Skip to content
Part 24 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Ya sake nuna wata saniya da danta tare da wani bijimi ya ce, “Hakan nan wadancan shanun nata ne, sanda mahaifinta ya kawo mini ita ya bani dukiyarta ya ce in rike in loakcin hidimar aurenta ya zo a yi mata da su, don haka babu komai nawa cikin kudin kayan dakinta da kudinta na yi mata hidima, ni dai na dauki nauyin ciyar da jama’a ne kawai a lokacin tun a sannan kuwa na gaywa wasu daga cikin ku hakan. Bayan an gama bikin ne na gayawa Rabi cewar ga sauran kudinta da sukai saura sai dai babu yawa, ta ce mini a sayo mata tunkiya a daure mata. To da ta yadune aka sayar da su aka sai mata karsana a kan idonku ne kuma ta haifi wannan ta yaye shi, ta kara wannan.

Na roke ku kar ku zalunccta a bayana, ita ma yar uwarku ce don ba ta da kowa sai ku.”

Daga Karama har masu tsaya mata babu wanda ya furta wani abu kan wannan kyauta da Baba ya yi mini, don sun riga sun ga abin da ya firgita su. In da da ne kuwa kafin auren Alhaji Baba ya yi mini wannan kyautar da sun ce ya yi bambanci tsakanin matan danshi a wannan lokacin kokarinsu bai wuce Karama ta dawo kafin tarewar amarya ba, wacce aka dibar mata kwana bakwai kacal. Shi kuma Alhaji ya ce ta yi zamanta tukunna sai amarya ta zo ya ga kamun ludayin zamana da ita tukunna, don yana son gane waye mai fitina a tsakanina zaman. Baba ne ya ce a’a kar ya yi haka ya barta ta dawo dakinta shi dai kawai ya zama tsayayye kan lamarin gidanshi. Ya ce  mishi to.

Karama ta dawo da kwana biyu. Ita ma amarya ta iso ta kuwa iso cikin matsananciyar gata, ita ma dai kam mai dangin ce. Da yamma kafin zuwan nata Baba ya kirani ya ce mini, “Wani alheri nake so ki yi mini.”

Na ce mishi, To baba.” Ya kalleni cikin nutsuwa ya ce mini, “Hakuri za ki yi ki dauki nauyin da yake kan ki duk da ke din kin yi wa hakan kuruciya, ita wannan amaryar liman ya rokeni ta tare da danta mai shan nono wai watanninshi goma ne kawai bai son a raba ta da shi, ni kuma sai na ji ban son ya sha nonon nata tana gidan nan, don kar a haramta mishi auren ya’yanku, don ba a san abin da gobec za ta haifar ba.”

Na ce mishi, “To Baba in ta zo din sai ka karbi yaron ka ba ni shi zan yaye mata shi.”

Baba ya yi ta murna yana sanya mini albarka.

Ummana ta sake shafa hannuna ta kar jaddda laushin jikina kafin ta ce mini, “To kin ji yanda aka yi na mallaki dukiya cikin gadon su Alhaji, Baba ne ya yi mini kyauta.”

Na yi ajiyar zuciya mai karfi kafin na ce mata.

“Umma.”

Ta ce, “Mene ne Adawiyyah?”

Na ce, “Lallai Baba gadon alheri ya yi wurin mahaifinshi, tun da ni kar han taba jin labarin mutumin kirki irin shi ba.”

Umma ta ce, “Uhum! Me kika sani game da Baba tun da ba zama da shi kika yi ba?” Na sake ce mata, “Umma.” Ta ce mini, “Ina jinki Adawiyyah ke nake sauraro”

Na ce, to shi wannan Amarya ta zo da shi shi ne ya zo ya zama yaya Almu ko kuwa da ta zo nan gidan ma ta haifi.wani?

Umma ta ce, “Wannan ne kuma ba zan iya amsa miki yanzu ba, don in na biye miki sai in kwana idona biyu.”

