Skip to content
Part 7 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Ina ci-gaba da kallon ta kafin na miƙa hannu na ɗauko ta, jarumta sosai na sa wurin buɗewa  hawaye  na sauka kan takardar ganin rubutun Abakar, ina tuna haɗuwa ta da shi a poly da sanadin barin shi makarantar korar da aka yi masa ranar farko da na fara ɗaukar lacture a poly Course daya za mu karanta Mass com mun zauna kusa da juna da na tashi na bar wayata na fita mun yi sallama da Nabila na tafi wurin Baba Isa na daɗe a Office ɗinsa don sai da ya kammala abin da yake yi muka fito tare na hau bayan mashin ɗinsa da yake da shi a lokacin za mu wuce na ji ana kiran sunana mamaki ya rufe ni na wanda ya san sunana daga fara halartar lacture yau.

Ɗalibai na department ɗinmu tuni sun kusa gama watsewa ya ba ni wayar bayan ya gaishe da Baba Isa Baban ne ya tambaye shi sunansa bayan mun yi masa godiya.

Tun daga ranar muka saba idan mun fito mukan yi karatu ni da shi da Nabila da abokansa guda biyu, ina yawan zuwa Office din Baba Isa don shi ke ba ni kudin da nake sayen abin da zan ci da farko idan na sayi abin da zan cin Office din nake komawa in ci idan za mu sake shiga lecture in yi zama na har sai lokaci ya yi, sai na kula Abakar za ka gan shi ba shi da kuzari ban kuma ganin ya sayi komai sai nake kawowa mu ci tare amma ba ya ci.

Da tafiya ta yi tafiya ya shaida mini jakunkuna yake sayar wa a kasuwar barci, idan ya tashi makaranta sai ya gangara kasuwar, ina yawan wuce shi idan na shiga keke napep yana tafiya a ƙafa.

Semester ɗinmu ta farko ya samu carry over har guda biyu saboda rashin biyan kuɗin makaranta da wuri duk text ɗin da aka yi ta yi saboda rashin Reg no ko sun yi su da ba su biya ba a banza man kare, kuma a sana’ar tashi da yake matuƙar karɓar gashi saboda rashin ciniki yake ma kansa hidimar makarantar da ƙyar ya ƙulla kuɗin registration ɗin ya ce mini shekaru bakwai kenan da kare Sakandire ɗinsa bai samu ya cigaba ba sai a wannan shekarar.

Jarabawarmu ta second semester last paper ɗinmu an kama ɗalibai da dama sun shiga da takardun satar amsa abin baƙin cikin har da Abakar a cikin su sai dai shi waya suka samu wadda ƙarama ce ba ta da ko caji shi ya ma ciro ta da ana caje shi ya ce ba ta da caji sun sanya su cike malpractice foam don babban tashin hankalin External da kamen ga shi har da masu zana exam din final year ‘yan HND Mutum biyar aka kama.

Ni dai jikina ya yi matuƙar sanyi komai kasa yi na yi na mike na je na yi submit na fita hall ɗin.

Ina tsaye ɗalibai na ta fitowa kowa da maganar da yake don kamen yan  HND din nan ya taɓa kowa wasu ɗalibai da na tsaya kusa da su na ji suna faɗin Saboda Allah ƙa’ida dokar ba sai an ga takarda a hannunka ba aka ce ba? Amma sai a  kama caje ka don dai abincin da za a ba su da bai fi su cinye shi na ɗan lokaci ba sai su yi masu wannan sanadin tsiyar.

Abakar da ya fito jiki a mace ya sa ni barin sauraren su na nufe shi abokansa ma fi kusanci da shi kewaye da shi kowanne na tambayar shi me ya sa ya shiga da waya ya ce ya ga ƙarama ce kuma ba ta da caji ta ina zai saci amsa da ita.

Mun daɗe tsaye cikin jimami kafin muka fito ni mota na shiga Abakar da abokansa suka gangara.

Da na koma gida daga Mama har su Hassana sun gano ina cikin damuwa na ba Mama labarin abin da ya faru da Abakar ita da kamar ma ta fi ni tausayin shi hawaye ta yi ta share wa tana mishi addu’a.

Ba mu ƙara haɗuwa ba sai da muka fara  Siwes da yake ba mu waye ba a poly ba mu san in dai External suka kama ka kora ce kai tsaye ba haka muka yi ta jigilar zuwa gidan Radion Freedom da ka ga Abakar ba sai an faɗa maka yana shan wahala ba a ƙafa yake zuwa tun daga Tudunwada har Freedom din ya kuma koma a ƙafa ba mu da yawa mu da muka zaɓi can ɗin mu goma ne sai da muka kusa kammalawa result ɗinmu ya fito malpractice aka sanya ma Abakar hakan ya sa ya bar zuwa don mun tabbatar an kore shi.

