Skip to content
Part 37 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Yamma nayi yan uwa da abokan arziki suka soma yin sallama suna tafiya gida da fahimtar juna in ce amin, ta bangaren amarya kuwa duk wacce zata tafi sai ta fito tsakar gida sai ta daga murya ta ce to mu zamu tafi kan badi kuma muna sauraron a kira mu suna don ba mun kawo ki ba ne kawai don ki rinka ci kina juyewa a masai mun kawo mishi ke ne don ki cika mishi gida da ‘ya’ya tunda haihuwa kam ai kin gaje ta sai kuma akwashe da dariya a tafa hannu kafin a rangada wata irin matsiyaciyar guda.

Suma su Hajiya Hauwa da Hajiya Furera suka yi shirin tafiya kan su tafi kuwa sai da Hajiya Hauwa ta ta cafke kunnena ta rike tana fadin bari ni da kaina in kara jaddada miki cewar kwana bakwai ango yake yi a dakin amaryarshi budurwa don haka kar in ji kar in gani, nayi murmushi kawai na ce mata to Umma ku gaida gida, Allah ya kara girma suka ce amin suka kuma fita da kwarin gwiwa saboda ganin irin sallamar da muka yi.

Gaba daya an gama tafiya daga ni sai Baba Talatu da ta gama gyara min wajena muna zaune ne tana matsa min kafafuwana tare da jaddada min irin kokarin da take cewa wai nayi. Na daga ido na kalle ta cikin natsuwa na ce mata shi kenan Baba yau burin yaya Almu ya cika ya maidani uwargida a gidanshi.

Tayi maza ta ce babu komai dama abin da ya dace dake kenan, kiyi shugabanci ki jagoranci iyalin gidanshi baki ga kuma yanda hakan ya kera miki kwarjini fa kika ce Baba? Zubewar da nayi fa’? Ta ce ai bai baiyana kowa ya gane ba saboda ke dama jikinki mulmulallen jiki ne gashi kuma kin kame babu alamar wata damuwa a tare dake. Shigowar yaya Almu ta katse hirar tamu, tayi mishi murnar tashin taron lafiya kamar yanda nima nayi mishi sannan ta tashi ta tafi wurinta.

A natse yaya Almu ya kalle ni ya ce mun nasan a gajiye kike to amma kuma yaya zanyi?

Nayi maza na ce mishi me ya faru? Ya ce matsananciyar yunwa nake ji.

Cikin hanzari na mike na shiga kicin don shirya mishi abin da zai ci meat roll ga abubuwan da nayi amfani dasu.

(1) Naman cinyar baya na yanka sa

(2) Albasa guda uku

(3) Mangyada ko Butter,

(4) Murmushen Biredi

(5) Kwai guda daya

(6) Tumatur manya guda hudu

(7) Maggi

(8) Karas

(9) Green beans

(10) Kayan kamshi

Na fara da yin amfani da wuka mai kaifi na rinka yiwa naman nan yankan faifai tanfar dai irin na masu tsire sai dai wannan yafi na maitsire fadi tsayi da kuma kauri, sannan na dora pan a kan wuta na soya butter da albasar da na riga naa yanyanka kanana na kawo sauran kayaiyakin nan amma banda karas da green, beans na zuba, sannan na koma murza naman nan akan rolling boad da kwalba har sai da na ga yayi fale-fale sai kuma na soma debo kayan cikin pan din nan wato su murmushen biredin nan da maggi da albasa chese da na hada da butter ina shafe fallen naman na gaba da baya ina ajiyewa har sai da na gama da su duka sannan na koma na nade su kamar tabarma ina jefawa cikin ruwan buttern da na dora yayi zafi akan wuta na kuma zuba albasa har na gama soye shi tas sai da yayi jajajaja sannan na zuba tumatur da kavan kamshi a ciki na kuma zuba ruwa kadan na rufe tukunyar ya dahu sosai, sai na kawo plate masu kyau na shirya yankakken karas din nan da green beans a ciki sannan na tsamo roll din naman nan na jera su akai romon kuwa sai da yayi kauri tukuna shima sai na juye cikin plate din wato kan roll din naman. Sai kuma abin shan da na shirya mishi, ga abubuwan da nayi amfani da su.

1. Tanjarine guda takwas (8)

2. Sugar

3. garine captard cokali daya

4. Madarar gongoni guda daya

5. Madarar shanu rabin kofi..

Na kammala komai cikin natsuwa na dauko shi akan tire nazo da shi falona in da na bar yaya Almu na same shi kishingide har bacci ya soma daukarshi, saboda tsananin gajiya cikin natsuwa na tashe shi na ce mishi ga abincin an kawo ya mike zaune cikin yanayin gajiya da wahalar da yayi, ya kalli abincin cikin sha’awa da farin ciki yayi min godiya tare da addu’o’i masu dadin ji har ya mika hannu zai fara ci sai na ce mishi a’a ango muje dai can sabon masaukin naka babu mamaki itama amaryar tana tare da yunwar yayi maza ya mike cikin jin dadin maganar da nayi yana fadin, gaskiya ne Rabi, lalle kuma na yarda uwargida ta sosai kike shirin zama.

