Skip to content
Part 29 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Nima bayan dawowana daga katagun na shirya naje musu wuni ni da yara na taf maimakon Karama ta sauke ni a dakinta a matsayinta na babba sai taki ta barni a tsakar gida sai Maryam ce ta matsa na shiga dakinta na dawo gida ina tunanin mahakurci dai shine mawadaci don kuwa daga kyan gida zuwa tsarin dakunan nafi su morewa gasu kuma su su biyu a can sun kuma kasa daidaita kansu su zauna lafiya.

Rannan ina gida da yamma ni kadai saboda yaran gaba daya sun tafi Islamiya sai ga Alhaji ya shigo ranshi a bace. Cikin natsuwa na tambaye shi abin da ya bata mishi rai, ya ce haba Zuwairah, ace mutanen unguwa suna ganin mutuncina amma kullum burinsu Maryam bai wuce su tozarta ni ba, kowane lokaci gidana yana cikin hayaniya wai yau har makwabta suna shigowa rabon fada? Nayi maza na ce assha, abu bai yi kyau ba sai kayi hakuri, ya ce a’a yau kam na gaji na bar musu gidan suje suci kansu, zasu dade basu sani a ido ba.

Na sake sassauta murya na ce, “kayi hakuri kar ka yi abin da za’a zo maida magana ace kaima ga naka laifin, tsawon lokaci ina rarrashinshi kafin ya hakura ya tafi bayan ya ci abincin dare.

Kwana biyu bayan naje gidan kai tsaye dakin Maryam na shiga bayan mun gaisa da Karama a tsakar gida na kalli Maryam na ce mata ba zan ci komai ba yau a dakinki dama kin tattara kin kwashe, ta ce haba-haba ai sai in yi fushi, na ce to kiyi fushin mana Maryam sai me, tunda ke kullum baki da aiki sai na batawa mijinki rai, ribar me kika ci a hakan da kike yi? Ta soma zata bani labarin Karama na ce mata kece za ki bani labarinta ko ni ce zan baki? Ta ce min to kiyi hakuri daga yau kuma ba zan sake kula ta ba ko me zata yi tunda dai nasan bata isa ta rufe ni da duka ba, tunda tasan ba kwashewa kalua zata yi ba in tayi hakan.

Na ce to da yafi miki mutunci a wurin mijinki dama mutanen unguwa ga baki daya sai ki same shi ki bashi hakuri kar kuma ki yarda ya sake fushi dake saboda ita ta ce min to daga wannan lokaci Maryam ta daina fadan baki da Karama sai dai kuma zaman babu dadi.

Yarda da shawarata da Maryam tayi sai naji dadi na dauke ta tamfar kanwa in naga tayi ba daidai ba ko in mijinsu ya gaya min laifinsu sai in gaya mata ta kiyaye yi mishi hakan duk abinda na hana ta kuma tana bari in kuma tana da damuwa zata zo ta gaya min in bata shawara haka kawai kuma zata shirya tazo min wuni don haka sai muka kulle sosai ni da ita tana bani girma nima ina mata adalci ko wani abu na gani ya bani sha’awa in zan saya tare nake saya mana in ma tayi min kukan wani abu zan kawo kudi in bata in ce taje tayi donni ban yarda na zauna bana sana’a ba babu abin da bana sayarwa in banda tsiya na riki Maryam ‘yar uwa sosai saboda dalilai guda biyu na farko ta yarda dani tana amfani da duk shawarar da na bata bayan haka kuma ita ce mahaifiyar Babangida tunda kuwa ina son Babangida babu dalilin da zai sa in ki Uwarshi ko da rashin kirki take min balle tana ganin girmana.

Nayi sabo da mutane sosai saboda sana’ata gani kuma da yara wadanda abokansu na makaranta ke biyo su gida don wasa ni kuma duk yaron da ya shigo ban barin shi ya fita haka kawai sai na kawo dan abin tsarabar yara na bashi, nan da nan sai muka yi fice gidansu Junaidu, Junaidu da Babangida ne suka yi fice sosai saboda ita Uwa bata fita ko ina bata kuma da wasu kawaye kowane lokaci muna tare a gida.

