Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Wa Ya Kashe Zahra'u? by Fatima Galadima

Kwance take idanunta a lumshe fuskarta fayau. fara ce amma ba za ka ce mata sol ba, eyelashes ɗinta zara-zara kwance luf a saman idonta dake lumshe, hannuwanta da kafafunta sun sha ƙunshi ja da baƙi Wanda da ka gani ka san na amarya ne ko ba a faɗa maka ba.

Gefe daya kuwa mahaifinta ne zaune dirshin a ƙasan tiles sai kuka ya ke kamar ƙaramin yaro, a ɗayan gefe mahaifiyarta ce an rirriƙeta tana kuka tana fizge-fizge kamar wacce ta kamu da cutar hauka domin ta gama fita a hayyacinta, ga jami’an tsaro su na ta bincike, su na ta ɗaukar hoto.

ACP ne ya kalli Alhaji ya ce.

“Alhaji don Allah ka dai na kukan nan haka,nayi maka alƙawari In sha Allah sai inda karfin mu ya ƙare wajen binciko gaskiyar wanda ya shigo har gidan ka ya yi maka wannan aika-aikan, ya kashe maka ‘yarka i promise.”

Cikin kuka ya fara magana.

“wa ya kashe ki zahra’u? waye ya shigo har cikin gidana ya yi mini wannan ta’addancin? duk camera da Securities da bodyguards ɗin gidan nan, ya kashe mini ke? don Allah ACP ka taimaka mini zan iya kashe ko nawa ne akan wannan case din, ‘yata ɗaya tilo,kuma a rasa ranar da za a kashe ki sai ranar auren ki!?”  Ya kuma sakin kuka har yana sharɓe majina.

Hajiya tana ihu tana fizge-fizge domin

mata sun kai kusan goma waɗanda suka rirriƙeta.

“Wallahi karya ne! karya ku ke yi munafukan banza munafukan wofi!! Alhaji karka yarda da su Zahra’u bata mutu ba, jiya mun jima da daddare muna hira da ita har wajen 2:00pm sannan yanzu ku ce mini ta mutu! daga kawai zuwa tashinta ta shirya, Don Allah babyna ki tashi kinji?,Don Allah ki tashi ban san ki da nauyin bacci ba, ga dubban jama’a mata da maza sun taru duk saboda ke babyna, har da yaranki na gidan marayu ma duk sun zo tayaki murnan aure, ki tashi kinji lokaci yana k’urewa, don Allah ku barni na tashi ƴata!”  ta ci gaba da kokuwa ita da matan da suka rik’eta, sai kukan tausayin Umma suke yi, shi ke nan yanzu daga zuwa hidimar aure za a zarce da zaman makoki.

Bincike sosai jami’ai ke yi, wuyanta ya yi jan shati bisa alama dai shek’eta da wayar  wuta aka yi, kuma an nemi wayar wutan an rasa, ga kaya duk a hargitse bisa alamu wanda ya kasheta sun sha dambe da shi, domin azabar fitan rai, ga shi shi makashin bai bar wata alama ba.

Waya ACP ya ɗaga ya yi dealing number , ringing biyu aka yi picking, wanda ya ɗauki wayar cike da girmamawa ya sara masa kamar yana ganin sa,ya ce.

“yes Sir”

ACP ya ce.

” *DSP SARDAUNA*  ka shirya yanzu ka taho gidan *ALHAJI ALIYU IBRAHIM MD.”*

DSP SARDAUNA, ya ce.

“Eh Sir, gani nan ina shirin zuwa wajen ɗaurin auren ne ma,na ga ya kusa shiyasa nake sauri.”

“Dsp, idan ma shirin zuwa wajen ɗaurin aure  kayi to ka canza, ka saka uniform din aiki ka taho yanzu-yanzun nan” ya katse wayar.

ACP, ya ce.

