Skip to content
Part 40 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Da gudu Baba Talatu taje tana dukan kofar dakin dake rufe cikin kuka tana rokonshi ya bude bai fasa abin da yake yi ba sai da ta ce mishi zata kira Umma a waya ta gaya mata sannan ya bude ya fito ya nufi wurin shi.

Lailatu tana ta faman gurnanin kuka tana fadin an zage ta din an gaya mata magana munafukar tsohuwa kawai, menene nata ban sani ba tayi nuku asiri a gishirin miyar gidanku ta shammace ku sai ta rinka nuna wai ita mai kirki ce saboda ta iya munafurci mugu….bata kara sa ba ya sake fadawa cikin ba zato don haka tayi kus, takardar saki ya danka mata jeki gida na hakura da auren bana yi tunda dai shine ya baki damar da kike zagin iyayena, to na bar shi duk da abin da ke tsakanina da Lailatu na kishi da kin zuwanta gidan da nayi ga kuma tasa mun uwa a gaba da tayi da wulakancim ban ji dadin sakin da Yaya Almu yayi mata ba, jikina yana rawa naje na same shi don in ba shi hakuri ya ce kar in yi mishi magana na dawo dakina cikin rashin jin da di ban taba sanin haka sakin aure yake ba. Yaya Almu ya sake lekawa dakin Lailatu fita a kaiki gida ga mota can nayi waya na gaya wa Umma abin da ya faru.

Da yamma kuwa sai ga Umma ta iso kai tsaye falon Yaya Almu ta shiga na same ta a can fada sosai take yi mishi ina amfanin wannan abin da kayi don ta zagi iyayenka sai me? Aure ai ya wuce haka, sai ka shirya kaje donni daga gidan nasu nake yanzu sun ce ba zata dawo ba sai kaje kai da kanka. Yaya AImu yayi maza ya ce a’a Umma tunda dai ki kaje ba su ga girmanki sun dawo da ita ba to babu abin da zai kai ni su barta tayi ta zama, ta ce mishi kar kayi haka, yayı maza ya ce a’a Umma wannan ai wulakanci ne zuwana har yali naki muhimmanci?

Ba za ni ba, akan dole yaya Almu ya amsa wa Umma za shi tà kuma tilasta shi tafiyan tun tana nan, da daddare ranar Lailatu ta dawo, sai dai dawowan da tayin da wani damaran ta sake zuwa. Wuni take yi tana habaici ina kallonta donni ban saba irin wannan abin ba, ban ga kuma kamar zan ya shiga cikinshi ba, ilai rannan ta sake yi mun irin wannan abin ran girkina ban yarda na bita bashi ba tana karbar girki nima nayi mata abin da ya yi matukar kona mata rai, gari na wayewa kuma na tsala kwalliya ina kaiwa da kawowana, da hantsi wajen karfe goma sai ga su Umma sun zo ita da Umma Amarya saboda wayar da Yaya Almu yayi musu tun cikin dare ya shaida musu cewar bani da lafiya wata irin lalura ta same ni.

Ina zaune gaban Umma Amarya da ta shigo dakina bayan fitowarsu daga dakin Lailatu yayin da ita Umma ta shiga wurin Yaya Almu, Umma Amarya ta kalle ni cikin natsuwa ta ce mun me ya same ki Adawiyya? Mijinki ya ce lalura ta same ki kwanannan sau biyu abin yana tashi, me ya same ki? Na daga ido na kalle ta ba zan iya yi mata karya ba, na ce mata lafiyata kalau Umma na soma bata labari hawaye suna gudu a idona saboda ni kaina ba akan son raina nake yin abin da nake yin ba, na fi so da Lailatu ta yarda mun zauna lafiya tunda zama ya hada mu.

Umma ta zuba min ido sai da na gama bai wa Umma bayanin komar sannan sai ta ce min to don me za ki kirkiranwa kanki rashin lafiya?

Yaya Almu ya biyo bayan Umma Amarya don ya gaishe ta ya same i ina kuka a gaban Umma, yayi zaton ko kararshi na kai mata, don haka ya zauna Cikin sanyin jiki a sanyayc ya gaishe ta, Umma ta shigo bayan ta baro dakin Baba Talatu aka hadu a falon.