Na dawo aikin hajji da dukiya mai yawa saboda dalilai biyu, na farko dai nayi aikin hajjin ne a shekarar da dala take matsayin kwabo tamanin da biyar wato sule takwas da sisi don haka kudaden da Alhaji ya ajiye min sai suka yi min auki sosai, gashi kuma ya hada ni da abokanshi guda biyu, Alhaji na maibindiga mijinsu Hauwa ga kuma Baba Wulle wadanda su kuma suka tafi da matansu a wannan lokacin ne muka kulle sosai da Hauwa na kuma amfana kwarai da kawance na da ita don ita ta koya min kwalliya da gold maimakon yawan daura zani.

Nayi kwalliya sosai na kuma yi kyau har ba’a magana ga hakorana biyu a lokacin nan da na sanyo sai daukar ido suke yi suna sheki suna walwal saboda kasancewarsu jajaye wata mace tayi sallama ta shigo tana tashe da danta dake ta faman kuka yana shan majina, nayi mata sannu da zuwa na kuma shiga gaisheta tunda banga alamar zata karaso ba, sai dai bata wani amsa ba ta shiga ce min kece mamansu Junaidu? Na ce mata eh ta ce to kinga ki yiwa ‘ya’yanki kashedi don bai zamo min komai ba in sanya a nada musu dukan tsiya sun tasa min yaro a gaba da duka na menene hakan? Na kalle ta a lalace na ce na menene za ki kisa ayi musu duka in baki yi haka ba baki haihu da kyau ba, a fusace ta ce ai abin da za ki gaya min kenan? Na ce na gaya miki ni sau nawa yaran unguwar nan suka fasawa ‘ya’yana kai da duwatsu a garin jefe-jefensu kin taba ganin kafata na shiga wani gida don kai kara sai ke naki dan don an doke shi, to dan gwal ne da ba za a dake shi ba? Ta ce to shi kenan ta juya zata fita sai ga Alhaji ya fito daga falonshi ranshi a bace, ku zo nan mai yaro kiyi hakuri kiyi hakuri kin ji ko za’ayi musu fada yasa hannu a aljihu ya ciro kudi ya mikawa yaron ya ce gashi ko don Allah kuyi hakuri suka yi godiya suka fita, suna barin gidan ya rufe ni da fada kan me zanyi mata irin maganganun da nayi mata ina laifi da ta kawo min kara? Na ce to amma ni gunwa nake kai kara? Ni sau nawa ana yiwa yaran nan ciwo wa na taba gayawa?

Yau inda da Junaidu kadai ake yi da da sauki, tunda shima ya iya dukan ya’yan Jama’a amma Babangida fadawa yake fada ga tabon dutse nan a kanshi har yanzu bai gama warkewa ba sai kuma ni ta shigo min gida zata yi min bakar magana?  Haka ake yi? Ni ban taba ganin irin wannan rayuwar ba kai kasan darajar naka amma baka san na wani ba iyaye idonsu akan ‘ya’ya babu kunya babu kawaici, yayi murmushi ya ce to ai banbancin zaman birni da na karkara kenan, yanzu mü a gida ka isa ma kace zaka yi magana akan abin da aka yiwa danka? Na ce ba a isa ba ya ce to ki rinka yin hakuri in an kawo kara ki bada hakuri in kuma an yiwa naki kiyi hakuri, na ce mishi to.

