A haka na yi zaman makaranta tun ban iya hidimominta ba har na koya kullum ba ni da wani aiki in na kwanta sai na lissafin ranar hutu.
Ranar da Yaya Almu ya gaya mini kenan zai kawo ni gida in sadu da Ummana ranar da zuciyata ta rinka shakkun isowarta, saboda tsaikonta da nake gani.
Duk ranar ziyara dai Yaya Almu bai fashin zuwa, in zai zo kuwa hatta ruwan sha kawo mini yake yi, amma duk da haka a banza ban ganin alherin shi. Kawayena dai ba su da wata hira in banda hirar kai Yayan Rabi’atu yana sonta, ji rannan ma da ya zo ya yi mata abu kaza da kaza, muma ya ba mu abu kaza da kaza.
Ni kam zuba musu ido kawai na yi ina kallon su.
Ana gobe za a ba mu hutu kuwa ni kam kwana na yi idona biyu ko gyangyadi ban iya yi ba, saboda zumudi, gari na wayewa na gama shirina ko wanka ban yi ba na tasa jakata a gabana ina zaman jiran zuwan Yaya Almu da na rinka ganin kamar ba zai iso ba.
Sai wajen karfe goma sha biyu ya iso kan nan kuwa na riga na gaji da jira wai da ya kalleni sai ya ce mini;
“Na dan sarara ne ki samu ki gama kintsa kayanki: “
Ban tanka mishi ba, kawai yaran ajin mu suka biyo ni da jakata suka kawo mini ita cikin motar, Yaya Almu shi kuma ya kawo kudi ya ba su.
A gida rannan Ummana da Baba Talatu kuka suka yi ta yi suna fyace majina ana ba su hakuri da suka ganni.
“Mu je in yi miki wanka in dirje miki wannan dattin da ya zauna miki a jiki, saboda rashin wanka mai kyau.”
In ji Baba Talatu. Na ce mata, ‘A’a zan yi wankan da kaina.”
Da daddare muna kwance a kan gadon Umma tana kankame da ni, tamfar so take ta maida ni cikinta ta ce;
“Bari hutun nan ya zo karshe zan ga yadda za a yi Lamido ya ce zai maida ke wannan makarantar ja’irin yaro káwai, ya je ya kai ki wata munafukar makarantar da ya ki fadar inda take balle in rinka zuwa duba ki.
Inda na san inda kike ai ko ban rinka zuwa ganinki kullum-kullum ba zan je kowanne sati.”
Ni kam tun da Umma ta ce ba za ta bari Yaya Almu ya maida ni ba, na samu kwanciyar hankalinan da nan na dan yi kyau na yi kumari kibata ta soma dawowa.
Kullum ina tare da Ummana ita da kanta dai ta yarda cewar wai zaman makarantar ya canzani, na zama nutsatstsiya mai son aiki na daina zagin mutane ba na ma shiga harkar su in ba sune suka tsoma ni a ciki ba, to amma kuma ta kafe kan cewar wahalar ta ta yi yawa, don haka zan dawo gida a canza mini wata wacce za a rinka ba ni cikakkiyar kulawar da ta dace da ni.
Shi kam Yaya Almu harkokin shi kawai yake yi, tsakanina da shi dai ina kwana ne ina gajiya?
In na yi kamar ban ganshi ba, kuma shima ya yi kamar bai san da ni ba, ni kuwa ko motsin tahowar shi na ji sai in yi maza na shige dakin Ummana, don ban son ganin shi.
Rannan da safe ranar wata litinin ya shigo falon Unma da safe cikin shirin fita, shigar shi ce dai a tare da shi ta fareren kaya kamar kullum, kuma ya yi kyau yana sosa kunnenshi da dan makullin motar da ke hannun shi.
“Ina Rabi take Umma?
Ba tare da ta yi wani tunani ba ta ce masa,
Tana ciki.” Ya bude bakin shi ya kirani, “Rabi zo mu je nan ki yi mini rakiya.”
Kullum kalmar da yake amfani da ita kenan in zai ce in yi mishi rakiya.
Hakan nan ya sha fita da ni don haka abin bai zamo mana wani sabon al’amari ba.
Mun fito mun hau kan hanya muna taifya ya dan juyo kadan ya kalleni kafin ya tambayeni,
Yaushe ne butun makarantar ku zai kare?”
Sai da na ji kirjina ya yi dam kafin na shiga kici-kicin kokarin tunanowa cikin fargaba da tsoro sai dai ban iya tunowa ba, saboda tunda aka ba mu hutun ban taba damuwa da son in san yaushe hutun zai kare ba, ni dai bukatata kawai ita ce in ganni a gida.
Tsawon lokaci ina nazari ban iya bashi amsa ba, sai shi da kan shi ne ya gaji ya ce mini,
“Hutun ya kare tun shekaran jiya, don haka yanzu daukoki na yi zan maida ke makarantar kár kuma ki ce za ki yi mini kuka, don wancan karon wahalar da kika ba ni ba karama ba ce, in kika ce za ki sake yi mini haka a yanzu ba zan rinka zuwa duba ki ba.”
