Skip to content
Part 4 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Duk yadda na so sanya juriya na bar shi ya yi yadda yake so kasa jarumtar hakan na yi  kuka na yi ta mishi wanda ban tunanin ya san ina yi ba.

Wuya sosai na sha kafin  na samu ya haƙura ya bar ni, na rufe ido ina sauraren raɗaɗin azabar da nake ji ya dawo wata wahalar ya kuma ba ni ni dai sai gefin asuba na samu ya sarara mini na shiga barci ko sallar asuba ranar ban ji ba, na farka ne na ga haske tarwai da ya shigo cikin ɗakina, na yunƙura na tashi zaune àaàaaaaaàaà na rufe fuskata.

“Tashi to ki yi wanka.” Ya faɗi da nishaɗi mai yawa a cikin muryarsa ƙin motsi na yi “Yi haƙuri ki tashi ga ruwa can zan kai miki.” Ya miƙe tsam fita.  Ya dawo ya ce mini “To mu je, saboda ke ban fita ba Ummuna.” Na zuro ƙafafuwana sai na sauka ban kuma yarda ya kama ni ba ko na tayar da kaina mun haɗa ido, har bayin ya raka ni.

Gabana na fara gasawa da ke yi mini raɗaɗi kafin na yi wankan tsarki na yi ƙarshe da na sabulu.

Na fito Abakar na tsaye a ƙofar ɗaki ya tare ni yana riƙe da ni muka shiga ɗakin, sallah na fara yi sai na isa gaban mirrow na yi kwalliya sama-sama don wani zazzaɓi da nake ji yana barazanar lulluɓe ni doguwar rigar atamfa ya miƙo mini na karɓa na zura na ja ƙafafuwana zuwa gado zan kwanta “Daure ki karya sai ki kwanta.” Ya faɗi cikin muryar lallashi zaune na tashi cikin mamakin abin da zan cin alhalin na san ban dafa ba sai dai idona ya gane mini kayan karin da tun shigowa ta ban kula da su ba, Tea ya haɗa mini da hannunsa ya daidaita zafinsa kafin ya miƙo mini haɗe da faranti mai ɗauke da soyayyen ƙwai.

Na ci na sha na miƙa mashi na koma na kwanta na juya baya ina jin shi har ya ƙare shirin shi,  kansa ya kwantar a daidai fuskata “Zan tafi Ummuna, ki kwanta ki yi barci anjima za a kawo miki abinci .”

Na buɗe baki a hankali na faɗi “Zan iya idan na tashi zan yi.”

Hannunsa ya kai bisa laɓɓana “Ban ce ba ki huta, sai na dawo.”

Na ambaci Allah ya tsare cike da nishaɗin da ke ratsa zuciyata na kular da yake ba ni.

Ina jin takun shi ya wuce sai dai me wani irin kira da yake ƙwala mini sai da cikina ya hautsina kafin na sauka gadon na fita a sukwane sam na manta ni ce ban jin daɗi nake lallaɓa jikina.

Ƙofar Haj Iyami na gan shi tsaye cikin firgici “Me ya faru? Na tambaye shi gabana na dokawa hannunsa ya ɗaga ya nuna mini inda jini ya taho tun daga ƙofata har zuwa kofar Haj Iyamin, na ƙara kallon jinin ba tare da na gane komai ba na ƙara tambayarsa “Jinin mene ne?  “Shiga ciki ki duba mana.” Sai sannan na tuna tun tashi na ban ga Haj Iyami ba ko motsin ta.

Na ɗaga labulai ina baza ido shaidar jinin na bi ta kai ni har ɗakin barcinta, cak na tsaya abin da na gani ya sanya ni ɗora hannayena biyu aka na ƙwala ƙara!

Lamarin da ya shigo da Abakar a sukwane “Mene ne Ummu? Ya faɗi cikin haki kamar ya yi gudu, ya wuce ni ya isa inda Haj Iyami ke kwance goshinta na fitar da jini!

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un! Anya matar nan ba ita ce magen jiya ba?

Abakar ya faɗi maganar da ta sa ƙirjina ƙara dakan lugude ƙwaƙwalwata ta tafi tunanin abin da yake nufi tahowa ya yi ya wuce ni ya fita ɗakin na take mishi baya da mugun sauri saboda tsoron da ya dirar mini na jin furucinsa ko Haj Iyami ce ta zama mage.

Ina tsaye a tsakar gida ya dawo da maƙobta tare suka shiga suka  fito da ita a hannu, ban da kalaman da ke fitowa bakinsu na tana da rai ni dai na ƙaddara matatta ce.

