Skip to content
Part 19 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Wurin Baba maigadi na nufa, don can na hango mutane a tsaye. Wasu mutane ne su uku sai zazzare 1do suke yi, alamar rashin gaskiya, shi kuwa Baba maigadi yana zaune hankalinshi a kwance.

“Ba zan bude gidan ba, sai gari ya waye yau ma,”

Umma Karama ta iso wurin tare da wani alamar kiranta ya je yi, ganina a tsaye ya sata ta yi wani iri alamar rashin jin dadi.

“Maigadi ka ce ba za ka bude musu ba? Bayan ni na ce ka bude musu?”

Ya ce, ‘Ki yi hakuri Hajiya Lamido ne ya ce kar a bude sai gari ya waye tukunna.

Ta daka mishi tsawa, ‘Na ce ka bude musu da umanina da na Lamido wanne ne gaba?”

Yaya Almu ya fito daga dakin baba maigadi, ashe dama yana ciki ya ce mata.

“Ki yi hakuri Umma ba umarnina ba ne, umarnin Baba ne ya ce kar wanda ya shigo mishi gida bayan karfe goma, kar kuma a bar kowa ya fito bayan wannan lokacin. Yanzu karfe biyun dare ne an zo ana cewa a bude mishi gida kuma su wadannan mutane idan gari ya waye zan hada su da hukuma nc, don su amsa tambayoyi kan abin da suka shigo mana gida babu izinin mu, suka keta mana haddin gidan. Bayan haka suna cikin gidan nan dazu aka yi ihun barayi, duk wani wanda yake cikin gidan nan ya fito, amma su ban gan su ba, don haka ban yarda da su ba.”

Umma ta soma fadin maganganu. Ya ce mata, “Ke uwata ce Umma, don haka na roke ki ki yi hakuri, ba zan yi komai don cin mutuncinki ba, abin da kike tunani a kaina kuma ba haka ba ne, ni na kowane a gidan nan duk wanda yake ciki nawa ne, ba ni da wani bangare in kin ga ana yi miki wani abu wanda bai yi miki daidai ba gaya mini na yi alkawarin zan yi miki maganin abin ko waye mai yi mikin, kai ko Baba ne ki gaya mini, don shi mai karbar nasihar na kasa da shi ne.”

Yaya Kabiru ya fito da moto ya zo ya tsaya.

“Su shiga mu tafi.”

Da sauri ta ce, “Ina?”

Yaya Almu ya ce, Police Station za’a kai su, don su yi bayani.”

Jikin Umma ya yi matukar yin sanyi ta kira yaya Almu yabi bayanta suka tafi. Nima na koma daki na kwanta, sai dai ba barci na yi ba, har gari ya karasa wayewa, idona biyu. Sai da gari ya waye na fito bayan na gama komai na kimtsa sashin Ummana na nufa don in ga abin da ake ciki. Yaya Almu na samu a wurin ko’ina a bude yake gaba daya kayan sashin Umma an yi waje da shi. Cikin nutsuwa ya kalleni ya ce mini, “Kin karya ne?”

Na ce mishi, “Eh.”

To ki koma can, nan ba ki ga ana aiki ba?”

Na koma na je na gaida Umma Karama, na kuma tafi dakinsu Baba Talatu na hau gadon ta na  kwanta muna hira da ita ta ce mini, “Au dama can haka ake zaune in ba a binne wannan ba yau gobe za a binne wancan. Na da bai yi komai ba, ai na yanzu ma ba zai yi ba.”

Na ce, ‘Haka ne.”

Muka yi hirarmu. Ban fitò ba sai da yaya Almu ya aiko ya ce a kira ni. Na same shi a motarshi cikin kwalliya sosai, ga kamshin shi mai dadin ji.

“Shigo mana unguwa,za ki raka ni.” Na yi maza na shiga, saboda ina son tambayarshi labarin

mutnaen nan.

Muna tafiya muna hira na ce mishi, “Yauwa yaya Almu.”

Ya ce, ‘Na’am Uwale.”

