Skip to content
Part 34 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Na kalle shi nayi murmushi na ce, na gode Yaya, abin da duk kake nema na alheri a rayuwa Allah ya baka shi, ya ce to amin.

Da daddare ranar ina tare da yaya Almu bayan na tsala mishi kwalliyar da tayi dalilin al’amura masu yawan gaske, yana kwance can gefe kan faffadan gadon nashi cikin matsananciyar gajiya, lumshe kuma da ido yana maida numfashinshi a hankali, zuwa can sai naji ya ce min “kinyi bacci ne Rabi? Na ce mishi a’a, ya ce to kar kiyi bari in zo muyi magana, na ce mishi to. Mikewa yayi ya shiga toilet yayi wanka ya fito nima ya bani umarnin yin hakan, naje nayi nazo nima nayi sallah raka’a hudu saboda abin da na samu yana yi kenan, ya gama addu’a ya shafa fatiha nima na shafa tawa sai ya juyo ya kalle ni cikin natsuwa babu alamar wasa a tare dashi, sai ya buda baki ya ce min, wannan maganar da na zaunar dake zan gaya miki a yau Rabi ta dade tana katse min dadin baccina saboda nauyinta a wurina yana da yawa, to amma babu yanda zanyi in yi ta boye miki ita musamman da yake abin kara matsowa yake yi, zuba mishi ido nayi ina kallonshi ina kuma sauraron bayanin nashi, sai ya ce min ni dake akwai fahimtar juna a tsakaninmu shine kuma muhimmin al’amari dama a tsakanin ma’aurata, ni na yarda dake na amince miki don nasan ba za ki taba yin wani abin da zai cutar dani na ba, Kuma sani kema kin san in zan hango abin da zai cuce ki to zai gama dani ne kafin ya iso gareki, ban taba zaton zanyi abin da nake shirin yin ba a wannan lokacin in ban da wasu al’amura masu tsanani da suka tasa ni a gaba.

Na ce mishi menene ya faru Yaya Almu? Menene ya taso mai tsanani da zai saka kayi abin da baka shirya ba? Ka gaya min kawai ba sai ka tsaya kana yi min dogon bayani ba, ya ce natsuwarki nake bukata so nake ki bani hadin kanki don hakanne kawai zai taimake mu ni da ke na ce na baka ka gaya min menene? Ya sassauta magana ya ce aure nake so in yi, amma ba ni na nemi auren ba, ba ni yarinyar aka yi, na zuba mishi ido ina kallonshi cikin kaduwa ban taba tsammanin abin da zai gaya min ba kenan, na daga ido cikin natsuwa na kalle shi na ce don ni ba zan haihu ba kenan? Yayi maza ya ce a’a, a’a ba haka bane, kinsan shi aure zuwa yake yı, kuma don kisan ma babu wani abin da zai cutar dake Umma ta sani ita ce ma ta ce dole in karbi auren don da nace bana so nayi maza na ce Umma? Nan da nan ya canza zancen da cewar ba Umma nake nufi ba, amma ni dama can kinsan ina gaya miki cewar sha’awar uwargidanci nake yi miki, na rinka yi miki hakanne don in fahimtar dake cewar ni din bani da burin zama da mace guda daya na ce haka ne, amma tun lokacin nima na gaya maka cewar bai bani sha’awa ba kuma zan taba yarda in yi shima har ma na taba gaya maka cewar kara auren mijina alama ne na shi din ya gaji dani, don haka yanzu ma kan abin da zan tsaya kenan ka gaji dani ai ma kayi kokari ban haifar maka kowa ba bayan kana ganin duk wadanda muka yi aure tare ‘ya’ya uku-uku suke shirin samu, gidan Yaya Junaidu kuwa tuni akayi ukun na hudu ake nema, lokacin ne na fara kuka sosai musamman da na kara tunawa cewa ni da kaina na karbo sakamakon Likita da ya tabbatar da cewar ba zan iya haihuwa ba ban da wanda yaya Almu ya dade yana boyewa.

