Skip to content
Part 23 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Muna cikin wannan hali ne kawai Baba Rabi ta kamu da zazzabi ko a jikina ban damu ba, don ta saba yin rashin lafiya irin wannan tana warkewa, don haka na dauki matakin kulawa da ita kawai, kamar yanda na saba. Na kai mata ruwan wankanta na riketa na ka ta ta yi na rikota na dawo da ita dakinta. Bayan ta yiwo alwala muka dawo daki ta kwanta, na gyara mata ruhuwa na je na kawo mata gaurwáshin wuta na zauna ina dama mata furarta ina shirin ba ta sai na ji ta kama shakuwa mai karfi, da sauri na dago ta ganin halin da take ciki ya sa na yi maza na maida ita na je kira Baba muka shigo tare na sake dagota na rumgumeta ya zuba mata ido yana kallonta hawaye suka zubo sharrr! Daga idanuwanshi. A hankali ya ce, “Ashe haka za mu yi da ke ke ma Rabi? To Ubangiji ya baki sa’ar tafiya, sai na zo.”

Yana fadin haka ya soma shafa mata ruwa, yana salati yana nanatawa, har ita ma ta kama yi.

Zuwa can sai ta yi shiru.

Baba ya yi ajiyar zuciya mai karfi, ya yi kalmomin godiya ga Ubangiji da nemar mata rahama ya kalleni ya ce mini, “Shi kenan Zuwaira Rabi ma tabi bayan yan’uwanta su duka ukun sun tafi sun bar ni. “

Rasuwar Baba Rabi a gidan nan ba karamin al’amari ba ne a gidan nan. A wurina dai rasuwarta ita ce ta sankar da ni yanda dacin mutuwar mahaifiya take. Ko kwana arba’in da matuwarta ba a yi ba aka ware ni a gidan, ba ma shiga harkata, babu mai magana da ni. Maganganu iri-iris suke yi ta fitowa ciki har da haihuwar da na yi ni kadai a daki ban kira su ba. A ka’ida kuma wai uwar gidan yaya babba ake kira in ana nakuda sai kuma ta kira sauran matan da ta zaba su zo su kewaye mai nakudar, ita Baba Rabi a kan je ne kawai a gaya mata an yi haihuwar amma ni da mijina ba mu yi haka ba. Wasu suka ce to in dai ma namiji ne ai alkawarinshi ragagge ne muna nan da ku zai yi mata kishiya sai kuam mu ga tsiya, tun da tana zauni ita kadai ba ta kama mu ba, ai kishiya ba za ta zo ta ce mana ta san da mu mu yarda ba.

A wannan lokacin ne na gane Baba Rabi ta tare mini abubuwa da yawa a gidan nan.

Ni kam ina jin su ba na kuam ta tasu, na maida hankalina wurin baba, wanda ya rasa lafiya tun bayan mutuwar matarshi kowanne lokaci ina tare da shi, ina yi mishi hidimominshi ko in taya shi hira ko shi Alhaji a wannan lokacin nan wurin nashi yake hira.

Koda Baba ya watstsake nan wurin shi muka mayar da hira da safe da daddare, nima na maida kicin din baba Rabi wurin aikina, saboda yafi kusa da wurinshi ina aikina muna hirarmu, don fito mishi da shimfida nake yi a inuwar bishiyar da ke nan sashin, sai na zama in ba Alhaji ne ya dawo ba ba na zuwa sashin da nake, saboda ba na wani jituwa da wadanda muke taren. Kullum dai baba ya kan gaya mini,

“Kar ki yarda ki tanka musu duk abin da za su yi miki nan in da kike ganinsu babu wacce ba ta haifeki ba, in ban da Bilki.” In ce mishi to Baba.

