Skip to content
Part 22 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Sati biyu bayan wannan lokacin ya dawo gida ya zo ya same ni na yi kuka har idanuwana sun kumbura ko abincin dare rannan ban fito na dora ba.

“Lafiya dai na same ki a haka?”

Ina kuka na ce mishi, “Wani abu ne yake yi mini motsi a ciki.”

“A ciki?” Da sauri ya yi tambayar na ce mishi, Eh.” Ya nemi wuri ya zauna ya dora hannu a cikin nawa yana kokarin jin motsin da na gaya mishin, sai kuwa ya ji. Ya kalleni cikin nutsuwa ya ce,

“Anya kuwa ba ciki ne da ke ba kuwa Zuwaira? Kin ga fa tun da kika yi al’adar nan sau daya ba ki sake ba.

Sannan gashi yanzu cikinki yana motsi ina ji mutum ne don in ciwo ne ai ba zai yiwu ki yi kiba haka ba.”

Na zuba masa ido ina kallon shi, ya ce, “Ko kuma bari in je in gayawa Baba in ji abin da za ta ce.”

Na yi maza na ce mishi, “A’a kar ka gaya mata bari in je in dora girkina, murhu biyu zan yi yanzu zan gama.” Ya ce mini, To yi sauri don akwai wani labarin da nake son baki, amma sai kin yi wanka kin shafa jan bakinki tukunna.”

Kwana uku ne kawai bayan nan na gane ashe dama su Baba da Baba Rabi sun san ciki ne da ni, shiru dai kawai suka yi suna kallona. Wanki na zo karba wurin Baba Rabi, kamar yanda na saba yi in zan yi nawa in hada da nata. Sai ta ce mini wai a’a ita ta yafe wankin nan, yanzu in ji da kaina kawai za ta rinka yin kayanta, in ya so in Allah ya sauke ni lafiya na gama jego na yi mata.

Daga ni har Alhaji kunya ce ta kama mu shi kam mikewa ya yi ya bar dakin, ya bar ni ina mutsu-mutsu. Baba kuwa ya yi ta yi mata fada, yana fadin.

Wannan wane irin girma ne, ba dama ki ce mata kin hutar da ita wankin kawai sai kin tsaya yi musu bayanin dalilinki.”

Ban san lissafin ciki ba, gani dai kawai na yi baba ya tara lodin itace a bayan kicin, har sai da ya kere tsawon kicin din.

Rannan ina hira ni da Baba da Baba Rabi, Alhaji ya shigo ya tsugunna ya gaishe su. Dabarar da ya gano kenan wai in ganshi zai wuce daki, baba ya kalleshi ya ce mishi, “In watan nan ya kare Zuwaira za ta dawo dakin uwarta don kar haihųwa ta zo mata cikin dare ba ta sani ba.”

Alhaji ya sunkuyar da kai kasa ya yi shiru ya ki amsawa. Ya sake tambayar shi, “To ko za a bar maka ita ne tukunna?”

A nutse ya amsa mishi, ‘Eh.”

Baba ya ce, “To me za ta yi maka?”

Baba Rabi tana dariya ta ce, “Ka ji mini malam shi da matarshi ka tambayeshi me za ta yi mishi?”

Ya ce, To kar in ji na gaya maka kar ka yarda ka matsa mata.

A haka muka yi zamanmu ni da Alhaji, komai a nutse yake aiwatar da shi, nima kuam na riga na fahimci mijina bai samun wata matsala a tare da ni, don haka hankalinshi a kwance yake, gashi bai ganin girman cikin nawa don gaba daya yaki fitowa.

Wannan dalili ya sa ko na nemi bijire mishi, bai daukan atakure nake, sai ya dauki matakin yin rarrashi da bada hakuri.

Rannan cikin dare tun yunkurin da na yi na baro mishi shinniidar shi in dawo tawa in kwanta.