Hakan da nake yi ya kara sanyaya jikin Yaya Almu, ya matso kusa dani ya rungume ni “ki yi hakuri Rabi, ina tabbatar miki bana murnar wannan auren na sani ban taba sha’awar zama mijin mace daya ba, amma lalurarki sai tasa ni jin tausayinki matsananci da yasa na hakura, na hakura da duk wadannan abubuwan, to amma a yanzu ya zama mun dole inyi Baba da Umma sun tasa ni a gaba ta kaima nayi, watanni ban je in da suke ba amma basu hakura ba sai kuma kwatsam ga maganar wannan yarinyar ta taso. Umma kuma ta ce in karbi auren kin kuma san ba zai yiwu in ki bin umarninta ba.

Ko da yake nasan yaya Almu kullum kan bin umarnin Umma yake amma sai na kalli wannan biyayyar tashi har da dama yana so, duk yadda na kai da son kaina ya zama dole in yarda da cewar yaya Almu zai bukaci kara aure don samun haihuwa ko da kuwa kullum hadiye shi a ciki nake yi ina fito dashi, don tsananin kyautatawa, shi ne da guda daya da baba yake dashi ko kafin in mallaki hankalin kaina kuwa nasan babu wani abin da ke da daraja a gidanmu irin haihuwa, to yaya Almu bai samu ba an kuma ce nice mai matsalar, in baba ya sanya shi yayi aure bai yi laifi ba, don nasan yana son ganin danshi koma in ce ‘ya’yanshi yanda duk ya kai da sona kuma ba zai bani mamaki ba in ya fifita son da yake yi mishi akan nawa, to amma ita Umma fa, don me zata shiga zancen auren nashi? Tana nufin itama tafi sonshi a kaina?

Wadannan sune tambayoyin da suka zo cikin zuciyata na kuma kudurawa raina ganin Umma don ta bani amsar su.

Har gari ya waye ban sake daga ido na kalli Yaya Almu ba, balle in bashi amsar maganganun da yake ji, har yayi alwala ya fita sallar asuba nima na idar da sallah ban tsaya jan carbi ba don kar ya dawo ya same ni na yiwo waje mota na nema shata zuwa gida don nasan Umma bata Legos.

Na iso gida wajen karfe goma, don haka kai tsaye sashin Ummana na nufa na kuma yi sa’a sanyin da ake yi yasa Baba maigadi ne kawai a waje, ina shiga sashin Umma ‘ya’yan yaya Junaidu na fara gani su uku, baban Umma, Zuwairiya da Halimatus-Sadiya cikin tafka-tafkan suwaitu suna wasan tseren kekuna, suna ganina suka nufo ni da gudu suna yi min oyoyo, nasa hannu na dauki Halima na karasa falon da ita Umma tana ciki tana zaune ita kadai na durkusa gabanta da nufin in gaisheta, sai dai ban iya cewa komai ba saboda hawayen da suka kama zuba daga idona, ban gama kukan ba sai ga yaya Almu ya shigo da alamar dama ya riga ni zuwa gidan, koma yana ganin shigowata ban fasa yin abin da ya kawo ni ba, na ce mata me nayi miki Umma da zaku hadu ke da Baba ku yanke min hukunci iri daya? In shi yafi sonshi dani kema za ki fi sonshi dani ne?

