Skip to content
Part 3 of 5 in the Series Tsinuwar Uwa by Salis M. Reza

Sosai Siyama ta samu alheri ga kuma mutane masu neman lambar ta, wasu kuma burinsu suyi hoto da ita, haka dai al’umma suka hanata samun lokacin da zata zanta da ƴan team ɗin ta har sai da komai ya lafa. Shugaban team ɗin nasu mai suna Oga Fita shine ya fara zuwa gurin ta, yana zuwa kuwa ya ware hannuwa cikin farinciki itama baki har kunne ta shige jikin sa har yana ɗaga ta yana yawo da ita a sama kamar ƴar Baby, ya ce ” You are the best Siyam! I no you can do it thank you Siyam! Ya faɗa yana ƙara ɗagata. Itama sai dariya take tana jin daɗin yabon da kowa yake mata. Bayan ya gama ne sauran ma suka zo suka fara nasu suna ta murna ana rungume ta. Ita dai tasan masu taya ta murna har zuciya, kuma tasan munafukai karmar dai wannan ta gaban nata mai suna Adawiya da ɗaya ƙawar tata mai suna Badawiya, tasan yarinyar bata sonta tun lokacin da Oga Fita ya fitar da ita akan ita zata wakilci team ɗin su, tun daga lokacin yarinyar ta fara gaba da ita, kuma ta hana sauran members ɗin ma, yanzu ma ta tabbatar da cewar basu ji dadin wannan nasarar ba, kawai dai babu yadda za suyi ne. Wani irin kallo Adawiyar tabi Siyama da shi, har tana cije baki, ita dai bata ko ce mata komai ba, domin yau ranar farinciki ce.Aida ce ta ce “Ke manta da ita aniyar ta ta bita, duk zakaran da Allah ya nufa da chara, to wallhi ko ana ruwan muzuru da shirwa sai yayi”. Aida ita ce babbar ƙawar Siyama, kuma a bokiyar shawarar ta, sannan tafi kowa bada gudunmawa a wannan nasarar ta Siyama domin kuwa ita ke tsaya mata a komai duk da cewa itama taso ta wakilci team ɗin nasu amma Allah bai yi ba. Siyama tayi dariya suna ci gaba da hotuna.

*****

YAYA BALA

Ana gama komai ya samu ɗaya daga cikin shugabannin kamfanin nasu ya sanar da shi zai tafi gida yanzu idan an gama komai sai yasa a gyara gurin, mutumin ya amsa da to in sha Allah. Haka Yaya Bala ya tattara iyalan sa suka bar gurin duk ransa a ɓace. Ita dai Anty Zainab jikinta ne yayi sanyi sosai tana so ta sake yiwa Yaya Bala magana amma tana tsoro, ko da suka zo zasu shiga motar sai da tace karyayi tuƙi a haka ya bata ko ya bama Nasiru amma Yaya Bala ya daka musu tsawa. Haka dai suka ja baki suka fara tafiya duk a tsorace.

