Skip to content
Part 25 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Da safe da muka tashi kunun gyaɗa na dama na kawo masa anan na shigo mana da shi muka sha bai fita ba, na riga shi kammalawa na yi  matashin kai da ƙafarsa na janyo wayata na kunna, wa’azi still na kuma kunnawa aka yi knocking sai da na tashi sannan na amsa Easter ce ta buɗe ƙofar sai da ta gaishe mu ta ce za ta gyara wuri ya ba ta izni ta shigo ta fara aikinta na goge-goge ni da shi muna sauraron wa’azin na sheck Albani Zariya Allah ya jikansa yana yi ne kan Sallah matsayinta ga rayuwar musulmi yin ta cikin lokaci har ya gangaro yin ta cikin jam’i.

Ni da shi duk ba mai magana ya ajiye wayarsa wuri ɗaya ya tura hannunsa cikin gashina yana yamutsawa, Easter ta kammala goge wuri za ta fara gyara gado na yi saurin tashi zaune na ce mata ya aka yi ta ce gyarawa za ta yi na ce ta bar shi ta yi godiya ta fita.

Ya ce “Kin hana ta ta yi aikinta za ki iya? Na ɗaga kai sai na miƙe turaren wuta na sanya wurin ya ɗauki fitinannen ƙamshi na turara kayan da zan sanya sai na gyara gadon na goge saman mirror na shiga wanka da na fito na same shi riƙe da wayata da alama ba ya son wa’azin ya wuce shi da zai shiga wanka ya kashe sai da ya fito lokacin ina ɗaura ɗankwali na atamfar da na sanya ɗinkin riga da skirt kallona ya yi ta yi har ya gama na shi shirin kayan da ya sanya na gane ba zai fita ba don riga da wando ne na shan iska ya kama ni muka koma bakin gado ya sani jikinsa yana cewa “Daga dawowa ta har kin fara ƙiba dama da gaske ni ne damuwar?

Murmushi na yi ta saki ban ba shi amsa ba ya fara wasanni da ni aka yi knocking ni na tashi na buɗe ƙofar, Suhaima ce sai da ta sha mur sosai da gani na ta ce Ina Papi? Na ce yana ciki ina rama irin kallon da take mini “Ki faɗa mishi Mama Zulai na jiran shi.”  Ban magana ba juyawa kawai na yi na dauki phone ɗinsa da ya bari bisa kujera ya kwanta ƙafafunsa na ƙasa ya yi   pillow da hannayensa na miƙa masa wayarsa ina faɗa mishi sakon ya tashi zaune wayarsa ya duba ya ce Amal ta kira six missed call ya miƙe yana mamakin zuwan Mama Zulan ba a faɗa mishi ba.

Bin bayansa na yi in yi ma baƙuwar maraba duk da ba  wani yi na take ba.

Zaune suke gabaɗaya a Main parlor ya zauna yana faɗin tafiya ba sanarwa? Ta yi yar dariya “Wallahi kuwa.” Na ɗan matsa na ce  “An zo lafiya? Ta yi kamar ba ta ji ba ta ci gaba da labarinta na ƙara faɗi  sannan ta amsa yadda ta saba yi mini a gidan Haj.

Ganin ba a kawo mata komai ba na tashi na tafi kitchen na haɗo lemo da ruwa na kawo mata ba ta taɓa ba ta ce ma Suhaima “Ba ku da abinci ni fa ban karya ba? Ta ce  “Sun  cinye na safe ba a yi na rana ba. Lemon ta ce ma Suhaima ta kai ma Direban da ya kawo ta wanda ya tuƙo su Dina da za mu zo, ba ta tafi ba Easter ta kira ta ba ta kai mashi nan na bar su na tafi kitchen shinkafa da miya na ji ina sha’awa a maimakon Alale da na ji ina so jiya.

Na fara aikina Peter na yin nashi a gefena sai aka yi rashin sa’a ita ma Mama Zulan ganyayen a ka dafa na gama girkina na fita na wuce su, ko da ya ce mini in zo mu je cin abinci na ce na yi nawa shi dai ya ce ba zai ci shinkafa ba ya ci jiya. Ya ce in zo in raka shi na bi shi ɗauke da flate dina su Mama Zulai na fara hangowa an ƙwame a kujera Peter na ta shirya tebur.