Bin bayan su na yi bayan na suro hijab din da na yi sallah.

A motar Abakar aka sanya ta na marairaice mishi zan bi su, ya ce “Ki koma gida Ummu ba ki da lafiya.”

Na ce “Tsoron gidan nake.” Ya ce “To ki tafi gidanmu.”

Kamar zan yi kuka na juya gayyar mutanen da suka fara taruwa suka bi ni cikin gidan musabbabin lamarin suke tambaya ta ni kuma na yi gum, me suke son in faɗa musu Haj Iyami ta zo ɗakinmu a siffar mage Abakar ya buge ta babu tabbacin za ta tashi?

Share gumin da ke mini zuba na yi kamar ba safiya ba, na fara ƙoƙarin rufe ɗakina daidai da shigowar wata aminiyar Haj Iyami, sunan asibitin da aka nufa da ita tambaye ni na ce ban san inda za su kai ta ba.

Ganin ina rufe ƙofa ita ma ta rufe mata ta ta ita ce kuma ta tattara taron mutanen da ke ƙara dannowa gidan kamar an kaɗa ƙaraurawar sanarwa.

Ina fita na kama hanyar gidansu Abakar  zuciyata na cikin wani irin zullumi.

A tsakar gida na samu baban bai kai ga fita ba ina shaida mishi abin da kenan salati ya yi ta maimaitawa hannunsa dafe da bango jikinsa na wata irin rawa lamarin da ya fito da Haj Nasara tana tambayar abin da ya faru Baba bai yi magana ba ni na faɗa mata yadda ta kasance ita ma salatin ta ɓarke da shi ta ɗora da faɗin wautar da Abakar ya yi na kashe mage ga shi nan ya ɗauko fitina, tana mutuwa shi ma kashe shi za a yi.

Furucinta na ƙarshe ya ƙara rikita mu ni da Baba, ni dai ƙasa na zauna na dafe kai na fara rera kuka wani sanyi da ke ratsa ɓargona shaidar zazzaɓi ya ziyarce ni cikin rawar hannu na lalubi lambar Abakar don jin halin da suke ciki rawar hannu na lalubo lambar Abakar don na ji halin da suke ciki amma kamar an aiki loma zagayen wuya shiru ba a ɗagawa, har Allah ya gaji she ni na haƙura.

Lokaci mai tsawo muka kwashe ni da Baba don Haj Nasara tuni ta bar mu ta shiga ɗaki, Baba ya ce in kira Amiru ya zo ya tafi da shi asibitin, da Amirun ya zo bai tafi da ni ko Baban da muka dage ya tafi da mu haƙuri ya ba mu ya ce zai je ya binciki inda suka tafi shuɗewar awa guda ina zaune a inda nake ina kaɗuwar sanyi kiran Amiru ya shigo wayata suna asibitin Fada ya shaida mini da na ce za mu taho, ya ce a’a ga shi nan.

Wani zaman jiran muka ƙara yi kafin ya iso ya zo da mummunan labari, yan sanda sun tafi da Abakar don ba a karɓe ta ba sai da yan sanda.

Haj Iyami na can kwance ƙarƙashin kulawar likitoci an dai nemi jini yana ganin ma na Abakar ɗin ne aka ƙara mata.

Sai dai har ya taho an ce ba ta farfaɗo ba.

Na tausaya ma kaina amma na fi tausayin mahaifin Abakar mu uku muka nufi police station ɗin da aka garƙame shi ba su bar mu mun gan shi ba duk yadda Baba da Amiru suka kai ga roƙon su.

Ni dai hawaye nake ta zubar wa abu ɗaya muka samu nasarar ji daga gare su  case ɗin Abakar babban case ne kotu za a miƙa shi don da kansa ya bayyana abin da ya faru.

Gwiwa ba ƙwari muka koma hanyar gida Baba ya ce in bi shi mu je can gidan .

Muna shiga Haj Nasara ta taso tana tambayar ya aka yi Baba ya ba ta bayanin yadda al’amarin ya kasance ni dai buta na ɗauka na kewaya na fito na yi alwala na gabatar da sallah ina zaune a inda na idar da Sallar na haɗe kai da gwiwa tunani ya karaɗe raina wannan wace irin masifa ce?

Ita Haj Iyami kenan mayya ce don ƙawata Nabila da take ma’abociyar karance-karance ta kan ba ni labarin labaran da ta karanta na mayu, na yi Allah wadai na yi da na sanin kama gidanta da ya yi daga ita ɗin tsumma ce maƙunshin cuta zaman gidanta ya zame mana mummunar ƙaddara.

