Skip to content
Part 38 of 67 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Yau duk tasoshin da ta saba kallo basu kai da saka wani abu da taji yayi mata dadi ba. Dan haka ta kashe kallon, ta koma daki tabi gado ta dauki wayarta, wayar da takejin dadin amfani da ita sosai, gashi fitar da tayi rannan tasa an tsaya shagon saida kobobin ta siyi me kyau sosai, aka kuma sake mata screen guard. Wani lokacin sai taji kamar ba ita bace a rayuwar da take ciki yanzun. WhatsApp ta bude ta duba, ta amsa mutane masu son kunun aya da zobo tana tuttura musu account number, data fita saita shiga twitter yau, ta samu sun bude gardama kan zogale da kaza. Dariya kawai take sha, musamman tweet din wani da yace

“Koni fa akwai lokacin da nake bayan yan zogale tafi kazar nan, sai yanzun na fahimci irin maganar nan ne da talaka yake fadawa kanshi na lallashi, tunda yasan ba samun kazar zaiyi ba, ni yanzun da nake da kudinta waya sake jin bakina? Yaushe rabonma da wata zogale ta burgeni”

Aikuwa anata comment, na wani ne yafi bata dariya

“Nifa kashin kaza ma yafiye mun wata zogale”

Kamar yanda ta saba, in dai zataga ka fadi wani abu da yayi mata, bayan like da retweet, wani lokaci saita shiga ta duba profile dinka. Yau ma haka tayi, profile dinshi ta shiga. An rubuta Officer AB, sai daga kasa kuma AB_Karaye. Hoton hannune daya nuna alamar nashine, sai kuma na mace akan nashin, nata da yasha kunshin ja da bakin lalle, ga wani zoben azurfa mai jan dutse ya kara kawata hannun. A wajen da zai danyi takaitaccen bayanin shi kuma, abu na farko shine cewar shi musulmi ne, sai kuma yace yana da aure, dan yasa yana ma alfahari da auren nashi, kuma matar shi ta karanci fannin hada magunguna ne wato Pharmacy tunda ya saka (Proud husband of a Pharmacist) sai kuma dan hoton magani a jiki, sai na gaba ya nuna yana daya daga cikin mutanen da suke bala’in son abinci, abu na karshe ya bata dariya, ya saka kaza ne harda hoton cinyar kazar.

Haka kuma duka hotunan da ya taba wallafawa da kanshi to na abinci ne dauke da naman kaza, ko kuma naman kazar zallah cikin nau’ika kala-kala, haka abubuwan da yayi retweeting ma duka dai kan abinci ne, sai ta tsinci kanta dayin following dinshi, daman haka takeyi, inta gama duba profile dinka tas, taga kamar abubuwan da kake wallafawa ko taya wallafawa abune da zata karu dashi koya sakata nishadi saita bika. Tunda ita dai da kanta ba zatace ga ranar data wallafa wani abu ba. Daga nan saita wuce Instagram tana kallon girke-girke tunda dai yanzun tana da datar da har saita rasa abinda zatayi da ita lokutta da dama. Tana da sauran abincin da tayi, shisa data tashi dankali kawai ta fere, tayi sallar azahar, ta soya shi, ta zubawa maigadi nashi ta dawo taci nata, sai karfe hudu zata harhada order din da akayi ta bayar a kaiwa kowa nashi.

Ta koma ta kwanta ta dauki wayarta ne taga sakon Jabir

“Kimun kifi zan shigo anjima”

Yau kwana biyar kenan data fara shan maganin daya kawo mata, ta kuma fada masa tun ranar farko ya amsata da Ok.

“Gasashe ko farfesu?”

Ta tambaye shi

“Kowanne na samu”

Ya bata amsa, saida ta gama hada order din tas ta kira mai delivery dinta ta bashi. Tukunna ta shiga kitchen din. Akwai wani farfesu da Badr ta koya mata, kuma tayi shi sau biyu ba karamin dadi yayi mata ba.

“Akwai kifin ko in aiko dashi?”