Umma tana kallona ta ce min, ke Adawiyyah ban sanki da wata lalura ba menene dalilin wannan abin da yake faruwa? Nayi shiru ban ce mata komai ba, kul na sake jin wani abu makamancin haka ya faru, yaya Almu yayi galala yana kallon Umma cikin mamaki, Umma ai ciwo ne ciwon ciki ne yake murde ta tayi ta fama da shi yayi ta bayani bata ce mishi komai ba, sai bayan da ya fita ta sake kallona ta ce min na ce miki kul kema za ki wahalar da shi ne? In ki ka yi hakan ribar me ki ka ce? Na ce to amma Umma shi bai san ita din abin da take yi karya ne ba yake biye mata? Ta ce bai sani ba tunda kema da ki ka girma a gabanshi bai gane wanda ki ka yi ba balle ita da ya ganta da girmanta.

Umma Amarya ta yi tsaki ta ce, zama dai irin wannan yana da wahala sai dai addu’a kawai.

Bayan tafiyar su Umma dole na zuba wa Lailatu ido tana shakiyancin ta, tunda ta ce ni kar in sake yin haka sai dai daga baya da na ga abin nata ya ishe ni ni nayi shawara kan abin da zanyi tunda ba zai yiwu in zuba mata ido ta raba ni da mijina ba. Rannan na karbi girki tun rana yaya Almu yake so in bashi lokacina ni kuwa naki yarda na bata lokacin a kicin ina shirya mishi abin da zai ci da daddare mun shiga wurin shi kenan sai kawai muka jiwo ihun Lailatu. Gabadaya muka fito muka same ta a mimmike tana ta faman furzar da yawu, yaya Almu yayi mata addu’o’in da zai iya tana kwance da ya dan natsa yana hutawa sai na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi Yaya Almu ko zamu je daki ne tunda ko mun zauna ba yanzu zata farfado ba, ni kuma yau ban ga kamar zan iya hakura da kai ba, tun kafin in karasa fadin abin da nayi niyya yayi maza ya ce muje, muje Rabi kira Baba Talatu tazo ta zauna da ita na ce to.

Cikin dare Lailatu ta faki idon Baba Talatu ta fita ta nufi gidansu ita kuwa Baba Talatu ta yi ta binta ckin sanda har sai da suka isa kofar gidan da zata shiga ciki sai ta ce mata, to ni zan juya daga nan ta dawo gida ta karasa kwana da gari ya waye ta yiwa Yaya Almu bayanin yanda suka yi duka bai bi bayan Lailatu ba kwana da kwanaki har dai iyayenta suka gaji suka zo da kansu. Ina jin shi yana gayawa wanta da aka turo wurinshi cewar shi lokacin da za’a bashi ita ba’a gaya mishi cewar tana da wata lalura ba don haka tunda sun ce ba su yarda a kaita asibiti ba, to shima ya gaji da kwana ido biyu da yakc yi yana gadinta don haka a barta a gida kawai ta zauna a neman mata magani in ta warke shi kenan ta dawo dakinta, amma in bata warke ba to a barta a gidan kawai ya hakura, ‘yan kwanaki kadan bayan nanne suka aiko wai sun karbo mata magani don haka zata dawo dakinta, ya ce to shi kenan amma in ciwo ya sake tashi to zai turo ta gida daga wannan lokacin ne Lailatu ta warke ciwonta don ganin zai iya yi mata sanadin aurenta.

Tun daga wannan lokaci kuma sai Lailatu ta tasa Baba Talatu a gaba da rashin kunya da wulakanci ga sa aiki na rainin hankali abu ko a kusa da ita yake ba zata sa hannu ta dauka ba sai ta ce wai sai Baba Talatu tazo ta mika mata rannan dai da abin nata ya ishe ni sa na ce mata ke Lailatu Baba Talatu ba mai aiki ba ce a gidan nan uwata ce in kin lura da kyau za ki ga ba umarni nake bata rokonta nake yi ta taimake ni tayi min abin da nake so tayi min don haka daina yi mata tsawa kina maida ita kamar wata wacce take zamanki. Sai kawai Lailatu ta kalle ni ta ce mun tunda kuwa zan tuka in bata ta ci ai dole in sata aiki tayi nace to daga yau kar ki sake yin girki da ita kar kuma ki yarda in sake jin kin ce tayi miki wani aiki na hana, kan wannan takai.

