Skip to content
Part 61 of 67 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Kuma wannan kalmomin sune sukayi masa jagora suka kawoshi inda yake yanzun.

“Ta haihu, tana da yarinya, Kausar. Dinaar”

Bashir ya fada masa yana dorawa da

“It’s really not my place, baima kamata in fada maka aurenta ya mutu ba, amman kaine, Sa’adatu ce, bansan waya kamata ya sani ba idan ba kai ba.”

Shi dai yanzun da yake kallon Sa’adatu baiga duk wannan abubuwan da Bashir ya fada bai gansu a tare da ita ba, baiga auren da tayi ba balle kuma haihuwa, haka baiga rabuwar aure ba, baiga komai ba sai Sa’adatu, Sa’adatun shi. Shi daman bai taba cewa soyayyarta ta bar zuciyarshi ba, baima taba kokarin cireta daga zuciyarshi ba, to akan wanne dalili ma zaiyi hakan bayan ya san har abada zata kasance wani bangare na rayuwarshi duk kuwa da bata cikinta.

“Ina wuni.”

Sa’adatu ta tsinci kanta da furtawa saboda shirun yayi mata yawa yana kuma yi ma zuciyarta wani irin duka, abubuwa ne suketa taso mata.

“Asabe akace tayi asirin daya rabasu fa.”

Maganar Anty Talatu ta fado mata, da ma maganganu makamantan wannan da ta zabi ta toshe kunnuwanta, ta hanasu yi mata tasiri, saboda idanma ta barsu, idan ma taji haushi amfanin me zaiyi mata? Bayan Asaben ta rasu, bata nan balle ta dauki alhalin komai ta dora mata, amman a yau, da ta sauke idanuwanta akan Tahir sai komai yake ta dawo mata, kamar ciwukan da tayi tunanin sun warke sai tabone suke ta budewa suna neman fara zubar da jini.

Da yanzun tana gidan Tahir.

Da yanzun suna zamansu cikin rufin asiri.

Hayatee din da Bashir baya gajiya da turo mata hotunanta da yanzun ‘yarsu ce.

Da ba zaune suke a haka ita da Tahir din ba, cikin gida zasu shiga ana musu maraba saboda sunzo ziyara.

Da yanzun…

Da yanzun…

Duka saboda son zuciya sai Asabe ta zabi ta datse musu wannan kwanciyar hankalin.

“Dinaar din fa”

Wani sashe na zuciyarta ya fada mata, da duk hakan bai faru ba da bata sameta ba, ya kamata ta duba wannan bangaren, amman dai…amman dai ciwon da yake taso mata ta sassa daban-daban na gaske ne, dan tanajin hawayen da suketa mata barazana

“Sa’adatu…”

Muryar Tahir ta ratsa dodon kunnenta, haka kuma amon da yake cikin muryar, amo ne mai dauke da abubuwa kala-kala, sunanta kawai ya kira, bai kara wani abu akai ba, amman a cikin kiran sunan nata taji abubuwan nan da bai furta ba, ta karance su tsaf.

Kewa

Kauna

Tarin kauna mai yawa.

Burikan da suka yanke kafin suyi nisa.

Hakuri, ban hakuri da neman yafiya.

Duka ta jisu, data daga kanta ta kalle shi, abinda yake cikin idanuwanshi ya kara danneta har tanajin numfashinta na mata barazana.

“Sa’adatu…”

Ya sake kira, saita saka hannu ta dauke kwallar da ta zubo mata.

“Na yafe mata Yaa Tahir, na yafe mata duniya da lahira. Allaah Yasa tana cikin salama Ya kuma sanyaya mata kabarinta.”

Hannuwanshi duka biyun Tahir yasa ya dafe fuskarshi, wani irin sanyi-sanyi ne yake rantsa duk ilahirin jikinshi, jijiyoyin shi da suke a kulle suna warwarewa, sai yaji yanayin iskar wajen ta canza, sanda ya bude fuskarshi zai rantse har kalar hijabin Sa’adatu ta kara haske a idanuwanshi, komai ma ya kara kyau, ya kara fitowa tar, kaman anyi masa wankin ido, haka bayajin komai a tare dashi sai haske.

“Alhamdulillah”

Ya furta a hankali, ya maimaita yana sake maimaitawa a cikin zuciyarshi, ya sake kallon Sa’adatu da duk da alamun hawayen da yake idanuwanta murmushi takeyi masa, ita kanta sai take jinta sakat, kamar an dauke mata wani nauyi da ta jima tana yawo dashi, kuma yanzun da take kallon Tahir sai take jinshi a wani bangare na rayuwarta da ba zata iya kankarewa ba, watakila zata jima idan ta tunashi tanajin ciwon rabuwa dashi, tabo ne yabar mata, watakila kuma tabon ya bace mata a cikin abubuwan da yau da gobe take tafiya dashi. Amman a yau dai, ga Tahir zaune a kusa da ita, gata zaune a kusa dashi batare da nauyin komai akanta ba, sun sake halatta a tsakaninsu, amman batajin komai, batajin son sake zaman aure dashi ko na minti daya, duk da tanajin da ace basu rabu ba da yanzun suna tare.