“Alhaji, pls ka dai na kukan nan haka, ka kwantar wa da Madam hankali, wai ma duk ba wannan ba, shi angon ya sani kuwa?” girgiza kai Alhaji Aliyu ya yi  ba tare da ya yi magana ba, ACP ya ce.

“to gsky ya kamata a sanar da shi, tun da auren karfe 2:00 za a ɗaura, ga shi saura ‘yan lokaci ƙalilan”

ɗaga waya Alhaji Aliyu MD ya yi yana neman layin *ZAYYAN* yana tunanin kalar tashin hankalin da Zayyan zai shiga ,to ma me zai ce masa ka zo gida yanzu amadadin zuwa wajan daurin aure an *kashe zahra’u?*

ya sake goge hawaye da majina.

*****

ZAYYAN tsaye a jikin drees’mirror

Yana shiryawa abokansa su na zaune su na hira ,sai tsokanarsa suke yi, yasha babbar riga fara sol da ita sai baza kamshin angonci yake yi,kansa ya kalla a mirror ɗin ya hau murmushi “wow gaskiya yau ji nake babu wanda ya kai ni farin ciki,zan mallaki abin da zuciyata ta ɗaɗe tana muradi kuma take so wato *Zahra’u”*

Ɗaya daga cikin abokansa mai suna Salisu ya ce “wai irin wannan zumuɗi haka Zayyan? sai wani rawan kai ka ke yi.”

Kamal ya ce.

“A’a fa Salisu bar shi ya yi,wlh Zayyan kayi dacen mata,da badin ba da sai na ce ka ɗauki ta karshe,dan Zahra’u

akwai ilmi, hakuri, hankali,natsuwa, daraja mutane, uwa uba kuma ga ta kyakkyawa, gaskiya ina tayaka murna abokina.”

Zayyan ya yi ihun daɗi da murna gami da jujjuyawa a cikin babbar rigarsa ya ce.

“kai dai bari kawai, nan da awa daya da rabi,zan angwance, ka bari sai  a lokacin ka ji daɗin mini murna, wani abu ma sai ance *an ɗaura auren Zayyan da sahibarsa Zahra’u* wayyo daɗi barni da raina!”

Suka kwashe da dariya, Zayyan ya ce.

“wai ina su Adam da Kabeer ne kam?” Salisu ya ce.

“Su na parlour tun dazu” ya ce.

“okay, Dsp Sardauna bai ƙaraso ba?”

Kamal ya yi dariya ya ce.

“ka san fa shirin manya sai a hankali” Zayyan ya ce.

“don Allah ku tashi ku gama shiryawa kun ga

lokaci ya kusa wlh, bana so mu makara, yanzu saura awa daya da rabi a ɗaura aure,amma gamu cikin gida, plss ku tashi ina wayoyina suke ne?”

Kamal ya ce.

“Su na hannun Adam dazu kana wanka ya shigo ya  ɗauka wai zai yi wani abu da shi ne”

“Okay”  kawai ya faɗa ya dauki rolex dinsa ya ɗaura dama already sun gama yi masa wanka da turare ,ya zura takalminsa ,ya ce.

“ku tashi mu tafi” mik’ewa suka yi,har sun iso bakin kofa, Zayyan shi ne a gaba sai buga sauri yake yi kamar zai tashi sama,karo suka yi dasu Adam da Kabeer gabaɗaya ba su cikin hankalin su.

Zayyan ya ce.

“Lafiya dai ko? yana gan ku haka wujiga-wujiga, meya faru?” sun kasa magana dan ba su san me zasu

ce masa ba,illa zazzare idanu da suke yi cike da tashin hankali marar misaltuwa.

“Mtsww! kun ga malamai idan ba za ku yi magana ba ku wuce mu tafi plss lokaci yana tafiya ga shi yanzu har 1:00, ga shi yau friday ne kar mu rasa sallah, ga kuma ɗaurin aurena” ya faɗa yana sakin murmushi yana neman hanyar da zai rab’a ta gefensu ya wuce, amma sun tsaye k’ik’am.

Kamal ya ce.