Text din Jabir ya kara shigo mata, ta amsa masa da akwai, YouTube taje ta lalubo littafin data fa saurare a tashar abokiyar hira, na Batul Mamman ne mai suna al’adun wasu. Dariya kuma take tasha ba kadan ba, littafin ya tayata hira har tayi aikinta, zuwa Magriba ta gama, ta wanke abinda ta bata, sai dai Jabir baima shigo gidan ba sai takwas da rabi, yanayin shi ya nuna a gajiye yake, idanuwan shi kuma sunyi wani irin nauyi daya sata jera masa sannu har sau biyu bayan sun gaisa ya zauna, sai kallon yanda ya shiga cikin kujerar sosai yakeyi, yana tuna mata ranar farko data fara ganin shi a motar nan, bambancin kawai idanuwan nashi basu rine ba, da sauran haske a tare dasu yanzun, amman alamu sun nuna yaci bashin bacci.

Kuma da gaske bashin baccin yaci, tunda Aisha ta tafi bai samu baccin daya wuce awa hudu a dare ba, saboda yana bata shine wajen tunanin da ace tana nan da yanzun tana jikinshi, sauran lokacin kuma yana karasa shine wajen kokawa da kanshi da kuma duk wani abu da yake mintsininshi cewar ga Sa’adatu, yaje wajen Sa’adatu, to jiya kam yana rufe ido aka kira sallah, kuma gashi an kawo wasu kaya, wuni yayi shago suna lissafi, kanshi baya ciwo, abinda ma ya bashi mamaki, yayi masa nauyi na gaske. Tun kafin la’asar yasan yau ko ya koma gidan bashida karfin yaki da kanshi, shisa baiko yi yunkurin gwadawa ba, ya bari abinda ke mintsininshi yayi nasara. Yana gama abinda yakeyi, a hanya yayi Magriba, ya biya ta gidansu suka gaisa da Hajiya Hasina da ko tayin abinci batayi masa ba, duk da tasan Aisha bata nan, saida ya bar gidan yana motane ma yayi tunanin ai zatayi zaton yana wajen Sa’adatu, to zatonta dai yau ya zama gaskiya.

Ya tsaya yayi isha’i dai, sannan. Wai daya shiga gidan kuma sai gajiya ta karasa lullube shi, ganinta kawai ya saukar masa da gajiya har wadda baisan daga inda take tasowa ba. Data kawo masa kifin ma, yanayin shi yasa ta zuba masa, ta saka masa cokali a ciki, taje ta kawo masa kunun ayar data kula kamar yafi so, sanda ta dawo ya sauko kasa, yadai jingina bayanshi da kujera, idanuwanshi a lumshe, ta rasa dalilin da yasa gajiyar da take gani a tare dashi duk ta dame shi

“Sannu…”

Ta sake fadi, saiya bude idanuwanshi yayi mata murmushi a maimakon amsar sannun da tayi masa, kamshin kifin ya daki hancin shi, duk da gajiya na neman danne yunwar da yake ji, yaci, sosai, saida ta kara masa akan wanda ta zuba, ya kuma shanye kunun ayar, sai yaji bayason komai banda kwanciya.

“Bacci nakeji Sa’adatu.”

Ya furta, ko yanayin shi bai nuna ba, muryar shi data bude ta kuma shige cikin makoshi ta nuna hakan.

“Ka tashi kaje gida saika kwanta, sannu.”

Sai ya tsareta da idanuwanshin nan, yana kokarin raba gajiyar tare da ita, dan lokaci daya taji kasala na neman rufeta.

“Aisha bata nan.”

Da rashin fahimta take kallon shi.

“Tana Saudi…bata nan tun last week, saini kadai.”

Kallonshi takeyi zuciyarta na bugawa da sauri-sauri, sai dai batason yanke masa hukunci, bata son yin tsalle ta fada inda tunaninta yake janta.

“Kona koma ni kadai ne.”

Ya kara fada cikin wata irin murya.

