Skip to content
Part 20 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

To haka aka yi gari yana wayewa daga fitowa daga sallar Asuba Baba ya tasa ni a gaba da dan kullin kayana a kaina muka je muka shiga mota zuwa Katagun. Wajen Azahar muka isa.

Duk da tsawon shekarun da suka yi ba su sadu ba, ga kuma halin rashin lafiya. Kai tsaye Baba ya kai mu gidan bai zauna ba, yana daga tsaye tamkar bai gaji ba ya tura wani yaro cikin gidan ya ce, “Ka shiga nan gidan ka ce wai ana sallama da mallam Mai Hadisi.”

Nan da nan sai ga yaran nan ya fito tare da wani kyakkyawan dattijo kakkarfa, gabadaya kasumbar shi ta yi furfura da ganinshi ka ga ma’abocin tsabta irin ta addini. Yana ganin Babana ya buda baki nuna alamar mamaki da sauri ya zo ya rumgume shi yana fadin,

“Malam Ali ashe mafarkin da nake yi da kai na rabon saduwa ne? Ai ni har na tara yara na yi musu bayaninka na gaya musu watakila za ka zo ne a bayana, ashe, ashe za mu sake ganin juna ne. To ka shigo.”

Ya rike hannun Baba suka shiga ciki; nima na bi bayanshi zuwa dakin da aka sauki babana. Baba da kan shi ya dama mana fura. Nan da nan ‘ya’yanshi magidanta suka yi ta shigowa suna gaida baba, shi kuwa yana gaya musu Gashi nan wanda nake baku labarinshi shekaran jiya nake gaya muku kar ya zo bayana ku ce ba ku san shi ba,”

Nan da nan sai gashi an kewaye mu da kayan Sauka iri-iri su kuwa su Baba suna hira. Zuwa can sai baba ya kalleni ya ce,Wannan yar yarinyar dai Saratu ce ta haifar mana ita, ko da ban sani ba.

Babana ya yi murmushi bayan ya kara kallona ya ce mishi, ‘Eh. “

Baba ya ce, ‘To ina Saratun take?”

Babana ya ce, “Bana shekarunta biyar tana kwance a kasa.”

Maganar ta yi matukar girgiza baba. Nan da nan ya shiga yi mata addu’o’i iri-iri na neman rahama.

Da aka natsa sai Babana ya ce mishi, “Malam nauyi fa na zo zan dora maka sai ka yi hakuri.”

Baba ya ce, ‘Nauyi wane iri Malam Ali?”

Babana yay gama yi mishi bayanin halin da yake ciki. Da ya gama sai ya ce mishi, ‘Shi ya sa na dauko Zuwaira na kawo maka ita ka saka ta cikin Iyalinka ta zauna ka reneta tare da su, in har ka yarda ka karbi wannan amana da nan kawo maka to ni zan koma gida, cikin farin ciki in je in saurari isowar lokacina cikin kwanciyar hankali.”

Baba ya kalli Babana cikin sanyin jiki ya ce mishi, “To in ban da abin ka małam Ali wannan irin amana da ka kawo mini ni kwana nawa zan kara bayanka in biyo ka? Daga ni har kai ai daya muke a bakin gaba muke, don haka ina ganin tunda ka amince ka kuma, samu iko ka kawo mini ita amana, to bisa yardarka nima bari in bai wa yara ita in sun yi yawan rai sai su rayu tare, don haka in ka yarda zan bai wa Bello aurenta.

Babana ya kalleshi ya ce, “Ta ka ce fa ikonta yana hannunka duk abin da ka hukunta a kanta daidai ne.”

Baba ya mike ya kama hannuna ya ce, “Mu je Zuwaira in kai ki wurin uwarki.”

Na mikc muka shiga cikin gidan mai sassa da yawa ya ratsa ya kai ni na shi sashin. Matarshi tana ta faman aikinta cikin nutsuwa tana ganinshi ta mike tsaye tana gyara yafenta ta yi murmushi ta ce, “Kana labarinshi ashe yana kan hanya.”