Karana wurin Yaya Almu ya kira ni ya tambaye ni dalilin da yasa na hana Baba Talatu ta rika taimakonta na ce mishi in tana son mai aiki a dauko mata amma Baba Talatu uwata ce zamana kuma take yi, ya ce haka ne to a bari in gaya wa Umma ta kawo muku mai taimako na ce mishi to, na tashi na tafi na bar su Lailatu fuska a daure ba haka taso yayi ba, ba a cika kwana bakwai ba kuma sai ga masu aiki har guda biyu Tanbai da Larai. Lailatu ta ce sai kowa ya dauki mutum daya shi kuwa Yaya Almu ya ce a’a su din zasu yi zaman gida ne gabadaya.

A wannan lokacin Lailatu ta rasa inda zata tsoma ranta ta ji dadi ta rasa inda zata yi ta shiga tsakanina da Yaya Almu kullum na karbi girki kan in fita girkin sai tayi kuka idonta yayi luhu-luhu, ko kuma ta yi ta fushi in na gama girki na kai mana wurin Yaya Almu na ce tazo muci sai ta ce ita ta koshi, in kaga tana walwala to girkinta ne, ni kam ina kallonta tun dai nasan bata da yanda zata yi dani. Muna cikin wannan zama ne aka wayi gari Lailatu babu lafiya, ni da Yaya Almu muka kaita asibiti bayan yan gwaje-gwaje da yan tambayoyi yan kadan Likita ya tabbatar da cewa ciki ne da ita na tsawon makonni shida, ban taba ganin fuskar Yaya Almu cikin yanayin da na ganta a wannan lokacin ba, don haka in na tsaya cewa yayi farin ciki to bata bakina kawai nake yi. Likita ya sallame mu da magunguna muka fito daga ni har Yaya Binta da sannu-sannu muke yi tana ganin wata kujera taje ta zauna akai wai ba za ta iya tafiya ba saboda jiri gashi kuma jikinta ciwo yake yi, makullin mota Yaya Almu ya miko min ya ce muje ki tuka mu na ce to shi kuwa yasa hannu biyu ya suri Lailatu ya rungume a kirjinshi nayi maza na yi gaba naje na bude musu kofar motar ta wurin zaman mai mota suka shiga yana kankame da ita ni kuwa na koma wurin direba na tashi motar muna tafiya yana yi mata wasu maganganu masu kama da sambatun

Dadi, yayin da ni kuma zuciyata ta tafi wajen tunanin wata shida kacal da auren Yaya Almu da Lailatu zata zama uwar iyalınshi shi kenan abin nema ya samu tun daga ranar da Likita ya bayar da tabbacin Lailatu na da ciki to tun daga ranar kuma komai ya sauya gaba daya gidan ya zama Lailatu ce mai juya shi ko ni ke da girki to abin da ta ce nake girkawa, saboda ita mai juna biyu ce yaya Almu kuma a yanzu komai take so shi ma abin da yake so kenan ko da kuwa ba dai dai ba ne na yi kamar in kai karar yaya Almu kan sabuwar dabi’ar tashi sai kuma naga zan tada hankalin Umma sauran jama’a kuma suce don naga Lailatu na da ciki ne yasa nake bakin ciki da ita don haka dole naja bakina nayi shiru.

A wannan lokacin kusan kullum ni ce mai yın girki saboda kowane lokaci Lailatu tana kwance wai bata jin dadi bata da lafiya don haka ya ce in karbi abincin gidan gaba daya, na ce mishi to gashi kuma a hakan ma babu mutunci a gaban shi ma sai ta mulmula bakar magana ta gaya min sai ya ce wai in yi hakuri mata masu juna biyu a fusace suke don haka hakuri ake yi dasu na sake cewa to don haka ina zaune Lailatu take gaya min abin da taga dama ina kallonta, wani lokaci Baba Talatu ta yi ta kuka tana bani hakuri in ce mata babu komai Baba kowa da irin kaddararshi don haka ya zama mun dole nima in yarda da nawa.