“wai Adam miye haka ne kam don Allah ku wuce mu tafi mana”

Adam ya ce.

“AN KASHE ZAHRA’U!”

Da karfi Zayyan ya ce.

“whatt!!!

Hahaha haba Adam,ko dai ka fara shaye-shaye ne kam?”

Kabeer ya dafa kafaɗar Zayyan ya ce.

“mu ma yanzu Abba ya kira yake gaya mana,wai an kashe zahra’u.”

Zayyan bai san lokacin da ya ban gaje Adam da Kabee ba ya fita a sukwane , ko gani da kyau ma ba ya yi ,da lalube ya shige motarsa ya tayar da ita sannan ya figeta da mugun gudun gaske.

Allah ne kaɗai ya kai Zayyan gida lafiya,saboda ƙetare motoci da ya riƙa yi.

Isowar sa ya yi dai-dai da isowar Dsp sardauna, ga jami’ai kace-kace, Dsp Sardauna sanye yake da uniform dinsa, ya kalli Zayyan wanda ya fito mota a hauka ce, ba takalmi hular ma ta faɗi, da gudu ya hau

Kutsa kai cikin mutane yana gudun yana ambatan sunan.

“Zahra’u! Zahra’u! Zahra’u!”

Duk wanda ya gansa, sai ya sake fashewa da kuka.

Har upstairs ya haura yana kiran sunanta,tamƙar mahaukaci, babbar rigarsa ta karkace gefe.

Yana zuwa wajan bakin kofar bedroom dinta,ya ci ƙaro da jami’an tsaro kace-kace nan ma wani ihu ya kurma da karfin gaske ya ban gaje kofar yana shiga ya ci  wani wawar burki…!

Sakamakon cin karo da Zahra’un sa kwance bata motsi,idonta a lumshe, fuskarta ɗauke da annuri,kamar tana murmushi.

  “Zahra’u!?” Ya fada da karfi, zaiyi kanta, a hanzarce

police suka riƙe sa yana fizgewa yana ihu, ba su so ya taɓa ta saboda kar tambarin hannunsa ya fito a jikinta.

Dsp sardauna zubewa ƙasa ya yi, ya ɗurƙushe ya saki kuka.

Sulalewa ƙasa Zayyan ya yi,ya rarrafa har izuwa gaban Abba ya kamo kafafunsa, Abba ya kuma sa kuka,ya duƙar da kansa ƙasa,haƙiƙa shi ne mahaifin zahra’u amma halin da Zayyan zai shiga sai ya fi kowa,su da suka taso tare,komai tare suke yi, skull ɗin su ɗaya suka yi saboda shaƙuwar dake tsakaninsu, bacci ne kawai yake rabasu, sannan yau auren su amma an kashe ta! har kunyar ɗaga ido yake yi ya kalli Zayyan.

Da sauri-sauri Zayyan ke kiran sunan Abba.

“Abba! Abba! Abba!

Pls ka faɗa mini cewa karya ne,ka fada mini cewa zahra’una bata mutu ba, Umma!Umma! Umma!

Don Allah ki ce wani abu mana.”

Kwanciya ya yi a ƙasa tamƙar wani gawa.

Acp ya kalli Dsp sardauna, yadda yake kuka sai kace ba jarumin Ɗan sanda ba, dafa kafaɗarsa Acp ya yi sannan ya lumshe masa ido alamun rarrashi.

Dai-dai nan ambulance ya iso domin daukar gawar zahra’u,dan za aje hospital a sake zurfafa bincike.

A lokacin da doctors suka shigo daukar gawar Zahra’u ,Zayyan  ya yi kukan kura zai kama gadon,sosai  ‘yan sanda suka riƙesa, yana fizgewa,Umma ta sulale ƙasa a sume,Abba yana kuka yana kiran sunanta.

Zayyan ma faɗuwa ya yi a wajan tamƙar gawa,dan numfashinsa ya tsaya cak.