“Kibarni in kwana anan…”

Hannu take so takai ta dafe zuciyarta ko zata rage saurin bugun da take kafin ta fito waje, ta kuma kasa dauke idanuwanta daga cikin nashi.

“Dan Allaah…kinji.”

Ya karasa cike da rokon daya dauketa ya wullata wani lokaci can baya, ranakun tafsir a Islamiyya, daya daga cikin tafsirin Surah AI-Mu’minun, Ayat 12–14 inda akayi magana akan halittar dan Adam. So takeyi ta tuna ko akwai abinda zai iya zama kankara a tare da ita, wani abu dai da idan aka kara masa wuta zai narke ya zama ruwa, saboda abinda kalaman Jabir suka haifar mata kenan, wani abune taji ya narke yana binta daga cikin jikinta, abinda batasan ko menene shi ba.

“Kibani riga da wani wando da zan iya sakawa…ba zan iya kwana da kayan jikina ba.”

Sai lokacin tayi jarumtar sauke idanuwanta daga cikin nashi da taji kamar sun riketa a matsayin ganima a yakin da batasan lokacin da aka fara shi ba. So takeyi ta mike, amman bugun zuciyarta ya kwashe duk wani karfi da take tare dashi, saida ta dafa kujera tukunna ta iya mikewa ta nufi dakinta, ta karasa wajen wardrobe ta rike murfin tana haki kamar wadda tayi gudu, so take ta tattaro nutsuwarta, da tunaninta gabaki daya ko zata iya hassala wani abu, amman Jabir bai bata wannan damar ba, kamshin shi ta faraji bayan turo kofar da yayi, sai kuma ya zabi yazo ya tsaya a gefenta, ta fito da duka wasu kananun kaya da suke cikin akwatinanta, haka kayan bacci ma, yanda zasu dinga yi mata saukin dauka. Haka kayanta da tazo dasu daga gida, suma suna nan sai kamshi wardrobe balls din data jefa ke fitowa.

Data bude wardrobe din, taji kamar jikinta rawa yakeyi, sai dai murfin ya danyi mata tsakani da Jabir, hakan ya bata damar maida numfashi, haka kawai sai hannunta ya nufi bangaren da kayanta na gida suke, ya sauka akan wata riga, koriya ce mai haske, Habibu ne ya siyowa Abdallah lokacin, tayi tsaye ta saka rigimar ita bai siyo mata ba, saiya dauki wannan ya bata, sai daga baya data bude taga girman rigar ta dinga dariya, koshi Abdallah dinma tayi masa yawa, haka Habibu ke siyo masa su yaita yawo a ciki, sai dai rigar na da laushi tunda cotton ce. Nabila saida tace ta mayarwa Abdallah taki, ta bude jakarta ta sakata daga can kasa, lokacin batajin anyi wata daya da wannan diramar, Habibun ya rasu, rigar saita zame mata wani abu da take matukar riritawa, haka kawai ma saita daukota ta ajiye a kusa da ita ta kwanta idan kewar Habibun tayi mata yawa.

Zata kirga ko sau nawa ta taba sakata a jikinta, duka yan gidansu kowa yasan muhimmancin rigar a wajenta, shisa ma suka hado mata da ita, bata gama yanke shawarar zata ba Jabir ko zata dubo masa wata ba, taji shi ya zagayo, ya kuma mika hannu ya karbi rigar da take rike da ita.

“Wando fa? Bacci fa nakeji, ki dauko mun da sauri…”

Batajin tana da wani wando da zaiyiwa Jabir, kamar ya kula da hakan yace mata.