Ana cikin haka ne aka wayi gari daurin aure da safe a gida, ashe wai kanin Baba mai binshi ne ya bai wa Alhaji auren yarshi bisa hujjar wai ni din ba mai haihuwa ba ce. Ran Baba ya yi matukar baci da jan maganar tasu ya ce da ba shi auren kawai aka yi aka yi shiru da ban ji takaici ba, amma a ce Zuwaira ba ta haihuwa? Ai ta haifu ba a bar mata ba ne. Yana maganar cikin hawaye ya kalleni ya ce mini,

“Kar in ji kar in ganni, kar ki yarda in ji kin yi wa miinki wata magana, wannan auren da kike gani an dade ana son bashi Rabi ta yi uwa ta yi makarbiya ta ki yarda, don haka ki yi hakuri ki daure ki bai wa mara da kunya.” Na ce mishi to Baba.

Umarnin da Baba ya bani na in zuba ido shi na bi na yi matukar kokarina wajen cire auren daga raina, duk da tsananin kishin da ke damuna babu halin in ga ya shiga dakinta sai in rinka ganin tamkar shi kenan abin da yake yi mini ita ma shi yake yi mata, bisa wannan dalili sai zafin kishi ya ringaye ni, na shiga yi mishi rowar kaina, na bijirewa duk wani rarrashi nashi, gashi kuma dama mutancn gida gabadaya suna tarc da amarya ne, ita yar dangi ce ko ba haka ba ma dama sun riga sun kosa su ga an yi mini ita. Sai na zama ba ni da wani abokin mu’amalla mai dadi sai Baba. Bisa wannan al’amari sai Karama ta yi amfani da abin da ta gani na juyawar Alhaji wurinta de goyon bayanta da takc da shi wurin dangi duk ta ki yarda ta marawa kokarina na ganin mu zauna lafiya.

Ana cikin haka sai aka ce wai tana da ciki, gabadaya gida ya dauka matar Bello juna biyu ne da ita, ko bako ne ya zo sai an gaya mishi, in aka gani a wurin ma an fi tsananta bayanin.

Rannan ina zaunc gaban Baba kuka nake yi, Kuka kuwa ba na wasa ba, saboda na fara gajiya da ganin abin da nake gani. Rarrarshina yake yi yana ba ni hakuri. Da ya ga na yi shiru sai ya kalleni ya ce mini, “Ashe ba ki da hakuri ban sani ba? Ai ita rayuwa babu abin da ya dace da ita irin hakuri. Ashe ba za ki iya zuba ido ki kalli Bello da mutanen nan ba ko da na shekara daya ne? To me zai yi wa wata mace a duniya wanda bai yi miki shi ba?”

Kullum Baba ke rarrashina, hirarmu ta koma hirar bada hakuri. Gaba daya na zube na rasa girmana da hasken fatata, saboda tsananin bacin rai, abu daya dai dana rike shi ne ban yarda na daina kwalliya ba, kullum a cikinta nake.

Rannan bayan fitar Alhaji daga dakina, sai na dauki buta na shiga wanka, saboda al’ada na gama, ga zaton Karama wani abu muka, ba ta sani ba ni tun zuwanta babu wani abu tsakanina da shi, da yake ta zo gidan da girmanta, don ta kai shekaru sha biyar. Ashe dama ita ake ta son bashi, Baba Rabi ta hana su, kuma suka ki aurar da ita, shi nema dalilin da ya sa ta yi ta shige mini tana maida dakina wurin hirarta, don ta rinka sa ido kan mu’amallata da mijina. Na fito daga bandaki sai na same ta tsaye kan hanya na yi kokarin kauce mata wurin wucewa, amma ina shige ta sai na ji  tasa hannu ta jawo mini zanin da na ruhu da shi.

“Ke ba kya ganin mutane ne kike ture su, saboda rashin hankali?” Tuni na riga na zo wuya da ita, saboda irin cin kashin da take kawo mini, don haka ina juyowa na dauke ta da mari. Ta yi maza ta cakume ni da dambe, don dama abin da take so mu yi kenan, a ganinta tana da abin da za ta dauka a jikina, saboda ganin ta fini girma, ga ta kuam da masu mara mata baya sai sai dai sabanin hakan ne ya faru, don duka sosai na yi mata, kafin a kai ga raba mu ba a dauki lokaci mai tsawo bayan yin damben namu matan gida suka cika a dakinta aka ce wai ta yi bari a dalilin dukan da na yi mata, sai cewa suke yi, A’a dama da gangan ta yi ai dama ba ta yi karin komai ba illa cikin dama so take ta yi sanadin shi, ita ba ta haifa ba, kuma ba za ta bar mai haihuwa ta haifa ba.”

