Skip to content
Part 33 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Hankalina bai kara tashi ba sai da na ga Anti Rahma da danta a gadon asibiti suna kwance abin gwanin sha’awa, danta gabjeje mai kyau dashi. Nasa hannu na karbi yaron na mikawa yaya Almu hannu biyu yasa ya karbe shi yayi ta karanto mishi addu’o’i yana tofa mishi cikin farin ciki da murna saboda yaya Junaidu baya nan yana waje sai kawai muka tsaya akayi sallama muka dauko Anti Rahma da danta muka kawo su gidan Baba don umarnin da Umma ta bayar kenan na a kawo mata ita tayi jego a nan.

Daga nan na wuce sunan Anti Kubra da aka gama komai kuma na sake komawa Legos na Jira sunan Anti Rahma inda muka samu Aliyu wato sunan Baban Umma, bayan dawowarmu daga sunan Baban Umma kamar yanda na ji kowa yana kiranshi ko sati biyu bamu yi ba muka nufi birnin Cairo don ganin wani Likita da Baba ya tura mu wurinshi, tun daga wannan lokaci muka tsunduma cikin maganar neman haihuwa yau muna nan gobe muna can shiru babu ciki babu dalilinshi ko batan wata ban taba ba balle akai gayin bari, ana nan a haka daga baya sai yaya Almu ya soma nokewa tafiye-tafiyen asibiti da na same shi nayi mishi magana kan sabon halin nashi sai ya ce min mu nemi haihuwar kawai wurin mai ita Rabi na gaji da wadannan tafiye-tafiyen ni ban natsu na maida hankalina kan cikina ba ke ba ki zauna a dakinki kin huta ba, yanzu Junaidu da yake da ‘ya’ya biyu a gidan shi asibitin ina yaje aka duba shi? Inda Likita na bada haihuwa ai da mun samu.

Gashi dai gaskIya ya gaya min amma ban ji dadin gaskiyar ba, saboda zuciyata a yanzu babu abin da take so irin in ganni da da in ga dai na haifarwa yaya Almu da Umma da inga dai irin son da zasu nuna mishi a duniyar nan, tubburewar da yaya Almu yayi kan cewar shi kam ya gama zama a gaban Likita don rashin haihuwa ba wata lalura ta rashin lafiya ba ana mishi gwaje-gwajen da suka kamata dama wadanda basu kamata ba, na kawo wannan kawo wancan, yasa na nufi Legos Wurin Baba don kai kara Umma na ce na samu a can, ban kuma samu fadin abin da ya kai ni ba saboda rikicin da na samu anayi a gaban Baban, yaya Junaidu da Anti Rahma ne suka samu sabanin da yayi dalilin da yayi mata duka irin wanda ban taba tsammanin mutum mai hali irin nashi zai iya yin hakan ba.

Ummana na samu a durkushe tana goye da Zuwairiya yar da Anti Rahma take goyo, tana kuka ga kuma yaya Junaidu can gefe a takure ya sunkuyar da kanshi kasa itama Rahman tana ciki kallo daya nayi mata na shiga taya Umma kukan da take yi saboda zaluntar ta da Yaya Junaidu yayi zagewa yayi da iyakacin karfinshi ya nada mata dukan tsiya, ban iya zama a wurinta ba saboda tausayinta na tashi na tafi wurin Umma na zauna ina jiran fitowarsu sai zuwa can sai ga Umma tana tashe da Anti Rahma sun shigo har lokacin Anti Rahma bata daina kuka ba itama Umma bata daina yi mata fada ba. Yau inda haka kawai Junaidu yayi miki wannan zaluncin da kinyi mamakin abin da ya same shi, to amma akan me akan me zaki yi abin da kika yin?