Bayana ya amsa gaba daya wani irin kidimammen ciwo ya kamani hankalin Alhaji ya yi mummunan tashi, don gani yake tamkar shi ya jawo mini ciwon ya yi yunkurin zuwa kiran Baba Rabi, ya kasa saboda tsoron kar su gane an yi wani abu ne ya sa ciwon ya tashi. Nima a tsoracen nake don haka na ce mishi ya barta kawai, na yi ta fama in mirgina nan, in mirigina can. Shi kuwa sai faman kamo ni yake yi yana ta tare da yi mini alkawarin daga yau ba zai sake kula ni ba.

Zuwa can dare ya yi nisa sosai, na rude, na kidime na yi zaton mutuwa zan yi. Na kalleshi cikin rawar jiki da rawar murya na ce mishi, ‘Wani abu zai fasa jikina ya fito.”

Da sauri ya sake ni ya yi waje da gudu kiran Baba Rabi. Ya tafi kafin su dawo har abin da ke son fitowa ya fito. Na yunkuro ina kokawa don in ga ko mene ne saboda ban yi zaton haihuwa na yi ba, sai ga su sun shigo daidai yaron yana atishawa. Nan dan ya kyanyara kuka. Baba tana salati tana fadin, ‘Ai haihu ta yi ga yaro nan, ga yaro. “

Ta sa hannu ta dauke shi. Nan da na aka taso matan gida aka fito da ni daga dakina aka kaini dakin Baba. Bayan an hura wuta a dakin na hau gado na kwanta, gani nake tamkar ba haihuwar na yi ba, sai zazzaro ido na ke yi ina kallon mutane. Ina jin matan yayan Alhaji suna cewa ai da an bar ni a dakina kawai, don su ba su ga amfanin daukonin ba. Wata ma har tana cewa kin ga yaron kuwa kafin a wanke shi ai duk jikinshi kazanta ne, ba su rabu da juna ba har ta haihu. Ni dai na yi lamo na rufe idona kamar ina barci, nan kuwa ba barcin nake yi ba. Cikin zuciyata dai tsoro nake ji kar ita ma Baba Rabi ta gane hakan ta yi muni fada.

Farin ciki wurin Baba bai misaltuwa, sai kaiwa da kawowa yake yi, sau goma ya shigo gidan nan sau goma zai tambaya Zuwaira kalau ko? A ce mishi kalau dinta. Ya ce to shi wannan mutumin su? A ce mishi shi ma kalau din shi. Ni kam ko kałon yaron ban yi ma saboda kunya, sai dai na ji baba Rabi tana yawan cewa wannan da da karanbani yake wai shi kuma da malam yake kama. Wannan al’amari ya yi mata dadi, don duk wanda ya zo barka in ta mika mishi yaron sai ta gaya mishi gashi nan karambana ya tsallake iyayen shi kaf bai dauko su ba sai ya dauko mini mijina gata daya, sai a yi dariya a ce to baba ai shi ne mijin na asali. Ta ce a’a, a’a mijin kazanta dai ko.

Alhaji ya kan yi kokarin shigowa wurina a dakin Baba Rabi da Asuba lokacin da takan zauna gaban wuta wai kar ta rika mutuwa, sai turoni dan ya tafasa tukunna. A duk lokacin ya shigo zubawa yaron indo yake yi yana kallonshi.

“Dan miko mini shi nan.”

In ce mishi, ‘A’a idan Baba Rabi ta shigo ta same ka fa?”

Sai ya dan yi waiwaye ko zai ganta tana zuwa in bai hangota ba sai ya yi maza ya dauke shi ya dan jujjuyashi ya maida shi ya kwantar, sai ya kallen ya ce mini, “A gadona zan rinka kwanciya da shi mu bar ki a na ki gadon, don kar ki zo ki danne shi garin wannan wawan kwanciyar na ki.”

In ce mishi, ‘Ai ma kafin in dawo ya girma Baba Rabi ta karbe shi.”

Ya zaro ido yana kallona.

“Wai nan wankan bangali kike yi ne?”

In ce, ‘Eh mana.

Ya ce, Kai ba yarda zan yi ba, na san abin da Zan yi ai lokacin da zan bukaci dawowarki ya yi.”