Ashe duk jama’ar da suka tsaya a cikin gidan da wajen duk nafila ne, sai da aka fito da gawar Zahra’u a sama an lullubeta da farar yaɗi wanda shi kadai zaka iya hangowa daga sama ,jama’a kowa so yake ya riƙe ,wanda kuma basu samu dama ba ,daga nesa suke hangowa.

Masu ɗaukar hoto masu video duk suna yi.

Gida ya riƙice, yaranta na gidan marayu, masu suma su na yi ,masu kuka su na yi,sai kiran sunanta suke yi amma inaa yau ga zahra’u an fito da ita babu rai ,yarinyar da take fitowa da kafafunta tana dariya,amma yau ga shi an fito da ita a sama a hannu ,kuma ba zata iya magana ba, innalillahi wainna ilayhirrajiun!! Abun da jama’a masu kuka da majina suke ta nanatawa kenan,

Zaman aure ya juya ya koma zaman makoki.

Da kyar doctors suka samu hanyar shiga mota, kafin kace mai labari ya karaɗe unguwa an kashe Zahra’u.

Amma abun tambayar anan.

*WA YA KASHE ZAHRA’U.?*

Bayan ambulance sun samu hanya da kyar suka bar layin, 

Aka fito da Umma da Zayyan, tamƙar basu raye,Abba ma dai gashi-gashi nan ne,tafiyar kawai ya ke yi amma ba ya gane komai.

Asibitin Aminu Kano suka nufa,

Inda aka ƙarbi su Umma da Zayyan,

Abba a ƙasa ya zauna daɓas.

Yana nan zaune har commissioner of police (CP) ya iso ya same su a hospital ɗin.

Dafa kafaɗarsa CP ya yi ya ce.

“Alhaji Aliyu ka yi hakuri.”

Abba ya share hawaye ya ce.

“Ka gani ko? Ka gani ko CP? a ban shiga siyasa ba ma ga shi an kashe mini

‘ya ta tilo, an kashe min sanyin idaniyata, ah..!!ah…ahhh.ranar aurenta..!! 

Ya faɗa da karfi, kafin shi ma ya faɗi timm!!! A sume.

Tashin hankali wanda ba’a sa masa rana.

Abba ma taimakon gaggawa a ka hau ba shi.

Umma ce ta fara farfaɗowa,amma ba ta gane komai ban da zubar da hawaye da idonta ke yi.

Abba ma ya farka ya ga CP na zaune a kusa da shi ya buga tagumi yana tunani,domin abun akwai ɗaurewar kai, a ce har a shiga cikin gidan *ALHAJI ALIYU IBRAHIM MD*,a kashe masa ‘yar sa wannan bincike ta ina za’a fara shi? Domin abun akwai ɗaurewar kai,

Ita dai margayiya Zahra’u yarinya ce wanda kwata-kwata ba ta da hayaniya ga saukin kai ga ladabi ga biyayya ga girmama mutane ko da ba ta sansu ba, to *WA YA KASHE ZAHRA’U*? tambayar da CP yake ta yiwa kansa kenan amma ya kasa samun gamshashshiyar amsa,gabaɗaya kansa ya ɗaure, duk yawan securities da bodyguards din da suke gidan MD ga Camera, amma har a  shiga aka kashe masa ‘yar sa,? innalillahi wainna ilayhirrajiun!!  Shi ne abin da CP yake ta nanatawa.

Abba ya miƙe zunbur yana cewa “CP an kamasu? Don Allah kar ka ce mini ba a kama su ba.”

