Skip to content
Part 35 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Hajiya Karama ce fa sanadin auren, sannan kice dake ake yi? Dogon bayanin da Baba Talatu tayi min shi ne ya fahimtar dani cewar lalle kishiyar da ake nufin yi min din ba karamin al’amari take nufi ba, sanin da Umma Karama tayi cewar ni din ba zan haihu ba shi yasa tayi kutun-kutun din da Aminiyarta tasa mijinta ya fake da tsohon zumuncin dake tsakaninshi da Baba ya ce ya baiwa yaya Almu auren yarshi don ita tazo ta haihu don itama ta samu wata dama akan yaya Almu ta haka ne take ganin zata iya karbarwa Umma shi.

Kishi mai tsanani ya kama ni da na tuna duk sanadin wannan abin rashin haihuwata ne, na tuna kalaman yaya Almu game da haihuwa na tuna kafin ya debe tsammani daga gare ni irin alkawuran da yake yi min daga ranar da kika yi min albishir da daukewar wannan fitinanniyar al’adar taki da duk wata sai tazo ta takura min Rabi ni kuma zanyi miki albishir da farin cikin da ba zai yanke miki ba, daya daga cikin kalamanshi na wancan lokacin kenan. Ashe ba ni ce zan yiwa yaya Almu wannan albishir din ba, na daga ido na kalli Baba Talatu na ce mata, zamana ne kawai yazo karshe ni da Yaya Almu, komai kuma yana da sanadinshi, ina fadin haka sai ta kama kuka tana rokona kar in yi haka, dama abin da ake son gani kenan, na ce ba komai Baba gara mun hakan ba zan iya zama da yaya Almu ina gani wata mata tazo ta haifar mishi ‘ya’ya ni bani da ko daya ba, yau in da ina da ko guda daya ne to da shi kenan sai in iya fuskantar kowace irin kishiya ce zata zo min, to amma bani da ko daya ba kuma zan haifa ba, yaya zanyi? Baba Talatu tayi kuka har ta gaji.

Rannan ina zaune akan gadona cikin dare ina rungume da filo akan cinyata na makalkale shi a kirjina da hannayena duka biyu, tunani kawai nake yi in saka wannan in kwance in saka wancan. Ina cikin wannan halin ne sai naga yaya Almu ya turo ko far da ta hada mu ya shigo yana sanye da doguwar jallabiya fara a jikinshi, matsowa yayi ya karbe filon yayi jifa dashi ya kuma sa hannu biyu ya sure ni ya nufi dakinshi dani kan gadonshi ya aJiye ni ya kuma zauna a gefena ya dora hannunshi kan cinyata yana magana cikin natsuwa, kwanakin nan duka bana bacci Rabi kar ki dauka ko ina jin dadin abubuwan da suke faruwa ne, bana ji ni dake bamu taba samun wani sabani ba a shekaru biyar din da muka yi in ban da wannan karon ban gaya miki maganganun da na gava miki don komai ba sai don ba zan iya hakuri dake akan batawa Umma ba, don haka kiyi hakuri ki kuma yafe min marin da nayi miki. A hankali cikin natsuwa na ce mishi na yafe ya ce to na gode, ya canzawa hannunshi wuri don bukatarshi ta ci gaba da sake taba ni, na ce mishi ka taba yi min alkawarin ba zaka taba son kanka a kaina ba, ya ce eh nayi ban manta ba, ba kuma zan saba ba, na ce to na roke ka yanda kake kokarin samun abin da kake so nima ka taimake ni in samu, ya ce me kike so in taimake ki akai? Na ce ka taimake ni kar ka sake taba ni ka kuma taimake ni ka nuna min zumunci ta hanyar kin marawa Umma da duk wani mutumin da zai nemi tilasta ni zama da kai baya tilasta ni zaman zai zamo kuntatawa a gare ni na kuma san ba za ka so in kuntata ba, cikin sanyin jiki ya ce min me kenan kike nufi? Na ce abin da nake nufi kenan zan tsaya kan maganata, da dama na taba gaya maka in kuma aka nemı tilasta ni zaman to zan iya daukar kowane irin matakı, to maimakon ayi haka kuma gara ayi komai cikin zumunci da mutuntawa juna rai. Bai sake ce min komai ba har gari ya waye, sai dai daga ni har shi babu wanda ya samu runtsawa.

