Skip to content
Part 27 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Baba ya ci gaba da magana yana fadin “Za ta tsallake ya’yanta ta tafi ne ko kuwa so kake ta kwashi ‘ya’yan ku tafi ta bar ni? Ai tasan ko tuwo bana cin na wata a gidan nan in ba nata ba ne.” Nan da nan Alhaji ya sunkuyar da kai kasa yayi ta bai wa Baba hakuri yana fadin “ya yi kuskure da bai yi wannan tunanin ba, amma tunda haka ne to a bar maganar tafiyar kawai na tashi na tafi na barsu saboda Baba ya sallame ni.

Nayi matukar jin dadin yanda Baba yayi mishi wanda yasa nan da nan ya janye tafiyar da kowa saboda gudun bacin rai, amma kuma daga baya sai naga to ribar me naci in nayi hakan? Nasa an hana shi tafiya da matanshi alhalin ni ina da uzurin da ba zai yiwu in bishi ba, zai je ya cigaba da zama cikin kewa da kadaicin da yake cewa ya ishe shi, bayan ga matanshi guda uku a gida suna zaman jiranshi? Kwana biyu bayan nan sai na koma gaban Baba na ce mishi a bar shi ya tafi da duk wacce yake son tafiya, Baba ni na hakura na yafe mishi, Baba yayi tasa min albarka alamar ya ji dadin abin da nayin, sai dai kuma abin da Baban ya fada ne ya tabbata lokacin da Alhaji ya ce zai tafi da Maryam sai Karama ta ce bata yarda ba, don haka Baba ya ce ya tasasu a gaba dukansu ya tafi dasu. Hakan kuwa akayi.

Shi kenan sai sashin namu ya zama ba kowa daga ni sai ya’yana muka sake muna ta sha’aninmu, in gari ya waye muna idar da sallah in na fito Uwa zata biyo ni ina abin karyawa tana wanke-wanke, kafin in yi dumame in dama kunu in toya kosai tuni har ta gama share wurin nan tas, har taje ta share turken dabbobi, ta kai musu dusarsu da ruwa tana dawowa sai mu kwashi abin karyawan mu ja kofar kara mu rufe wurin namu don kar kaji ko Akuyoyi su shiga suyi mana barnma, sai mu nufi wajen Baba can muke karyawa in mun gama in tura su Makaranta ni kuma in yi mishi abubuwan da zan yi mishi kamar su ruwan wanka da wanki da share-share in rana tayi in dawo wajena don in yi mana abincin rana.

Muna zamanmu a haka ko tunanin zuwan Alhaji ban fara ba saboda ganin dama can da yake shi kadai yana yin sati uku sati hudu balle kuma yanzu da ya tasa matanshi a gaba ya tafi dasu, don haka sha’anin gabana kawai nake yi.

Kwatsam! Rannan sai naga Uwa tana tsalle tana murna cikin tsananin farin ciki ko magana bata iyawa a dalilin tsananin murnar da take yi, sai fadi takc “Babanmu yazo Umma, Babanmu yazo, Baba yana jin haka shima ya kama murna, ni kuwa nayi kamar ban damu ba.

Wajen Baba ya fara shigowa tsarabar da yazo da ita ma a nan nasa aka jibge ta nan take na dibi ta yara na raba musu na kuma shiga kasa tsarabar gidan ina bayarwa Uwa tana kaiwa sassa-sassa tana dawowa na gama na juye naman saniya da yazo dashi na wanke na dora akan wuta sai naga wucewarshi zuwa daki nayi maza na shirya mishi abincin da ya samu nayi mana na kuma hada da danwaken da na jefa mishi don shi mai son danwake ne, na kawwo ruwa na ajiye mishi ina kallon shi yana cin danwaken sai ya dan kallen yace min dama kinyi zaton zanzo ne yau? Nayi maza na ce ko kadan, me ka gani? ya ce na same ku cikin kwalliya dukanku har da Baba gashi kuma ke da Uwa lallenku sai sheki yake yi, na yi murmushi nace ai yau Juma’a ne amma ni kam ai ban ma soma sa rai da zuwanka a yanzu ba, na dauka sai nan da wata biyu ko uku tukuna amma ba yau ba sati biyu kacal da tafiyarka, daga ido yayi ya galla min harara saboda ya gane abin da maganar tawa take nufi.