Rinka haihuwar su kina kawo mun su Rahma ni zan rike ba zan gaji da su ba, ai ni na rike ubansu Umma tana fadin ta soma kuka, a gigice na shiga tambayarta me ya faru ne Umma? Bata tanka min ba ta tashi tana cewa tashi ki bishi ku tafi zan rike ta tare da dan uwanta in kin haifi na cikin kima zan karbe shi ki zauna kar ki wahala tana barin dakin na kalli Anti Rahma na ce wani cikin ne dake Anti Rahma? Ta gyada kai cikin takaici ni ke nan kullum ciki shi ne daga naje don a cire min munafukin Likita yayi waya ya tambaye shi shine yayi min wannan wulakancin, kuma zanga…..ban barta ta karasa ba nayi maza na mike ina kallonta, na ce mata kije ki cire Anti Rahma kije kiyi abin da kika ga dama, ni in yi kuka don ban samu ba ke kiyi kuka don kin samu sun ishe ki saboda butulci, saboda rashin adalci irin naki, kuma wai har kina kawo maganar gaban Umma na kin mance matsayin ‘ya’yan yaya Junaidu a wurinta kin manta da cewar yaya Almu bai samu ya haifan mata ko guda daya ba, mun gode. Na yi maza na fice na bar mata dakin ban nemi kowa ba na bar gidan kawai na dawo gida cikin zuciyata ina mamakin butulci irin na mutane.

A gida ban yiwa yaya Almu tadin ba musamman ma da yake na same shi yana fushin na fita gida ba tare da na nemi izininshi ba, don haka sai kawai muka ci gaba da zamanmu a haka sai dai kuma kwana daya ne kawai da dawowana sai ga yaya Junaidu ya biyo ni, ina daki sai yaya Almu ya shigo fuskarshi a daure ki zo ga Junaidu yazo yana son ganinki, na ce to na tashi na dauki hijabina na sanya na nufi falon nashi nayi sallama yaya Almu ya amsa na shiga na nemi wuri na zauna a kasa, bayan na gabatar mishi da abinci da na sha ya gama amsa gaisuwar da nayi mishi sannan sai ya ce mun jiya sai kika taho ba kiyi sallama da kowa ba har da Baba me yasa kika yi haka? Na ce kayi hakuri kawu nayi kuskure hankalina ne ya tashi naje gida don in kai karar yaya Almu ya ki yarda muje asibiti kan mas’alar mu sai kuma naje na samu maganar ku shi yasa na hakura na dawo. Yaya Junaidu ya kalli yaya Almu ya ce yaya Mustapha akwai wani abu ne? Yaya Almu ya ce a’a ni dai ayuka sunyi min yawa ne kawai, ya ce to ko zaka ba da izini a shirya mata tafiyar ita taje? Ya ce eh to babu laifi amma a hada ta da wani, yaya Junaidu ya ce Umma Amarya zata ganin Likita ai sai su tafi tare ya ce ba laifi.

Wannan tafiyar da muka yi da Umma amarya muka je asibiti ita ce ta baiyanar da asirin da yaya Almu ya dade yana boyewa, don kuwa a wannan tafiyar ne na samu damar da na karbi sakamakon Likita da hannuna.

Ina zaune gaban Ummana ni da ita kuka muke yi yaya Almu ya shigo ya same mu saboda kiran da Umman tayi mishi.

Cikin natsuwa ya tambaye ta ko lafiya? Ta mika mishi takardun da nazo dasu ya gamna dubawa ya mayar a hankali ya ajiye ya ce ni ban yarda da wannan gwajin ba, Umma ban yarda da su ba in na samu sarari zan sake kaita ayi mana dukannmu, don haka ki kwantar da hankalinki kar ki samu damuwa, yayi ta rarrashin Umma har sai da ya kwantar mata da hankali sannan ya tasa ni a gaba muka dawo gida.

Muna isowa ya balbale ni da fada ba tare da ya ji tausayin abin da nazo dashi ba, dama bukatar ki kenan kije asibiti ki zowa Umma da labarin da zai bakanta mata zuciya? Kina tsammanin tana da wani karfin da zata iya daukan wani bakin ciki daga gare ki? Abin da ta gani a rayuwar ta ya ishe ta kar ki sake binciko wani mummunan labari kije ki gaya mata, ki rike abinki a cikinki, kema ki koyi zama jaruma kina rike damuwarki ba sai kin maida ita ta zama damuwar kowa ba.