Na yi maza na ce mishi, “Kai! Kai!! Yaya Almu gaskiya ba na son wannan sunan ko Baba ma Uwata yake kirana ba Uwale ba.”

“To, to shi kenan Adawiyya.”

Na ce, “Yauwa. To mutanen nan nake son jin yanda ká yi da su.”

Bai kalleni ba, ya ce, “Ina ruwanki da

maganarsu? Saura kuma ki ce za ki gayawa Umma abin da ya faru, don ke baki da wayo ba ki san abin da za ki rinka yi kina kwantar mata da hankali ba, kin dại san ba dabarar ki ba ce yasa kika ga wadannan nutanen za su iya yin abin su su gama babu wanda ya gansu, musamman da yake kin fito ne aka shiga, don ba a yi zaton komawarki a wannan lokacin ba, to kuma da sun bari kin yi barci ma da za su shiga Su yi abin su, su gama babu mai ganinsu, amma saboda Umma ba ta da alhakinsu ita tana zaune da komai zuciya daya shi ya sa duk abin da ake yi babu wanda ya taba samunta. Ai kin ji Baba maigadi ya ce irin wadannan bakin sun saba zuwa ko?

Na ce mishi, “Eh.”

To kar ki yi mata maganar na kuam san su Junaidu ba za su yi mata ba, yanzu dai za mu je ne ki zabar mata kayan da za su dace da wurin nata, don na sa an fitar da komai a mayar mata da sababbi.”

Na ce mishi, “To.”

Muna tafiya yana jaddada mini dole ne in zama mai hakuri kan al’amu masu yawa in gani in ki ji in ki gani, ko a gabana a ka yi abu in ba a ce in ganni ba sai in kawar da idona.

“Da na ki da wanda ba naki ba, duk ki maida shi naki. Yanzu kamar Umma kina iya gane nata da wanda ba nata ba? Babu wani wanda bai da alaka mai karfi tsakaninshi da Umma Karama, saboda ita kanwar Baba ce, amma hakan ya hana su son Umma?

Bai hanan su ba ko ba su sonta kuwa dole su hadiye su maida ita abokiyar mu’amallar su, saboda halinta, masu kin Umma na wajen gidan ne sune masu cewa wai abin da ya sa in ka zauna a gidan dole ka so ta, ko ka rinka jin maganarta wai asiri take yi a gishin miyar gidan ko?”

Ya waiwayo ya dan kalleni cikin murmushi ya ce, “Nima ki zo mini da irin wannan gishin Rabi. Na taya shi murmushin kawai a zuciyata na ce, ashe shi ma ana fada yana ji. Yana kallon hanya bai kalleni ba, ya ci gaba da magana.

“Da kike ganina na fiki sanin Umma, na fiki sanin sirrinta, domin nine na santa tana ganiyar kuruciyarta, na san ta tun loakcin da kishi yake yi mata zafi, na santa a lokacin da ake yi mata abu ranta ya baci ta yi fushi, ba yanzu ba da komai aka yi mata take kawar da ido akan shi, in da tana da dabi’a ta bin masu binne-binnen nan fo da nati kowa sanin hakan.

Na kuma gayawa Umma Karama ban boye mata ba cewar inda Umma tana yin irin abin da ake yi mata, to da an yi nasara a kan ta. To amma ba ta yi, don haka babu abin da zai faru da ita, sai alheri; don shi ta sani take kuma yi.”

Cikin kwanaki biyu kacal aka yi wa sashin Umma gyara na ban sha’awa, harabar wurinta gaba daya tiles ne masu tsadar gaske, sun yi matukar kawata wurin babu sauran a yi mata haka wurinta.

Gaba daya furannin wurin babu Su, sai yan kadan da aka kawata wurin da su ta hanyar ajiyewa kawai, amma ba shuka ba. Hatta labulayenta sabbbi ne farare Sol, marasa nauyi. Sai kuma aka bi, bayan su da masu ruwan sararin sama. Kayan falon gaba daya irin kalarshi kenan, bai yiwu ma in tsaya kwatanta kyan da wurin Ummana ya yi. Sai da aka gama gyara komai.

