Skip to content
Part 4 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Washe gari kuwa da safe sai na ji shigowar Yaya Almu wurin Umma. Bayan sun gaisa sai ya ce mata,

“Umma da za ki amince da sai yan matan gidan nan su karbi aikin abincin daga hannun Baba Maigyada ita ta zama tana sa musu ido ne kawai, amma ba ta rinka yi ba.”

Umma ta dan jinjina lamarin kafin ta ce mishi, “Abincin baya dadi ne?” Ya ce, ‘A’a Umma mun dai gaji da cin natan ne.

To kawai ita ma ta dan huta ai ta girma tun muna yara fa muke cin abincinta.”

Umma ta yi murmushi ta ce, “Za ku gaji da komai ma yanzu ai Alhajin ya rike ku da yawaa a gidan nan bai taba rike samari haka ba ko Kabiru da ya gama karatu baya bayan ku yafi shekara da kama aikin shi rannan ma sai da na ce mishi ni me yake jira da ku ne haka?”

Ganin da ta yi Yaya Almu bai amsa maganar tata ba ya sa ta gane kunya yake ji, ta ce mishi, “In kun ga hakan zai gamsar da ku sai ka yi.”

Ya yi mata godiya kafin ya ce mata,”To Umma tun da su Kubura dukkansu suna zuwa karatu ita Rabi ce har yanzu ba a samar mata wata makarantar ba, saboda matsalar jarrabwarta, ina ganin sai su rinka yi daga Monday zuwa Juma’a na dare kawai ban da na rana, ita sai ta rinka yin na Asabar da Lahadi na rana da na dare.”

 Ina zaune ina sauraron jin abin da Umma za ta fadi akan wannan mummunan hukunci na Yaya Almu. Sai kawai na ji ta ta ce mishi, “To.”

Haba ai ban san lokacin da na kurma musu ihu ba, na shiga birgima ina cewa,

Gaskiya na gaji na gaji da ‘yan ubancin da Yaya Almu yake nuna mini, na gaji da takurar da yake yi mini.

Na gaji da tsanata da ya yi ta sani a gaba ya hana ni sakat, ni da gidan ubana ni ina cikin ‘yan matan gidan nan ne da zai yi kason girki har da ni? Gaskiya ni Umma ni ki karban mini.

Ban karasa maganar ba na ga ta zabura ta sunkuto wani murfin tangaran da ke gefenta wai shi za ta rotsa mini. Yaya Almu ya yi maza ya tare ta yana fadin;

“Ki yi hakuri Umma in na bar ki kika rotsa mata wannan a gabana ai sai yan ubancin na mu ya kara bayyana.”

Bayan fitar Yaya Almu Umma ko kallona ba ta sake yi ba sai dai na ji ta tana ta rokon min shiriya alamar dai ranta ya kai matuka wajen baci kenan da abin da na yi. Ni kuwa ko a jikina, saboda na samu na dan gayawa Yaya Almu abin da ya dade yana cina a rai, shi ne yan ubanci ke sawa yana takurawa rayuwa ta, yana bakin cikin ganina cikin walwala.

Fuskarta a daure ta kalleni ta nuna mini bokitin da ta shake da damammiyar fura ta ce mini, “Dauki ki kai wa su Babangida.”

Hada fuskar da ta yi ne ya sani daukan bokitin, amma in ban da haka da na ce mata gaskiya Umma aiki wani ya kai musu.

Daga nesa na hange shi a kan bayan motar shi yana zaune a gindin bishiya baba maigadi ne á gefen shi a tsaye suna yin hira, na matsa wurin na ce mishi;

“Ga damammniyar fura mai sanyi Umma ta ce in kawo muku.”

Ya kalleni cikin nutsuwa ya ce, “Kai wa su Zubairu suna dakin su sai ki zo.”

Na je na kai musu na dawo na samu ya sauka daga kan motar yana cikinta har ya tayar da ita shi ma baba maigadi ya tafi ina ce mishi gani ya ce mini shigo mu je in kai ki wani wuri ladan rashin kunyer da kika yi mini.

Ban yi musu ba don kuwa ni in har akwai abin da ba ni musun shi to fita yawo ne a zaga gari.

“Me kike so yau a sai miki?”

Na yi maza na ce mishi, “Oho.” Ya ce, “Uh kin san ni yanzu lallabaki zan rinka yi tun da kin

gane ‘yan ubanci ne ya sa nake yi miki abin da na ke yi miki na takura, na tsane ki na takura miki, na tasaki a gaba abin da kika fada kenan, ni kuma a wurina ban taba tsanar ki ba, ban taba takura miki ba, balle in kai ga saki a gaba ni in kika bar nima a wautata sai in ce miki ko Umma ba ta fini sonki ba, sai dai nina bambanta son da nake yi miki da irin wanda ita take yi miki, ita taná yi miki so ne irin wanda babu kwaba a cikin shi, ba ta iya bude ido ta kalle laifin ki, balle ta ga kuskurenki, ta yi miki gyara ita komai kika yi a wurinta daidai ne, saboda ba ta son bacin ranki, ba ta so ki wahala, farin cikin ki kawai take son gani, saboda tana so ta jiyar da ke dadi ko da kuwa me hakan yake nufi in ba kya son abu to komai alherin shi sai ta taya ki kin shi.”