Mamakin tashin hankalin yaya Almu naji da ko in kula kan sakamakon likita dana zo dashi na cewar ba zan haihu ba amma sai na hadiye na daure na ce mishi amma yaya za’ayi in iya hadiye wannan maganar ban gayawa Umma ba?

Ya ce eh saboda ba kya tausayinta shi yasa ba za ki iya hadiye wa ba da kika dawo ai ni ya kamata ki fara gayawa ruwana ne in ce to mu gayawa su Umma da Baba ruwana ne kuma in ce to mu barwa cikinmu. Wannan test din naki ni ban shekara hudu da samunshi ba? Tun zuwa asibitin farko da muka yi aka gaya kin ga na gaya miki? Saboda kar in tayar miki da hankali, yana mikewa yaje ya kwaso takardun ya watsa min su ya ce kin ki yarda ne da baki je kika jiwo ba balle kije kina fada.

Tattara takardun nayi na rungume su a kirjina ina wani irin matsanancin kuka ina fadin shi kenan shi kenan ni ba zan haifar maka dan da Umma zata dauke shi ba.

Yaya Almu ya durkusa da gwiwowinshi biyu a gabana ya ce ban taba yarda da hakan ba Rabi, shi yasa na ce miki mu nemi haihuwar kawaai wurin mai bayarwa ban kuma fidda ran zai bamu ba kiyi hakurin fadan da nayi miki ki bar kukan da kike yi, amma ina so ne ki sani cewar ni dake ba zai yiwu mu zama sanadin bacin ran Umma ba don haka kar ki sake kai mata wani labari da zai tayar mata da hankali na ce mishi to.

An dauki lokaci mai tsawo yaya Almu yana rarrashina kafin na dawo cikin natsuwa ta hankalina ya dan kwanta saboda irin kalaman da yake yi min wai kenan ance miki dole sai an haihu ne ake farin ciki? Ba ki san wasu suna nadamar haihuwar da suka yi ba? Ai ita rayuwa gamsuwa ne kawai Rabi in ka yarda ka gamsu da ni’imar da akayi maka kayi godiya kan hakan sai a baka kwanciyar hankalin da kake bukata, kina sona ina sonki hakan bai ishe mu godiya ba? Kullum irin kalamanshi kenan har dai na dan hakura, na tasa al’amarin mijina a gabana, na maida tattalinshi shine farin cikin rayuwata, kowane lokaci cikin shirya mishi nau’o’in abinci iri-iri nake a kowane lokaci kuma in dai yana gida to ina manne dashi in ma tafiya zai yi to mafi yawancin tafiye-tafiyen nashi tare muke yi.

Mun bar hirar haihuwar da maganar nemanta sai dai kuma kullum a cikin yin addu’a muke ko na ce ni na gaji zan huta sai ya ce baki da hankali Rabi, kin taba ganin wanda ya gaji da rokon alheri wurin mai bayarwa? In ce a’a ya ce to kiyi ta addu’a ki kuma yawaita istigafari in ce mishi to.

Abu daya dai da yafi damuna shine na rage zuwa wurin Umfa na sai dai na kanyi mata aike akai-akai, saboda na gane ganina yana tayar tayar mata da hankali mafi yawancin lokaci in ina tare da ita ba ma rabuwa sai tayi kuka ko ni kuwa cikin zuciyata mafi yawancin damuwata kan rashin haihuwar tawa saboda Umma ne in ga dai ta rike da a hannunta ace ni na haifan mata shi mana wannan shine abin da yafi muntsinina amma in don ta yaya almu ne ya hakura, ya shanye ya boye ya, ya barwa cikinshi in ma yana da damuwa to ban sani ba a zahirin abin da ya nuna min shi ne nice komai dinshi, nice farin cikinshi da kwanciyar hankalmshi ni kadai kuma na isa in cike mishi kowane irin gurbi na abin da ya rasa.