Shikenan, iya nan tunanin ya tsaya mata, da ace… Kuma sai basa tare, kaddara ce ta rantse akansu, kuma sun faru gashi har sun kare kamar ba’ayi ba, sai dai tashin zancen, sai idan an lissafa matan daya taba aure a lissafa da ita, kuma ko da take ganin kaunarta a idanuwanshi, bata ga komai ba bayan wannan, bata ga wata alama ta nuna yanaso ya sake raya wannan soyayyar ba.

“Nagode…”

Saita jinjina masa kai, tana kuma fatan ya karanci cewa godiyar shi batayi mata kadan ba, kuma ko bai furta ba tasan ya gode.

“Ina yarinyata, ko rowarta za’ayimun”

Dariya tayi.

“Ni na isa, bacci takeyi, matar Yaya ta goyata, amman bari in karbo maka ita.”

Saurin girgiza mata kai Tahir yayi.

“Haba dai, barta tayi baccinta, zanyi mata nata zuwan na musamman, ina Yaa Abdallah? Ya kowa?”

Gyara zamanta ta danyi kafin ta amsa masa.

“Kowa yana lafiya, Yaa Abdallah inajin wani abinne ya tsayar dashi, amman kowanne lokaci yana iya shigowa, shima yana nan lafiya. Ya kake? Ya Madam da Hayatee?”

Wannan karin shi yayi dariya.

“Suna lafiya, suna Lagos.”

Dan ware idanuwa tayi.

“Yaa Tahir kayi mana nisa da yawa, har Lagos?”

Sa’adatu ta fada da mamaki, shisa ya bace bat, kaman bai taba zaman Kano ba, ashe Lagos ya tafi ya boye, hira ta bude a tsakaninsu, kamar basu dauki wasu shekaru basa tare ba, su duka suna tuna ai kafin ma alakarsu ta canza, su din kamar abokai ne, kamar kuma Yayaa da kanwarshi. Shiya duba agogon hannunshi.

“Tafdin, danfa kece da yanzun Bash ya hayyaceni.”

Dariya tayi sosai, ya tuna mata koma gaisawa basuyi da Bashir din ba ya fice, mikewa Tahir yayi.

“Bari kiga, dan na tabbata kawaicin nan ke kadai Bash yakeyiwa, da yaga mu kadaine zai sauke mun kwandunan daya tara.”

Dariyar ta sakeyi, ta mike itama, sai tayi saurin saka takalmanta tana shigewa gida, ledojin da suka rigada suka hada ta dauko. Tazo tana bashi.

“Dawainiya ko Sa’adatu?”

Tahir ya fada lokacin daya karbi ledojin yana dorawa da.

“Mu da muka taho daga nesa bamu kawo tsaraba ba.”

Kai ta girgiza masa.

“Haba ai gida kukazo, daman ya kamata ayi muku tanadi.”

Sai ya numfasa.

“To mungode kuwa. Allaah Ya saka da alkhairi Ya bar zumunci.”

Har bakin kofa Sa’adatu ta taka masa, sai kuwa sukaga Bashir zaune a cikin mota, ya bude murfin yana danna wayarshi, ya dago kai ya kallesu, Sa’adatu tayi dariya, sai ya harareta.

“Kiris kawaicina ya kare, ina shirin lekowa inyi magana.”

Tahir ya kalli Sa’adatu.

“Aina fada miki.”

Dariya ta sakeyi.

“Kace dana leko ma, tunda gulmata kukai tayi.”

Sai lokacin kuma Sa’adatu ta gaishe da Bashir ya amsa, tukunna tayi musu sallama gabaki daya. Ta koma cikin soron, saida ta tattara dardumar data zauna da wadda Tahir ma ya zauna tukunna ta shige gida. Bata boyewa Fa’iza yanda sukayi da Tahir ba, ta kara da.

“Jina nake sakat Matar Yaya.”

Sai Fa’iza tace.

“Ai riko abune mai nauyin gaske, duk da tarin ladan da aka tanadarwa masu yafiya da kuma matsayi a lahira, tun a duniya ma zaka fara cin ribar wannan yafiyar, saboda zaka rabu da kuncin zuciya, zaka kuma kara samun fili a cikin zuciyar taka…”

Kai Sa’adatu ta jinjina.

“Hakane wallahi, amman yafiyar ce akwai wahala, wani abin idan akayi maka matar Yaya sai kaji kamar kawai ka rama da kanka, karma ka jira aje can.”

