A rikice ya dago yana duban wacca tayi maganar ,cikin bacin rai yace”Munira ni kikewa tsawa?” cikin ko in kula da rashin ishashiyar tarbiya ta ce” Daddy nifa tambayarka nayi waca ‘yar iska ce wannan?ko da gaske ka fara bin yaran mata sa’anin jikokin ka da sunan aur…” bata kara bay a sauke yatsunsa guda guda biyar akan kuncinta yana huci yana nunata ya fara cewa” daman da gaske ne tabarar da ake cewa hajjan tai miki, banga laifin Shuraim ba dan yaki auran mara tarbiya irinki ba, a cikin mutane ki dubeni ki fadan wannan maganar. . .