Daga ido tayi cikin natsuwa ta kalle ni ta ce min kiyi hakuri Adawiyya, babu wani wanda yafi son Babangida a kanki tsakanin ni da Alhaji dukkan ku ‘ya’ya ne, hukunci na adalci aka zartar a tsakaninku, ba zai yiwu babangida yayi ta zama dake ke kadai ba tare da lalurar dake gare ki, koda baki da wata lalura ma yana da yancin yin mata hudu don haka kiyi hakuri ki koma dakinki ki zauna mu rungumi kaddarar data same mu ta rashin haihuwa sai dai n….ban san yanda akayi ba jina kawai nayi na katse Umma ina ta fadin maganganu, bani da wata kaddara da zan runguma Umma, in ku kun yarda da cewar ba zan haihu ba toni ban taba yarda ba, ba kuma zaku tilasta ni in yarda ba, ba kuma zai yiwu ku fake da hakan ku taimaki yaya Almu a kaina ya cuce ni ba, ba zan yarda, ba ban yarda da cewar ni dashi daya ne a wurinki ba, kin fi sonshi dani na bar mishi ke, na barwa yaya Almu ke Umma, ki maida ni kawai in da kika je kika dauko uba…Ban samu karasawa ba na jini kife a kasa, saboda wani irin wawan marin da aka kife ni dashi, tsawon lokaci ina kife kafin na dago kaina na kalle su Umma tana zaune ta sunkuyar da kanta kasa yan yatsun hannunta take kallo. Shi kuwa yaya Almu ni ya zubawa ido cikin matsanancin bacin rai, abin da ya tabbatar min da cewar shi ne yayi min wannan dukan na tare jinin dake ci gaba da zuba daga hancina ta tafin hannuna, na sake kallon shi na ce mishi, ko zaka kashe ni ba zaka hanani fadin gaskiya ba, in ban da taje ta dauko ubana yazo nan ya haife ni me zai hada ni da ku? In ban da ta…kan in fadi abin da zan fada din yayi wuf ya cukume ni yayi waje dani yana fadin tunda kinyi hauka Rabi muje gida kiyi a can ba a gaban Umma zakiyi wannan rashin mutuncin ba.

Mun fito yana kokarin tura ni cikin motarshi saboda tuburewar da nayi, ba zan bishi ba sai ga Umma amarya ta fito daga wurinta tana ganin mu tayi mishi tsawa, menene haka? Ya juyo yana kallonta kan yayi magana ta sake cewa menene haka? Wane irin rashin hankali ne wannan? Cikin ladabi ya ce mata gida zan kaita Umma wani abu ya sanme ta baki ji maganganun da take gayawa Umma ba, ta ce mishi sake ta, ya sake ni na tsuguna a kasa inä kuka, ta ce mun tashi ki shiga ciki, nabi umarnin da ta bani ina shiga ta biyo bayana bata bar ni na zauna ba ta ce inje inyi wanka na fito na gyara jikina na sanya wata doguwar riga da na samu ta ajiye mun, na fito na same ta a falo tana zaune abin karyawa ta fara bani nasha ruwan zafi don abin da kawai naji zan 1ya sha kenan.

Ta zuba min ido tana kallona cikin natsuwa ta ce min, “Alhaji ne yake son mijinki yayi aure laifin Hajiya guda daya ne da taja ta tsaya kan lalle sai ya karbi wannan yarinyar da aka bashi, ni da naso ne ta fita cikin maganar ta barshi ya bijirewa wannan auren kamar yanda ya bijirewa saura da aka bashi ya ki karba, in yaso daga baya shi yaje ya nemarwa kanshi auren da kanshi tunda ita wannan yarinyar ma da aka bashi ai munafurci ne yasa aka yi hakan ina dalilin da za ace Alhaji duniya abi sannu ne zai bashi aure? Tun yaushe ne mu’amalla taja baya tsakaninshi da Alhaji? Lokacin ne na san na dago kai na kalli Umma amarya na ce Umma ‘yar gidan Hajiya Hairan kenan zai aura? Ta ce eh ita ce, nan da nan naji gumi yana feso min a jikina, saboda ganewar da nayi cewar da hannun Umma Karama cikin maganar auren don kuwa bata da wata Aminiyar da ta wuce Hajiya Hairan, haka nan saboda daukar zafi irin nata da taya Umma Karama kishi da take yi ko magana bata yi da Ummana, sai in Ummance ta gaishe ta, to wai ita ce zata baiwa yaya Almu aure, sannan ita Umma tana sane amma wai taja ta tsaya kan sai lalle yaya Almu ya karbi wannan auren cikin ladabi da natsuwa, na ce mata zan je mu tafi Umma kar yayi ta jirana, ta ce to kuje gida lafiya karki nemi wata magana ina amfanin wannan abin da yayi miki? Gashi ya kunbura miki gefen fuskarki babu kyan gani, ban ce mata komai ba nayi mata sallama na fito banga yaya Almu da motarshi ba, abin yayi min dadi nayi maza na kama hanyar fita gidan, ina fitowa sai gashi a bakin get yana zaune a bayan motar yana ganina ya diro yazo ya bude kofar motar ya ce min zo ki shiga kawai, girma da arziki kin dai san nan kofar gida ne, kafin Umma amarya ta kawo miki agaji kin riga kin ji jiki, ban yi musun shiga ba saboda nasan gaskiya ya fada.

