Na sha kwalliya sosai, an yi mini gyaran jiki na ban mamaki, an kuma kawata jikin nawa da adon lalle mai kyan gani, ga wasu kaya na alfarma da Hajiya ta sanya mini. Sannan ta dauko mayafi ta lullube ni ta kuma wuce gaba tana rike da lullubin nawa ta yadda babu mai iya ganin komai nawa. Ta wuce muka shiga ni da ita mota, muna baya direba shi kadai a gaba ya ja muka bi bayan sauran motocin da aka basu umarnin su fara tafiya.
Sannan wasu suka biyo bayanmu. A haka har muka isa gida. Wajen karfe tara. . .