*****

SIYAMA

Siyama kuwa basu bar gurin ba sai bayan sallar magriba, bayan sun gama amsar duk kyaututtukan su. Lokacin da suka isa office ɗinsu ko nace gidan su da suka saya na team ɗin su, sai Oga Fita ya nemi da Siyama ta kwana a nan zuwa gobe sai ta tafi, saboda yanzu dare yayi kuma wasu zasu iya bibiyar ta, duk da kuwa yasan bata kwana a gurin, kuma yasan duk wannan abun da take yi babu sanin iyayenta. Siyama ta ce ita ba zata kwana a gurin ba, gida zata tafi yanzu ma haka tsoro take ji. Haka dai Oga Fita ya sako ta a mota ita da Aida, bayan ya sauke Aida ne ya faka a gefen titi ya juyo ya kalli Siyama wacce ta yi nisa a tunanin halin da zata shiga idan taje gida. Cikin harshen turanci ya fara mata magana kamar dai yadda tun tuni ya saba akan ta bar gidan iyayen ta dawo nan da zama tana da kyau zata iya zama komai da ta ke son zama a duniya, kamar yadda tun farkon haduwarsu ta sanar masa da ƙudurinta, amma yanzu iyayen ta sun hana ta sakewa, bata ganin sauran ƴan matan da suke tare da shi ne. To duk idan yayi mata irin wannan maganar bata yarda domin ita batayi wannan ƙwarin kan da zata ma iya mayarwa da yaya Bala magana ba bare kuma ma Umma. Lokacin da ta tuno da Umma sai da gabanta ya faɗi domin ba karamin shakkar ta suke yi ba. Ya ce “Siyam yanzu ke ba kamar yarinya bace, ki sani yanzu sunanki da fuskar ki sun zagaya duniya, saboda haka yanzu kin fara zama salebiriti, babu inda zaki shiga a duniya da za’a wulaƙanta ki, kuma babu abun da zai iya gagaranki yanzu a gidan duniya. Kin ga yanzu kina da motoci sun kai goma, ga zunzurutun kuɗaɗe wanda har yanzu babu wanda yasan lokacin da zasu daina zuwar miki, saboda haka, ina so kiyi amfani da kuɗin ki ki jawo hankalin iyayenki, idan kuma basu yarda ba, to yanzu ba da bace, kizo duk irin gidan da kike so a garin Abuja zaki saya. Siyama dai sai jin sa take yi, tana sauraron shirmen sa, domin kuwa ita tasan ko giyar wake tashs ba zata iya duk wadannan abubuwan ba. Ita yanzu Babbar damuwar ta ma ta ƙarass gidan ko yankanta ne Yaya Bala yayi kowa ya huta. A haka Oga Fita ya kaita har ƙofar anguwarsu domin bata yadda yaga gidan su ba, Kallonta yayi ya sake cewa “Dubi unguwar da kike dan Allah Siyama, ki tsaya dai kiyi tunani. Yana faɗa ya mika mata wayar ta da take a kashe tun lokacin da ta isa gurin taron.

A hankali ta tura ɗan ƙaramin ƙofar gin nasu mai ɗauke da wani tsohon get ɗan ƙarami ta shiga, ta kalli gurin da yake ajiye tsohuwar Motar sa amma bata ganta a gurin ba, lokaci ɗaya gabanta ya fadi, basu dawo ba kenan, ta ci gaba da tafiya tana jin gabanta na ƙara faɗuwa. Kafin ta ƙarasa cikin gidan taji ana kiran sunanta. A ɗan tsorace ta juyo jin muryar Ibrahim, ai kuwa dai shine, yau ma dai kamar jiya ko wanka bai yi ba, waɗannan kayan ne dai na aikin sa, dukda kuwa yace yau basu da aiki domin yau Lahadi ranar hutu ce, amma gashi da kayan aiki, take ranta ya ɓaci. Ya ce “Zuwa na kenan sai kuma na hango ki zaki shiga gida shine na kira ki”. Ya faɗa yana murmushi yana binta da kallo ganin yanda yau ta rufe gashin kanta, ga kuma wani irin kyau da tai masa, ga doguwar rigar ta tasa bai taba ganin ta da ita ba. Sosai asalin kyawun Siyama ya baiyana wanda shi kansa sai da ya ƙara tabbatar da cewar gaskiya Siyama matar manya ce, domin shi wallhi sai yaga yau ma kamar ba zai ma iya kallon cikin idon ta ba tsabar kwarjini. Sai kawai ya tafi tunanin shin me Siyama ta gani a tare da shi tace tana sonsa, gashi baƙi, talaka ƙazami,mara wayo kamar yadda ake cewa, anya kuwa bai yaudari kansa ba, to dama yana da kuɗi ne sai yace sabo da kuɗin sa ta ke sonsa. Ta ce “I B (Kasancewar wani lokaci bata ce masa Ibrahim sai tace IB)jiya fa na ƙara tabbatar maka da cewar ka daina zuwa idan baka yi wanka ba, kuma gashi ka ƙara zuwa haka” Ta faɗa da ɗan damuwa a muryarta. Wani suna da ita ta saka masa wanda yanzu kusan duk unguwar haka suke kiran sa da shi, duk lokacin da ta kira sa da I B wani irin farin ciki yake ji. Ya ce “Wallhi aikin motar jiya ne, sai yau muka ƙara sa ta, ina gida oga ya kirani wai dan Allah muzo mu ƙarasa masa yau zai tafi da ita ne, to shine fa naga yauma dare yayi, kin ga kuma idan takwas ta wuce bazan samu damar ganin ki ba shine yasa na ce ko ganin ki  nayi. Ya ƙarasa yana ƙoƙarin ganin ta ina suka dace da Siyama. Ta ce “To sannu da aiki, yau dai an gama da wannan motar kowa sai ya huta ko?  “Hamm sosai fa, ai gobe idan na fara hutu sai rana ta fito. Ya faɗa yana dariya. Kafin tayi magana wayarsa ta fara ƙara. Yana dagawa ya ce “Ina zuwa gani nan. Siyama ta kalli wayar hannunsa, a fili ta ce “Wannan wayar dai kai jin daɗin ta kake yi ko? Ibrahim ya ce “To yaya zan yi ko bana jin daɗin ta, bari dai kuɗi su shigo in sha Allah zan samu ƴar babba nima na siya ko fecbook da TikTok ɗin nan da ake faɗa nima na fara.  Ya na faɗa ya miƙa mata ledar hannunsa yana fadin sai da safe. Karmar ta ce a’a, amma ta amsa tana masa sai da safe ganin yana ta sauri. Ya juya yana ɗaga mata hannu itama haka har ya tafi. Sai da taga ya fita kafin ta sauke ajiyar zuciya ta nufi ciki.