Washe gari wurin taran safe naga wayar yaya Junaidu wai baba yana son ganina, don haka duk abin da nake ciki in bari inzo ni da yaya Almu, na ce to naje nayi shirina nayi kwalliya sosai ta yanda zan boye duk wata damuwa dake tare dani, don nasan zan samu Umma Karama a can. Kwalliyar da na dade ban yi ba nayi, na daura wani tsalelen leshi na kuma kawata kwalliyar da adon gold na yane jikina da gyale mahadin takalmina loeshoe da jakar da nake rike da ita wadanda suka yi matukar kara wa kwalliyar tawa kwarjini.

Ni da yaya Almu muka isa gidan kai tsaye falon Baba muka wuce inda muka same shi shi da Umma Karama da yaya Junaidu. Na sake kallon Baba cikin ladabi na sake gaishe shi sannan na ce mishi Baba ance kana son ganina, ya ce eh uwata mijinki ne yayi waya ya gaya min wata magana da yace wai a bakinki ta fito, kin kuma ce mishi za ki tabbatar da cewar kin tsaya akanta, shi ne nace bari in neme ki in ji kina da matsala ne game da auren nashi da har kike nema ki kawo mana wani sabani?

Na kalli Baba cikin natsuwa kamar in gaya mishi abin da ke raina sai kuma na tuna ba a gaban Umma Karama zan yi hakan ba, don haka sai na ce bani da wata matsala Baba, Baba ya dan ji dadin hakan da na fada ya ce to maganar da ya ce kin fada din fa? na ce baba wannan tsakanina dashi ne bai yi tsananin da zai kawo ta gabanka ba.

Baba yayi maza ya ce haka ne Uwata, na kuma yarda da cewar ke ba za ki so kiyi abin da zai tayar mana da hankali ni da Uwarki ba, don haka komai zaki yi kiyi shi cikin fahimta da sanin cewar babu wata mata da Lamido zai aura ta kaiki balle ta wuce ki a wurinshi, ke matarshi ce auren saurayi da budurwa, ke kanwarshi ce da ku ka girma daki daya, sannan shi din kanin mahaifiyarki ne, yanda kema ke da shi ku ka girma gaban Zuwaira haka shi da uwarki suka yi, bisa wadannan dalilai ne na kira ki in gaya miki cewar zanyi bakin ciki in har kika yi abin da Lamido ya cemin kina shirin yi ina kuma so in kara jaddada miki cewar girman Zuwaira a wurina yana da yawa, don kuwa babana bai bar min wasiya kan komai ba sai kan abu biyu, na farko in rike zumunci na biyu kuwa in rike mishi amanar Zuwaira, kar kiyi abin da zai kawo matsala tsakanina da ita tunda kin san tana sonki.”

Na sunkuyar da kaina kasa na ce Baba tana Son yaya Almu fiye dani….da sauri yaya Junaidu ya katse ni ta hanyar daka min tsawa, ke Adawiyya! dakata kai Junaidu, shima Baba ya dakatar dashi kyale uwata tayi min magana gaya min menene damuwa rki? Me Zuwaira tayi da ya nuna miki cewar tana yiwa wani irin son da take yi miki? Kin san su wanene suka haife ki? Kin san matsayinsu a wurin Zuwairah? Kin san Uwa? Kin san yanda take a gaban Zuwaira? Kin san Muttaka? Ko kinsan Zuwaira bata taba mu’amalla da wani nata ba sai a kanshi? Ko kin san har yau din nan shekaru kusan ashirin da rasuwarshi ni da ita ban taba yarda hirarshi ta hada mu ba? Kina nufin amincewar da tayi na Lamido yayi aure fifitashi tayi a kanki? Adalci ne kawai irin nata da irin wannan adalcin nata ne kuma dama ta zarcewa sauran mata, ita babu son zuciya a cikin al’amarinta yanda kike ‘ya haka Lamido yake haka Junaidu dukanku

ya’yanta ne dukanku kuna bukatar tayi muku adalci amma tunda har maganar tazo gabana to gaya min abin da kike so ni inyi, na daga ido cikin natsuwa nace mishi, bani da wata bukata baba bani da damuwa kan maganar auren nashi.