CP ya ce “MD kayi hakuri ka zama namiji, na roƙe ka, yanzu mu samu a gama binciken, sannan a bamu gawar Zahra’u mu kai ta gida ayi mata sutura,sannan mu kai ta gidanta na gaskiya,Alhaji Aliyu MD kai aminina ne, ba zan so ganin ka cikin damuwa ba,  na san da ciwo kam mutum ya yi rashin abin da yafi ƙauna a duniya dole sai ya jijjiga,barin ma kai da ka rasa ‘yarka a ranar da kake murnan sauke nauyin da Allah ya ɗora maka a matsayinka na mahaifinta, a ranar da kana murna za ka ga auren ɗiyarka, wanda na san burinka kenan yanzu a rayuwa, ka aurar da zahra’u, ranar da za’a lullubeta a kawota gabanka, kayi mata nasiha a matsayinka na mahaifi, har ma ka rakata a sakata a mota, amma a wannan ranar ne maƙiyanka suka sauya maka wannan farincikin ya dawo baƙin ciki, sun sanyaka kuka da idanun ka, sun sanya iyalanka a cikin damuwa da tashin hankali marar misaltuwa,ba ma iyakar iyalanka ba kawai , har ma da jama’ar gari bakiɗaya,dan kuwa Zahra’u yarinya ce abin alfahari ga kowa, saboda haka, MD ina so ka ɗaure duk da na san ba sauki, amma mu yiwa gawar yarinyar nan gata, mu yiwa gawarta sutura mu kai ta makwancinta, don Allah, Ka ɗaure”

Kuka Abba ke yi kamar ba zai dai na ba, wai shi da kansa yau zai ɗauki ‘yar sa ya sanyata cikin ƙabari ? Anya zai iya kuwa? 

Kallon CP ya yi yana kuka yana magana har muryarsa  ta dashe.

“CP an ya zan iya kuwa? Na ɗauki zahra’u, na sanyata a ƙabari da hannuna?”  Ya durƙusa a gaban CP yana kuka.

“CP ni da ya kamata a ce zahra’u ce ta ga mutuwa ta ,amma ni ne na ga nata?”

“Haba MD kar kayi sab’o mana ,Allah ba ya barin wani domin wani, Allah da Ya baka zahra’u ya fi ka sonta, a lokacin da Allah ya baka zahra’u, a ka haifa maka ita karɓanta kayi kana murna , kana farinciki,a lokacin ita kuma take kuka tazo gidan wahala,yau kuma ta koma ga mahaliccinta, tana farinciki,amma ku kuma kuna mata kuka, kuka ga mamaci ba kyau Alhaji Aliyu addu’a shi ne gatan zahra’u, balle ita kam ma ta yi shahada tun da kasheta aka yi,duk wani alhaƙinta da kurakurenta sun koma kan wanda ya kasheta,kuka azaba ne ga mamaci Alhaji Aliyu , Ka yi hakuri mu je idan sun gama binciken mu karɓeta kar tayi kwanan keso”

Da kyar Abba ya tattaro sauran jarumtarsa suka fito a tare shi da CP ,wasu jami’ai suka rufa musu baya har office ɗin doctor suka je a lokacin an kammala bincike, dan result din ma yana hannun ACP ya miƙawa CP gami da sara masa, karɓa CP ya yi yana kallon doctors din da suke tsaye,a gefe kuma zahra’u ce kwance lullube da farin yadi a gado.

CP ya ce.

“Wannan takardan ba zai gamsar dani ba, ko da na duba ma ba zan fahimci komai ba a halin yanzu, zan fi buƙatar kuyi mana cikakkiyar bayani, da bakin ku kafin wannan taƙardan.”

Ɗaya daga cikin doctors din ya ce.

“Amm wato commissioner, a iyakar binciken mu da muka yi, mun gano kafin wanda ya yi nasarar kasheta sai da suka sha dambe, bcox fatar jikinta na wasu gurare,akwai yaƙushi,tambarin shatin wuyarta kuma, shi ne wanda makashin, ya yi amfani da wayar wuta ya kasheta da shi, domin ya maƙure mata wuya har sai da numfashinta ya bar gangar jikinta.”

Abba ne ya yi zaman ‘yan bori ya toshe kunnansa yana hawaye masu zafin gaske, kunnansa sun kasa ɗaukar jawabin da doctor ke yi, na kisan wulaƙancin da aka yiwa ‘yar sa ɗaya tak a duniya.