Da sallama ta shiga cikin falon, sai dai bata ga kowa ba, hakan yasa ta fara sanɗawa tana yin hanyar shiga ɗakin su. Har ta shiga babu wanda ya ganta. Tana juyawa ta ga Fati a gefen gado tayi kuka har idanuwanta sun yi jaa! Tana shiga itama Fati ta ɗago ai kuwa suna haɗa ido Fati ta ƙara fashewa da wani sabon kuka tana faɗin Aunty Zainab ta ta ta rasu! Cikin wani irin shok da faɗuwar gaba Siyama ta saki ledar hannunta tana tambayar ta wacce anty Zainab ɗin, mutuwa kamar yaya me take nufi? Fati ta ce “A hanyar dawowarsu daga gurin gasar ne sukayi hatsari shine wai ita ta mutu, yaya Bala kuma yana kwance rai a hanun Allah ga Nasiru shima ya samu karaya a kafaɗa da  hannun”. Siyama ta kurma wani uban ihu tana kiran sunan Yaya Bala da anty Zainab. Tashi tayi ta nufi sashen Umma tana tafiya tana kuka koda taje sai ta tarar da ƙofar Umma ɗin a rufe alamar bata gidan. Da sauri ta koma ɗaki tana tambayar fati wani asibiti suka tafi. Nan ta sanar mata da yadda itama taji wai kusa da gurin da aka yi taron ne domin waɗan da suka kira number Umma sune suka fadi sunan asibitin. Haka ta shirya ta saka hijjab ɗin ta ta fita, bayan ta sanar da Fati cewar ta rufe gidan.

Ko da ta fita wani asibiti da ke kusa da gurin da a kayi taron ta fara zuwa, ai kuwa tana ta tambaya aka tabbatar mata da cewar gurin ne. Koda taje asibitin ta tarar da Umma nata kuka domin da gaske anty Zainab ta rasu, sai yaya Bala da har zuwa yanzu bai farka ba. Umma tana ganin Siyama ta ƙara fashewa da kuka. Haka Siyama tazo suka zauna sai sharar kuka suke yi A nan asibitin suka kwana sai washegari Umma ta tafi gida ta bar Siyama a gurin, kuma har lokacin babu wanda ya farka.