Tafiya daya Alhaji ya yi bayan wannan lokacin ya dawo ya sauka a gidan su Karama bai zo gidanmu ya ganmu ba sai da ya kwana biyu abin da yayi matukar kona min rai, har na kasa boyewa. Ya shigo gidan nayi kamar ban san daga tafiya yake ba, ban da sannu da zuwan da rfayi mishi ban kara ba, ko ruwa kuma ban kawo mishi ba da dai ya lura ba wani tarbar arziki zanyi mishi ba sai kawai ya tashi yayi ficewarshi ya tafi, ban sake ganinshi ba ya gama saura kwana biyunshi na can gidan ina tunanin  yau dai ai dolenshi zai dawo nan din da ba ya so zan kuma gaya mishi na fara gajiya da hakurin da kullum nake yi, baya gani tunda bai gudun bacin raina sai nasu, ban taba ganin ranar da ya dawo ya wuni a gari bai je ya duba su ba sai ni da ya raina. Ina cikin jira yazo in jera mishi wadannan maganganun sai kawai ga dan aike an kawo min kudin cefane wai shi yayi tafiya na ce tafidijam, ban taba yin sha’awar yin yaji ba irin wannan ranar sai dai kuma inyi yaji inje ina?

Haka na hakura na zauna raina a bace bai dawo ba kuwa sai da yayi sati uku ya sauka anan gidan. Rannan kuwa kwana nayi ina yi mishi kuka ya zuba min ido kawai yana kallona sai da nayi ya 1she ni nayi shiru sannan ya ce min, ai na dauka akwai wani sassauci a tsakanina dake ban taba dauka kina lura da wani abin da nake yi musu ba, na dauka tsakanina dake kawai kika sani, to amma tunda haka ne shikenan ba zan sake ba zan rinka kiyaye abin da nake yi musu in tabbatar nayi miki kamar yanda kema zan kiyaye wanda nake yi miki in rinka yi musu.

Kunya ce ta kama ni da yayi min wannan maganar don nasan abin da yake nufi sai dai ban yarda ya gane naji kunyar ba ne eh ai gara ka rinka yin hakan, cikin raina dai na kudurawa kaina cewar babu wani abin da zai sake yi min in bude baki in yi magana.

A wannan shekarar ne Alhaji ya kaini kasarmu ta Senegal tare da yara na tafi tare da tsaraba mai yawan gaske, abin mamaki ashe wai har kanine dani wanda muke uwa daya uba daya, kuma wai tuni Alhaji ya dade da sani amma bai taba bani labari ba sai ran da muka isa. Bayan mun natsa sai ya kalle ni ya ce min, ina jin fa Muntakan nan shi ne kaninki da Baba ya bani labari da sauri na kalle shi na ce mishi kanina? Ya ce eh ita Inna ba wurin haihuwa ta rasu ba? Lokacin ne na tuna Babana ya sha gaya min Innata wurin haihuwar kanina ta rasu, na kalle shi na ce tafdijam, amma shine baka taba gaya min ba? Yayi murmushi ya ce, “to ai tayar miki da hankali kawai zanyi, na ce haka ne.

A zaman bakuntar da nayi, nayi kokarin jan Muntaka a jikina muka yi sabo na kuma nuna mishi cewar ya bini muje yaga inda nake abin da kanin Babanmu wanda yake shine marikin shi yaso ya ki yarda nima kuwa na tasa Alhaji a gaba da kuka na ce mishi ai da ganin Muntaka ba dadinsu yake ji ba, ba gashi duk sunyiwa ya’yansu sa’o’inshi aure ba amma shi basu yi mishi ba, ya ce ai sun ce bara rashin lafiyar da yayi ne yasa ba ayi mishi bikin ba, na ce eh to muje dai yaga wuri, ya yi murmushi ya ce to bari muji abin da Baban zai ce.

A haka muka dawo da Muntaka gida akan zai ga wuri ya koma sai muyi zamanmu nan da nan ya wastsake daga duk wata wahala ya zama santalelen saurayi gashi tunda yazo ciwon cikin da suka ce yana dashi din bai sake tashi ba, gashi nan da nan Alhaji ya sanya shi cikin harkokin dukiya har ya shiga yin tafiye-tafiye dashi Alhaji ya kara nuna mishi gatan da ya tabbatar min da matsayina a wurinshi.