Karba sosai nayi mishi a wannan zuwan da yayi don kuwa maimakon kwana uku ko hudu da yayi niyyar yi bai tafi ba sai da ya kwana bakwai cif. Sati biyu kuma da tafiyarshi sai gashi ya sake dawowa, a haka sai ya ajiyewa kanshi yin sati biyu ko uku a can in ya dawo kuma sai yayi kwana biyar ko bakwai ya tafi.

Nan da nan kuma sai maganganu suka soma yawo wai ya kwashi mata biyu ya kai birni ya ajiye ya dawo ya tare a wurina, ni kam ko a jikina jinsu kawai nake yi a wannan lokacin ne kuma kasuwa ta kara budewa. Alhaji duk wani abin da ya taba da nufin sayarwa sai ya ci riba a kanshi duk abin da ya kawo don sayarwa kuma sai ya zama tamfar warwarcnshi ake yi saboda saurin karewarshi, don haka in yazo gida zai tafi zai kawo kudi masu yawa ya bani ya rinka gaya min cewar komai zaku ci kuci mai kyau in ce mishi to yanda yake bani kudi haka yake baiwamBaba shi kuma Baba in baya nan baya barina in sai komai ko da kuwa fura ne da nono komai saya mana yake yi don haka nan da nan sai ga kudi a hannuna na tara.

Rannan ina hira da Baba sai ya tambaye ni.

“Babu komai ne a hannunki? Ko mijinki bai baki komai ne?” Na ce mishi “Akwai Baba, yana bani in kawo maka su ne?” Ya ce min “eh to kawo.” Naje na kawo mishi su dukansu, ya karba ya kirga su ya ce “eh lalle kina da kudi to bari yayanku na tudu yazo sai in tura shi yayi miki cinikin wata fadamar rake da akayi min tallanta na ce mishi to Baba.” Da haka sai na mallaki fadamu guda biyu ga wacce Baba ya bani ga kuma wacce ya saya min da kudina.

Cikin shekaru uku na samun kudin Alhaji da nayi ina tare da Baba a gida yayi min tattalin dukiya mai yawa bai bari na in sayi komai da kudina, gashi kuma ko fita yayi yaga wani abin sayarwa da za’aci riba zai dawo yace min “kawo kudin nan a dan gwada juya su ko za’a samu wani abu akai in ce mishi to, a wannan lokacin suma su Karama tuni suka goge suka zama matan birni sai dai dukansu a rame saboda-zaman lafiya ya gagara a tsakaninsu, fitinar safe daban ta yamma daban, gashi gidansu su biyu saboda Alhaji ya sai nashi gidan sun tashi daga gidan hayan da suke zaune a duk lokacin da suka zo gida suka yi bakunta suka tafi in muna hira da Baba zai zolayen da maganarsu ya ce min yan uwanki sun zo suna kyalli sun baki sha’awa ko?” Ni kuwa sai in yi murmushi in ce “ai kyallin kawai na’ gani Baba, amma naga kamar na fisu cika ido.” Shi kuwa sai yayi dariya ya ce, “ai ba ki sha mamaki ba ma sai randa kika hadu dasu wuri daya kika ga suna neman rance a wurinki lokacin ne za ki kara gane kyallin ne kawai, su matan birni da kike gani ba duka ne suke da hikimar juya kudi ba, zama suke su mike kafa wai su nan ga masu jindadi kin taba ganin jin dadi ga wanda bai da anini?” In yi murmushi in ce “A a, sai ya ce to kar ki yarda ki zauna ba kya sana’ar komai ko ba kiyi da kanki ba rinka baiwa wani amintacce yana juya miki, in ce mishi to Baba.

Alhaji ya kwaso matanshi suka dawo gida gaba daya, gida hankali ya tashi ganin halin da Baba yake ciki, ni kam nayi kuka har na gaji tunanin mutuwar Baba Rabi ya dawo min da halin da na tsinci kaina a ciki bayan mutuwar tata, ban taba samun ta kare min wasu abubuwa ba sai da bata nan na gane ashe ita din idonta ya tsare al’amura masu yawan gaske, ya hana su aukuwa sai da aka daina ganinta, to balle Baba da na san bani da wani gata sai shi, shi ne komai dina shi kuma in na rasa shi a wane hali zan samu kaina? Wace irin rayuwa zanyi cikin wadannan mutane?”

