ar Allaah Yasa Sa’adatu tayi abinda yace mata kar kukan da takeyi ya saka mata ciwon kai, haka kawai kuma sai sakon Abdallah da yayi masa a waya ya dawo masa.

“Idan nace na baka amanar kanwata, bansan ko zaka dauka ba, idan na rokeka ma bansan ko zaka amsa mun ba, banyi maka sanin da zan dora duka yardata akanka ba, zan bar kai da Sa’adatu a hannun Allaah”

Ya karanta sakon yafi sau goma, amman har yau yawo yake masa batare daya gane duka ma’anar shi ba, ya barsu a hannun Allaah Ya ce, wannan kalaman sunfi komai tsaya masa. Ko a yarjejeniyar su akwai inda yayi alkawarin zai kula da Sa’adatu da dukan iyawarsu I a iya lokacin da zatayi a karkashin shi, me yasa dan uwanta zai fada masa wannan maganar? Me hakan yake nufi? Bayajin yana da wata fuska ko kamannin da suke nuna zai iya cutar da wani da har sai an hada shi da Allaah irin haka. Maganganun sunyi masa wani iri, kuma suna yawan fado masa tunda Abdallahn ya turo masa su jiya. Haka ya karasa gida, maigadi ya bude masa ya shiga da motar, daya fito yana takawa zuwa ciki, a karo na farko sai yayi abinda bai taba ba, yayi saving din lambar Sa’adatu da SA kawai, tukunna ya goge kiran da yayi mata, ya kuma tura mata sako.

“Babu abinda zai faru. Good night.”

Shima ya goge, daya shiga gidan Aisha na tsaye a falo, tana jin sallamar shi a tsakiyar falon suka hadu tana rungume shi hadi da sauke ajiyar zuciya, da ya saka wayar shi a aljihu, yaji ta danyi vibrating alamar sako ya shigo, sai yaji wani yanayi da bai taba sanin shi ba ya lullube shi tare da dumin Aisha.

Rashin gaskiya.

Karo na farko yaji wani abu na rashin gaskiya a tsakaninsu.

<< Tsakaninmu 24Tsakaninmu 26 >>

1 thought on “Tsakaninmu 25”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×