Gaskiyar magana ita ce a wannan lokacin ne nasan lalle yaya Almu yayi aure don duk abin da ya taba faruwa a baya sai da ya zama wasan yara kan sabbin abubuwan da suke faruwa a yanzu, Umma karama ma duk sati take zuwa wai tana zuwa gaida mai laulayi haka nan yan uwanta gidan ya zame musu wurin wuni wai suna jinyar mai laulayi shi kuma Yaya Almu sau goma zasu shigo sau goma zai yi musu hidima ya kuma sa a maida su gidanjensu, bayan ya yi musu godiya mai yawa akan idona dana Yaya Almu ‘yan uwan Lailatu suke hirar karshen mulkin matan da basa haihuwa sai kuma a kwashe da dariya cikin Shewa da tafa hannu. A wannan lokacin in na ce ban shiga wanı hali ba to ban yiwa kaina adalci ba, to amma bani da yanda zanyi yaya Almu da ciki kawai yake ji zai samu abin da yake nenmå za’a haifan mishi da wannan shine abin da yake gabanshi, gashi Ummama da ta zo duba Lailatu ta jaddada mun muhimmancin inyi hakuri don haka sai na dukufa wajen addu’ar neman karin hakuri

da juriya, sai dai kuma hakurin nawa bai hana zuciyata ciwo ba.

A wannan lokacin Yaya Almu babu ce kawai bai dauko ya kawo wa Lailatu ba, wuni yake yi yana jido kaya yana kawo mata da sunan sayayyar kayan haihuwa. Baba Talatu ta zo ta same ni tana tambayata anya uwardakina ba za ki sa ayiwa Babangida magana kan irin dukiyar da yake kwasa yana bai wa mutanen nan ba? Nayi murmushi na ce Baba kenan to Lailatu ko ya bata dukiyarshi ko kar ya bata ai ta zama tata da fa zata haifan mishi bar su kawai suyi duk abin da suka ga yayi musu daidai, ta ce to shi kenan, kema ai ba mu fitar da rai ba, in yi murmushi kawai in kawo wani zancen don ni kam na riga na hakura na fidda raina kan zancen haihuwa.

Ni da Yaya Almu sai da ta kai ma bai iya tantance girkina da wanda yake na Lailatu saboda tsaban kowanc lokaci yana dakinta, gashi kuma a yanzu kusan kullum sai mutanenta sun tashi cikin dare wai suna zuwa tayata murnar juna biyun da ta samu.

Saboda tsananin samun wuri kuwa rannan magana kawai ta yi na amsa mata saboda na gane shirun da nake yi mata yayi yawa sai kawai ta warwarc hannu ta share ni da mari a fuska a gaban Yaya Almu, cikin tsananin fushi na yunkura zan yi maganinta sai kawai yayi caraf ya rike ni ai ba za ki kula ta ba Rabi, ai hakuri kawai za ki yi ta ci darajar abin da yake cikin cikin nan nata, na tsaya ina kallonshi yana rike da hannun da na kawo mata marin dashi, sai ya ce min haba Rabi yanzu ke in aka ce miki ki bugi Lailatu sai ki buge ta?

Mai ciki ce fa? Ko so ki ke ta haifi dan da shatan duka a jikinshi? Ya juya wajen Lailatu ya ce mata ke kuma ki daina saurin hannu kinji na gaya miki abin da kawai ya fada kenan ta fashe mishi da kuka wai ya goyi bayana ya yi rarrashi har ya gaji ban san yanda suka karc ba, don kuwa tashi nayi na fita na basu wuri na dawo dakina wunin rannan cikin tsananin bacin rai na yi shi haka nan ban samu damar yin baccin dare ba, don kuwa marin da Lailatu ta yi min yayi matukar kona min zuciya.

<< Wace Ce Ni? 39Wace Ce Ni? 41 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×