Na shiga na zauna muka kama hanyar tafiya, na ce mishi dama ‘yar gidan Hajiya Hairan zaka aura? Bai kallen ba ya ce eh menene? Na ce ban yarda da auren ba ne tunda kai ma kasan munafurci ne yasa aka baka ita, in ma kaga kana son yin auren ne to na yarda kaje ka auri wata yarinyar amma ba ita ba, in dai har kana so in kayi a zauna lafiya.

Sai da ya galla min dan banzan harara kafin yaja wani irin uban tsaki ya ce in anyi ki hana zama lafiya, sakarya mara hankali, mara kunya, mara mutunci, wacce gata ya maida ita shashasha, a gabana kika zagi Umma? Har kina ce mata wai kin bar min ita? Kin taba jin ance miki takice? Sai da ya waiwayo ya kalle ni sannan ya ce min wai me kika dauki kanki ne ma tukuna? Ke kin dauka kin fini matsayi ne a wurinta? In ba ki sani ba in gaya miki, ni danta ne da ta shayar da nononta kinga kuwa tafi karfin in barwa wani ita na kuma fi karfin ace an bar min ita, dama tawa ce tare kika ganmu tare kuma zaki barmu, da cikin girma da arziki ne kika ce min in bar wannan yarinyar in nemi wata da kinyi mamakin adalcin da nayi miki, amma tunda kika gayawa uwata maganar banza akan idona to sai nayi aurcn inga iyakar tsiyar da kika iya.

Har muka isa gida ban daina kuka ba, ban kuma cewa yaya Almu komai ba saboda ban saba irin wadannan maganganun dashi ba, ban saba gayawa mijina bakar magana ba, gashi dai maganganu sai zuwa mun suke yi a zuciyata wadanda zan gaya mishi in rama abin da yake fada amma sanin da nayi in na fadi tawa maganar ba kwashewa kalau zanyi ba, zunubi za a rubuta min tukuicin gayawa miji bakar magana sai naja bakina nayi shiru, in na ga abin yayi yawa dai na kan rama a zuci amma ba da baki ba, tunda sai na furta da baki ne za a rubuta min zunubin.

Muna isa gida na samu Baba Talatu tana jiranmu don yaya Almu yayi mata bayani ina shiga dakina ta biyo ni’ tana fadin hakuri kawai zaki yi uwardakina, ni tausayin Hajiya ne ma ya fi kama ni nayi maza na ce mata tausayin Umma? Umma ai ita ce ta ce sai yaya Almu ya karbi auren cikin tausayawa ta ce waiyo to yaya za tayi?  Zata hana shi aure ne? Wannan kishiya indai kina da hankali ai ba ke za’a yiwa ita ba.

<< Wace Ce Ni? 33Wace Ce Ni? 35 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×