Na ce mishi, “Madallah. Dawowar yaya Almu ne ya tsara zaman gidan ya zamo samarin gidan suna da karfi sosai akan al’amuran gida sune ma suke tafiyar da mafi yawancin al’amuran gidan maimakon da da matan gida ne suke sa ido akan komai tunda Baba ba mazauni bane.
Tsarin da yaya Almu ya yi ne yasa gabadaya yaran gidan suna karkashin kulawar yaya Zubairu ne in an kawo sabbin yara shine zai basu wurin zama da sutura shi zai yi maganar sanya su a makaranta.
Wurin shin ake kawo kara babu wani mai hukunta yara a gidanin ba shi ba, sabanin da da kowa aka yiwa laifi sai yayi duka, to an hana yin hakan babu mai yanci hukunta kowa sai dai a kawo kara wurin yaya Zubairu hakan sai ya tabbatar da bin doka da oda, karami ya girmama na gaba da shi, shi kuma babba ya yi wa na kasa dashi adalci.
Yaya Junaidu kuwa shine yake kula da sito din gida, shi ke fitar da duk wani abin bukata tun daga kayan abinci har zuwa na masarufi, duk wani abin amfani a wurinshi ake karba hakan ya taimaka kwarai wajen rage yawan ta’adin da ake yiwa Baba a gida.
Haka nan in Baba zai zo gida shi ke zuwa dauko shi a airport.
Sai yaya Kabiru shine yake kula da cefanen gidan a hannunshi komai na cefane yake.
Saboda dama matan Baba basa cikin wadanda ake yin girkin da su.
Shi kuwa yaya Almu shike kula da tsabtar gidan, dabbobin gidan da ma’aikata da kuma lafiyar mutanen gidan gabadaya duk wani wanda bai da lafiya wurinshi yake zuwa.
Wannan tsari da yaya Almu ya yi ya kawo, canji mai yawa da kwanciyar hankali gurin mutanen da ke gidan sabanin da da ake gwada karfin tsakanin matan Baba, in wannan ta bayar da umarni sai wannan ta ce a’a ba abinda, za’ayi ba kenan.
Kamar yadda ake da manyan samari haka nan ake da manyan yan mata.
A wannan lokacin ni ba na cikin manyám yan matan gidan don akwai biyar a gabana wadanda a lokacin da nake final year dina a secondary su sun fara karatunsu na HIND’ sune su Aina’u, Basira, Rahma, Kubra da Rashida su din su yaya Almu ya baiwa kula da abinda ya shafi yara mata, ganin yadda suke tafiyar da al’amuran shugabancin da aka basu ya sani zakuwa da ganin anyi musu aure don in zamo ni ce babba a gida, tunda sauran ‘yan matan da za su biyo bayana duk na girme su.
Kullum ina kadaicin tunanin na baya wuce in aka kawar da su ni yadda zan tafiyar da nawa shugabancin gashi kuma zanyi hakan ne a lokacin da shima yaya Almu ya bar gidan shine kuma dama mai takura min a duk lokacin da nayi wannan tunani to bana sanin lokacin da zanke kyalkyalewa da dariya don dadi.
Baba yana da wata dabi’a ko al’ada da yake burge mutanen da suka sanshi da ita take kuma kara baiyanar da darajar shi wurin yaran da yake rikewa ita ce ta hada aure a tsakaninsu.
A duk lokcin daya reni samari da ‘yan mata suka kawo munzalin yin aure mazan suna gama samun aiki zai tarasu ya gaya musu cewar ga ‘yan matan da zai basu wane zan hada shi da wance, wane ma da wance tun da yake yin hakan kuma bai taba samun tangarda ba.
Umma na ita ce matar baba ta farko auren saurayi da budurwa ita ce kuma marikiyar yaya Almu.
Don shi yaya Almu amaryar gidan Umma, amarya ita ce ta haifeshi, Umma karama itace matar baba ta biyu ita ce kuma ya auro daga cikin danginshi, haka nan ita da Ummana sune suke fafata matsanancin kishi a cikin gidan don kuwa har a shekárun nan nasu na girma babu sassauci a cikin lamari.