Tana zaune a gurin kafin Umma ta dawo ita kuma ta ciro wayar ta. Ganin babu abun da take yi ne yasa ta kunna Data. Lokaci ɗaya ta dinga ganin saƙonni suna shigowa tako ta ina fecbook da TikTok da Whasopp. Sosai hankalin ta ya tafi kan wayar har bata san lokacin da likitan ya shigo ba. Har sallama yayi amma bata ko sani ba.tana kallon daga iya jiya zuwa yau ta samu mabiya a TikTok da fecbook na ban mamaki har yanzu ma ƙaruwa suke yi. Tana shiga Whasopp taga group ɗin su na ƴan team ɗin su, sai posting hoton ta na jiya a keyi, ga sitatus ɗin mutane ma, nan take taga message ɗin Oga Fita tana shiga tagan su da yawa,  ta fara buɗe na farko taga saƙon magana ne yana cewa ta ɗora wannan bidiyo ɗin da hotuna a shafin ta na TikTok da fecbook tayi jawabi domin har mutane sun fara buɗe account da sunanta, duk da cewar dama tana da nata mai suna Siyam Olosha wanda babu wanda yasan ta da shi a gidan su. Ai kuwa nan take ta fara posting, kafin ta yi na biyu ta fara samun like da comments, bata da lokacin dubawa hakan yasa tana gamawa da fecbook ta koma TikTok, shima bayan ta gama sai ta fara shiga comments tana kallon masu yabo da zagi. Likitan ne ya ƙara faɗin “Madam kina tare da ni kuwa?” Sai a lokacin ta jisa. Da sauri ta ɗago a ɗan tsorace ta ce “Yes ina tare da kai”. Ya ce “Ina ta magana kin mai da hankalin ki izuwa waya, alhalin zaman jinya kike yi. Kafin tayi magana taji kira na shigowa wayar ta amma ta share ta ce “Eh ina yin wani abu ne” Sosai likitan ya kafe ta da ido kamar dai itace yarinyar da tazo ta biyu a gasar jiya, kamar kuma ba ita ba, domin daga jiya zuwa yau indai kana yin media to zaka ci karo da hotunan ta. Siyama da ta lura da irin kallon da yake mata sai ta ce “Yanzu me ake buƙata?” Cikin diriricewa ya ce “Amm umm dama ɗaya ne ya farka daga cikinsu, kuma yana buƙatar abinci mai ruwa-ruwa kafin mu ƙara masa allura. Siyama ta kai kallonta izuwa gurin ai kuwa suka haɗa ido da Nasiru da ya buɗe ido yana kallon ta tun ɗazu ita bata sani ba. Ta ce “Sannu yaya Nass ya jikin? Me zaka ci? Ina yake maka ciwo? Nasiru ya lumshi ido ya buɗe yana jin jikinsa ya masa nauyi. Sallama suka ji anyi Umma da wasu daga cikin kawunansu suna biye da ita, sai Fati da ta ɗauko kwanukan abinci. Ganin haka likitan fita yana satar kallon Siyama. Daidai lokacin shima yaya Bala ya buɗe ido yana bin ɗakin da kallo. A hankali ya ce “Ina Zainab?” Kawunsu ƙanin mahaifinsu mai suna Kawu Inuwa ɗan bala’i ne na gaske, yana da faɗa sosai domin duk faɗan Umma tana tsoran sa, shine ke bin Gambon Hassan da Hussaini duk da ita Gambon Allah yayi mata rasuwa, shima Al-Hasan ɗin wato mahaifin su Siyama shima ya rasu, yanzu daga Kawu Inuwa ɗin sai Baba Husaini ɗin.

ya ce “Ka natsu tukunna Bala yanzu ta lafiyar ka ake yi”. Ganin Bala yaƙi tsayawa ne yasa suka kira likita, nan ya sanar musu cewar babu abun da ke damun sa, kawai karya ce a hannun kawai, kuma an ɗaure. Shima ɗayan karaya ce hannu da ƙafaɗa shima an ɗaure. Sai da aka zuba musu abinci sukaci ƙadan kafin aka ƙara musu allura likitan yace zuwa gobe in sha Allah za’a sallamesu, sai suje su cigaba da jinyar hannunsu a gida. Sai da barci ya ɗauke su kafin kawu Inuwa da sauran suka koma gida aka bar Umma da Siyama da Fati.