Tsawon sati biyu komai yiwa Baba ake yi, a kwantar dashi a tayar dashi. Ana nan a haka sai kuma Allah da Ikonsa ya soma samun sauki kowa sai murna amma zan iya cewa babu wanda ya kaini daga samun saukin nashi kuma sai ya sallami kowa da kowa ya ce su tafi wurin gurin iyalansu ya baiwa Alhaji damar diban abinda yake da yake bukata. Ai kam ai ta wuce Zuwaira, sai dai mu ce Allah ya bamu ikon cikawa da Imani.” Na yi ajiyar Zuciya na ce, amin.

Baba ya riga ya rasa karfi mai yawa don haka ko kofar gida bai fita sai dai in yi mishi shimfida a gindin bishiyar dake kusa da dakin Baba Rabi ya fito ya zauna, saboda masu shigowa gaishe shi gaba daya hirarmu kuma sai ya maida ita yin nasiha. “Ki zama mai hakuri da juriya Zuwaira, sannan kiyi kokari ki rinka kawar da kai kan abin da idonki zai rinka gani, ba komai ki ka gani ne zaki bata rai ko kiyi magana a kanshi game da al’amarin mijinki kuma ki rike shi da al’amarin mijinki kuwa ki rike shi da al’amura guda biyu, hakuri da godiya in ya yi miki laifi kiyi hakuri, in yayi miki alheri ki gode mishi, kar ki yarda wani canjin rayuwa ya same ki kice mishi ya kai ki kasarku kiyi hakuri da duk abin da za ki gani watarana zaki bada labarinshi bayan ya wuce.

A duk lokacin da Baba yake yi min wadannan maganganun, kuka nake yi saboda nasan duk abin da yake cewa in yin yana nufin komai ba Zuwaira, addu’a kuwa kullum ina yi miki ita. Ubangiji ya wadata zuciyarki da hakuri ya kuma baki dauwamanmen rufin asiri in ce mishi amin.

To a haka muka zauna Babu ya rasa karfi nima na rasa kuzari zuciyata ta karaya na zama komai ma sa ni kuka yake yi. A haka Alhaji yazo ya same mu yayi kwana biyu ya tafi bisa cewar zai dawo sati mai zuwa tun daga nan ya koma zuwa duk Alhamis suyi sallar Juma’a tare sai ranar Asabar ya tafi.

Rannan ina tare da Baba miyar kuka nayi mishi da naman kaza na kuma tuka mishi tuwon Alkama nasa mishi man shanu muna zaune ina yi mishi hira cikin natsuwa don dai in samu yaci tuwon da dan yawa sai ga yara sun shigo wurin nashi bayan dawowarsu daga Makarantar allo suna fadin “Umma yau kin manta ba ki bamu kudin Laraba ba, na ce eh ku kuma baku tuna min ba, Baba ya zuba musu ido yana kallonsu ni kuma na basu umarnin su bi Uwa taje ta sa musu abinci bayan tafiyarsu sai ya ce min yanzu da wadannan fararen kayan nasu kal- kenan kike sanye musu kema kin sake fararen kaya ba ki gajiya da wanki. Na fara kallon Baba cikin tsoro na ce mishi Baba nima ba fararen kaya ne a jikina ba hankalinshi a kwance ya ce “au Haba? To ai shi kenan watakila idanuwan nawa sun gama aiki? Na kama kuka shi kuwa ko a jikinshi sai ma ya ce in kina yi mun haka ba zan rinka gaya miki magana ba, to menene don na fadi haka tsofaffi nawa ne hakan yake samunsu? Nayi shiru na bar kuka, don Baba kar yayi fushi wurin rannan wuni nayi ina tunanin in Baba ya daina gani irin abubuwan da zan rinka yi mishi don in rinka taimakonshi kan hakan.