CP da ACP ne suka ɗagosa suna rarrashinsa. 

gaban gadon yaje ,yana shafa kanta ya bude fuskarta yana kallo ,domin ya san kallon karshe yake mata ,har yanzu fuskar zahra’u kamar tana murmushi, Abba ya sake share hawaye

CP ya ce.

“To yanzu a bamu gawar yarinyar, amma dole zamu neme ku ,idan buƙatar hakan ta taso ,domin ba zamu bar shaida ba ,ko da kuwa ƙanƙantarta ta kai kwayar acca ne, zamu neme ku,ko a police headquarters ɗin mu domin bincike, ko kuma idan muka dangana da court”

Doctors suka amsa da “to ba damuwa In Sha Allah.”

CP ya kalli ACP, sannan ya ce.

“Ina DSP Sardauna?”

ACP ya ce.

“Yanzu Sardauna ba ya cikin hayyacinsa” girgiza kai CP ya yi kana ya ce.

“Al’amari dai sam bai yi dadi ba ,ku saka a fito da gawar mu koma gida, shi Zayyan din bai farka ba ko?”

ACP ya ce 

“Eh bai farka ba”

CP ya ce.

“Okay bari naje na ga Sardaunan, ku yi hanzari don Allah ,kun ga yanzu har karfe hudu kar yarinyar nan ta kwana ,dan bazan manta ba ,na taɓa zuwa gidan su wata rana,tayi mana girki muna hira ,take ce mini ta tsani ta ga mutum ya rasu ba’ayi gaggawar kai sa maƙabarta ba,dan haka nake so mu kaita yau” yana fadi bai jira amsar su ba ya fice domin ya ga Sardauna.

DSP Sardauna zaune a mota ya kifa kai da gwiwa yana kuka,yana tunanin zahra’u , don ya taba cewa yana sonta ,amma ta ba sa hakuri ta gwada masa ita ɗan uwanta Zayyan take so.

CP ya ce

” DSP Sardauna, don Allah kayi hakuri ka dai na kuka, kai fa jarumin Ɗan sanda ne ,kar ka ƙara karyawa jama’a zuciya ,domin kukan ka barazana ce ga ahalin zahra’u, DSP Sardauna kai ne nake so ka karbi case din nan. Ina so kayi

amfani da basirar da Allah ya baka, ka zurfafa neman gaskiya duk da na san sai an sha wahala,amma In sha Allah za mu dace domin Allah ba ya barin zalunci a doran ƙasa”

Share hawayensa DSP Sardauna ya yi ,ya ɗaga idanunsa wanda suka koma jajaye, 

Ya ce.

“in sha Allah yallabai na maka Alƙawari sai inda karfina ya ƙare, ko da zan rasa raina”

CP, ya dafa kafadarsa ya ce 

“That’s very good DSP Sardauna”

A lokacin aka fito da gawar Zahra’u ,aka sake sakata a ambulance

Su Abba da Umma suka shiga  motar CP, aka ɗauki hanyar gida “

Tun daga farkon titi layi har i zuwa bakin gate din gidan Alhaji Aliyu Ibrahim MD, jama’a ne birjik, kaman an buga tambari, sai ka rantse shugaban ƙasa ne ya rasu.

Da ture-ture, da tare-tare ,aka samu damar shigewa da gawar Zahra’u cikin gidan.

Kawayen Umma su ne suka yiwa Zahra’u wanka ,aka shiryata cikin likafani, Sai da aka gama yi mata komai tukunna aka kira su Umma da sauran yan uwa da abokan arziƙi azo ayi mata adduah”

Ko da Umma ta durƙusa a gaban gawar ‘yarta Zahra’u kwance cikin makara, Umma ta rasa wani addua za tayi mata ,illa bin gawar da ido da ta ke yi.

Da kyar Umma  take fizgo kalman “Innalillahi wainna ilayhirrajiun!.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×