Baba ya ji dadin zancen nawa, ya ce yauwa Uwata maza kiyi koyi da halin uwarki ki zama jaruma mai yiwa kishiya adalci, ba don ita ba sai don mijinki cewar da zuwaira tayi Lamizo ya karbi auren da aka bashi tayi hakan ne don ta mutuntani, ni uban ‘ya’ya mata ne kin sani akan idonki nasha bayar da aurensu ba tare da na tuntubi wadanda zan baiwa din ba, in na zubawa mijinki ido kowacce aka bashi ya ce baya so saboda gudun bacin ranki, uwata in nima akayi min haka na bada kannenki aka  dawo mun da su aka ce ba a so ba za ki taya ni bakin ciki ba? Na ce zan tayaka Baba, ya ce tunda kuwa haka ne ai muma bai dace muyi ta maida na wasu ba ko kuwa na ce haka ne.

Tsawon lokaci Baba yana yi min kalamai na kwantar da hankali zuwa can sai ya ce min yanzu me zaki gaya min da zai kwantar min da hankali in san ba za ki yi abin da zai batawa Zuwaira ba, na kara sakin fuskata nace zan karbi auren yaya Almu da hannu bibbiyu baba zan kuma yiwa matar da zai aura irin abin da Umma tayi wa nata kishiyoyin. Da sauri Baba ya shiga sanya min albarka, ya kalli yaya Junaidu yace mishi kai Junaidu a gabanka nace na danka al’amarin auren Lamido a hannun uwata taje ta shirya duk wani abin da tasan ana yi tun daga kayan zane har na aure ta aike dashi sai ka shirya bata kudin hidimar da zata yi duk abin da ta nema a bata, yaya Junaidu ya ce to Baba, ya sake waiwayowa wurina ya ce min uwata kije ki shirya duk wani abin da ya dace in zaki yi kuma kar ki kalli Lamido ni za ki duba.

Na ce to Baba, ya sallame mu muka tashi muka fita na bar Umma Karama a zaune rai a bace, ga dukkan alamu ba abin da taso ji ba kenan, ina fitowa wurin Umma na na shiga na nemi wuri na zauna ina kallon hotonmu dake dakin ni da ita ne tun ban fi shekaru goma ba, cikin zuciyata kuwa tunani nake yi ya dai tabbata kenan yaya Almu zai yi aure tunda har gashi baba da kanshi ya danka al’amarin bukin a hannuna, ina cikin haka sai ga Yaya Almu ya shigo, nan zamu kwana ne ko gida zamu tafi? Na kalle shi cikin natsuwa na ce wanne yafi maka daidai? ya ce duk inda kika zaba duk daya ne Rabi, illa iyaka dai ina so ki zabar mana inda za mu fi sakewa tunda ni ban saba irin wannan abin da kike yi min ba, ban saba kina yi min rowar jikinki ba ki daina kinji Rabi? Ki bar ni inyi yanda na saba yi dake aike tawa ce Rabi kin kuma sha gaya min cewar komai naki nawa ne ke din mallakina ne har abada kuma ni kadai ne zan mallake ki, na daga ido kawai na kalli yaya Almu wani sabon kishin ya sake mamaye zuciyata, sai dai ban ce mishi komai ba har na kammala duk wani abin da zanyi nazo na hau gadon Umma na kwanta da shirin yin bacci sai gashi shima ya shigo gadon nata yazo zai hau, nayi maza na kalle shi na ce mishi gadon Umman zaka hau? Ya ce menene? Gadon uwata ne tunda kika hau ai nima kin san zan hau tunda Kin san na gaya miki wurin da zamu sake zaki kai mu, na sake kallonshi a natse nace mishi wai me kake nufi da sakewa ne? Ni fa ina nan akan maganata ba kuma zan canza ba, cikin kaduwa ya zuba min ido yana kallona, maganganun da kika yi a gaban Baba fa Rabi? Kina nufin yaudararshi kika yi? Kina nufin ba za kiyi mishi alfarmar da ya nema a wurinki ba na ki barshi ya zauna lafiya da matarshi?