Har akayi sallar azahar kafin na tashi na koma wurinmu na gyaggyara ina shirin dora miya sai ga Babangida da gudu yana fadin wai in ji Baba wai kizo nayi maza na wanke hannuna na bi bayanshi naje na same shi a zaune a bakin gadonshi ya kalle ni cikin natsuwa ya ce min, “alwala nake so kiyi min.”

Na yi maza na ce mishi “Ba ka da lafiya ne?” Ya ce min a’a kalau dina fitanne kawai bana so na ce to na daura mishi alwala ya sauka kan shimfidarshi ya zauna yayi sallarshi ban fita ba sai da naga ya idar sannan na ce mishi bari in je in dora miya zan turo maka su Junaidu su maka hira kafin in dawo, ya ce to na dawo wurin mu na samu har Uwa ta ajiye mun sanwar miyar, mamaki ya kama ni don komai ta tsaida shi kamar yanda taga ina yi.

Washe gari wajen azahar Alhaji ya iso tun daga nan ya karben yiwa Baba alwala ya ma. Ya sani na kawo ruwa mai zafi yayi mishi wanka ya goge shi ya shafa mishi mai ya canza mishi kayanshi yayi tsaf sai kamshin turare yake yi da daddare na shigo dakin bayan sallar Isha’i na samu bai ci abincin da na kawo mishi ba, ya ce min cikin bai mishi dadi don haka sai ya lafa, Alhaji ya ce dan damo mishi kunu shi da yake ruwa ruwan na ce mishi to na damo na kawo na dawo dakina na gama abin da zanyi na hau gado na kwanta har bacci ya dauke ni, Alhaji bai shigo ba na farka ban ganshi ba gabana ya đan fadi saboda tunanin ko jikin Babanne babu dadi, na tashi na gyarawa yara kwanciya na dawo na zauna a bakin gadona cikin tunani iri-iri naga dai wannan ba zai min ba na fita nayi alwala na dawo nayi sallah raka’a hudu nayi addu’a na shafa na dawo kan gadona na kwanta sai dai kuma bacci bai sake daukana ba zuwa can sai gashi ya turo kofa a hankali ya shigo ina ganinshi nayi maza na tashi na zauna a bakin gadon nace yau kuma jikin Baba babu dadi ko?

Bai wani yi magana sosai ba sai ya zauna a gefena cikin natsuwa sai ya ce min Allah ya saka miki da alheri kan dawainiyar da kika yi da mahaifinmu, Ubangiji ya saka miki da mafificin sakarmako.” Maganar tashi tayi min wani iri don ban taba jin yayi min irinta ba, don haka cikin rawar jiki da rawar murya sai na tambaye shi “babu shi ne Baban’?” A hankali ya buda baki ya ce min, “Babu shi Zuwaira, yau kam Baba ya barmu sai kiyi hakuri kar kice za ki tsananta yi mishi kuka, kiyi mishi abin da zai amfane shi shi ne addu’a.” Tsawon daren nan ba zan iya tunawa da irin addu’o’in da na kwana ina yi mishi ba, illa iyaka dai nasan daga mutuwar Baba ban sake yin lattin sallah ba balle in je ina hada azahar da La’asar ko Magariba da Isha’i.

Sai na rinka ganin tamkar lokacin sallolin nan lokacin ne kawai nake dashi, na mika addu’ata a gare shi bana hirar bakin cikin da nayi na rasa don ba zan iya kwatanta komai ba iyaka dai abin da na rike shi ne bayan rasuwar tashi ne nayi wata irin jinya mai tsanani irin wanda ban taba yi ba a rayuwata don sai da takai ma yayan tudu ya dauke ni daga sasanmu ni da yara ya maida mu sasanshi in da yaya Balki ke tafiyar mana da mafi yawancin al’amuran sai ko Uwa.

A wannan lokacin komai ya sauya mun duniya tayi min fadi na kara tabbatarwa kaina da cewar bani da kowa in ban da yan yarannan guda uku da suke manne dani har a halin rashin lafiyar da nake ciki basa rabuwa dani ta sani a gaba suke yi suyi ta kuka. Alhaji kam tun bayan zuwan da yayi akayi arba’in din Baba ya kwashi matanshi suka tafi ban sake sanya shi a idona ba.

<< Wace Ce Ni? 26Wace Ce Ni? 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×