Ranar suna Baba ya radawa yaro suna Aliyu, takwaran Babana kenan. Ni kaina cikin zuciyata na yi murna. Tun da aka yi suna kullum aka yi mishi wanka aka sanya mishi kayan shi wurin baba ake kai shi ya yi ta barci, har sai ya farka Sannan a dawo da shi a ce in ba shi nono.

Satinmu uku rannan aka tashi baya kama nono ya sha, cikin shi ya kumbura, har ya haura kan kirjinshi sai nishi yake yi daidai, alamar dai baya cikin hayyacinshi. Hankalin su Baba ya yi matukar tashi su jika wannan su bashi, su jika wancan su ba shi. Ni kam ina kwance har ma barci ya daukeni.

Tashina aka yi daga barci na ji Baba Rabi tana fadin magana cikin kuka.

“Dama zuwa ka yi mu ganka ka koma?”

Na shiga dube-dube don jin maganar tata da kuma hakurin da ako ta ba ta. Lokacin ne na hango yaron shimfide a tsakar daki a Rasa an nade shi cikin zaninta, baba ya zo ya tsaya a bakin kofa ya ce mata, “Miko mini shi nan.”

Ta mika mishi shi suka tafi, ita kuma ta kara tsananta kukan da take yi Shi kan shi Alhaji kasa hadiye damuwar shi ya yi kan rasuwar yaron, har na ji Baba yana ce mishi, “Sai ka yi hakuri wannan sai an je can za’a more shi, haihuwa kuma ai soma ta kuka yi.”

Ni kam na hadiye babu wanda ya gane damuwata, sai dai kuma na shiga wahala ga ciwon nono, gashi a yanzu ruwan zafin da ake kwara mini safe da yamma kona ni yake yi, ba na son wankan ba abin da nake so irin a ce an gama wankan nan, gashi kuma sai na jiwo magana cewar wai ai arba’in biyu zan yi, hankalina ya yi mummunan tashi da jin hakan.

Rannan Alhaji ya dawo daga kasuwa da yamma ya shigo wurina ya zuba mii ido yana kallona cikin tausayi.

“Daga gobe dai za ki huta da wahalar wankan nan tun da gobe ne arba’in din.”

Na kalle shi cikin nutsuwa na ce mishi, “Ai arba’in biyu, aka ce zan yi.” Ya sake kallona ya ce,

Har da babu yaron ma Zuwaira ba za a tausaya miki ba? Kin fa rame.” Ban tanka mishi ba ya juya ya fita.

Ban san me ya faru ba, ko kuma me ya yi? Illa dai kawai na ji baba yana cewa Baba Rabi, “Ke Rabi. Ki baiwa yaron nan matarshi ki bar wankan nan haka, watakila wani rabon ne mai tsanani ya kori wancan kin ga ya gama zagaye-zagayen shi ban kulashi ba, to jiya ya fito fili ya yi mini magana ya ce a yi hakuri a bar wankan haka.”

Baba Rabi ta ce, “To ai ba ta gasu ba.”

Ya ce, “Eh maida mishi da ita in ta sake wata haihuwar kya hada gaba daya ki. gasata da kyau, anma yanzu yana ganin babu dan ai ba zai iya hakuri ba.”

Kememe baba Rabi ta yi ta ce ba za ta maida ni ban gama wanka ba, ai in na zo wata haihuwar sai in rinka kumburi, jikina ya danyace. Ya ce, “To babu laifi Rabi rike ta ku zauna.”

Alhaji ya maida dakin Baba Rabi ya zama nan ne wurin zaman shi yana fitowa daga sallar Asuba na zai zo ya zauna in an ce in fito a yi mini wanka ya ringa tsaki kénan yana cewa, “Ke ba za ki rinka yi mata kuka a wurin wankan nan ba, don ta san wahala kike sha?” In yi kamar ban ji shi ba. Da daddare ma in ya fito daga wurin yawonshi nan zai zo ya zauna suna hira shi da ita, tun tana amsa hirar har ta koma gyangyadi sai jifa-jifa ne za ta rinka amsa abin da yake gaya mata, ni kuwa in yi ta barcina.