Ya dan waiwayo ya dan kalleni a hankali cikin sakin fuska ya ce, “Soyayyar sangartarwa kenan Rabi, idan na taya Umma muka yi miki irin wannan son dukkan mu to ni da ke ne za mu cutu, don ke kan ki ba za ki ji dadin kan ki ba, ni kuma sai a bar ni da wahalar ki. Wannan dalili ne ya sa na bambanta nawa son da nata.

Ma fi girman yan ubancin da na yi miki dai na san bai wuce raba ki da ita da na yi na kai ki makaranta ba, inda za ki je ki yi wa kan ki komai, ki zauna da mutanen da ba ‘yan’uwanki ba ne, balle su saurara miki. Ki yi mu’amalla da mutanen da suke son ki da wadanda ba sa son ki, maimakon zaman ki na gida da kowa gudun bacin ranki yake yi.

Abin da kika ga dama kuma shi za a yi wannan dai na san shi ne babban ‘yan ubancin nawa ko akwai wani da ya fi shi?”

Ban tanka mishi ba sai ya ce, “To in ba ki sani ba ni bukatata ta biya kan abin da na yi na kai ki makarantar ne don ki je ki yi mu’amalla da jama’a kin yi don ki koyi ki wa kan ki hidima, kin koya, da kin tsaya kin yi karatu to da kin jefi tsuntsu biyu ne da dutse daya, ina nufin kin yi mini nawa kin kuma yi wa kan ki karatu da ba ki yi ba kuma wannan ko a jikina don ni fitowar ki da credit biyu bai shafen ba, na dai ji miki takaici ne kawai a a ce kin shekara shida kina karatu kin fito da credit biyu.”

Raina ya kara baci da yaeda Yaya Almu yake cire mini B3 din da na samu sai credit biyun kawai yake ambata.

Wani babban shagon kayan kwalliya ya kai ni ya ce, “Shiga ki zabo abin da kike so dan ni yanzu zan kara ka fa-kaffa da ke ne, don kar ki sake cewa ina yi miki ‘yan ubanci, duk abin da kika ce yan ubanci ne ya sa na yi, to ba żan sake, shi ba.”

Wadannan kalaman na Yaya Aimu ba su sa ya cire ni cikin masu girkin gidan mu ba, kamar yadda na yi zato, tunda ya ce ya daina duk wan abin da zan ce ‘yan ubanci ne.

Ranar da girkin ya iso kaina har dakin Umma ya biyo ni da bulalarshi ta dorina a hannun shi ya ce mini; “Rufin asirin ki kawai shi ne ki fito ki yi girkin nan in kuwa ba haka ba to sai na tara yara kanana, sannan in yi miki dukan tsiya a gaban su.

Ya juya ya tafi, sanin halin shi da na yi ya sa ban bata lokaci ba na fito cikin zuciyata dai sai fadi nake yi,

“Ba ka dai yi sa’a ba, tun da ba kai kadai baba ya haifa ba.”

Na kama aikin girki duk ranar da ya zo kaina sai kawai in kwaba shi yadda na ga dama, ni kaina ba na iya cin abin da nake girkawan, balle kuma sauran jama’ar da ake yi wa.

Yara sun rinka zirga- zirga da kofunan gari kenan ko kuma in sun hango Yaya Junaidu su ruga wurin shi suna tambayar ko akwai indome a store a ba su.

Wani lokaci yaba su indome, wani lokaci ya raba musu biredi ya ce su je su sha tea, wani lokacin garin rogo.

Rannan ina zaunc a dakin Umma da safe ina shan kunun gyada da Umma amarya ta aiko mini da shi, sai ga Yaya Almu ya shigo. Sa hannu ya yi ya karbe kofin da ke hannuna ya dangwarar ya ce mini,

“Wuce mo je.”

Na tashi sum-sum na bishi. Wurin wankc wanke ya kai ni. Duron guda aka shake da abincin da na yi jiya na rana da na dare aka kasa ci ya kama bakin duron din da hannunshi ya rike yana kallona cikin wani irin yanayi da ke kama da na tausayin kai, ya kalleni cikin nutsuwa ya ce mini.

“Wannan abincin da Baba ya nemo ne ya kawo mana don mu ci kika yi dalilin da aka juyec shi anan ana neman inda za a kai shi, don a zubar da shi.