“Barshi kawai…rigar ma zatayi”

Ya raba ta bayanta ya wuce yana nufar bandaki, tana jin alamar wanka yakeyi. Saita koma falo ta zauna zuciyarta na cigaba da bugawa. Jabir zai kwana a gidanta yau, Jabir fa, gidanta da zata kirga sau nawa ya taba awa biyu a cikinshi. Yau kwana zaiyi, kallon da takeyi ma sai taji ya fita data kanta, taje ta kashe ta dawo ta sake zama, duk girman gidan, duk kuma fadin dakin, data mike tsaye saita rasa inda zata sa kanta. Fa’iza sanda tazo ne take ce mata tayi kokari ta dinga ganin suna canjen dakin kwana, saboda bakyau a dinga barin sauran dakunan haka, sai take danyi, amman dai tafi son inda Jabir din yake, yanzun can zata koma su kwanta? Amman ai da ya nemi ya kwana, bataji inda yayi jimla yace tare da ita ba.

“Kinga ki rufawa kanki asiri ki tafi wani dakin.”

Kwakwalwarta ta bata shawara, dan zuciyarta gaya mata takeyi taje dakin da Jabir din yake. Data dauki wayarta saita nufi dayan dakin da yake kusa dashi bayan ta kashe wutar falon. Ta nan dinma a kashe take, tana sharewa kullum, in kuma ta kunna turaren wuta ko ina take kaiwa. Da hasken wayarta tayi amfani, ta kusan awa daya a kwance kafin ta dan fara dawowa cikin natsuwarta, ta karanta Surah Al-Mulk, tayi addu’ar bacci. Saita fara jero Istighfar. Bata san lokacin da bacci ya dauketa cike da tunanin Jabir ba. Jabir da anashi bangaren duk baccin da yakeji yana kwanciya saiya neme shi ya rasa, inda duk ya juya bakon kamshi yakeji, kamshin da yake tuna masa ba a gidanshi yake ba, yana bakon waje, amman tare da Sa’adatu. Yaja daya daga cikin filon da yake kan gadon ya rungume ya rufe idanuwan shi, amman fur bacci yaki bashi hadin kai, zuwa wani lokaci ma sai ya soma jin kanshi na sarawa, ga Sa’adatu taki shigowa, ya kuma sa karfi ya ture duk wani tunani da yake kokarin ce masa inta shigo menene?

Ya rungumi wanda ke fada masa shigowarta na da muhimmancin, shigowarta na nufin zai samu bacci. Da yaga alamar lokaci naja sosai saiya mike ya dauki wayar shi ya haska da ita, ya bude kofar, ya mamakin shi wutar falon a kashe take, cikin falon ya karasa yana haskawa ko tana kan kujera yanda tayi masa a Abuja, sai kuma ya tuna ai nan akwai wasu dakunan har biyu da zata iya zuwa ta kwanta, batare da wani tunani ba ya nufi daya ya bude ya haska, bata ciki, yaja kofar. Daya nufi dayan saiya tura a hankali ya shiga ciki. Ya kuma nufi gadon kai tsaya, a hankali ya hau gudun karya tasheta, kuma da niyyar ya kwanta a dayan gefen ya shiga dakin, daya hau gadon ne wannan niyyar ta murmushe tabi iska, sai gashi ya matsa sosai, ya zagaya hannun shi ya riko Sa’adatu, ya kwanta a bayanta, yana saka rabin fuskarshi ta gefen wuyanta, wani irin numfashi ya sauke, numfashin da yanzun daya fito dashi zaice tun ranar walimarsu daya saka hannun shi cikin nata yake rike dashi.

Lumshe idanuwan shi yayi dai-dai da budewar na Sa’adatu da taji kamar wani abu yayi mata rumfa, da bugun zuciya ta farka, da gaske mutum ne, Jabir, Jabir ne, Jabir ne, zuciyarta ta cigaba da fadi tana maimaitawa kamar karatu, kamar kuma wani fata, saboda kamshin shi ya cika wajen gabaki daya. Data motsa sai taji ya sake riketa sosai a jikinshi, yanda yake sauke numfashi kuma na tabbatar mata da bacci yakeyi. Baro dayan dakin yayi ya biyota nan yazo ya kwanta, tun yaushe? Ko yanzun nan? Take tambayar kanta, mai bata amsar kuma gashi nan yana bacci a jikinta. Ta nemi yawu dakyar ta hadiye, tanajin yanda dumin shi yake ratsa rigar jikin shi yana ratsa tata itama yana samun waje ba iya fatarta ba har cikin tsokarta. Data lumshe idanuwanta, gayawa kanta takeyi ita da bacci kuma sai Allaah, sai dai baccin ne da kanshi ya karyatata, dan ko mintina talatin ba’ayi ba tsakani, bugun zuciyarta ya hadu da Jabir da yake rike da ita ya saukar mata da gajiyar data sa bacci yin nasara akanta.