Aurenmu ya cika shekaru biyar banyi niyyar tunawa yaya Almu da zagayowar ranar ba don hakan yana nufin tuna mishi da dadewar mu ne babu da, don haka naja bakina nayi shiru sai dai na shirya yi mishi abinci mai dadi don in kara mishi farin cikinshi Pasta mould na shirya mishi.

ABUBUWAN BUKATA:

1. Shinkafa ne ko taliya, sai nayi amfani da shinkafa saboda sanin shi Yaya Almu ba ma’abucin cin taliya ba ne sosai.

2. Kayan kamshi

3. Mangyada

4. NikaRken nama

5. Tumatur

6. Alaiyaho

7. Maggi

8. Butter

9. Albasa

Na tafasa shinkafa, ta dan fara dahuwa kadan sannan na juye ta na tsantsameta na barta tasha iska kafin na soyata a cikin Butter. Nasa a abinda zai iya zama a oven na ajiye a gefe.

Na kawo rabin butter na soya da albasa na zuba naman, tumatur, kayan kamshi da magi, na hada na dafa sannan na dan dafa alaiyaho da maggi kadan.

Na hada alaiyaho da naman nan na wuta na gauraya na zuba akan shinkafar na rufe da foil paper nasa a oven na barshi cikin madaidaiciyar wuta, tsawon minti arba’ in.

Na kuma shirya mishi abin sha mai dadi, shima ga abubuwan da nayi amfani dasu.

Kankana

Lemo

Sugar

Citta

Lemon tsami cokali (1)

A cire jan kankanan a bar bakon asa a bulanda a markada, a markada lemon zaki bayan an cire fari-farin abin da ke jikinshi, a matsa ruwan lemon tsami cokali daya akan ruwan kankana da lemon nan sai asa citta kadan da sugar daidai yanda ake bukata.

Gaba daya na hada na juye na shirya mishi yana zaune yana kallon abincin sai ya kalle ni yace min hala dai an shirya min wannan abincin ne yau don a tuna min na sheka ra biyar yau da angwancewa?

Na sunkuyar da kaina kasa cikin zuciyata na ce ashe shima yana sane da zagayowar ranar, na dago kaina a hankali na kalle shi na ce mishi eh yaya yau shekarunka biyar da angwancewa sai dai har yanzu….bai bari na karasa abin da nake shirin fadin ba, sai yasa hannu ya tallabe habata ya ce, har yanzu amarcinmu yana nan kullum kara son juna muke yi ni da ke babu abin da ya taba shiga tsakaninmu muna da fahimtar juna muna ganin darajar juna saboda akwai kauna mai yawa a tsakaninmu, don yi min alkawari a yau kamar yanda nasha yi miki a sauran shekaru hudu da suka wuce, na kalle shi cikin murmushi na ce alkawarin me zanyi maka yaya Almu? Ya zuba min ido yana kallona ya ce irin wanda nake yi miki a rana irin ta yau, na ce ai ni bani da abin yi maka ko baka yayi maza ya ce kina da su da yawa Rabi, don haka zan roke ki kiyi min alkawarin har abada zaki yi tayi min abubuwa guda uku, na ce sune me? Ya ce za ki yi ta sona ko da kuwa a wane hali muka samu kanmu? Na yi murmushi na ce wannan ai rubutacce ne a zuciyata, ya ce to na gode yi min alkawari Rabi za ki bani hadin kai a duk lokacin da na nemi hadin kanki kan wani abin da ya taso min, na ce zan baka, ya ce to ina so ki zama mai taimakona a kowane lokaci na nemi taimakonki, na sake cewa zanyi hakan ya ce to na gode, yana fadin haka ya mike ya shiga dakinshi ya fito wata ‘yar leda ya dauko da ya fito da wani dan akwati daga cikinta ya bude shi ya fiddo wasu warawarai masu asalin kyau ya kama hannuna ya zare wadanda nake sanye da su ya maida mun sabbin ya ce tukuci ne na kin shekara biyar kina hakuri da mijinki.

<< Wace Ce Ni? 32Wace Ce Ni? 34 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×