Umma ta kalli Siyama ta ce “Jiya bayan fitar su Yayanki ina kika je? Umma tayi tambayar ne badan tasan komai ba, domin ita bata ko kalli shirin ba kasancewar babu wuta. Siyama ta ɗago daga chatting ɗin da take yi da Aida ta kalli Umma. Umma cikin faɗa ta ce “Ina miki magana kina danna waya tsabar raini ko Siyama” Ai da sauri ta kashe wayar tana dawo da hankalin ta ga Umma. Umma ta sake faɗin “Ina kika je baki dawo bar har wannan abun ya faru tun safe? Siyama ta kalli Fati taga itama ita take kallo sai kawai ta ce “Gurin taron nima naje”. Umma da dama tasan dole gurin taje, domin yadda Siyama ta ƙwallafa wannan gasar a ranta tasan ko masu shiga gasar ƙare kenan. Umma ta ce “Amma ai Yayanki ya hana ki ko, kuma nima na hana ki, amma kin nuna mana cewar bamu isa ba ko? Siyama kibi duniya a hankali, yanzu gashi kina kallo yadda ake mutuwa cikin rashin shiri, yanzu da nice na mutu ina fishi da ke Siyama yaya zaki ji! Lokaci ɗaya gaban siyama ya faɗi jin kalmar mutuwa, ga kuma tunowa da yanzu fa da gaske Anty Zainab ta rasu ko. Umma ta ci gaba da cewa “Ki duba yadda yake fadi tashi akan mu, shi kansa ba wani samun kirki yake yi ba, amma haka yake kokari damu, yanzu ko wannan ba zaki duba ba ki riƙe maraicin kiba Siyama, yanzu ba kya tsoron wani abu ya dameki a hanya da kika tafi har gurin ke ɗaya bayan Uwar da ta haife ki tace karki je?. Daidai lokacin Siyama taji ƙarar shigowar message a wayarta hakan yasa ta kalli wayar ba tare da Umma ta kula ba, shigar kuɗi ne cikin account ɗin ta wanda tun ɗazu take jin shigar su. Haka dai Umma tai mata faɗa sosai wanda Fati dake kusa da ita tasha kuka ita kuwa rabin hankalin ta naga wayar ta ne. Haka dai Bayan farkawar su Nasiru Umma da Fati suka tafi gida. Har lokacin yaya Bala bai ko yi wa Siyama magana ba, yakan dai saci kallonta lokacin da take chatting yana ganin irin dariyar da take yi ko tayi murmushi. Sosai ya shiga tunanin meye laifin sa a riƙon da yayiwa Siyama, sannan tayaya har ta shiga team har ta samu damar halartar gasar batare da ta bar wata alama ko ɗaya da zai gane ba, ta yaya duk irin tsaron da ya saka mata, sosai wannan tunanin ke masa yawo akai.