Kankame bakina na yi na rike don kar ya ji karar kukan da nake yi na yi ta zubar da hawaye kawai, har muka isa makaranta kuwa maganganu yake yi mini kan muhimmancin ilimi da kuma iya mu’amalla da jama’a.
Muka isa makaranta ya bude bayan motar shi ya yi ta ciro jakankunan da ya riga ya yi mini.sayayya yara suka dibar mini jakankunan ni kuma na bi bayan su ina kuka.
Ina shiga dakin mu yaran da na tarar a ciki suka hayayyako mini.
“Kai Rabi’atu hutun ma ke da kuka ki ke dawowa? To Maman ki ta bar ki a gida mana kawai ta rinka dora miki tallan kamu.”
Gaba daya suka kwashe da dariya, suna fadin, ‘Ai kuwa wannan za ta yi kyau da daukan tiren kamu da sassafe.”
To a kwana a tashi haka dai har na hakura na saba da zaman makáranta, har na kwaci kaina wurin yaran da sakarcina ya sa suka rainani a farkon shiga ta makarantar a haka na kasance har na zo aji uku muka yi jarabawa na dawo gida ina jiran fitowar sakamakona, har a wannan zaman ma Yaya Almu bai bar ni na sarara ba, samin ido ya yi ya kafa mini dokar tashi in je masallacin gidan mu da Asuba in yi sallah, bai yarda a ce mishi na yi a daki ba, in na zo másallacin ma wai sai na bari ya ganni tukunna kafin in bar masallacin in dawo daki.
Ni kam cewa Umma na yi sai dai ya san yadda zai yi da ni ba dorina ba ya sa takobi ya fillce mini kai, in ga karshen kiyayya kenan da tsana.
A ce tun daga nan sai na tafi har masallaci kafin in yi sallah? Umma ta zuba mini ido tanan kallona ta ce.
“Ba dai Babangida kike wa wadannan naganganun ba ko?”
Na kara daure fuska na ce mata, Shi mana…
Umma ai kina kallon abubuwan da yake yi mini na ‘yan ubanci, amma ba ki taba yi mishi magana ba.”
Ta kama baki ta rike nuna alamar mamaki ta ce, “Babangidan ne mai nuna miki yan ubanci?”
Na ce, “Eh mana.”
Ta gyada kai tare da cewar, “Lalle ba ki da wayo.”
Sau biyu na san Yaya Almu ya kiranı ya jaddada mini dokar da ya kafa mini ta zuwa sallar
Asuba a masallaci, bai kuma yarda in zo in tafi ba tare da na jira mun hada ido da shi ba, ni kuwa na yi ko in kula.
Rannan da Umma ta zo tana tashina da Asuba ma kurma mata ihu na yi na ce,
“Ni Umma ki bar ni ki daina tashina a wannan muku mukun sanyin.”
Ina jin Yaya Almu lokacin da ya zo gaishe ta yana gaya mata har yanzu Rabi.ba ta soma zuwa sallar Asuba a masallaci ba, kamar yadda sauran yaran gidan suke zuwa?
Umma ta bashi labarin sakarcin da na yi mata sanda ta zo tashina tana dariya da ta gama sai ta ce mishi ai ina ganin hakuri za ki. yi da wannan dokar sai badi war aka kan nan ta kara kwari.
Bai ce mata komai ba ya sauko musu wata hirar.
Washe gari kuwa da Asuba ina cikin kwanciyata ina lullu6e cikin bargona mai laushi sai kawai na ji an fige bargon na shiga rarume- rarumen-abin rufawa, ina fadin, “Umma me ye haka? Umma me ye haka? Umma ba na son irin wannan.
Kan in karasa fadin abin da zan fada din sai kawai na ji saukar bulala a jikina tsal! Tsal!!
Saboda gigicewa sai na saki fitsari akan gadon, kafin na iya kurma ihu da gudu Baba Talatu ta shigo tana fadin, “Me Uwar dakina ta yi wa Lamido? Ka yi hakuri, ka yi hakuri, ka huce ka hadiye wannan fushi da ka yi.”
Da sauri ya juya ya fita ya bar dakin, ni kuwa na samu damar kurma ihu ina birgima a cikin fitsarin da na yi, ita kuwa sai rarrashina take yi tana kakkama ni, da kyar ta shawo kaina na yarda na je na yi wanka na yi alwala na zo na yi sallah.
Tun daga ranar tashi daya Umma take yi mini ta ce mini tashi ki yi alwala ki tafi masallaci an kira sallah, in kuma kin ki kin san sarai Babangida zai shigo bar nan ya zo ya same ki.
Inaaa! tana fadi hakan zan tashi in je in yi alwala in nufi masallaci, tun ina tashin ina tsaki har na saba ya zame mii dabi’a.
A wannan zaman da na yi ne Yaya Almu ya tilasta mini cin abinci, tare da yaran gidan mu.
A farko ya hada ni da wadanda na girma da na ce mishi ba su iya tauna ba, kuma in muna cin abinci suna ci mini gabana.