Na sake matsawa jikinta na kwantar da kaina a gadon bayanta sosai na cc mata, “Lallai kin yi gwagwarmaya da Umma Karama, Umma.”

Ta ce, “Ba kadan ba ai shi ya sa duk abin da take yi yanzu kallonta kawai nake yi na san ba zai yiwu ta maimaita abin da ta yi a baya ba.”

Na ce, “Haka ne gashi Kuma kin yi sa’a Baba yana matukar Sonki shi ya sa ma da kika tayata yi mishi laifi ya yi fushi da ke matsanancin fushi fiye da wanda ya yi da ita.” Umma ta yi dariya ta ce, “Mu yi barci Adawiyya.” Na ce to Umma, amma dai gayamini yaushe ne kika haife ni? Ta ce, ‘Ba yau ba.” Na ce to gaya mini abu daya kin sake haihuwa bayan wancan haihuwar da kika yi? Ta yi maza ta ce na sake mana. Na ce to me kika haifa? Ta cc Rabi’atu. Na yi murmushi na kara nutsuwa cikin raina dadi ya kamani. Nan da nan barci mai dadi ya dauke ni.

Washegari kuwa farkawa na yi na ga haske vana kashe mini ido na tabbatar ba lokacin gari ya waye ba, na yi maza na dauki agogona na duba karfe goma ne na safe. Da iya kacin karfina na shiga kwalawa Umma kira, amma ba ta amsa ba, sai Baba Talatu ce ta shigo tana murmushi.

“Kin farka ne uwar dakina? Za a shirya miki ruwan Wanka ne?

Na ce mata, ‘Eh.”

Na yi maza na yi waje, don ganin me Umma take yi. Tana zaune a falonta tare da su Anti Aina’u, lissatin kudi suke mata, ita kuma tanan tare da Jakarta alamar tana shirin ba su. Na juya żan koma in da na fito ta kalieni ta ce mini, “Kin gaishe su ne?”

Na ce, “Bari in wanke bakina tukunna.”

Na shiga wankana ban sake fitowa ba sai da na tabbatar sun fita. Sannan na fito cikin kwalliya mai matukar kyau na zo na zauna kusa da ita na fara gaishe ta. Ta kalleni a lalacc ta ce, ‘Ai ba zan yi wata magana da ke ba yau, sai bayan kin je kin gaida su Aina’u, kin dawo.”

Sai kuwa kawai ta ja tsaki alamar dai ta ji takaicin kin gaishe su da na yi. Na fita waje don in je in gaida su Aina’u, dama duk wani wanda yake cikin gidan na san in ba hakan na yi ba ba shiryawa za mu yi da Umma ba. Ina fita na ga wani abin da ban san da shi ba. Mutane suke ta shiga motoci ana ta fita da su, ga alama kuma tafiyar ba ta kusa. ba ce, don sai jefa jakunkunan ya’yansu suke yi a bayan motocin.

Sannan gabadayansu Jama’ar da na sani ne wato yan’uwa ko kuma abokan arziki na kusa.

Ina cikin kallon na su sai na ga Anti Rahma ta fito da saurinta ta sha kwalliya tana rungume da Jakarta, sai wani irin kamshi take yi. Na kalleta cikin nutsuwa na ce, ‘Anti wadannan fa ina za su?” Ta ce za Su jere. Na ce tun yau? Ta ce eh to a wurinki kam tun yau mana, amma ni kam da na san har Lagos za a tafi nawa jeren ai na san ba a yi sauri ba. Na sake kallonta na ce Lagos kuma za a kai ki? An yi wa Yaya Junaidu transfer ne? Ta saki wani lallausan murmushi ta ce ‘Lah ashe baki da labarin ajiye aikin Junaidu ai shi Baba ya zaba ya zama shugaban kamfanoninshi. Ai can Lagos za mu zauna a wannan sabon gidan na Baba da ke unguwar My one.’