Ya ce mata, ‘Eh Rabi sai, dai ya kawo mana aiki amana kin kuwa san in banda girman darajar shi a wurina babu abin da zai sa in karbe ta a wannan kurarren lokacin, don haka me kika gani cikin yaran in zan bai wa wani aurenta, wa ya kamata in ba?”

Ta dan yi shiru cikin tunani, kafin daga baya ta ce, “To ka bai wa Bello mana, duk da dai akwai na gaba da shi.”

Ya ce, “To mun yi daidai nima dama shi na fada, shi zan bai wa.”

Ya juya cikin sauri ya fita ya bar ni a wurinta.

Nan da nan ta maida ni ‘yar gida ta hanyar dauko mini wannan wancan, ci wannan, karasa wannan, abin da take fadi kenan.

Washe gari da hantsi sai kawai aka shiga gida ana raba goro da dabino. Ana fadin an daura auren Bello da bakuwar yarinyar, Gaba daya gida ya dauka ikon Allah, dama ashe matar Bello ce ta zo.

Baba Rabi ta yi maza ta sanya ni a lungun dakinta. Bayan ta kawo sababbin tufafi ta bani na. Sanya ta lullube ni ta ce, “Yi zamanki anan kar ki bari kowa ya ga fuskarki.” Na ce mata to.

Na wuni anan a lullube, sai dai bini-bini zata zo ta kawo mini wani abin da zan ci. Ta ce mini maza cinye kar mutane su ganki, in ce to, ba tare da na san abin da hakan ke nufi ba. Kan ka ce me ye wannan sai ga gida ya cika da jama’a masu zuwa murnar Bello ya yi mata. Da daddare bayan jama’a masu tafi ne Baba Rabi ta tasani a gaba ta kai ni dakin da Babana yake ta tsugunna daga bakin kofa ta gaishe shi ta juya. Ni kuwa na shiga ciki na zauna a kusa da shi. Ya kalleni cikin murmushi duk da kaduwar sanyin da yake yi ya ce,

“Ashe gidanki na kawo ki?”

Ban kula wannan maganar ba,  saboda hankalina ya tashi da ganin yana rawar sanyi. Baan ga wuta a dakin. Na ce mishi, “Baba ciwonka yau ma zai tashi ne?”

Ya ce, ‘Ai babu komai tun da na riga na kawon ki inda ya kamata in kawo ki, ke dai ki zama mai hakuri da bin na gaba da ke, musamman mijinki.”

Dan zaman da na yi a wurin nan baba bai yi shiru ba nasiha yake ta yi mini har aka zo aka tafi da ni cikin gida.

Halin da na samu babana a ciki ya sa ban iya nutsuwa ba, ina ta tunanin jikin na shi inda a gida muke da ina tare da shi ina dan bashi ruwa yana sha, don jika bakin shi. Yanzu kuwa babu hali an kankane  shi. Ina nan a kwance na ji baba ya shigo yana salati.

Yana karawa da sauri baba Rabi ta tashi tana taya shi salatin tare da tambayarshi.

“Ya ya dai malam?”

Ya ce mata, ‘Malam Aliyu ya cika, wa’adi ya cika.”

Kalmar ya cika din da ya yi amfani da ita da kuam fadan da Baba Rabi ta yi mini na in koma kwanta ya sa ban gane rasuwa ya yi ba. Sai da gari ya waye na yi kuka har na gaji baba Rabi tana ta rarrashina, amma ina, ko da nake yarinya a lokacin mai shekaru bakwai na riga na gane mutuwa, saboda yawan labarinta da babana yake ba ni, gashi kuma na riga na shaku da shi, shi kadai na sani, shi kadai nake mu’amalla da shi. in banda jiya da na shigo cikin sababbin mutanen da suka karbe ni hannu bibbiyu har na ji zuciyata ta dan samu nutsuwa a tare da su.

Jama’a masu yawan gaske ne suka yi jana’izar Baba, tamkar ba bako ba, aka yi zaman makoki na kwanaki uku aka gama.