Na daga ido na kalli yaya Almu na ce mishi nike rike da aurensu? Kafin namu auren ai nasu ya shekara arba’in suna yinshi kar kuma ka sake kai karata gaban Baba in kuwa ka sake yin hakan to zan tabbatar da cewar baka sake ganina ba nayi shiru na juya nayi kwanciyata. A haka muka dawo gida ni da yaya Almu abin babu dadi sai dai kuma bai bari wani-ya gane hakan ba balle aje ga kanwa gaban Baba, ni dashi dai abin ya ki dadi babu irin rarrashin da banyi min ba naki in sauko to ki bari mana sai anyi auren kinga anyi miki ba daidai ba in yaso duk matakin da zaki dauka sai ki dauka, maimakon kice daurin auren kawai yana nufin naki auren ya kare, ina alkawuran da muka tayiwa juna Rabi? Kina nufin don kana son matarka ta gida sai hakan ya hana ka karo wata? Shi Namiji fa mijin mata hudu ne an halatta mishi yin hakan sai wanda yasan ba zai ya adalci ba ne aka ce mishi ya zauna da guda daya, ni kuwa ai ba mara adalci ba ne balle ko kice kan haka ban cancanci zama da mata biyu ba, ban tanka mishi ba shiru kawai nayi yayi ya gama yaja bakinshi yayi shiru.

Kwana biyu bayan wannan maganar ina zaune a falona wajen karfe goma na safe tunda gari ya waye ban leka wurin yaya Almu ba balle inyi tunanin abin da zan shirya mishi don karyawa, zuwan Baba Talatu biyu tana tambayata ko za’a dama kunun gyada ne tunda taga yana so na ce mata a’a kyale shi kawai yana azumi ta ce to ta juya ta tafi ta kama aikinta, ina nan wurin a zaune cikin kwalliya sai dai kuma kwalliyar ce kawai amma can cikin zuciyata abin babau dadi, ina cikin tunanin abin da zai faru tsakanina da yaya Almu matukar bai je ya ce ya janye daga wannan auren na gulma da munafurci da ake shirin kullawa ba, sai kawai naga Hajiya Hauwa ta shigo cikin gidan babu wata wadatacciyar sallama ta kuma sha kwalliya cikin wata tsaleliyar atamfa da ta yiwa kanta wani irin dauri mai kama da rawani ta kuma turo shi gaban goshinta. Cikin zuciyata na ce kai Allah kadai yasan irin kwalliyar da Hajiya tayi sanda take cikin kuruciyarta, kas din da naji ya fito daga bakin Hajiya ne yasa na gane cingam take taunawa, nan da nan na shiga taitayina don kuwa na santa kamar yanda na san yunwar cikina, cikin sanyin jiki na ce mata sannu da zuwa Umma, yaushe ki ka dawo?

Ta zuba min ido tana kallona, ta ce ran Uwarki kinjini ko baki jini ba? Ungo nan, ta sake miko min dakuwa da hannayenta duka biyu tare da fadin ja’ira mara kunya marà hankali, mara wayo, sakarya wacce bata san ciwon kanta ba, haka kawai Zuwairah ta kyale ki kina shashanci tana kallonki tana nema ta barki sai kin ja mana abin kunya a gari, in baki bar gidan Mustapha ba yau to baki haifu da kyau ba, tana fadin haka naga ta yaye safcecen gyalenta ta ajiye ta cire dan kwalinta data bata lokaci wajen nadewa ta ajiye, gashin kanta ya bayyana wanda Yasha gyara cikin tsabta duk da furfura ta ratsa shi.

<< Wace Ce Ni? 34Wace Ce Ni? 36 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×