Skip to content
Part 36 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Ina cikin kallon wannan abin mamaki da ya soma tsoratani sai kawai naga Umma ta kama rigarta zata tubbe ni kam nan take na fashe da kuka yayin da ita kuma baba Talatu ta shiga bata hakuri kiyi hakuri Hajiya, kiyi hakuri taja ta tsaya tana kallon Baba Talatu cikin huci barni kawai in tube Talatu a gaban yarinyar nan yau don ta nuna min tabon da kishiya tayi min a jikina, wanda take tsoron ita kar tazo tayi mata shi, Baba Talatu ta shiga bada hakuri da ban baki kala-kala da kyar ta samu Umma ta hakura da tubewan ta maida rigarta har taja gyalenta ta rufo ko’ ina a jikinta ta gyara zama ta kalle ni ta ce min tunda kika san Zuwairah a rayuwarta kin taba saninta ita kadai a wurin mijinta? Nayi maza na ce mata a’a, ta ce ni a nawa gidan mu nawa ne? Na ce ku hudu, ta sake kallona a saninki guda nawa aka yi min? Na ce ban sani ba Umma, ta ce to goma sha uku goma sun tafi muna tare da uku kin taba zuwa gidan kin samu wata a zaune a kaina? Na ce mata a’a, ta ce to yan uwanki da akayi musu kishiyoyi kin taba jin anyi wata magana? Kin taba jin wata maganar a ta fito bakinsu? Na girgiza kaina cikin zuciyaia kuwa ina tuna gaba daya ya’yanta mata amare ne da su, na ce kin taba jin su suna irin sakarcin da kike yi? Na ce a’a kan in gama rufe bakina sai kawai tayi caraf ta rike min shi da iyakacin karfinta tana fadin sai naki bakin ne baya iya yin shiru saboda ba a gasa miki shi da kyau ba? Na shiga fadin uh’un cikin zafi da kokarin kwatar kaina daga hannunta sai dai nakasa sa’boda irin rikon da tayiwa bakin nawa Baba Talatu ta sake shiga wani sabon ban bakin da ba da hakuri, ita kuwa Umma ko a jikinta sai fadi take yi bárni da ita kawai Talatu ai wannan laifin na Zuwaira ne data zuba mata ido tana yin abin da taga dama bata sanar dani ba, ai da tuni nayi maganin rashin hankalinta, da kyar na samu ta sake ni a dalilin jinin da taga yana bin yan yatsunta ina ganin haka na kama kuka, ita kuwa ko a jikinta, sai fadi take yi Lailatu za ki barwa mijinki? Karama da Aininiyarta sunyi nasara kenan akan Zuwairah?

Baba Talatu tayi maza ta ce ai fa kam nima abin da ya fi kona min rai kenan, Umma ta ce barta kawai ai mun gamu da ita jiya a wurin wani buki muka gaisa ta ce min ashe kuma Lamido biki yazo? Na ce mata ch, ai kinyi kokari da kika yi hakan gara ke da Zuwairah ku sake haduwa a gidan Mustapha don wannan kishin naku na gidan Alhaji Bello ya tsufa gara ku sake sabunta shi.

Nayi maza na katse kukan da nake yi saboda umarnin da Umma ta bani na in hanzarta kawo mata abin karyawa sai dai Baba Talatu bata bari nayi hakan ba, ta karbe ni ta hanyar shiga kicin don ta shirya mata, tana baria dakin ta sake kallona ta ce min duk abin da kuke ciki ke da mijinki ya gaya min, ina so kici gaba da yin hakan ba zan ce miki ki daina ba, in kinga dama ki shirya kayan aure ki jagoranci hidimar da za’ayi don ki mutunta kanki kamar yanda Alhaji Bello ya mutunta ki ya danka lamarin a hannunki in kuwa ba ki ga dama ba ki bari biki sai za’a yi shi don Zuwairah ta tabbatar mun da cewar zata tsaya wajen ganin Lamido yayi wannan auren don tana son ganin Karama tavi amfani da Lailatun wajen samun abin da take nema wurin Lamido ko ubanshi, ita kam Zuwairah ai bata da matsala, jaruma ce bata taba sai wa makiyi damar da yayi mata dariya ba, sai dai in ke kika ja mata hakan.