Na bi bayan Yaya Almu da tiren abincin a hannuna naje zan shiga dakin sai naji Lailatu tana magana cikin shisshikar kuka giurkina ne fa yau amma kaje ka mike a dakinta har kana yin bacci, gabana ya yanke ya fadi da jin ana yiwa yaya Almu togaciya da kashedin zaman shi a dakina, karo na farko kenan da aka taba yin hakan a rayuwarmu.

Sallama sosai nayi kafin aka iya amsawa har nayi kamar in juya da tiren dake hannuna, sai kuma na fasa nayi ta jira dai har na samu aka bani izinin shiga ita kam fuskarta a daure babu alamar wasa shi ne dai yake ta kokarin murmushi da jawo hankula wuri daya don ya daidaita al’amura.

Na kalle su nayi murmushi na ce amarya sauko daga nan don kiji dadin ci ban jira amsawarta ba na juya na koma dakina inda na samu Baba Talatu tana jirana, to ke kin kai musu abinci kin dawo kin hau gado kin kwanta ke ba za ki ci komai ba ne? Na ce ba na jin yunwa Baba cikina a cunkushe yake ban ci komai ba tun safe in ban da ruwan sanyi da nayi tasha amma kuma har yanzu ban ji kamar ina bukatar ci ba fatana dai kawai bai wuce in samu in yi bacci ba.

Baba Talatu ta kara matsowa kusa dani tana yi min tausa tare da fadin uhun ai namiji da kike kallonshi kyale shi kawai ya kamata kiyi in har kika ce zaki biye mishi to sai yayi dalilin da zaki rinka tafiya kan hanya kina sanbatu, baki san lokacin da kika yi hakan ba mutanen gari kuma maimakon su tausaya miki sai suce dama aka hada su bada ke ba? Tunda in kishiya ce ai ba a kanki aka fara yinta ba, ai ni nan da kike kallona ni na san kishiya tunda dai ita ce tayi dalilin da na hakura da zaman aure tun a shekaruna na kuruciya ta raba ni da mijina, bayan kuma ina sonshi kamar inyi yaya?

Cikin sauri na zubawa Baba Talatu ido ina mata kallo na ban mamaki da kaduwa na ce amma baki taba sanya wannan labarin cikin jerin labaran da kiká yi ta bani ba, taja wata irin ajiyar zuciya mai karfin gaske ta ce uhun to wannan labari in ba dalili yayi dalili ba me zai sa kayi ta bai wa yara shi? Kamar yau din nan dai da hali ya kama ai kinga zan gaya miki komai, na kasa kunnuwwa na saki baki na zare ido ina sauraron labarin da Baba Talatu take shirin ba ni, sai kawai na jiwo ihun Lailatu daga tsakar gida tana kiran taimako, da iyakacin karfinta take fadin waiyo ta shiga uku waiyo za’a kashe ta, sanin da nayi na baro dakin tana kunkumin girkinta na yaya Almu yazo ya zauna a nawa dakin sai nayi nmaza na zabura zan kai mata taimako ga zatona maganar ce tayi tsanani har yaya Almu ya tunzura ya rufe ta da duka, sai naga Baba Talatu tayi wuf ta cafo ni ta maida ni kan gado ta danne da hannayenta duka biyu cikin haki saboda zafin naman da ta gwada wajen kamo nin, take tambayata, ina zaki haka da saurinki kamar kin ji ana neman ki, na kalli Baba cikin damuwa na ce yaya Almu zanje in bai wa hakuri ya kyale yarinyar nan kar ya ce zai biye mata.

Baba Talatu ta zuba min ido cikin takaici tace, lalle ke kam da sauranki to ina ruwanki ina ganin ki da abin da suke yi? Ko kuwa wane karanbani ne zai kai ki ba da hakuri don kin ji ana kama hannun kishiyarki? Da sauri ciki wani irin mummunan faduwar gaban da ban taba jin irin shi ba na kalli Baba Talatu a firgice na ce mata kama hannu? A hankali cikin natsuwa ta ce min eh mana wannan ihu ai yai kama da ihun shakiyanci da amare keyi yayin kama hannunsu, ban sake tankawa Baba Talatu zancen ta ba a hankali cikin karaya na maida kaina kan filo na kwantar yayin da wasu zafafan hawaye da suka fi kama da hawayen kishi suka yi ta zubowa daga idanuna cikin zuciyata kuwa sai fadi nake yi ka cuce ni yaya Almu, ka cuce ni..”

Mu gamu a littafi na hudu don mu ji yadda za’a kwashe tsakanin Rabi’atul Adawiyyah da wannan kishiya tata.

Littafin ya fito tare da na ukun, don haka a neme shi a karasa shan labarin.

Na gode,

Taku, Hafsat C, Sodangi.

<< Wace Ce Ni? 36Wace Ce Ni? 38 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×