Rannan ina zaune a falona bayan mun dawo daga umrar da muka tafi ni da Hajiya Hauwa, hutawa nake yi cikin nishadi sai naga Muntaka ya shigo gida yana sanye da doguwar jellabiya fara sol a jikinshi da farar hula ‘yar karama yayi matukar yin kyau yayi sallama a bakin kofa ya cire silifas din wanka dake kafarshi ya shigo ya zauna na zuba mishi ido ina kallonshi na ce, Muntaka baka je kasuwa ba ka kuma san Alhaji ba ya nan? Ya ce naje yanzu na dawo ina son yin magana dake ne sai 1n koma, na ce mishi to, na dan daga murya na kira Uwa na ce kawowa kawunku abinci, ta ce to taje ta kawo ta ajiye mishi ya ci kadan sai ya kalle ni ya ce so nake in yaya ya dawo ki rokar min shi ina so in koma kasarmu da sauri na ce mishi Senegal Muntaka? Ya sunkuyar da kanshi kasa ya ce mun eh ai kinga ba na shekara biyu kenan har da watanni tunda muka zo da zamu taho kuwa cewa akayi zan zo in ga wuri in koma, na ce haka ne. Bayan fitar shi sai nayi ta kuka saboda ban son tafiyar tashi ina ganinshi a matsayin dangina gashi zai gudu ya barni, to ko dai wani laifi nayi mishi bai gaya min ba? Abin da ya tsaya min a zuciyata kenan, sai dai bance mishi komai ba sai da Alhajin ya dawo na bashi labari da ya gama sauraronä sai ya ce min ina ganin aure yake so ai ya girma bana shekarunshi ashirin da takwas kenan tunda ke kinyi talatin bana nace mishi hakane, ya ce to gaya mishi ya duba yarinyar da yake so sai a aura mishi, na ce to da na gayawa Muntaka sai ya ce min shi bai son auren don baiga wace yake so ba, Alhaji ya ce in gaya mishi yaje ya duba cikin ‘ya’yan abokanshi ya sake cewa baya so. Rannan nayi kuka a gabanshi ina tambayar shi me yasa baka Sona Muntaka me yasa baka son zama dani?

Kwana biyu bayan nan na kira Muntaka ina rarrashinshi don ya gaya min meye damuwarshi? Sai ya ce min tsoro nake kar in yi abin da ba a taba yi ba, nayi maza na tambaye shin me? Wane abu ne zaka yi wanda a duniya ba a riga ka yin shi ba? Ya sunkuyar da kanshi kasa muryarshi tana rawa kamar yanda jikinshi ma ya dauki rawa ya ce da kin barni kawai na tafi na ce ba zan barka ba sai ka gaya min gaskiyarka, a hankali ya ce min nesa nake so in yi da Uwa tsoro nake ji kar in ce ina son..Ya kasa karasawa, nan take kuma ya shiga shisshikar kuka saboda tsananin damuwar da ya shiga, da sauri nace mishi ai ba ni na haifi Uwa ba Muntaka, bani na haife ta ba, ‘yar wan Alhaji ce ai kana da damar cewa kana sonta, na zauna na kwashe dukkan labarina tun daga kuruciyata a gaban Babanmu har kawo ranar da nake bashi labarin ban rage mishi komai ba.

Shi kenan tun daga nan sai ya saki jiki ya koma al’amarinshi da Alhaji ya dawo kuma na bashi labari, yayi matukar jin dadi ya ce ai shi kenan sai kiyi tuwonki manki, na ce hakane.

Ana yin haka na shiga shirin buki amma sai da naje Katagun na shaidawa yaya Balki in da ta nuna min bacin ranta kan hakan da nayi bisa cewar wai ba sai na gaya mata hukuncin da zan zartar a kanta ba.

Ina dawowa na nemi izinin Alhaji na biyawa yaya Balki da Uwa kujera kamar yanda dama nasan Muntaka yana cikin mutanen da Alhaji ya ce zasu tafi.

<< Wace Ce Ni? 28Wace Ce Ni? 30 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×