Ya fa mutu tsohon ya kuma faɗe a rikice, cikin faɗa dattijon da ya kaɗeshi ya ce wai ta ya zaku dinga faman ƙaƙabawa mutun mutuwa ku likitoci ne, sosai hankalin dattijon ke a tashe dan shi kam bai shirya azimi sittin ba, eh mu ba likitoci bane anma ko ƙaramin yaro ya dubi na kwancen nan yasan ya mutu tsohon da yace Faruk ya mutu ya faɗa ya na nufa Faruk, Matashin saurin da ke sanye da kayan College of health ne yace muje asibiti please yanzu in bai mutu ba wannan tsayawa rikicin zai iya mutuwa tunda yana buƙatar taimako.
Kan matashin saurayin yayi wani abu tuni wasu matasa sun suri Faruk da ke kwance cikin jini sun nufi motar wanda ya bige shi.
Kai tsaye asibitin Murtala suka nufa yayin da dattijon ya ɗauki waya ya nemo sunan da zai kira bugu daya aka ɗauka. Please Ibrahim in cikin mutanen ka akwai ɗan sanda ka turomin shi asibitin Murtala munyi haɗari ne, ya kashe wayar.
Kusan tamkar tare suke da police ɗin suka ɗinguma zuwa cikin asibitin, tun agun neman gadon da za’a tura Faruk ɗin zuwa inda likita yake nurses suka faɗa musu ba gado shima gadon tura wanda aka kawo ɗin wata mara lafiya ce akai ana sa mata jini. Ran Dattijon ya ɓaci sosai ayadda yake ganin yaron da ke motar sa in har yana raye to tabbas in sukace zasu tafi subar nan zai iya mutuwar.
Ciki ya shiga yana ƙoƙarin kiran waya yayin da aransa yake ta Addu’a Allah yasa wanda zai kira ɗin ya ɗaga dan yasan wanda zai kira ɗin was quite busy, bugu ɗaya cikin ikon Allah ya ɗaga wayar.
“Please Dr Umar alfarma zaka min munzo da patient ne asibitin ku ba gado pls is their anyway to attend to us yaron yana jin jiki in munce zamu Nasarawa da ba tabbas ɗin gado shima zai galabaita in kuma munce zamu private ne shima da matsala doctors needs to do something ko daga baya ne ma tafi wani gun.”
Mutunin ya faɗawa wanda ya kira a waya ɗin cikin tashin hankalin. “Calm down prof everything will be fine am currently not at hospital anma kaje ka duk office din likitan da ya ma kace Director ne ya ce yayi attending naku yasa patient din a office din sa in ba gun sashi..”
Mutumin da aka kira da prof. ko karasa jin Director din asibitin murtalan ba ya yi gaba harda ɗan gudunsa office din da ya hanga cike da mutane ya nufa, da hanzari ya shiga office ɗin duk da tarin marasa lafiyar da ke bakin office ɗin aiko suna ganin sa suka hau mita wannan ai wulakanci ne tayaya mun riga mutun zai zo ya shige mu daman haka masu kuɗin nan suke kowa dai da irin abinda yake faɗe cikin kalar nasa ɓacin ran.
Cikin fushi Dr din da ke duba mara lafiya ya ɗago zaiyi faɗa sai dai yakasa ko dan kamalar mutumin ce oho, ahanzar ce likitan ya mike “sir welcome,” munada emergency patient ne Director Umar Khamis yace Please ka duba mana shi, ok sir Matashin likitan ya ce gami da cewa Nurse Nasir da zainab su tura gadon ya biyo su abaya.
Patient da ke kan kujera ya na bayanin meke damun sa takaici ya kama shi yahau zage zage aransa wannan ai cin mutunci ne karshan tama patient din nasu lau yake aiko bazan bar office din ba haka dai patient din ya cigaba da mita kan ya ɗauko wayan sa ya hau duba IG.
Matashin Dr din hakalin sa ya tashi dan duk da kasan cewar sa likita sai da ya tsorata da ganin jikin patient din da ake so ya duba shikam dan kar ya karya musu gwiwa da yace bazai iya ba sai dai shi ɗin likita ne dole haka yabi bayan nurse don koma wa office.
Hankalin patient din da ke ta faman mita ya mugun tashi sun tausawa wanda ke kwance agadon dan har lokacin jini ke zuba gun ya ɓaci da jini duk sai sukaji basu kyauta ba da suke zagin Dr da mutumin da yazo ya tafi dashi wasun suma sai duk suka ji tamkar sun warke dam da yawan su basu taɓa ganin haɗari ba sai yau.
Suna shiga office ɗin Dr din yace Please Nasir kaje ka kiramin Dr Mansur da Dr Nadiya kace suzo yanzu , ke kuma Zainab ki kirami Dr Mahmud da Dr Colins Please be quick ya faɗa sa’adda yake taɓa Faruk kwata kwata baya jin alamar rai a tattare da mutumin dan ko telescope din sa bai jiwo koda bugawar zuciyar sa, ba ko alamar harbawar jini maganar pulse kam babu, baya son yace ya mutune ya tadawa mutumin hankali yafison manya likitoci su kuma dubawa duk da bayajin suma din zasu iya gano abin da bai gano ba.
Fatima cike take da murna duk da wani ɓarin can ƙasan ranta tana jin tsoron auren faru anma in ta tuna ita ɗin mace ce ta nunawa sa’a wanda duk abin namijin indai ta masa kissa sai ya biye mata sedai yayi na dama daga baya sai ta ji sanyi aranta.
Wani zubin har hango Ummu Hani take in ta kalli kanta a madubin toilet ɗin ta dan ko ita a iya ganin ta tafi yarin yar komai indai na halittar mace ne shi yasa in son da Faruk kewa yarin yar ya tsone mata ido in tuna suffar yarinyar se kuma tayi dariya dan kuwa ita azaton ta da sun tare Faruk ya ɗan ɗana yarinyar zai gane ita dim dai Fatima ita ce mace.
Yauma kamar kullum tayi shigar ta tsaf tayi kyau tamkar ba bahaushiya ba taku take dai dai kamar bata son taka kasa domin ita din akwai iya kasaita kamar wata basarakiya.
Daga falon nata parking lot ta nufa inda taja motarta kirar benz baka wulik ta nufi gidan su Faruk dan ta ɗauki aniyar ita kam ko ba zaizo zance ba ita zata dinga zuwa har a ɗaura musu aure abinda ya hanata zuwa gidan ma kawai dan kar Abban ta ya gano da waye za’ai auren yace bata isa ba tunda ya kafe baza’ama Faruk dole ba…