Tuna ko an ba shi abinci da na yi ya sa ni ɗaukar wayata da ke gefe na na kira Amiru “Na kai mishi abinci Ummu Radiyya.” Amsar da ya ba ni kenan na sauke wayar ina share sababbin hawayen da suka gangaro mini.

Ina nan a inda nake zaune Fahima ƙanwar Abakar tsara ta ta gama abincin dare agogon ɗakin na duba bakwai saura su suka zauna suna ci amma ko Baban zaune yake jugum “Ki je ki zubo.” Na tsinkayi muryar Fahima shirun da na yi sai ta juya tana magana ƙasa-ƙasa.

Ban motsa daga inda nake ba duk da cikina a naɗe yake tun karyawar safe ko ruwa bai ƙara ganin bakina ba ban kuma jin zan iya kai wani abu bakin nawa.

Ina nan cikin saƙe-saƙe mai yawa har suka fara shirin kwanciya Fahimar ta sake dawowa ta ce in zan kwanta in zo ɗakinta ta fadi kamar an yi mata dole ta juya, na miƙe da ƙyar na bi bayan ta, katifa ce yashe a ƙasan ɗakin, sai wani ɗan tebur mai ɗauke da kayan kwalliya wata darduma da ke shimfiɗe na hau na zauna shaidar ni barci ba yanzu ba, ta kashe hasken da ke ɗakin ta bi lafiyar katifarta.

Sai sannan na tuna ban sanar da Mamanmu ba na ɗauki wayata da ke kan jikina na latsa ta ta kawo haske sai na latso lambar Maman ina yi ina share hawaye tana fara ringing ta ɗaga “Ummu Radiyya, ɗazu nake son kiran ki kuna lafiya?

Ban amsa ba sai na fashe da kuka take ta ruɗe ta fara tambayar abin da ya faru, cikin kuka na kora mata bayani Innalillahi tare da salati take ta kwasowa tana direwa kafin ta shiga lallashina ƙarshe ta ce mini tana nan tafe da safe na ajiye wayar na share hawayen da suka ƙi tsayuwa jikin bango na jingina bayana na dogare ƙafafuwana kaina na cikin gwiwoyina kafin safiya na yi wani irin kuka da har hawayena suka ƙafe da na ga yadda Baba ya koma a safiyar kuma sai na ga gara ni.

Tun da sanyin safiyar Mamana ta iso, da ita aka yi ta juyayi da ƙara mayar da yadda aka yi ita ta sa na sha kunun da Fahima ta kawo mini ruwa ta ƙara mishi na sha sosai bisa tilastawar ta yana sauka cikina sai na ji yan hanjina da suka cure suna warwarewa.

Da na shiga bayi ruwa na sa ma jikina na yi wanka da ruwan cikin bayin duk da ba ɗabi’ata ba ce wanka da ruwan sanyi, kayan jikina na mayar da na fito kuma na mayar da hijab ɗina.

Police station ɗin muka yi haramar komawa Amiru ya zo da mashin ya ɗauki Baba ni da Mamanmu muka hau mota a cikin yaran Haj Nasara da suka zo Fauziya ce kawai ta ce za ta Aunty Habashiyya ba ta garin.

Mu ukun muka ɗunguma zuwa police station ɗin da ke Kawo muna isa Amiru na kafe mashin ɗinsa tare muka shiga sai dai wata sabuwa yan sandan da ke bisa kanta sun ba mu tabbacin an ɗauke Abakar daga nan daya daga ciki Amiru ya samu ya faɗa mishi inda aka mayar da shi State CID.

Amiru ya ce mu koma gida su za su wuce can, kukan da na fara ya sa shi dole ya yarda muka je tare sai dai ba mu samu ganin shi ba muka koma gida.

Mamana ta kasance tare da ni har yamma lis mutanenta da suka ji labarin abin da ya faru sun zo sosai,haka ma yayata Lubna da Aunty Ya gana sun lallashe ni sosai sannan suka tafi.

Washegari tare da Hassana ta zo da Hanan, Hassana ta je ɗakina ta dauko mini kaya na canza ta ce Hassana ta kwashe wadanda na cire ta fita ta wanke tana kwashewar muka tsinkayi muryar Haj Nasara “Wannan fa ba abin da zai yiwu ba ne Alh, mutanen da ke cikin gidan nan a sake lale, a san abin yi  mai kawo abincin nan ba ta gari kuma ma dai abin yawa zai mata. Ko dai komawa za ta yi can gidanta? Ba mu ji amsar da tsohon ya ba ta ba sai muryarta da ta ci gaba da tashi.

<< Ummu Radiyya 3Ummu Radiyya 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×