Chatting suke yi a group ɗin su wanda ake sanar da ita dole sai tazo gurin aikin su wato shagonsu damin sa hannun akan komai nata, kuma ta warewa team nasu, kuma ga wasu manyan mutane dake son ganin ta. Ta ce duk Aida ta wakilceta amma Oga Fita yace, awa ɗaya aka bata ta shirya tazo, kuma ta tabbatar ta sha wanka domin ba ƙananan mutane bane zasu zanta da ita. Haka tace to zata zo.tana ɗago kai taga Yaya Bala yana kallon ta hawaye na zubo masa ta kumatu, ta kashe datar tana kallon sa, taje kusa da shi tana share hawayen ta kamo hannunsa, lokaci ɗaya ya dawo daga tunanin da yake ya riƙe mata hannun yana faɗin “Zainab baki mutu ba ko, kin dawo gare ni ko. Yana faɗa ya haɗa ido da Siyama ya sakar mata hannu ya juya kai gefe. Sai a lokacin Siyama ta ce “Dan Allah yaya kayi haƙu” Da sauri ya daga mata hannunsa mara ciwon ya juya baya. Siyama ta fashe da kuka tana toshe baki. Ta kalli Nasiru ta ce “Dan Allah yaya Nasiru” shima ya dakatar da ita. Ta juya ta fita daga ɗakin ta shiga Gurin likitan ta ce “Yanzu babu wani abu da ake binmu ko? likitan ya ce ba komai, sai maganin da zaki siya idan sun koma gida su dinga sha, amma sai zaku tafi za’a rubuta muku. Ta ce “Suma rubuta tun yanzu. Ai kuwa take ta fidda kuɗin maganin dama ita ce ta biya na komai, sannan ta kama hanyar gida. Ganin tana tafiya ana kallonta ne yasa ta samu wani guri a gefen asibitin ta tsaya ta kira Aida ta ce tazo da Mota yanzu ta dauke ta, bayan tai mata kwatancen gurin da take. Ai kuwa bata daɗe sosai ba sai ga ta nan da Mota, tana zuwa ta buɗe mata gidan gaba ta shiga. Aida ta kalleta ta ce “Ina muka nufa? Siyama ta kwantar da kanta a kujerar matotar tana tuna faɗan da Umma tai mata, ta ce “Muje gidan ki” Aida ta juyo ta kalleta bata ce komai ba har  suka isa gidan Aida ɗin da ta kama take zaune ita da ƙanwarta da ƙanin ta Jamila da jamilu. Kana shiga gidan Aida kasan ka shigo gidan Model, hotunan ta ne ta ko’ina a cikin palon, haka cikin ɗakinta, hotuna dai irin na Model wasu doguwar riga wasu iya kayan barci.

Ganin Siyamar ta kwanta a kan gado ne yasa Aida faɗin “Amma kinsan awa ɗaya Oga Fita ya baki ko? Siyama ta ce “Ban san kayan da zan sa ba, kuma ni barci naje ji wallahi na gaji tun jiya ban huta ba, kawai kije a maimako na please. Siyama ta faɗa Domin tasan tabbas Aida ita ce komai nata, zata iya rantse wa da Allah akan cewar duk wani abu nata Aida ta fita sanin sa, haka zaluka wasu abubuwan ma duk Aida ɗin ce ke mata su, haka ko a team ɗin su idan kaji Aida na faɗa to an taɓa Siyam ne. Aida ta ce “To dama waye zai tsaya jiran ki yaji kunya, ai daga yau zuwa sati daya duk na tana di kayan da zaki dinga sakawa, ai ke sai dai a barki da halinki, Malama ki tashi ki shiga wanka ko wankan ma sai na miki ne? Ta faɗa tana sauko da wata akwati mai kama da Zakara. Take ta buɗe shi ta ɗauko wata doguwar riga jaa, mai adon duwatsu sai  ɗaukar ido take yi, gefe ɗaya kuma ga taƙalmi da jaka duk irin ruwan riga, ga wata sarƙa mai tafiya da imanin wanda yasan darajar sa, kana ganin kayan kasan a haka suke zuwa a cikin wannan akwatin. Siyam na ganin haka ta shige toilet ta faɗa wanka tana tuno yadda suka yi da yaya Bala ɗazu.  Koda ta fito ta tarar da matar da take musu kwalliya tana jiranta, ai kuwa nan aka fara mata, tana gamawa ta saka kayan sannan Aida tai musu hotuna, nan take suka dora a Fage ɗin su. Sai da suka gama sannan suka fita izuwa gurin aikin su. Ita dai Siyama duk rabin hankalin ta na ga asibiti, ga shi bata sani ba ko anyi jana izar anty Zainab ko sai yaya Bala ya tashi, ko dai ɗazu da ƙanin babansu ya tafi aka je akayi, sai take ganin kamar bai dace ta bar gida yanzu ba, amma wata zuciyar take sanar da ita cewar ai yanzu zata dawo. A haka suka ƙaraso Team ɗin nasu.

<< Tsinuwar Uwa 2Tsinuwar Uwa 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×