Yaya Almu yayi sallama ya shigo ya nemi wuri ya zauna a kasa yana gaisheta cikin girmamawa, ita kuwa sai ta amsa mishi cikin natsuwa da sakin fuska da suka gama gaisawa sai ya sake rage murya ya ce mata Umma na kasa yin shiru ne kan abin da Rabi take yi min saboda bana son azo a same mu a haka, ta ce eh to in ta gane abin da ake nufi ta gyara ai shi kenan in kuwa bata gyara ba ba kowa ta wulakanta ba sai iyayenku, in kuwa bamu da mutunci a wurinta ai sai kawai ka zuba mata ko.

Rannan da daddare yaya Almu yana dakina dan dole na sallama mishi komai nawa yayi yanda yaso dani, kasancewar kuma na janye wunina daga gare shi na tsawon lokaci hakan ya jawo al’amari mai tsanani a tsakaninmu ina kwance daga gefe ina kallon shi yayin da shi kuma yake ta bacci saboda tsananin gajiya, kishi mai tsanani ya sake mamaye zuciyata yaya zanyi in yi hakurin mallakar yaya Almu tare da wata mace? Yaya zanyi in iya zuba mishi ido yana yi mata irin abubuwan da na san yana yi min in mun kebe? Lokaci mai tsawo ina cikin wannan tunanin kafin lokacin da zuciyatata tabbatar min da cewar dole ne in koyi jarumtakar kaina don ba zai yiwu in barwa Lailatu yaya Almu ba tunda hakan yana nufin Umma Karama tayi nasara kan Ummana kenan ba zan iya barin Umma ta tozarta gaban makiyanta ba, don haka dole ne in bi umarnin da Hajiya Hauwa ta bani na komawa kan al’amuran gidana da kuma mijina.

Washe gari da safe na tashi bisa tsarin da na saba, na kama hidimar gidana da sassafe ina cikin kicin wajen misalin tara na safe yaya Almu ya shigo kicin din sanye da doguwar jallabiya a jikinshi ga dukkan alamu murna ganina a kicin din yake yi, me kike shirya mana ne? Ban kalle shi ba na ce mishi waina ce da miya ga kuma kunun gyada, ya ce to kin kyauta Rabi, kamar kin san cewar da yunwa na tashi da safen nan.

Daga yaya Almu har Baba Talatu ji dani suka rinka yi suna ina aka saka dani saboda  ganin da suka yi na wastsake daga matakin da na dauka na kwana da kwanaki.

Ina sallamar yaya Almu da ya shirya ya fita sai na yiwa yaya Junaidu waya na shaida mishi cewar ina bukatar ya turo min kudi don in fara sayayyar da Baba ya ce inyi, tsawon lokaci yana yi min nasiha da maganganu masu kwantar da hankali kafin ya tambaye ni abin đa zai bani, na ce mishi ba zan iya sani ba sai dai kawai yanda ya kama ina kuma so a bani Anti Rahma don ta taya ni, ya ce to babu laifi.

Anti Rahma baro gidanta tayi a zo Kaduna ta zauna tsawon kwanaki hudu sai da muka gama hada komai na kayan kamu da na aure ta kuma jagoranci wadanda ta gayyató suka rakata suka je suka kai kayan sannan ta kama hanya ta koma gidanta.

An kai kayan washe gari da sašsafe ina tare da yaya Almu a dakinshi baba ya bugo min waya albarka yake ta sanya min kan labarin da aka bashi na irin kayan da na hada na aike dasu yayi min addu’o’i masu dadi ya kuma roke ni in zamewa yaya Aimu kamar yanda Ummana ta zame mishi na ce to Baba.