Wayarsa na ce ya ba ni zan yi kallo sai da ya cire password ɗin ya miƙo mini, na shige cikin kujera cikin zumuɗi na shiga gallery ido nake ta gwalewa ko zan ga Maman su Dina amma ban hango ko makamanciyarta ba ko’ina shi ne da ya’yansa sai shi da jar fata da baƙaƙe, na yi kallon har na gaji ban gan ta ba na ajiye wayar na mayar da hankalina ga TV dariyar su Suhaima ta sa na kai hankalina wurin su har na ji dalilin dariyar Mama Zulai dai ta kasa cin abincin ga uwar yunwa tana ji Peter kuma ya fita ballantana a sa shi ya dafa mata wani tasowa suka yi zuwa inda nake kowacce ta nemi kujera ta nutse Mama Zulai ta zo ta zauna kamar ta fasa kuka ta ce “Wallahi ban karya ba na fito yanzu wannan ganyayen da Cream ta ina zan fara? Ni dai na zuba kunnuwa idanuwana na kan waya,  bashir Lema kaɗai suka bari wurin cin abincin

“Ba na ga  kin yi girki ba ki ba ni in ci .”

Muryar Mama Zulai ta dira cikin kunnuwana da kuma na ɗaga kai sai na ga ni ɗin take kallo ban yi magana ba ɗaki na tashi na tafi na zo mata da duka abincin da na rage na dire shi gabanta gabaɗaya ta juye ta sauka ƙasa ta tanƙwashe ƙafafu, Amal na ce mata ta jira Easter ta shimfida mata ledar cin abinci ba ta saurare ta ba.

Bashir Lema ya miƙe hannu ya miƙo mini har na ji kunyar Mama Zulai miƙewa na yi ban ba shi nawa ba na yi gaba muka tafi ɗaki ya ce zai kwanta ne idan abincin da ya ci ya yi ƙasa, bai kai ga kwanciyar ba ya samu kiran waya sai ya fita.

Ni kam ban kuma fita ba sai tara na dare ya dawo lokacin har na fara jin barci amma dalleliyar wayar da ya shigo mini da ita ta sa na wattsake ina ta murna.

Washegari ma da na yi girki shi Mama Zulai ta ci amma da na gifta su sai suna dariya suna kiran Chiganvy ban kawo komai ba da farko sai da na buɗe fridge din ɗakina babu ruwa na fita in ɗauko a store  nan ma na ƙara jin suna ambaton Chiganvy na dubi atamfar jikina tabbas Chiganvy ce na tafi ɗakina saƙe- saƙe ya dabaibaye ni da son gano me suke nufi.

Abin sai ya zama jiki matuƙar zan gifta su,  Amal za ta faɗi sunan abin da nake sanye da shi Suhaima ta faɗi Price na shi, sannu a hankali na gane Mama Zulai da ke sana’ar zannuwa ita ke faɗa musu kuma ba kunya kullum abincina da ita nake yi raina na matuƙar sosuwa da abin da take jagoranci ake yi mini ita ɗin ma uwar ya’ya mata ce idan aka yi musu abin da take jan gora a ke yi mini za ta ji daɗi?

Na ƙosa ƙwarai Nabila ta zo garin da ta ce mini za ta biyo mijinta idan ya je Weekend na shaida mata tana dawowa ko mijinta bai kawo ta ba ni zan zo, sai aka yi sa’a ya dawo tare da ita washegarin da suka dawo kuma ina kwance a ɗaki Bashir Lema ya fita tun safe Easter ta shigo ta yi goge-gogenta ni kuma na yi sauran gyaran da ba na bari ta yi mini na baza turaren wuta a dakin na yi wanka da kwalliya cikin wasu riga da wando na material hannun Aunty Fatahiyya na saye shi da ta ɗora a status ya burge ni.

Na rufe kaina da siririn mayafi na yi salatud duha shi ne na kwanta kiran Nabilar ya shigo ina ɗagawa ta ce ga ta a Gate na tashi zaune ina cewa  son wasa ta rantse mini na lalubi mayafin kaina da ya faɗi na rufe kan na fita su uku ke zaune a falo Mama Zulai sai Suhaima da Amal na ce ma Mama Zulai ina kwana na fita.

 Sam mai tsare Gate ya taso ya gaishe ni ya ƙara faɗa mini ina da baƙuwa shi ya buɗe ta shigo sai kallon ta nake ganin alamun masu ciki duk ya bayyana gare ta ta hure mini ido ganin na naɗe hannaye ina kallon ta  “Me kike kallo? Na yi yar dariya “Abin duniya.” Ta kama baki “Iya shegenki mai lasisi ne Ummu Radiyya.”