Abin abin tausayi ne wai ke daya kamata ya yi kifi kowa jin tausayin shi, ke ce kike jagorancin yi mishi ta’adi, a shekarun shi na girma shekarun da ya kamata ya yi su cikin hutu tare da iyalin shi bai zauna ba, saboda kokarin ganinmasirin mu ya rufu, amma bai cancanci tausayawa ba a wurin ki, ko in kina yin hakan ne don in gaji da ganin abin da kike yi in fidda ke cikin masu yin girkin ba zan fidda ki ba, kin fi kowa cancantar ki ciyar da mutanen gidan nan, ban ga dalilin da zai sa ba za ki yi hakan ba, sai ki zauna ke ana yi ana ba ki, ranar da babu shi da su Umma kina nufin za mu bar mishi iyalin shi ne yunwa ta watsa mishi su?”

Ya yi tambayar cikin wani yanayi da ya sa jikina ya dauki rawa, ya zuba mini ido tsananin bacin ran shi ya kara bayyana. Ya ce,

“Kina so ne ki nuna mini ba za ki taya ni rike wa Baba iyalin shi ba? Kina so ne ki nuna mini cewar ba ki san kowa ba, sai kan ki? Yaran gida su rinka kwana da yunwa, hankalinki a kwance, saboda ke ba za ki kwana da yunwar ba?”

Yana ganin na fara kuka ya wuce ya bar ni a tsaye. Na jima a tsaye a wurin ina kuka, saboda kalaman da ya yi mini da kuma ganewar da na yi

ban cutar da kowa ba, sai baba. Na biyo bayan shi don in ba shi hakuri ban gan shi ba, sai Yaya

Junaidu na gani yana tsaye ana sauke katon-katon din taliya, yana kallo ana shiryawa a store shi ma cikin bacin ran.yake saboda irin kallon da na ga ya yi mini, kafin ya ce mini;

“Mustapha zai zabi daya cikin biyu…” Ban bar shi ya gaya mini dayan biyun da

Yaya Almu zai zaba ba, don na san bai wuce kan maganar zaman da yara ke yi da yunwa ranar da na yi girki ba, na durkusa na ce mishi, “Ka yi hakuri Yaya Junaidu.”

Bai amsa ba na mike ina dawowa kacibis muka yi da Anti Aina’u da Anti Basira.

“Ke.” Sunan da suka kirani da shi kenan. Na matsa kusa da su na ce musu, “Gani.”

Anti Aina’u ce ta fara bude baki ta ce mini; “Daga yau kika sake kwaba kwaba66en abincin ki kika turo a kawo mana a ce wai ke kar mu jira ki kin koshi, za ki ga abin da zan yi miki.”

Ita ma anti Basira ta dalla mini harara ta ce,

“Sakaryar yarinya kawai, sokuwa.” Na wuce na

bar su cikin raina ina cewa na dai kusa hutawa in a ka tattaraku aka kai ku gidajen mazan ku.

Gaba daya samarin gidan tsuke mini fuska suka yi ko gaishe su na yi ba sa yi mini amsawar da ta wuce guda daya shi kam yaya Zubairu d yake hakuri bai ishe shi ba, kwakkwara mini zagi ya yi, tare da tambayata so nake in nakasa yara da yunwa? Na ce mishi a’a, ya ce to ke kina cin abincin da kike yin? Na yi shiru ina kallon shi.

Ni da Umma gaba daya muka shiga cikin damuwa, don ba’ta son ganina a takure.

“In ban da Babangida ba zai yarda ba ai da sai in sa Talatu ta rinka tayaki wannan aikin a yafi karfinki,  ina ke ina girkin abincin mutanen gidan nan?”

Ranar Asabar da safe ina gama gaida su Umma wurin yin girkin na nufa ko bari in karya ban yi ba na gayawa Baba Maigyada in masu gyaran wurin sun gama ta sa a kira ni.

Na je na duba abin da ake da shi a cikin frezeer na fito na nufi wurin Yaya Kabiru na gaya mishi abin da babu a gida, wanda zan yi amfani da shi ya kalleni ya ce, “Ki je ki yi haka ba zan sayo komai ba, yau don mai bayar da kudin ba a kasa yake debo su ba.”

Yaya Junaidu da Yaya Almu sun riga sun fita.

Don haka wurin Ummana na koma na gaya mata abin da ake ciki ta yi murmushi ta ce, “Ai shi Alhaji sa’a ne da shi tun da yake bai taba rike dan da bai so shi ba, lissafa abin da kike son sai in sa akai Talatu kasuwa ta sayo miki.”

Na ce mata to. Na zauna na lissafo mata kasancewar miyar Afang na yi niyyar yi. Ga lissafin da na bukata.

Nama.                

Barkono

Ganda.               

Maggi, gishiri.

Busasshen kifi.   

Albasa.

Cray fish.          

Sai kayan kamshi.

Ganyen Afang.

Manja.

Umma ta kalli lissafin nawa tayi murmushi ta ce, ‘A ce dai ki iya tsarawa ya yi kyau, to je ki ki duba abin da babu a ciki sai ki zo ki gaya mini.” Na ce mata to.

<< Wace Ce Ni? 3Wace Ce Ni? 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×