Na ce, “Anti Rahma wane irin so Baba yaké yiwa yaya Junaidu haka?” Ta kalleni ta kyalkyale da dariya ta ce, ‘Ai fa kamn ni kin ga tafiyata.” Ta wuce ta barni a tsayc ina bin ta da kallo a zuciyata kuwa cewa na yi, kai to ko dai ma yaya Junaidun ne dan Baba na cikinshi, shugabancin kamfanoninshi da ya bashi ai yana nufin ya dauki duk dukiyarshi a hannun shi ne gashi kuma dama ance aure bai halarta ba tsakanina da shi, kuma shi yaya Almu ya tabbata kenan shi ne wannan da da Umma Amarya ta zo da shi.

Na wuce na gama gaida mutanen gida. Ina fitowa yaya Almu na fara gani ya yi adon karanan kaya, ya yi kyau har bai yiwuwa in yi ta,kwatantashi.

Yana ganina ya yafuto ni na isa gare shi ya kalleni cikin nutsuwa ya ce, “Ke kam kin yi sa’a, kunya ta anini baki da ita, gaba daya ‘yanmata sun yi sammako sun bar gida, ke kuwa kina nan kina yawo cikin mutanen da suka zo bikinki”

Na ce, ‘Aa ni kadai ce a gida da za a yi bikina kai fa?” Ya yi murmushi ya ce, ‘Ai ni ma yanzu zan bar gidan in je yawon bankwana da samartaka in za ki zo mu tafi.

Na ce, Aa ba inda za ni zan zauna wurin Umma mu yi hirarmu mai dadi.

To shi kenan.”

Ya yi maza ya juya ya bar wurin, in duba abinda ya kore shi cikin sauri haka sai kawai na hango jerin motoci suna shigowa gidanmu Kawayen Umma ne ina jin sun shirya isowa tare ne don Kila sune masu tafiya jere na. Na yi maza na bi bayan yaya Almu na je na bude motar da na ganshi a ciki Ya yi maza ya juya kan motar, don barin gidan. Sai ga Hajiya Hauwa tana shigowa wai maimakon ta yi maza ta wuce tunda yaya Almu ya kauce mata, sai kawai na ga ta ja ta tsaya tana tambayarshi.

“Kai Lamido ina za ka kai yarinyar nan? Da ita fa yau za ni gida, don ban riga na gama shirya maka ita ba.”

Yaya Almu ya yi magana a hankali, “Bari in fita in gaida Hajiya, don ga dukkan alamu ita ce Surukar tawa.”

Ya fito ya je ya gaisheta cikin girmamawa.

Sannan na ji shi yana ce mata, ‘A’a dauko Baba kawai za mu.” Ta yi dariya ta ce, ‘Alhaji Bello zai hada iyayenshi aure ai dole zama ya gagareshi, yana Zumudin kwanannan zai fara ganin kanne.” Ta yi wucewarta, muma muka sa kai muka fita muka hau hanya. Yaya Almu yana cewa,

“Kina jin abin da ta ce?”

Ban amsa ba ya yi ajiyar zuciya ya ce, Kowa sha’awar da yake yi mini kenan nima kuma ina yi wa kaina wannan sha’awar ‘ya’ya nake so Rabi ke fa?”

Na ce, ‘Uhum ni bas u damen ba”

Nan da nan ya fusata yana fadin, “Ai ke ba ki da hankali ke kam sai dai a yi ta yi miki addu’a, mutum mai hankali ya ce wai haihuwa ba ta dame shi ba? Ko da yake ma ai ba ki da wani abin mamaki tunda kin yi mini abin da yafi wannan a gabana ina kallonki kina kallona kika ce za ki bukaci Baba ya canza miki ni da Junaidu.”

Ya ja wani mummmunan tsakin da ya firgita ni, don kuwa na yi zaton kifa mini mari zai yi bayan ya gama tsakin.