Na yi dariya na kama hannunta muka shiga ciki tana ta santin gidan,  da za mu shiga ciki na toshe mata baki na ce “Yan rainin hankalin nan suna nan zaune su ji ki farashin iskancinsu ya ƙaru.”

Ta kama bakinta muka shiga ta gaishe da Mama Zulai muka wuce sai na ji sun fara faɗin kudin material din jikina 1700 per yard sai su kece da dariya Mama Zulai na taya su dariyar.

Muna shiga ɗakina Nabila ta kasa shiru sai sambatu take kan haɗuwar gidan.

Na fita ɗauko lemo don ruwa ne kawai a ɗakina, gifta su suka ci gaba da dariyarsu da faɗin 1700 per yard, dawowa na yi raina na zafi na zauna kusa da Mama Zulai na ce “Ki yi musu magana abin da suke yi mini na wulaƙanci,yanzu har na yi baƙuwa ma sai sun tozarta ni?

Idona na ji ya kawo ruwa na yi saurin mayarwa ta gyara zama “To in ban da ke da abin ki ki dubi wannan gida da kike ciki saboda Allah a samu matar gidan na sanya sutura irin wadda kike sanyawa ai zubar da ƙimar mai gidan ne, ko za ki kai gidanku abin da yake ba ki ya kamata ki sayi suturu da za su dace da muhallin da kike ciki.”

Saurin kallon ta na yi maganganunta suka kai mini wani irin duka musamman ta ƙarshen wai ko zan kai gidanmu!

To ina ta ji hakan? Hawaye da suka gagare ni tsayar da su suka kwaranyo mini na kai hannu na ɗauke Suhaima da Amal suka kwashe da dariya.

Na miƙe ina jin ƙafafuwana kamar ba za su ɗauke ni ba a daddafe na kai kitchen ɗin na ɗumama kazar ina tsaye ina ɗauke ƙwalla na haɗa da lemon na fito na ƙara wucewa.

Wayata na samu Nabila na kallo tana faɗin tsadar ta na ajiye mata ina ƙoƙarin shanye damuwa ta amma sai da ta gane “Wai me ke damun ki daga fita kin dawo wata iri?

Don kauda maganar na ce “Ashe har kin fara nauyi Nabila mun kusa zama iyaye shi ne ba ki faɗa mini ba? Ta galla mini harara sai in ce ina da ciki ko? Na ce “To mene ne don kin faɗi mani kunyata kike ji?

Ta girgiza kai”Ko ɗaya. Na dai so zuwa yanzu ke ma kin samu idan kina da babynki a hannu ba za ki dinga zama cikin kaɗaici ba, damuwar waɗancan ma za ta yi miki sauƙi hidimar Babyn za ta ɗauke miki hankali.”

Na shafa cikina ina tunanin wannan watan ya wuce ban yi period ba amma daga ba wata alama da ta same ni sai ban damu ba.

Na dube ta “Allah ya kawo mini Nabila, ina so sosai yadda kika hango mini matsalolin nan za su ragu idan na samu ni ma na hangar ma kaina.”

Zuciyata ta yi rauni sai na fara share hawaye hankalinta ya tashi ta bar cin naman ta matso kusa da ni “Kukan me kike Ummu? Na share fuskata sai na fara ba ta labari tun daga ranar da muka zo har abin da ya faru yau.

Huci kawai take ta ce  “Wallahi kar ki ƙara ƙyale ko wace shegiya cikin su duk yar banzar da ta ƙara miki ki shaƙo shegiya daga shi ba zai iya tsawata masu ba.

Ni tun da uwar da ta haife ni ban taɓa ganin inda ake wannan rayuwa ba, uwa ba kwaɓa uba ba harara.

Wallahi zane yarinya za ki yi.

Ta ja wani ɗan banzan tsaki “Sai ka ce ba jinin bare-bari ba, kanuri za a zauna ana ma wannan cin kashin? Na kwantar da kaina bisa kujera sai kuma ta dafa ni “Ki yi haƙuri Ummu Radiyya, kowane bawa da irin tasa ƙaddarar daga ba ki da matsala da mijinki ki bar su za su tsinci talatar su a Laraba.”

<< Ummu Radiya 24Ummu Radiyya 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×