Su duka wani irin bacci ne sukayi, gara ma Jabir zaice akwai bashin bacci akan shi, ita kuma fa? Ko da gari ya waye shiya fara farkawa, sabon shine daukar wasu mintina a kwance kafin ya mike, hasken daya gani yasan bana asuba bane ba, garine ya waye, a hankali ya zame Sa’adatu da dadin bacci yasa ta juyo, ta kuma dukunkune a jikinshi, ya zuba mata ido, bacci take mai nauyi, hular tayi wajenta daban, gashin da yakeso ya gani gashi nan, duk ya hargitse, yasa dan yatsan shi yana shafa wanda yake kwance a goshinta, ta dan motsa tana tura bakin daya kula ya rigada ya zame mata jiki, tunda gashi har cikin baccinta yin shi takeyi. Ya adana a bayan kanshi, zai tambayeta ko itace Auta a gidansu, saboda sangarta yake gani tattare da ita sosai, watakila itace Auta shisa.

Fuskarta dai tayi wani irin maiko tanata kyalli, kamar akan mai ta kwanta, musamman hancinta daya ga kamar ya dan kumbura, murmushi ya kwace masa, ba kowa bane yake kwanciya ya tashi irin Aisha, tana iya baccin awa takwas ko tara, ta mike ko launin idanuwanta basu canza ba, sai kayi da gaske ma zakaga alamar bacci tayi, kuma in bashi ya juyasu ba, zata iya kwanciya akan hannu daya daga dare har wayewar gari. Ganin idan ya tsaya kallonta ba zai tashi ba yasa shi mirginawa, wayar shi ya dauka, bakwai saura, ya mayar ya ajiye, bayi ya shiga, saida ya fara duba brush yaga sabo ya bude, ya wanke bakinshi, tukunna ya daura alwala ya fito.

Ruwan hannun shi ya yarfawa Sa’adatu a fuska saboda bayason tabata, ta kuwa bude ido tana dakuna masa fuska, sai kuma tayi wata irin mikewa tana kara gyara rigarta hadi da kai hannu tana kwantar da gashinta da wasu sassa suka tattashi, dariya ta bashi, gyare-gyaren me takeyi? Ko bata ga ya rigata tashi bane ba? Idan ma wani abin take boyewa ya rigada ya gama gani, sai kawai ya juya ya fita daga dakin da murmushi a fuskar shi. Yana turo kofar Sa’adatu ta diro daga kan gadon tayi bandaki, ta nufi mudubi tana kallon kanta. Fuskarta duk tayi kumburin bacci, wama ya sani ko bakinta a bude yake, duk ya gama gani, tasan in tana bacci, yinshi take bilhakki, shine ma dalilin dayasa take kwana da dogon wando tun daga yarinta saboda yanda take bajewa, ta sha dirka wajen Abida, haka ma Yayyenta data wakilta in sunga tayi wannan bajewar, ganin ta kasa dainawa yasa Abida wajabta mata kwana da dogon wando.

In har Jabir anan zaici gaba da kwana har Aisha ta dawo, kuma zai dinga biyota ko ta bar masa daki, dole ta koyi kwanciyar yan gayu, irin ta matan novel, yanda ko motsi tayi zaiji ta burgeshi. Numfashi taja ta girgiza kanta, tana ka dibar ruwa ta wanke fuskarta, saboda bata san hadinta da son burge Jabir ba kuma.

<< Tsakaninmu 37Tsakaninmu 39 >>

1 thought on “Tsakaninmu 38”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×