Mun dauko su Baba muna dawowa shi da Urmma Amarya suna bayan mota ni da yaya Almu a gaba, na ce, ‘Ai kuwa Baba babu wanda zai yi zaton zuwan ka a yau.” Ya ce, eh uwata zumundin aurenki ne ya dawo da ni gida, iyayena za su sake haduwa wuri daya zan sake zama dan gata daga ranar da zan ga aura aurenku ni din kuma ba maraya ba ne, ga ku wuri daya kun hadu sai kawai in yi ta fata da kuma sauraron isowar kannena, dan haka kuna hade wuri daya zan gaya muku ban yarda da tsarin iyali ba.”

Kalaman Baba suka san ya ni jin kunya, nan take kuma suka sanyaya mini jiki, wato ba yaya Alimu kadai ne yake bukatar ganinan ina ta haihuwa ba, har  da Baba, tuni na san ra’ayin Umma ne wannan.

Muna kawo su Baba muka bar gidan, don ya riga ya cika da jama’a tamkar ba sai rana ita yau ne daurin auren ba.

Wuni muka yi muna zaga wuraren shakatawa na ban sha’awa, mafi yawancin hirar yaya Almu a ranar magana ce kan muhimmancin haihuwa da darajar ya’ya a wurin iyaye. A duk lokacin da ya kalle ni kuwa sai ya jadada fadin, “Hakuri kawai za ki yi Rabi don ‘ya’ya da yawa nake bukatar ki haifo mana, Ummanmu ta samu, Umma Karama ta samu, Umma Amarya ma.” Haka na zuba mishi ido kawai na kallonshi ban iya cewa komai ba.

Har dare ba mu dawo ba. Hajiya kuwa sau biyu tana yi mishi waya, “Kai Lamido kafa kawo min yarinyar nan haka.”

Ya ce mata, “To ga mu nan zuwa.”

Sai wajen karfe goman dare ya ajiye ni a kofar gidanta.

Kwanaki shidan da na yi a gidan Hajiya kuwa sune suka tsareni daga sanir abin da ya rinka faruwa a gidanmu, na dai san kawai ana sha’ani mai yawa, don ko ita ma can take wuni, sai dare take dawowa, in za ta tafi ne dai za ta fara mini jike- jikenta ta ce wai in yi maza in shanye su kafin ta dawo. Tana isowa kuma za ta tasani a gaba da wasu kwayoyi ta yi ta sani ina hadiyesu, kamar zakara, tana kuma kara gaya mini kyan su har tana fadin Wai wadannan da kike gani kwanan nan za ki fara nemansu da kan ki in kika gane amfaninsu daga London na zo da su saboda ke, saura in kin je ya yi miki tabara ya ce sai kun ci amarci kafin ki fara haihuwa kul Kika yarda ai kina jegonki kina cin amarci, ina ganin kin dauki wani lokaci mai tsawo ban ji wani bayani ba da kaina zan zo har Kadunan in same ki,  kin san halina sari, don angwayen yanzu dabararsu kenan, wai a ce amarci kafin a fara haihuwa, to ni ba yarda zan yi ba, idan ita Hajiya Zuwairiya ta yi miku shiru ni ba kyaleku zan yi ba.”

Sai ana gobe daurin aure ne aka shirya dawo da ni gida.  Ina jin Hajiya tana yi wa Ummana waya tana cewa,  To uwar angwaye motoci muke so a turo su zo su dauke mu za mu kawo amarya wurin saka lalle. Umma tace bazan turo ba in motocin gidanku ba za su dauko ku ba, ki rike Amaryar kar a saka mata lallen. Hajiya

Hauwa ta kyalkyale da dariya ta ajiye wayarta lokacin ne na gane ita Umma ta tsaya matsayin uwar angwaye ne kenan, iyayen amare suna da yawa,  tunda nima Hajiya ce tawa uwar.

Maganar da Umma ta yi bai hana abokan yaya Almu yin jeri gwanon motocin su a kofar gidan Hajiya Hauwa ba,  dama kuma gidan nata a cike vake don mafiyawancin kawayen nasu nan suke taruwa kafin su hadu su tafi gidanmu.

<< Wace Ce Ni? 23Wace Ce Ni? 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×