Washe gari bayan an idar da sallar Asuba, ina zaune ina karanta addu’o’in da baba Rabi ta ce in rinka yi wa iyayena, sai na ga wani ya shigo, bayan na amsa mishi sallamar shi ya nemi wuri ya zauna cikin nutsuwa muka gaisa da shi, ya yi mini ta’aziyya. Ban damu da kallonshi ba, don dama samarin gidan sun yi ta shigowa suna gaishe ni, sai dai shi wannan dabi’arshi daban take da ta sauran. Nutsuwar shi ma daban take, hakan nan kalaman da yake yi mni na kwantar da hankali ne.

“Baba Rabi ba ta gaya miki Baba ya cika yana kalmar shahada ba?”

A hankali na ce mishi, Ta gaya mini.”

To kar ki sake bakin ciki, kar ki sake kuka, ki rinka yi mishi addu’a kawai. Cikawa da kalmar shahada alamar samun rahama ce, dama kuma mun san nan ba matabbata ba ce, hanya ce kawai ta wucewa zuwa inda muka dosa, ko ba haka ba?

Na ce mishi, “Haka ne.”

Ya sake kallona cikin nutsuwa ya cc mini, “Miko mini maburgin can na kan dankin Baba, hannunki zai kai?”

Na yi maza na ce mishi, Eh.” Na mike na dauko mishi ya yi kamar za karba, sai kuma ya ce,

Ko kuma maida shi ki yi zamanki kin taba kada miya kurwa”

Na ce mishi, Eh a gida ni nake mana da Baba bai da lafiya.” Sai ya ce mini ga yanda zan yi, ga yanda zan yi. Ban damu da kallon da ya rinka yi mini ba, hakan nan ban kula jana da magana da yake ta yi ba, ban fahimci komai a game da shi ba, sai da ya ce mini,

“Wai an daura miki aure da wani Bello ko?”

Na dan sunkuyar da kaina kasa nuna alamar kunya. Ya ce, “Kin taba ganinshi?” Na girgiza kaina a hankali tare da cewa, “A’a.”

Ya yi gyaran murya a hankali ya ce mini, “To nine Bello da aka daura miki aure da shi.” Ina jin haka na yi wuf na koma lungun da Baba Rabi ta nuna mini na jawo katon zanin da ta ba ni na lullube kaina. Ban san yanda aka yi ya fita ba.

An dauki lokaci mai tsawo Alhaji yána mini gizo ba na gane shi. Dukkansu gaisuwa daya nake yi musu, sai shi ne yake ce mini, “Ke wannan mijinki ne Zuwairiya rinka kallona kina gane ni.” Ina jin ya fadi haka sai in ruga in shige lungun da ke kusa in buya.

Ina gane Alhaji shi kenan sai na shaida kowa na gane wannan shi ne yaya Babba, wannan shi ne yaya Barau, ga yayan Tudu, sune maza manya da ke gaba da shi, sauran matane sai kuma kannen Alhaji. Baba ya’ya ne da shi sosai matr yawancinsu mata sunna gidajen aurensu.

Da na wattsake a gidan nan na zama ‘yar gida sosai na zama ba mai cewa ni daban ce a cikin gidan. Wasa sosai nake yi da yaran gidan sa’o’ina. Baba kuwa har kayan wasa yake sai mini, su tallen miya, su tandun tuya, su gadon ‘yar bebi. Komai na kayan wasa babu abin da ba ni da shi. Da daddare kuma in ya dawo zai kirani dakinshi mu yi dumi tare ya kuam ba ni abin tsarabar da ya zo mini da shi. Na yi sabo mai tsananin yawa da Baba, hira sosai yake yi mini, ya kuma yi ta tambayana abubuwa ina gaya mishi.

Rannan na je gaishe shi da safe da ya kalleni sai ya ce mini, Kina lissafi kuwa Zuwaira yau fa shekara guda ne tun da muka rabu da dan’uwana malam Aliyu?”

Na yi shiru cikin jimami, hawaye suka soma zuba a idona. Lokaci mai tsawo ya dauka yana ba ni labarin halin rayuwa ya yi mini hirar mu’amallarshi da babana.

‘Mahaifinki mutum ne mai son gaskiya wanda bai son nuku-nuku ko kunbiya-kunbiya kan wani lamari, ko nawa zai samu cikin har ka yana hango rashin gaskiya a ciki za ka ji ya ce ba ya so. Ki zama mai gaskiya ke ma kin ji ko?”