Suka danyi jim kowa na tauna maganar, sun jima kuma suna hira, har Abdallah ya dawo, nan suka yayyanka kayan marmarin daya shigo dasu, suka bude wani sabon shafin hirar, Sa’adatu ta fara tashi dan idanuwanta sun fara yi mata yaji, data shiga daki ko ta kan wayarta bata bi ba, ta kwantar da Dinaar ta sake kaya itama ta kwanta. Sai da asuba ta dauki wayar, da sakon Bashir ta fara cin karo ta twitter.

“Zobon nan yayi mun dadi, dan ance ba’a yarda da review dina in dai akan kaza ne, amman na cinye nawa, duka, da na fara bacci sai in tuna dadin dambun naman nan, sai in farka in kara, saida na cinye hankalina ya kwanta.”

Zata bashi amsa kawai wani sakon ya shigo, wannan karin ta text message, kuma sai da zuciyarta tayi tsalle ta kara ganin Jabir ne, wani irin yanayi taji yana saukar mata, ta bude sakon.

“Ya kuka tashi?”

Shine abinda ya fadi, to daman Jabir na dogon sakone? Kome zai rubuta ai saiya rarrabashi ko da kuwa a WhatsApp ne, wata zuciyar tace ta share shi, tunda sassafe, sau nawa yanzun sai yazo kofar gida zai kirata yace ta fito masa da Dinaar tunda yasan lokuttan da take zuwa makaranta da sanda take dawowa, idan sakone kuma sai dai taga direba ya kawo mata, inma kudine sai dai ta gansu a account, yau ya bushi iska kenan, ko kuma mafarkin Dinaar yayi shisa yake son addanarta da sanyin safiyar nan. Sanin cewa yana iya biyota da kira idan yaji shiru yasa ta bude camera din wayarta ta dauki hoton Dinaar da take bacci ta bude WhatsApp dinta ta tura masa da caption din.

“Lafiya lau”

Ta sauka ta koma twitter din, sai dai ta jima bayan ta amsawa Bashir sakonshi bata ga reply ba, sai itama ta sauka, ta karasa azkar dinta. Ta koma ta kwanta a gefen Dinaar. Bacci kuwa ya sake daukarta.

*****

Kuma kamar yanda Bashir yace mata,

“Tahir na rako, zanyi zuwana daban.”

Ya cika alkawarin shi, bayan kwana biyu sai gashi, a makaranta ma ya sameta da yamma, suka samu wata bishiya sukayi zamansu sunata fira, ko da direbanta yazo daukarta sai Bashir din yace ta sallame shi saiya mayar da ita gida, haka kuwa tayi, daman akwai wani lecturer dayace zaiyi musu test, class rep din yana ta kiranshi yaki daga wayar, to duk ana tsoron tafiya kuma yazo tunda ansan yanda yayi tambari wajen rashin kirki. Sun kara wajen mintina talatin kafin ta samu sakon cewa ba zaizo ba, dan haka itama ta mike, Bashir na tayata daukar jakarta da babybag din Dinaar, ita kuma tana goye da ita, suka nufi wajen da yayi parking din motar shi, saida ta kwance goyon Dinaar, tanata kalle-kalle, sannan ta shiga motar Bashir din.

Kamar kuma jira wayarta takeyi ta zauna ta dauki ruri, Bashir ne ya mika mata jakar, ta karba badan tayi niyyar ko ciro wayar ba, sai dai kira aka cigaba dayi babu kakkautawa, hakan yasa ta mika hannu ta ciro wayar daga jakarta, ta duba, Jabir ne. Sai wani abu kamar tsoro ya dirar mata, lokaci daya kuma taja wayar tana sakata a dan jirgi. Ta kuma mayar da ita a cikin jaka. Tana kallon Bashir taga ya nutsu yana nazarinta.

“Baban Dinaar ne.”

Maganar ta subuce mata, saiya jinjina kai kawai, ya tayar da motar, kamar kuma ya kula da yanda ta rasa sukuninta saiya kunna karatun Qur’ani a cikin motar har suka karya kwanar gidansu, inda taji zuciyarta na neman fitowa waje data hango motar Jabir. A nutse Bashir ya samu yayi parking, ya kashe karatun yana kallon Sa’adatu da ta birkice lokaci daya, a gefe guda kuma tanajin haushin kanta ya turnuqeta, duk yanda zata yakice Jabir, duk yanda zata ture shi gefe, da ta dora idanuwanta akanshi sai komai ya nemi kwance mata.

“Ki natsu Sa’adatu, muje in rakaki da jakunkunanku, in kika mika Dinaar saiki fito kuyi magana.”