Sai ya ce to ya raba ni da su ya hada ni da wadanda suka girme ni, ya kuma gaya musu cewar tun da ni ce karama to ni-ce zan rinka zuwa ina dauko abincin in an gama kuma in fita da kwanukan, su kuma abin nema ya samu don su dukkansu da wuya in akwai wacce ba ta jin haushina saboda rashin kunyar da na rinka yi musu a baya, don haka gaba dayansu tasa ni a gaba suka yi in na yi magana su kai karata wurin shi, suka hada suka takura mini babu halin in ce na koshi sai su daka mini tsawa su ce kwanon wa za ki barwa sudi? Na gaji da matsin su na ce mishi ya maida ni cikin yaran kawai ya ce a’a anan yake son ganina.
A haka na zauna a gida har lokacin komawa makaranta ya yi a wannan karon ni da kaima na gayawa Yaya Almu wasu daga cikin sayayyar da ya yi mini sai dai hakan ba vwai yana nufin na Soma son karatun ba ne, a’a sani dai kawai na yi ya zama dole zan koma don baka a yanzu Allah- Allah nake yi in gama makarantar in dawo gida in ga kuma inda za a sake turani da sunan karatu.
A makaranta a yanzu na wattsake na fita daga cikin mafi yawancin wahalhaluna da na yi gamuwa da su a karatuna na junior a yau na zama cikin yan mata masu fada a da yawan yara tsorona suke yi, wasu don tsiwata wasu-kuwa don Kullum cikin ba su abin masarufi nake.
A haka har muka zo ajin karshe wato S.S. 3 muka yi jarrabwa muka dawo gida sakamako ya fito na samu C guda biyu da B daya, ba zan iya kwatanta bacin ran Yaya Almu ba, ranar da ya duba sakamakon nawa ya zo ya tasani a gaba ya ce, “Credit a Hausa da Islamic Studies Rabi?”Na bata rai na ce, ‘Allah bai wa masu F9 hakuri.” Ya kalleni cikin takaici ya ce, “To amin.”
*****
Alhaji Bello Mustapha sanan nan mutum ne da sunan shi ya riga ya shahara saboda dalilai masu yawa.
Farko dai kasancewar shi babban dan kasuwa, yana rike da sarautar gargajiya a garinmu, ban da haka mai taimakon jama’a ne.
Gidan mu babban gida ne kwarai, ba zai yiwu in tsaya ina kwatanta girman shi ba, abin da zan iya fadi kawai shine da katangar gidanmu da ta pen House din mu sune suka mamaye sashin bangaren da muke.
Gabadaya girman gidanmu ya wuce a tsaya ana kwatantashi.
Akwai sashin baba da na wurin saukar bakin shi da wurin ajiye motoci da dakunan taro da sashan matanshi guda uku wadanda aka yi musu ne ba da juna, akwai sashan yara maza wanda shima kashi biyu yake bangaren samari dana yara kanana, haka nan sashin yan mata shima yake ga bangaren masu aiki da wurin yin girki haka nan can karshen bangon gidanmu ta baya wani babban fili ne da aka yi shuke-shuken bishiyoyi a wurinne kuma baba yake kiwon raguna amma basa iya shigowa cikin gida saboda a killace suke.
lyali ne masu yawan gaske a gidanmu a lokacin da na ta so ina karama ta mu kusan arba’in ne yara a gidan maza da mata manya da kuma kanana.
Amma daga cikinmu duka mu biyu ne kadai muke amfani da sunan baba da gani sai yaya Almu duk sauran ‘ya’yan dangine dana tsofafftin abokan da aka taso tare don ko akan idona ma an kawo yara da yawa daga kauyenmu wadanda suka isa sawa a makaranta don ma dawowar yaya Almu ya ajiye ka’ida na kawo yaro daya ko biyu daga gida guda in za’a kawo biyun kuma to sharadi ne a kawo mace da namiji ba maza kawai ba.
Shi ne abin ya danyi sauki amma in da don ta Babane shi babu ruwanshi. Ko guda nawa za’a kawo ba zai ce komai ba.
Baba mutum ne mai daukan nauyi da dawainiyar jama’a bai taba gajiya da hidimar mutane ba rikon ya’yan yan uwa da yake yi ya dauki hidimar komai na al’amarin rayuwarsu, bai hanawa kuma iyayensu su taho neman wasu bukatun nasa a wurinshi tun ma ba lokacin damuna ba kullum zaka sameshi yana aiken kudin takin zamani wai wanda zasu yi amfani da shi a gonakinsu.
Wata rana ina tare dashi yana ta fadin abinda za a baiwa kowanne nace mishi haba baba kudin takin ma kaine mai basu in sunyi noman fa, basa kawo mana komai gidan nan sai ya kalleni yayi murmushi ya ce ai sun taimakeni uwata da suke yarda in sun karbi kudin takin su tsaya su noma gonakin nasu, su samu abinda za su ci, ba su rinka jiran sai ni na kawo ba.