Tun daga nan muka rabu da Abakar ya koma kasuwa ya bar karatun da ya ƙwallafa rai ya kuma cinye ɗan jalinsa kaf kan hidimar makarantar.

Har gida ya zo ya shaida mini abokinsa ya sa mar masa mota zai fara tuƙi.

Tun daga nan ya dage zuwa wuri na, tun muna ganin shaƙuwa ce kawai a tsakanin mu har muka amince mun faɗa son juna don haka yana bayyana mini ban ja ba na amince mahaifinsa shi ya yi masa komai na auren wanda ya ƙara rura wutar ƙiyayyar shi a zuciyar Haj Nasara ganin ya sayar da filinsa ya yi hidimar auren.

Na share hawaye na zuba ma takardar ido a ƙoƙarin da nake sai na fahimci abin da ke rubuce a jikinta saki na hango rubuce raɗo-raɗo ban gama ƙarashen bayanin ban haƙurin da ya rubuta ba da ya sabbaba mishi sakin ya fahimci akwai ƙullin da ake a kansa ba za su sake shi don nan kusa ba shi ya sa ya yanke sahale mini aurensa.

Kuka na yi ta rusawa na wannan ɗanyen hukunci da Abakar ya yanke, kukan nawa ya shigo da Mama har da su Hassana da Husaini suka yi tambayar duniya ban saurare su Hassana ta ɗauki takardar ta karanta ta miƙa ma Mama ita ma ta karanta ta yi ta maimaita Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, kafin ta soma ba ni haƙuri da kalamai na imani da ƙaddara.

Wannan karon Gwoggo Mamu ta zo ta jajanta Baba Isa ma da ba ya gari Aunty larai ta zo haka kwanaki suka yi ta shuɗewa zuwa satittika su tafi zuwa watanni har aka samu wata uku zuwa lokacin na samu nutsuwa idan Lubna ta zo ta dinga mini mitar na koma kamar mai takaba wanka kawai ke zame mini dole sai na sanya bayan na shafa mai ko turare na bar mu’amala da shi sai dai na goga alum.

“Abakar dai ya riga ya sake ki tsakanin ki da shi addu’a ce a duk inda yake Allah ya kuɓuto da shi cikin aminci da yana buƙatar ki jira shi da bai saki aurenki ba, ki dinga kwalliya kina gyara jikinki ko kya samu ki samu wani mijin ki yi aure ko dan rage ma Mama nauyi.

Idan tana waɗannan maganganun jin ta kawai nake ni na san nauyin da ƙirjina ya yi.

Nabila ƙawata kuma kullum ta ta maganar in daure in saki raina in fuskanci rayuwata ta gaba mu koma mu ci gaba da  karatunmu.

Ni kam rashin Abakar ya goge duk wani buri da na ci a rayuwata sai dai yau da gobe Nabila ba ta fasa yi mini maganar ci gaba da karatu ba zuciyata ta fara karkata kan hakan sai dai rashin kuɗi da na ga Mama na fuskanta kan sanyaya mini gwuyawu, ana kwana biyu kafin Baba ya kawo wani abu ita ce komai na ci da shan mu a  sana’arta, ina ta tunanin inda kudin yin Registration za su fito ina dai ta addu’a lokacin ne bikin su Aliya da Juwairiya yaran Baba Ali ya tashi su biyun suka samu maza Fa’iza ba ta samu ba, Juwairiya da Fa’iza yaran uwargida Aya ne, Juwairiya ita ce ta Maman su Samira, Aliya ce sa’a ta Juwairiya da Fa’iza duk sun girme mu.

Har bikin ya rage saura sati biyu Baba bai samu ya haɗa kayan ɗakin su su biyun ba kuɗin ɗaya ne a hannu kowacce kuma ta ja ta tsaya kan kaya masu tsada za a yi ma ‘yarta.

Na shigo daga gidansu Nabila takalman Baba da na gani a ƙofar ɗaki na san yana ciki na yi mamaki don ba kwanan Mama ba ne idan kuma ba wurin ta yake ba zai yi wahala ka gan shi hanyar wurin namu, da ya shigo yaransa za su kai ma iyayensu labari ranar kuma su da Baban ba za a yi ta daɗi ba.