Aka yi ta wanko jini daga dakin Karama wai duk jinin barin nc. Haka Alhaji ya dawo saboda kiran da aka yi mishi, aka yi mishi bayanin abin da ya faru.

Ban taba yin nadama ba irin na ranar na yi ta dana sanin kulata da na yi, ban san za ta yi bari ba da ban kulata ba, dana yi tafiyata kawai na bar mata zanin nawa da ta rike.

Ina zaunc gaban Baba ina ta kuka, shi kuwa sai caccaka tokar kaskon shi yake yi da wani tsinke yana wasa da shi, bai kalleni ba. Zuwa can sai ya kallcni ya ce mini, “Kin dai san ya zame miki dole ki koyi zama da mutanen .nan tun da dai kin san zan barki a cikinsu.”

Rannan ko barci ban yi ba, saboda tunanin al’amurana. Baba Rabi ce ta rasu na shiga cikin wannan halin, to ran da aka ce babu baba fa? Wannan shi ne abin da ya zo cikin raina tausayin kaina ya kamani ba ni da kowa sai Baba in na rasa shi ina zan tsoma raina?

A wannan lokacin na shiga kunci mai tsanani gaba daya dangin Alhaji sun ce sarnun wurina ya yi yawa, ni ce bakuwa macce ma ba a san dangina ba, amma har na samu kwarin gwiwar dukan ‘yarsu, in hukunci da aka yi mini bayana. Bayan a wannan lokacin Alhaji fushi yake yi da ni,, baya ko kallon inda nake bai kuma cin abincina. Karama ta sake sani a gaba fiye da kowanne lokaci na yi ta kakkauce mata musamman da yake an sake cewa tana da ciki, shi kuwa Alhaji sai faman kai kawo yake yi, ga matarshi tana da ciki za ta haifar mishi dan dana kasa haifar mishi.

Sai da na kai ma ko girki na dora a kicin sai Karama ta kwarawa muruhun ruwa, saboda neman magana sai dai in je sashin baba in yi girki, don ina tsoron kar in bar girkin a ce na bar mutanen gida da yunwa.

Ina zaune a dakina cikin dare sai ga Alhaji ya shigo a fusace yana yi mini kashedi, ba zai lamunci abin da nake yi ba, dan an gaya mishi cewa ina neman in sake yin dambe da Karama, don na gane ciki nc da ita, wai har, yana cewa shi ya so bai so a fadi tana da cikin ba, don kar in sani. Na ce mishi haka ne. Ban sake wata magana ba na ja bakina na yi shiru, ina kallonshi yana ta maganganunshi bar ya yi ya gaji ya gama ya kwanta ya yi barcinshi. Gari na wayewa na je na gama yi wa Baba aikinshi na shirya mishi abin karyawa na. kai mishi. Ina zaune a gcfc ina kallonshi har ya garna karyawarshi sai na kalleshi cikin cikin ladabi na ce mishi,

‘Baba.”

Ya ce, ‘Mene ne Zuwaira?”

Na ce mishi, ‘Lokacin da Babana ya ce mini zai kawo ni wurinka ya gaya mini cewar ka san komai gamc da shi, in na bukaci sanin inda dangina suke za ka gaya mini?”

Ya daga ido ya kalleni cikin nutsuwa ya ce mini, “Kina bukatar su ne a yanzu?”