Don ma dawowan yaya Almu ya dauki matakan kawo gyara a tsakaninsu.
An kuma samu dan sassauci saboda kasancewar shi wanda Ummana take sauraro.
Yaya Almu ne ya kawo karshen zaman wariyar da Ummana da Umma amarya suke yiwa Umma karama.
Zuwan shi ne ya ki yarda da wareta da suke yi a cikin dukkan al’amura ya ce lalle ne a rinka sanya ta a ciki tun da dai ita ma matar Baba ce.
Ummana tana barin abubuwa da yawa, saboda Yaya Almu misalı, kowa ya san ita da Umma Karama ba sa jituwa, ni da kaina na san ranar da suka yi ‘yar tankiya tsakaninsu a falon Baba, don sun hadu dukkansu a can, saboda shi din yana gari Yaya Almu ne ya biyo bayanta har falo ranshi a bace ya zo ya durkusa a gabanta ya ce, ‘Umma ashe har yanzu ana yin wannan abin aa gidan nan? Har yanzu ba a kai lokacin da za ki daina sauraron irin wadannan abubuwan ba ki kawar da kan ki akan komai?”
Cikin yanayin jin kunya ta ce mishi, Yi hakuri Babangida ni ban san kana wurin ba da ban tanka mata ba.” Ya ce mata, “Ba na nan a wurin Junaidu ne ya yi waya ya kirani, amma ina so in roke ki daga yau kar ki sake daga ido ki kalleta balle ki gane wani abin da ta yi, don ranki ya baci in kin yi hakan ba tsoronta kike ji ba ni da Rabi kika rufuwa asiri.”
Ta yi maza ta ce mishi, “Ba za a sake ba na yau din nan shi ne zai zamo na karshe.” Ya yi mata godiya ya tashi ya tafi. Ni da kaina ba karamin tsayuwa Yaya Almu ya yi ba kafin na rinka zuwa gaida Umma Karama kullum safiya, saboda a bayyane yake ba ta so na, komai kankantar abin da na yi sai ta ce mini wai ai in ban yi haka ba sai a yi mamaki, ko a yi shakkun asalina, in kuma rabon abu take yi sai ta gama rabarwa ni ba ta ba ni ba sai da wata rana ya je ya same ta ya ce mata don Allah in abin da take da shi bai isa ta bai wa kowa ya samu ba to ta rinka ajiyewa kawai ko kuma ta aika da shi can a waje a bayar sadaka, amma ba a cikin gida a bai wa wasu a hana wasu ba. Ta ce mishi to.
Akwai kyakkyawar alaka ta soyayya da biyayya tare da ganin darajar juna tsakanin Yaya Almu da Umma, duk wani abin da ya shafi Umma yana da girma a vwurin shi, ko bakinta ya gani a gidan karbar da yake yi musu daban ne, ita ce abokiyar shawarar shi kan komai in kuwa ya ganta cikin wani yanayi na daban ya rinka gaya mata maganganu masu dadin ji kenan da kwantar da hankali, har sai ya ga ta samu nutsuwa.
Da yawan mutane dauka suke yi Ummana ita ce mahaifiyar shi, saboda yanda suke ganin mu’amalarsu, ba sau daya ba, ba sau biyu ba, ya sha zuba kudin shi ya gyarawa Umma wurinta, saboda kasancewar mafiyawancin bakin da ke zuwa gidan wurinta suke sauka sai ya zamo a duk lokacin da Baba ya yi musu gyara na ta wurin kan riga na saura bukatar a sake duba shi.
A duk lokacin da Yaya Almu ya lura da hakan sai kawai ya sa a fitar da kayan wurinta ya zuba mata sababbi.
Shi Yaya Almu da daya ne tamkar da goma kasancewar shi da namiji guda daya da Baba ya haifa bai sa shi ya maida kan shi daban da sauran mutanen da ke gidan ba, yana matukar girmama Yaya Junaidu da Yaya Zubairu, saboda dan girman da suka yi mishi, wanda bai wuce shekara, ko shekara da yan watanni ba.