Sannan yaya Almu ya rufe shi. Ni kuwa na koma da kwana a dakinmu tare da su Aina’u ko ba komai dai na lura da gani har su mun ji jiki a damben da aka yi, don kuwa a yanzu ba sa yi mini irin kama- karyar da suka saba yi mini. Na kuma lura na gane Aina’u ba karamin son yaya Almu take yi ba, duk da zirga-zirgar saurayinta a wurinta ta kasa kawar da kai daga al’amarinshi, ko wayata ce ta yi motsi sai ta kasa kunne ta ji dawa nake magana? Ni kuwa dana ganeta in tana wuri ya yi mini magana sai in sake mu yi ta hirarmu mai dadi, ina yalkyalewa da dariya, sabanin in a gaban shi na ke sakin baki da nake yi in yi ta gaya mishi maganganu masu dadin ji, in kashe murya in yi ta gaya mishi irin son shi da nake yi da darajojin da yake da su wadanda suka bambanta shi da sauran maza. Ya sa babu dama ya yi minti talatin bai yi mini waya ba, sai dai in wani aiki yake yi, bai sani ba ni don in kular da Anti Aina’u mai nuna kishi a fili nake yin hakan.

Rannan Ummana za ta dawo tun safe yaya Almu ya bude wurinta. Baba Talatu ta shiga ta gama gyara komai nima ina tayata, muka gama na faffesa turararruka kala daban-daban. Sannan ya sake rufewa Nima na je na yi wanka, muka yi shiri ni da shi muka tafi dauko su a airport cikin motar da ake dauko Baba.

Umma tana zaune a falonta bayan sun gama cin abinci, sun huta an maida kawayenta gida ta kuma gama gaisawa da jama’a ta kalle ni cikin murmushin dake kara bayyanar da farin cikinta ta ce mini, Wannan dai aikin Babangida ne?”

Na ce mata, “Eh Umm.”

Kamar in gaya mata abin da ya faru wanda ya yi dalilin da aka yi mata aikin. Sai kuma na tuna kashedin da ya ba ni na cewar ba wai zai boye maganar ba ne, don yana son a cutar da ita, shi mai yin komai ne wajen ganin ya kareta daga kowacce irin cuta, sanin darajar Umma wurin yaya Almu ya sa nima na kame bakina, na yi shiru, na bar ta ta yi ta farin cikinta.

Rannan muna kwance a kan gadon Umma da daddare, ko wurin yaya Almu ban yarda na je ba, saboda dokin dawowar Ummana, hira mai dadi muke yi. Maganganun da suka shafe mu muke yi cikin hirar ta mu ce Umma ta yi mirii maganar da ta sanya ni yi mata tambaya. Bayan ta kai karshen zancen nata, cikin nutsuwa na ce mata, “Umma!”

A hankali ta ce mini, “Mene ne ya faru Adawiyya?”

Na ce mata, “Kin taba gaya mini cewar ke din baki hada komai ba da baba a mu’amalla ta zumunci, amma kuma gashi a yau kina ba ni labarin gadon da kika ci a gidan su Baba.”

Ta miko hannu tana shafa hannuna, dana shagala kan wuyanta ta ce, “Kai Adawiyyah wane irin taushi jikinki ya yi haka?”

Na ce mata, Yaya Almu ne ya canza mini kayan shafa.”

Ta yi murmushi ta ce, “Bari yau in dan baki labari na dan kadan tun da kin girma kin yi hankali.

kwanaki kadan ne kuma suka rage mana za ki tafi gidan mijinki bai kamata a ce ba ki san komai a kan al’amarinki ba, ko da yake dai mijin da za ki aura ya san komai a kana, babu wanda ya san sirrina irin shi, shi ya sa nake kara son aurenku don kuwa mutumin da ,nake so fiye da kowane Alhaji zai bai wa ke wannan alheri da Alhaji ya yi mini ya kara bayyanar mini da muhimmancina a wurin shi.

Na ce, “Haka ne Umma, to ba ni labarin na ki in ji?”

Ta ce, ‘Yanzu kuwa.” Tana yin gyaran murya ta ce mini to.