Rannan ina jin baba yana cewa mata, Ai maganinki kenan duk inda kika dan zauna ki kama gyangyadi, saboda ba kya samun barci ga tashin Asuba, wannan dogon hirar da Bello yake yi miki ai ke ma ma kin san abin da take nufi da matarshi take dakinshi kina ganin shi ne a dakinki da daddare?”.

A hakan sai da ta yi mini wankan wata biyu safe da yamma. Sannan ta sa aka gyara mini dakina fes aka wanke mini kwanukana da tasoshina aka sake jere daki ya yi ras. Da Alhaji ya shigo mata hira da daddare ranar ta ce mishi “Ba ni wuri barci zan yi gobe war haka in ka dawo za ka samu matarka a dakinka.”

To haka aka yi na dawo dakina ina tare da mijina muna zaune lafiya, babu wanda ya taba jin tsakanin mu akan wani sabani. Yana matukar sona,

Yana matukar kyautata mini kowane lokaci idon shi a kaina yake, ga iyayenmu da ke matukar sona suke kaf-kaf da al’amurana. Sai dai shiru babu ciki, babu alamar shi. A wannan lokakcin ko atishawa mai karfi na yi sai Baba Rabi ta ce ai ina jin juna biyu ne da ita, saboda tsananin matsuwarta da son ta ganni da ciki.

Nan da nan sai ga ta ta shiga yi mini jike-iiken sauwowi, wai maganin haihuwa. Shi kuwa Baba sai ya ce mata, “Da kin yi hakuri ita haihuwar nan inta tashi zuwa ai za ta zo da can saiwa aka ba ta?

Alhaji da kan shi ya soma matsuwa da son ganin na haihu, dan kankani abu ne zai faru sai ka ji yana cewa da yanzu yana nan da an yaye shi, ga shi har yanzu shiru me ya faru ne? In yi shiru kawai in sunkuyar da kaina ina sauraron shi, sai kuam ya ce, ina ganin har da raba shimiida da kike sawa muna yi daga yanzu ba zan sake yarda ba.”

Yayin da Alhaj! yake wadannan maganganun a daki su kuma matan tsakar gida cewa suke yi ai ita mace in ta cika mannewa miji ma haihuwa gagararta take yi. Da na gaji da irin fitinarshi sai na ce mishi da ka dan rinka barina ina hutwa, saboda ga abin da su yaya suke lada. Ya ce, ‘Rabu da su ba su san komai ba, kar ki rinka zama a wurin hirarsu.” In ce mishi to.

A wannan lokacin ne Alhaji ya zama saurayi sosai,  ya kuma hada karfinshi wuri daya ya murje ya yi kumari, kwarjininshi ya soma bayyana sosai, kyansa ya kara fitowa, gashi ya Soma samun barka sosai, kasuwa ta bude mishi ta ko’ina, duk abin da ya taba sai ka ga alheri ne ke ta faman shigowa fiyc da yanda aka yi zato. Ni kaina yanzu ne ya dacc a ce na zama budurwa shekaruna goma sha bakwai ne, na yi kyau har ba a magana, na riga na san dadin mijina yanzu ne na kara fahimtar auren sosai, in muka shiga daki ni da Alhaji mu kadai mu ka san abin da ke faruwa, shi kuwa Alhaji dama zani ce ta tadda mujemu don haka da rana ma barin kasuwa yake yi ya taho gida duk lokacin da zai shigo kuwa ba zai shigo haka ba, sai ya riko wani abu ya ce “Raba ki kaiwa su Baba da mutanen gida ke ma ki dauki naki.”

A wannan lokacin dakin Baba da Baba Rabi bai rabuwa da naman kaji soyayyu a ajiye hakan ai hanawa kullum ya zo da wadanda za a yi musu farfesu, ga zuma a ajiye, ga yaji da manshanu. Kullum Baba Rabi ta gama cin abincinta in tana lashe yatsa za ta ce, “Ubangiji ka yalwatawa Bello arzikinshi don ya ciyar da jama’a.”

<< Wace Ce Ni 21?Wace Ce Ni? 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.