Shirin biki sosai na shiga don kuwa nasan biki za’ayi irin ‘ya’yan gata yaya Almu ta bangarenshi ba sai na tsaya ina wani dogon bayani ba, to itama Lailatu ta bangarenta ‘yar gata ce kwarai, mahaifiyarta ce uwargida a gidansu tana kuma yin yanda taso don kuwa amare dai-dai har bakwai akayi mata amma babu ko daya duk sun fita wadanda suka san sirrin gidan kuma sun ce Hajiya Hairan ce mai korar su don kuwa ‘ya’yan da suke bari a gidan masu aikin gidan sun fi su ‘yanci. Lailatu ce ‘ya mace babba a wurin iyayenta a gabanta kuma akwai maza biyar, don haka ni da kaina nasan da gatanta to amma na hakura na yarda da zuwan nata na kuma shirya zama da ita zan kuma yi duk abin da zanyi don ganin bukatar wadanda suke shirin kawo ta bata biya ba, duk kuwa da na san Lailatu zata iya zuwa gidan ta haifi dan da ake bukatar samu in na tuna wannan shi ne abin da ya kan daki zuciyata har in kasa daurewa in hana idanuwana zubar da hawaye, to amma yaya zanyi? In da don tani ne da tafiyata kawai zanyi in yi nesa dasu ta yadda zan kare kaina daga ganin bakin. Cike da bacin rai, to amma Umma tana son ci gaba da zamana a gidan ta jaddada min cewar tana son ganin Lailatu ta shigo ta same ni ta daukarwa Karama abin da take son dauka a gidan ina nan cikin shirin biki na sosai har ana saura kwana bakwai ayi bikin rannan da hantsi sai ga Ummana tare da da Hajiya Hauwa sun iso gidan da hannu biyu na karbe su cikin murna da farin ciki sai dai abin da na gani a tare da Umma ne ya daga mun hankali ya kuma tayar mun da hankali cikin hawaye na kalle ta ina kuka na ce Umma ramewa kika yi? Maganar auren yaya Almu ne ya tayar miki da hankali haka? Umma ai zan haihu kar kiji tsoron komai babu wani wanda zai karbe miki danki daga gare ki zan kuma yi duk abin da zanyi wajen ganin na tsare…..Ban karasa ba Umma ta katse ni wajen cewa kiyi bakin ciki don kinga ta samu rabu kowa yana rayuwa ne kan kaddarar da aka shirya mishi.

Kwana biyu da tafiyarsu Umma ta aiko aka zo aka kwashe duk wani abin da yake cikin gidan aka maida sababbi daga sashina zuwa na yaya Almu babu abin da bata canza ba, Baba ma ya aiko mun da mota sabuwa dal, Umma amarya ma tayi min aike na wasu warawarai da zobuna wai inyi adon biki gashi dama duk sayaiyar da muka yiwa amarya bibiyu Anti Rahma ta sani nayi komai dai ina dashi kenan ga yaya Almu wanda ya tasa ni a gaba da tambaya duk da da ya bani ke hidimar auren nan ba ai ya kamata ki gaya min me kike so in yi miki na fadan amarya? Na ce mishi babu komai ai su Baba sunyi ya kuma wadatar duk da haka sa da yayi min kyautar wasu sarkoki guda biyu, abin dai gwanin sha’awa kamar ace bani da wata matsala amma ina? A duk lokacin da na kalli tarin dukiyar da aka tara min a dalilin auren sai inga ai ba abin da ake nema ba kenan da kamar kawo ta za’ayi don ta kamu wani abu wurin yaya Almu to da sai in ce ta makara don na rigata samu, to amma ba haka ba ne da ake nema a wurin ta babu mamaki kuma tana zuwa ta samu tunda Likitoci da yawa sun tabbatar min da cewar ni ke da matsalar da ta hana samun haihuwa tsakanina da mijina wannan shine abin da ya fi komai dukan zuciyata.

Tun ana saura kwana biyu bikin gidan ya cika da mutane ‘ya’yan kawayen Umma na kusa da na nesa babu wacce bata zo ba.

Biki sosai Umma ta shirya ta kuma tsaya matsayinta ita ce uwar yaya Almu komai ita ke yi duk abin da ake nema ita ce mai bayarwa.