Na ce, To Baba.”

Ranar da daddare da Alhaji ya dawo ya kirani na je na same shi a bayan rumbu yana tsaye ya kalli tandun tuyan masan wasan da ke hannuna ya kalleni cikin nutsuwa ya ce mini, “Sai yaushe kike ganin za ki daina wasan nan Zuwairiyya? Yau fa shekara guda ne da auren mu ko kin manta ne?” Ban amsa mishi ba.

Badi iwar haka kuma ina ganin kamar zan bukaci baba ya ba ni ke.”

Kullum ya dawo zai nuna rashin dadin shi game da wasannin da ya kan samu ina cikin yara, kowanne lokaci sai ya gaya mini “Wadannan yayyanki ne, amma kina wasa da su, maimakon ki tsame kan ki daga cikin su, ki kama girmanki, ba ki girme su ba a shekaru, amma kin fi su daraja, saboda ke matar kanin Babansu ce.”

Da irin wadannan kalaman na shi na fita harkar wasanni na koma zama tare da baba Rabi, ina koyon aikin gida, tare da ita. A wannan lokacin komai na aikin gida ni na ke yi, Baba Rabi kan yi mini gyara ne kawai ta hanyar ba ni umarni mafi yawancin lokaci na kan yi aikin ne tana tare da mijinta suna hirarsu.

Mace mai matukar karamci. Na dade kwarai a gidan kafin na ngane ba ita ce mahaifiyar Alhaji ba. Ta yi matukar kokari wajen sabar da ni yin mu’amalla da shi, ta hanyar aikena wurinshi da take yi kai mishi, ko dauko mishi, maimakon da da sai ya ritsani ne a wani wuri yake gaya mini abin da yake son gaya mini.

Rannan Baba Rabi da Baba suna hira ina jinsu, ni kuwa ina dakin dahuwa tankadan tuwon dare nake yi. Lokacin nan kuwa shekaruna tara ne, sai naji ta tana ce mishi.

“Anya Malam ba ka ga kamar Bello zai bukaci a bashi matarshi da wuri ba kuwa?”

Ya ce, Na gani mana ja’iri bashi ita ne kawai ba zan yi ba, sai ta yi sha uku ta mori kuruciyarta tukunna.”

Da sauri baba Rabi ta ce, “Tabdijan! Ai kuwa dai abin da ba zai yiwu ba, kenan shekarun shi nawa ne yanzu? Yan’uwanshi suna kamar shi ai matansu sun tare musu, bana fa shekarunshi ashirin ne.

Baba ya ce, ‘Eh ba mancewa na yi ba.”

To shi ne za ka tsare mishi ita har shekaru hudu? Ai kai ma gara ka san ba zai yiwu ba, don kuwa zirga- zirgar nan tashi ta tsakanin nan a kanta ne babu abinda ya ke so irin ya shigo ya ganta ita kadai, don ma ita yarinyar ba mai dabara ba ce gudunshi take yi.”

Baba ya ce, ‘Gara ta yi ta gudunshi, tausayinta nake ji shi ya sa nake ganin inda mun dace mun raye to zan barta ta yi sha uku tukunna ta dan yi kwari ta kuma yi wayo.”

To shekara guda bayan wannan lokacin Baba da kanshi ya bai wa Alhaji umarnin gina mini inda zan zauna, saboda ya fito da maitarshi fili a kaina, ko da dai ba magana ya yi ba.

Ina jin baban yana gayawa Baba Rabi, “Ja’irin yaro yau dai na yi maganinshi na gaya mishi ya gina mata inda za ta zauna ban kuma yarda ya bai wa wani aikin ba, ya yi da kan shi. Bayan haka kuma babban daki nake so ya yi mata, inda za ta sake ita da ya’yanta”

Baba Rabi ta ce, To me ya sa ka yi mishi irin wannan tsananin Malam?”

“Don ya kai badi bai gama ba, kin ga kuma nan da watánni kadan ruwa zai sauka da alama ba zai je ko’ina ba uwa zai sauka kan ya gama ta kara kwari.”

<< Wace Ce Ni? 19Wace Ce Ni 21? >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×