Sallama na yi kafin na ɗaga labulai Baban ya amsa yana bi na da wata irin fara’a da na kwana biyu ban ga yana irin ta ba.

Na gaishe shi idona na kan Mama da ta sunkuyar da kai na shiga ɗakinmu zuciyata na mini saƙe-saƙe.

Mayafin jikina na cire na fita daga dakin na yi tsakar gida gindin bishiya da Hassana ke zaune da Hanan na zauna Hanan ta zo ta hau ƙafata.

Baba sun daɗe da Mama har kusan magrib sannan ya fito ya tafi har yana ba Hanan kuɗi a saya mata fresh yo mu dai muna jin abin banbaraƙwai a ka ce wai sabon salo shafa kwalli da taɓarya, da muka shiga ɗaki Mama a sanyaye take ko hirar da Husaini ya shigo muna yi ba ta sanya mana baki ba sai duk na sha jinin jikina na ce mata lafiya? Ta ce ba komai.

Tana miƙewa alwala ta ɗauro ta shige ɗakinta dama ita ce ƙarfin zaman mu in dai ta riga ta tashi hirar tamu ba ta zuwa ko’ina nan da nan muka yi ɗakinmu Husaini ya tafi nashi ba mu daɗe ba muka yi barci.

Da safe ina yi ma Hanan wanka Hassana na dama mana kunu da za mu karya da shi Baba ya aiko na zo, wani daban na ji don abin da bai taɓa faruwa ba ne na ce dai ina zuwa.

Ɗaki na shiga Hanan na kafaɗata, a gurguje na shafa mata mai sai na sanya mata kaya, ko kwalliyar da nake mata ban yi mata ba na sanya ta a baya na goya na fita ɗakin Mama  na shaida ma wa kai kawai ta ɗaga mini na wuce.

Idan kana raye ka yi ta ganin abubuwa fara’ar da Aya ta tare ni da ita ina shiga sasan nasu ta ba ni mamaki matuƙa, na dai amsa ta a sanyaye haka ma Maman su Samira da ke dama koko, ita ta ce mini na shiga falon Baba yana ciki.

Na wuce na shiga da sallama falon ƙaton gaske ne da ya lamushe kujeru saiti biyu amma da sauran fili, Carpet ce mai daraja aka malale tsakiyar falon da gabaɗaya tayels ne, kayan tun na marigayi kakanmu ne ba abin da aka taɓa haka ma labulayen.

Wani abin mamakin na ƙara tarar wa shi da Mamu ne zaune a ciki da na rasa yaushe ta iso garin, Baban ne ya ce in ƙaraso, na zube saman Carpet ɗin ina gaishe su da yi ma Mamu barka da zuwa, Aya ce ta shigo kafin mamansu Samira ta mara mata baya.

Baba ya fara bayanin da na kasa gane mishi kafin Mamu ta amshe shi

“‘Yan’uwanki da za a aurar, Babanku ya samu zarafin saiti ɗaya na kayan daki amma ɗaya ya ƙi samuwa, shi ne muke so ki taimaka Ummu a kai ma ɗaya daga cikin su kayanki kafin ki tashi wani auren.”

Saurin ɗagowa na yi na dube ta kafin kunnuwana su juyo mini Aya na cewa “A ba Juwairiya dai ai ita ce babba.”

Mamansu Samira ta katse ta cikin sauri  “A’a son kai dai, ba wani babba da kika ga kuɗaɗen dai ba su da kaurin da za su sayi masu tsadar na Ummu Radiyya.”

Baba ya ɗaga musu hannu cikin faɗa ya ce idan halin nasu za su kawo mishi zai miƙa masu kuɗin su san yadda za su yi da su.

Tsit suka yi Mamu ta cigaba “Ya tambayi mamanki ta ce kaya naki ne idan kin amince shi kenan.”

Wani ƙududu na ji ya tokare ni ban san wane irin haƙuri Mama ke da shi ba tana kallon kayan ɗakin nawa a matsayin su na yan’uwan mahaifinmu da ya kamata a ce su suka yi ba ma kamar Baban da ya dage yana son aurenta don ya riƙe mu, dukkan su gudunmuwa suka ba ta, mijin Lubna da ke aiki a wani kamfanin gadaje ya ce ta kawo abin da ke hannunta ya cika aka kawo mini set na ji da gan.

Dama su Maman Samiran sun yi ta magana kan kayan a lokacin.

<< Ummu Radiyya 6Ummu Radiyya 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×