Biki na kasaita akayi ta kowane bangare komai yaji nima anawa bangaren kawayen Umma ake waye dani suke ‘ya’yansu ga matan abokan yaya Almu da muke ma’amalla mai dadi wadanda suka yi matukar nuna min kauna da kulawa ga yan uwa su Anti Basira da su Anti Kubra, Anti Aina’u, Anti Rahma kam babu abin da zan ce mata ko da yake ban yi mamaki ba saboda irin tsayuwar yaya Junaidu kan al’amarina. Ranar daurin auren wuni yayi yana yi min waya yana tambayata babu dai matsala ko? In ce mishi a’a babu damuwa sai ya ce to kiyi hakuri ki kara akan wanda nasan kina dashi, in ce mishi to anyi daurin aure yaya Almu ya zama ango, anyi shagalin biki na halarci duk liyafofin da aka shirya na kuma yi duk abin da ya dace inyi wadanda basu san Lailatu ba sai a wannan lokacin sunyi ta gaya min cewar ai babu abin da zata nuna miki sai farar fata, bata kaiki kyau ba bata kaiki tsayuwa ba bata kaiki iya kwalliya ba, da kuma yin kyau da kwalliyar aike mai kyau ce Adawiyyah dolen miji ya soki ko don irin abin da aka kyautata miki halittar ki dashi, nayi murmush1 kawai na kalli Naja’atu yar Hajiya Hauwa da muke kai daya da ita na ce mata Naja, ba kyau yaya AImu yake nema ba wurin mace ko iya kwalliya haihuwa yake so ita yake nema in har ya same ta to bana zaton zai tsaya kallon wadannan abubuwa da kika lissafa tayi maza ta ce to ai kema zaki haihu lokaci ne kawai na ce mata abin da nake ta karfafa zuciyata dashi kenan to amma yau kam na karaya zuciyata kuma ta gama tsinkewa da al’amarin na kama yi mata kuka. Da sauri ta dafa kafadata tana ta faman gaya min maganganu masu kwantar da hankali tana fadin ba fa Likita ke bada haihuwa ba Adawiyyah tsaya kawai kan yin addu’a.

A gida anyi wunin biki cikin shagali mai yawan gaske da gude-gude daga bangaren dangin amarya a nawa bangaren ma ina cikin hayyacina da natsuwata kallon, komai nake yi don tun kafin a watse a barin da Lailatu na riga na gane lalle anyi mun ki shiya na kuma yarda cewar Umma Karama tana da dalilinta na jin sanadin auren yaya Almu da wannan yarinyar, duk abin da ke faruwa dai ban cewa kowa komai ba, jan bakina kawai nayi na tsuke ina kallon komai da idona, zuciyata kuma tana yi mishi irin fassarar da ta dace dashi, nayi kwalliya a bikin kwalliya kuwa irin ta burgewa irin wacce zata shaidawa Lailatu da duk wani nata duk abin da take takama dashi na gata to bata kama nawa kafar ba, don kuwa yadda na rinka canza zannuwa haka na rinka canza gold din da nake sanyawa, tsawon kwanakin bikin kuma ban fasa zuwa wurin mijina ba don kuwa abin da ya nemi inyi mishi kenan.

Ranar budan kai da yamma iyayen amarya suka kawo ta falona da yamma kamar dai yadda al’ada take na kaiwa uwargida Amaryarta don bada amana sai dai kuma su da suka zo cewa sukan yi to ga amarya nan min kawo ta gidan mijinta ta kuma zo ne don ta zauna ba wai ta leko ba ne zata koma.

Hajiya Hauwa ta kalli kanwar uwartata mai wannan bayani tayi murmushi ta ce Hajiya joda kenan ai mu bamu za’a kawowa amarya ayiwa wannan jawabi ba, mu kam ai an sanmu da barin kishiya ta zauna matukar zata iya zuba ido tayi hakuri kin kuma san ance kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi, don haka in har kun kwabi ‘yarku kunyi mata tarbiya to ni kuwa ina tabbatar miki da cewar zata zauna in har zata iya gani ta kyale, ana gama wannan bayani ta sake balla bakin jakarta sai da ta sake jefa wani cingam din a bakinta sannan ta zaro daurin naira dari biyar-biyar ta mika musu ta ce Adawiyya ta sayi bakin amarya suka tashi suka tafi.

<< Wace Ce Ni? 35Wace Ce Ni? 37 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×