Ni dai ko ban gaya miki ba kin san sunana Zuwairiya, hakan nan na sha gaya miki cewar ni din ban taba sanin mahaifiyata ba, ina dai kawai na san ina matukar kama da ita, abin da babana ya gaya mini kenan mahaifiyata mai hakuri ce kwarai. Na sha jin shi yana jaddada hakurin nata a lokuta daban-daban.

Babana ya yi abota ne da mahaifinsu Alhaji suka yi mu’amalla a kan harkar dukiya na dan lokaci kadan, sai suka rabu, saboda dama abotar ta su a kan harkar sana’a ce garin su ba daya ba ne. An yi hakan ne kuma shekaru masu yawa kafin a haife ni, amma har na yi wayo Baba yana bani labarin amana irin ta mallam Mai Hadisi, samun irinta wurin mutanen wannan zamani da wuya.

Bayan rasuwar mahaifiyata Baba bai sake aure ba, na sha jin aminanshi suna ce mishi mallam Aliyu ina amfanin wannan zaman nan ka a haka? Shi kuwa ya kan yi murmushi ya ce inda sauran auren sai wani dalili ya sa yi. Mafi yawancin sanin da na yi wa Baba na yi mishi ne a kwanakin da lafiya ta yi mishi karanci, watakila saboda yawan shekaru, watakila kuma saboda kusantowar wa’adi.

A irin hirarrakin da ya kan yi mini ne a wancan lokacin ya sanar da ni nufin shi na kaini wurin malam Mai Hadisi ya bayar da amanata a gare shi, sąboda ya san shi din zai rike ni kamar ‘yar cikin shi, koma fiye da hakan; don bai taba ganin mai amana irin ta shi ba.

A irin soyayyar da na san Babana yana yi mini nan kuma ji shi yana cewa zai bada rikona a wani wuri sai na tsorata na yi ta kuka ina rokon shi ya bar ni in zauna tare da shi: Ya kalleni cikin tausayawa ya ce “Ki yi hakuri kamar Yadda nima na yi, ina jin tsoron kar in mutu in bar ki a nan ba ni da wasu ‘yan’uwa a kusa tun da ni ba mutumin nan kusa ba ne.

Sannan ba zan iya bada amanar ki wurin kowa ba in ba shi ba, don ko na yi hakan hankalina ba kwanciya zai yi ba. Mai Hadisi shi ne kadai mutumin da na bai wa ajiyar dukiyata a lokacin da zan tafi kasarzmu na je na dawo na same ta ko kwanceta bai yi ba, balle ya taba bayan na je na yi shekaru uku maimakon watsa shidan da na ce mishi zan yi, sauran wadanda na bai wa ajiyar duk sun cinye, wasu ma cewa suka yi ban ba su komai ba.

A yanzu na riga na tsorata da rashin lafiyar nan don na san halin ciwon da ke tafiya yana dawowa, na san abin da yake nema. To gara in kai mishi ke da kaina duk da mun yi shekaru ba mu ji duriyar juna ba, in dai yana nan zai rike mini ke, in kuma baya nan zan bai wa iyalinshi in ya so in roke su su kai mini ko wurin dangina. Akwai bayanin komai a ajiye in kuma ma na same shi to shi ya san komai, don na taba bashi labarin kaina saboda lura da halin shi da na yi.

Mun yi wannan hirar da kwana biyu ne kawai Baba ya kwanta jinya mai tsanani, daga ni har shi hankalinmu ya yi matukar tashi, ni ina damuwar rashin lafiyarshi, shi kuwa yana damuwar bai samu kai ni Wurin amininshi ba.

Kwanaki kusan talatin yana kwance ni ke yi mishi komai, sai ko makwabtan da ke shigowa suna taimako na da abubuwan da na kasa. Rannan sai Baba ya dan samu sauki har ya fita ya bi sallar jam’i yana dawowa ya kalleni ya ce, “In har saukin nan nawa ya kai gobe da safe, to kamar yanzu a gobe insha Allahu kina Katagun zan je in kai ki ba zan sake wani bata lokaci ba.”

<< Wace Ce Ni? 18Wace Ce Ni 20? >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×