Haka kwanaki suka dinga tafiya Al’amura na juyawa acikin rayuwar Widad da ahalinta, zuwa yanzu ta fara gajiya da batun Murtala walkiya da na Hisham domin sun sakota a gaba sosai, kasancewar Hisham a cikin makaranta yana lura da takun SIR MURTALA WALKIYA wanda labari yaje masa har kunnansa , domin yasa asawa Widad ido sosai dan Hisham mutum ne mai kishin masifa , kuma a yanzu ji yake kamar Widad tasa ce dan Mami tana goyan bayan alakarsa sa da Widad sosai , ita dince har yanzu bai sami kanta ba.
Ban garan Murtala Walkiya kuwa kullum yana cikin kaf!kaf. . .