Komai aka zo nema a wurin shi sai ya ce a jira sai sun dawo ya yi shawara da su, in kuwa bakin Baba ne suka zo suka same. shi to ya kan saurare su ne kawai idan ya san ba sa nan a gidan, in kuwa suna nan to cewa zai yi bari ya kira musu Yayan shi, ga shi da kokarin gami da tausayin iyaye.
Tun dawowar shi daga karatu daya nutsu ya soma tafiyar da al’amuran shi a matsayin shi na Lauya, ya shiga taimakon Baba da hidimomin gidan ba komai sai an nemi Baba ya yi aiken kudi ba.
A lokacin da na ke karama ta babu abin da na ki irin in ga baki sun cika wurin Umma su yi ta furzar mata da goro a ko’ina su ajiye kunshe- kunshen bahunansu masu boye da daddawa da kukar da suke kawo tsaraba.
A duk lokacin da na gan su daure fuska nake yi, wani lokacin ma shigewa daki nake yi in yi kwanciyata ko gaishe su ban fitowa in yi sai in Umma ta kwala mini kira.
“Ke Adawiyyah ba ki ji zuwan baki ba ne?”
Sannan ne nake fitowa in gaishe su ina gama gaisawar kuma zan fara jidar kayan su ina kaiwa dakin baki, in na gama in ce musu ga kayan ku na kai muku can su ce mini to su bi bayan kayan na su, babu yadda Umma ba ta yi da ni ba in daina yin hakan na ki kowanne lokaci ta yi mini magana sai na ce mata to tun da yan ‘uwansu Baba ne su rinka zuwa gun Baba Karama mana, ita ma ba ‘yar uwarsu ba ce sai su zo nan su rinka gurbata miki yanayin wuri da warin daddawa? Kowanne lokaci na fadi hakan ita Umma cewa take yi Allah dai ya shirye ki Adawiyya.
Rannan sai muka yi haka da Umma a gaban Yaya Almu bai ce mana komai ba sai da ya tashi zai fita sai ya ce mini, To zo mu je mana Rabi.”
Na ce mishi to. Na yi maza na bi bayan shi zuwa dakinshi. Muna shiga ya juyo ya cafke mini kunnena ya rike da karfin shi, sannan ya soma tambayata.
“Sau nawa na ji Umma tana yi miki kashedi akan bakinta?”
Ihu nake kurmawa, saboda tsananin zafi shi kuwa sai kara matse kunnen yake yi yana fadin,
“Sai kin gaya mini abin da ya sa kika maida Umma abokiyar wasan ki, saboda kin ga ba ta iya yi miki komai sai rokon miki shiriya?”
Yaya Junaidu ya turo kofar ya shigo dama kuma su biyu ne da dakin.
“Sakar mata kunne Mustapha, ko ba ka rike shi ba za ta ji abin da kake son gaya mata.” Yaya
Almu ya kallé shi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ya ce mishi, “So nake in cire mata wannan guda dayan in barta da daya.”
Yaya Junaidu ya yi murmushi ya ce, “Kai da Baba kenan in ka cirewa Adawiyyar shi kunne.
Ya sa hannu ya rike hannun nashi da ke rike da kunnen nawa ya ce, ‘Sake ta.” Ya saki kunnen ba tare da ya sake ce mishi komai ba sai dai ya kallen ya ce mini ina so in sake ganin an yi baki kina kwashe musu kayan su ba tare da kin jira an ba ki umarnin yin hakan ba.
Washegari da safe ya shigo ya same ni a falon Umma ina ganin shi na mike tsaye na fara tafiya ina gaishe shi, bai amsa ba ya ce mini, “Zo mana.”
Na dawo na ce mishi gani. Ya nuna mini kujera ya ce mini, ‘Zauna mu yi hira.”
Na koma na zauna don tsoro da bin umarni ya zuba mini ido cikin nutsuwa ya ce, “Labari nake so ki ba ni.
Yanzu misali a ce ke din kin je gidan mijinki kin zama uwar gida a wurin miji mai yawan jama’a wane irin shugabanci za ki yi?”
Na daga ido ina kokarin in kalle shi na kasa saboda yadda ya tsura mini na shi idanun yana kallona.