A hankali ta daga masa kai, tana neman inda zata aro nutsuwar ta sakawa kanta, Bashir ya fara fita ya zagaya ta bangarenta, ya karbi jakunkunan, ya jira ta fito rike da Dinaar a hannunta, lokacin kuma Jabir ya fito daga cikin tashi motar ya jingina bayanshi a jiki ya zuba musu idanuwa kamar mashi zai fito ta cikinsu ya tsiresu gabaki daya. Kafafuwanta babu kwari take takawa har suka zo inda yake, sallama Bashir yayi masa, Jabir din ya amsa shi da wani irin kallo kamar idanuwanshi zasu fado, gajeran murmushi Bashir yayi, ya wuce gaba har bakin kofar gidan, Sa’adatu da take bayanshi tazo ta wuce da sauri tana shigewa ciki, saida ta kai Dinaar ta dawo ta karbi jakunkunan, Bashir ya koma motarshi yana dauko wata katuwar leda ya dawo ya tsaya, tana fitowa ya mika mata yana fadin.

“Sai munyi magana, bari in tafi kafin mutumin can yazo ya kamani da dambe, kinsan ba hakuri gareni ba, cikin ghetto na girma, mun saba gwagwarmaya, dukan tashi ka sha gishiri zanyi masa, ba kuma naso Dinaar ta kullace ni.”

Sa’adatu bata san lokacin da dariya ta kwace mata ba, Jabir ba karami bane ba, a tsayi ma zatace yafi Bashir din, sai dai shi Bashir a dunkule jikinshi yake, ta kowanne fanni ya nuna alamar karfi, kuma ko tayi rantsuwa da wahala tayi kaffara, Jabir bai taba fadan da za’a gwada yar kashi ba, Bashir kuwa ko bai fada ba, kana kallonshi kasan rigimamme ne na gaske, an kuma sha kwasar yan kallo dashi a unguwa, kuma hakan ne, dan ko tasowarsu irin gaddamar nan ma ba’ayinta da Bashir, yana da saurin hannu, ga fadanshi kamar kurma, baya rabuwa, haduwa goma zakuyi saiya sake nada maka duka. Har Bashir ya juya bata iya bashi amsa ba saboda dariyar da takeyi, yanzun kam duk kallon da Jabir yake watsa mata kamar kiris yake jira ya rufeta da duka saiya daina fadar mata da gaba.

Zuciyarta ta nutsu waje daya, a nutse ta karasa inda yake

“Waye wannan?”

Jabir din ya tambaya muryarshi a dakile.

“Bashir”

Ta amsa har lokacin tana murmushi, musamman da ta kalli fuskar Jabir din da kumatunshi da har yau din nan bata manta laushinsu a hannunta ba, sau nawa yake bacci take latsa jikinshi ta latsa nata cikin fata da inama ace itace da laushin fata irin nashi, tunda har halawar da tsautsayi yasata mika hannu da bikin Nabila aka manna mata ta tuna, saida aka danneta aka karasa cire mata shi, ashe duk rashin hutu ne da talauci, abubuwan da kudi suka bari ba masu yawa bane ba. Haka zaka ga masu kudi luwai-luwai sai tashin kamshi suke. Tunda tsakanin Jabir da rana idan ya fita a cikin mota ne, daga motar kuma ya taka ya shiga inda zaije. To idan dambe ya kama tsakaninshi da Bashir ai dole ne yaji jiki, naushi daya kumatun nan sai tashin zance, ga Jabir da son jikinshi, watakila sai an hada da tuwon kasa.

Sosai kuma take kokarin danne dariyarta, shisa bata wani fahimci bambamin fadan da yakeyi ba, ta daiji.

“Idan zaki shiga motar wani kato, ki dinga kirana kina fadamun saboda insa a daukomun ‘yata a dawomun da ita gida, babu yanda za’ayi ki dinga shigarmun motar kowanne stranger da ita.”

Kai ta jinjina masa tana fadin.

“To, In Shaa Allaah”

Dan har lokacin cikin nishadi take.

“Ina wuni, ya Na’im?”

Bata kuma jira ya amsa ba ta sake cewa.

“Zaka ga Dinaar dinne? A gajiye na dawo wallahi, inaso in shiga ciki in huta.”

Saiya tsaya yana kallonta da mamaki akan fuskarshi.

“Jeki to…”

Ya furta cikin gatse yana dubanta.

“Ka gaishe da Na’im da Maman shi.”

Sa’adatu tayi maganar tana juyawa ta shige gida tabar Jabir tsaye yana kallon kofar gidan, to ai a labari yake jin wulakanci, bayajin an tabayiwa wani a gabanshi ma balle kuma shi da kanshi.

Shifa

Jabir Hassan Paki

Shine mace ta wuce ta bari a tsaye kamar batayi komai ba.

 

<< Tsakaninmu 60Tsakaninmu 62 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×