Na yi maza na ce mishi, ‘Eh Baba.” Hawaye suka zubo mishi sharrr! Daga idanunshi ya ce, Ba ki bukaci saninsu a lokacin da zan iya kai ki ba, kin bukaci sanin su ne a lokacin da karfina ya kare, gabadaya bazan iya kai ki wurinsu ba, ba kuma ba zan wakilta wani don ya yi mini wannan aikin ba, amma ko ni na dade da gane kina bukatarsu don inda a cikinsu kike to da wadannan abubuwan ba su same ki ba, don kuwa dangine da ke masu yawan gaske.”

Fadin da Baba ya yi cewar dangi ne da ni masu yawa, amma gani nan ni kadai ban san kowa ba, kuma ba a tausayina kan hakar kullum sai an yi mini gorin dangi, ya sa na yi ta yi masa kuka. Cikin sanyin jiki ya ce mini,

“Hakuri za ki yi Zuwaira ni din nan da kike ganina ni danginki ne nine kuma uwarki, nine ubanki. Zan kuma tsaya miki matsayin hakan a kowanne lokaci matsalar kawai ita ce zan iya barinki a kowanne lokaci.” Yana fadin haka ya mike tsaye ya fita yana doddogara sandarshi, saboda rashin karfi ya je ya tura Kofar Baba Rabi ya bude ya shigo yana gyara dakin.

Na bi bayanshi na karbi tsintsiyar na ce mishi, “Bari in gyara maka Baba.”

Bai bari ba, tare muka yi aikin. Sai da muka gama ya ce mini,.’Dawo nan ki zauna kafin in ga abin da zan iya yi miki in Allah ya yarda ba zan tafi in barki cikin wannan halin ba, zan san abin da zan yi a kai.”

Na dawo dakin Baba Rabi na zauna kusa da Baba, ya kafa mini dokar kar ya sake ganina a wancan sashin kar in sake tambayar Alhaji komai, komai nake so in gaya mishi ko gaishe shi bai yarda in rinka yi ba, babu ruwana da shi. Na ce mishi to Baba. Girki ma namu mu biyu nake yi, in kuma aka kawo mishi na sashin Alhaji sai ya ce a bai wa almajirai shi ya riga ya koshi, in shiga wurinshi in yi hira in na ji barci in shiga dakin Baba Rabi in kwanta. A wannan lokacin babu abin da nake yi irin tunaninta.

Alhaji ya dawo daga tafiyar da ya yi ta kwana  biyu ya same ni anan ya shiga wurin Baba ya tambaye shi wai ko ya yi wani laifi ne ya sa ya ce mini in dawo nan? Ya ce mishi, “Ba ka yi komai ba na nishadi ne kawai na karbeta tun da dama sanda na ba ka ita ai ba kai ka ce kana sonta ba, hasalima ko ganintä ba ka taba yi ba na daura maka aure da ita, don haka in na karbeta ai ban yi laifi mai yawa ba ko?

An yi wata biyu Alhaji yana ncman sañin laifinshi, Baba yana cewa bai yi komai ba. Rannan ya ganshi ya zo zai shiga dakin da nake wai zai yi magana da ni don ya ga na ki kula shi. Baba ya yi maza ya dakatar da shi ya ce mishi, ‘Kai Bello na haramta maka shiga dakin nan in kuwa ka yarda na ganka a ciki to ranka zai baci:”

Zamana a wurin Baba sai na samu nutsuwa hankalina ya kwanta, na yi kiba, na yi kyau, na maida jikina. Kullum sai ya yi aike kasuwa an sayo mana nama na gasa mana in ya ga manshanu ko wani abu zai kare ya yi maza ya bada kudi a sayo mana. Komai Alhaji ya kawo mana sai ya ce, ‘A’a kaiwa iyalinka kawai, ita wannan na sauke maka nauyinta ni kuma na yafe maka ba sai ka yi ta wahala da ni ba.”

Hankalin Alhaji ya yi mummunan tashi, ganin irin matakin da Baba ya dauka a kan shi. Kowanne lokaci zai sa shi a gaba yana bashi hakuri, tare da tambayarshi.

<< Wace Ce Ni? 22Wace Ce Ni? 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×