Ya ce, “Gaya mini mana za ki sa hannu biyu ne ki rike shi tare da jama’ar shi ko kuwa za ki watsa mishi su ne?”
Na kawar da kaina don kaucewa idanun na shi, sai da na yamutsa fuskata sannan na ce mishi,
“To ni zan zama uwar gida ne?” Na tauna bakina kafin na ce mishi ba na so ni, in mutum ya ce zai karo wata bayan ni tafiyata zan yi in ba shi wuri.
Na sake hada rai na ce kai ni in mutum zai auren ma sai na yi mishi kashedi, don ya san da sanin shi yin auren shi bayan nawa auren yana nufin ne kowa ya kama gaban shi tsakanin ni da shi.
Zuba mini ido Yaya Almu. ya yi cikin al’ajabin jin kalamaina. Can dai ya daure ya bude baki ya ce mini, “To ita Umma anan gidan baba ya yi sa’a halinta ba irin na ki ba ne, ita ta amince ita din uwargida ce tana kuma iyakacin kokarinta akan hakan…”
Tun kan ya karasa na yi kasa-kasa da muryata, Ya yunkura yana tambayanta, “Me kika ce?
Na yi maza na soma yi mishi kuka ina cewa;
To ni me na ce?”
Ya mike ya kama hanyar fita tare da fadin,
Kwanan nan zan yi maganin ki tun da har nima kunkuni za ki fara yi mini.”
Sati biyu bayan wannan lokacin Yaya Almu ya dawo daga wurin aikin shi ya aiko a kira ni nayi maza na bi dan aiken zuwa wurin shi, don a kwanakin nan duk ni da shi dasawa mukė sai da na bi ta wajen Baba maigyada mai dafa abincin gidan mu nan karbi na Yaya Almu sannan na wuce na je na kai mishih tare da yi mishi sannu da zuwa, sannan na nemi wuri na zauna.
Yaya Junaidu ya fito daga bandakin da ke dakin ya kalli Yaya Almu da ke tashe da kwanon abinci ya ce ni fa gaskiya na gundura da.cin abincin Baba Mai gyadan nan.
Yaya Almu ya yi dariya ya ce, “Ka ce dai kawai ka kosa baba ya yi sallama a koma cin na iyali.”
Yaya Junaidu ya yi murmushi ya ce, “Ba ka ji Zubairu ba rannan yana fadin wai har yanzu Baba bai gane mun girma ba ne.”
Ya wuce ya fita ya nufi masallaci ya bar Yaya Almu yana dariya, sannan ya kuma soma cin abincin shi. Ko loma biyu bai gama hadiyewa bai sai ya kalleni ya ce mini gaskiya Rabi irin tunanin maida girkin gidan ya koma hannun yan matan gidan baba maigyadan nan ta gaji, ni kuma ba zan sake dauko wata mai girkin ba, alhalin ga kartin ‘yan mata a gidan. Na yi maza na ce masa,
“Eh Yaya Almu ka sa su girkin kawai don in ba haka ba zuwa za su yi suna kwaba muku shirme a gida don ba su iya komai ba in ban da su wanke goma su tsoma biyar in kana so. ka ga kokarin su to wurin iya kwalliya ne kawai, na kuma ji Umma ma rannan da Baba ya yi mata waya tana gaya mishi cewar ya fa tsare ku da yawa gara ya sallame ku haka ya ba ku matanku kowa ya koma inda zai zauna da iyalin shi, tun da duk kun dade kuna aikin ku kai da Yaya Almu, ina jin anti Aina’u za a ba ka, don duk cikin su ta fi su iya hadin kwalliya.”
Dago idon da na yi na kalle shi ne na gane tuni ya dade da hada fuska, nima sai na yi maza na kawar da murmushin ta hanyar tsukewa.
Tsaki mai karfi ya ja kafin ya ce mini, “Ke dai na gane ki kunya ta anini ba ki da ita, ni kike yiwa maganar aure? Me kike cewa a yi a sallame mu? “
Na yi tsuru-tsuru da ido saboda irin wannan maganar ba ta taba hada ni dashi ba.