Skip to content
Part 43 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Kalaman da Baba Talatu ke yi mun sun sanya ni din na zamo mai yawan godiya a duk lokacin da damuwar rashin haihuwa ta bijiro min na kanyi maza in shiga kirgo ni’imomin da aka ni’imtani da su misali ni din marainiya ce bani da uwa bani da uba ban ma sansu ba, to amma sai na girma cikin gatan da ya hana ni sanin ni din marainiya ce saboda samun Umma da Baba da nayi wadanda suka yi min gata suka maida ni yar lelensu har vau din nan kuma ban taba neman wani abu na rasa ba matukär abu ne wanda zasu iya yi min shi ba.

Rannan ina cikin kicin ina aikin abincina don ni ke da girki ina shirya abincin rana duk da nasan Yaya Almu ba ci zai yi ba saboda yakan kwana ashirin bai ci abincina ba wai ban iya ba, abincin nawa babu dadi (taste) wato dandano, don haka in daina yi dashi na ce mishi to.

Aikina nake yi ina rero baitocin Celine dion cikin wakarta mai taken Becouse u luv me.

For all the standu stood for me,

For all the truth dat u made me see

For all the joy u brouth to my life,

For all the wrong that u being right.

Aikina nake yi ban kula zirga-zirgar da Lailatu ke yi tana fadin za’ayi kwaba ba har na iso inda take cewa. I was blessed b/cos was loved by y, sai kawai na ji Lailatu ta kwashe da dariya tana fadin da kenan amma yanzu ba ta taki ake ba kina dai zaman rashin zuciya ne kawai.

Ta bayan Lailatu nasa hannu na cafke ta na wanketa da mari sau biyu, ta miko hannu zata rama na cafke shi na murde da karfi, ta kwallara ihu, Baba Talatu ta fito, kar kiyi fada da ita ga goyo a bayanta uwardakina, na ce mata to, na saki Lailatu na juya zan shiga kicin in ci gaba da aikina, sai kawai ta kama zagi tana ashar tana fadin wasu mugayen maganganu akan Ummana har tana tambayata wai menene bata sani ba namu? Ai komai an bata labarinshi da dai na ji rashin mutuncin nata ya ishen, sai kawai na fito na same ta nasa hannu na balla tawul din da tayi goyon dashi na kama yarinyar na ajiye ta a kasa, Tambai tayi maza ta dauke ta tana rarrashinta saboda kukan da take yi, Lailatu ta shiga fadin bar ta ta kashe ta dama duk abin da take mata munafurci ne taga anyi anci niba to anan babu wata ribar da zaki ci, na ce mata waye yayi ya ci riba? Tayi maza ta ce uwarki mana saboda itama a yanzu ta shiryawa danben musamman da yake taga ta ajiye teba, nayi maza na buge ta ga guiwar hannuna a baki abin da ya yi matukar kidimata duka na yiwa Lailatu ranar irin wanda bata taba zaton zan iya yi mata ba, sannan daga Baba Talatu zuwa su Larai da Tambai babu wanda ya yi kokarin rabawa sai cewa suke yi kuyi hakuri su dukansu suna daga nesa, ni da kaina ne na kyale Lailatu saboda ganin da nayi duk wani kokarin ramawa da take yi ta daina nace mata gobe ma in wata magana ta tashi ki sake zagin uwata ki gani mara mutunci wacce iyayenta ba su yi mata tarbiya ba na wuce na shiga wurina na bar ta tana fadin a zaga din sai dai bata sake ambaton Umma ba.

Yaya Almu ya dawo ko leka inda yake banyi ba don kuwa dama ni dashi ganin nanne kawai ita ce dai tayi ta zirga-zirga zuwa can sai naji yana kwala min kira ban amsa ba na dai tashi kawai na tafi na ce mishi gani, a fusace yake magana me ya faru tsakaninki da Lailatu yau a gidan nan? Na ce babu komai ya kara fusata babu komai kamar yaya? Wannan ciwon da ki ka jijji mata fa kamar wata maiya? Me tayi miki ki ka buge ta? Kina nufin don takamar kina da karfi sai ki buge ta ‘yarki ce? Ke wake dukanki, to ba zan yarda ba, don haka zaki yi mamakin matakin da zan dauka kan wannan abin da ki ka yi zaunar da ke zanyi ta rama dukan da ki ka yi mata a gabana, na daga ido na kalle shi nayi murmushi nace wannan shine tatsuniya, na tashi zan fita daidai ita kuma ta shigo saboda kiran da yayi mata naga bata da shirin kauce min a hanya nayi maza na hankada ta ta fadi a kasa don bata yi zaton zanyi mata hakan ba a gabanshi na wuce na shiga falona, ya biyo ni yana fadin in baki yi hankali dani ba za ki raina kanki, da sauri Baba Talatu ta shigo ta shiga tsakanina dashi tana bashi hakuri, cikin kuka na ce mata bar shi ya buge ni Baba kar ki hana shi dukana bar shi ya ramawa Lailatu dukan da nayi mata ai uwar ‘yarshi ce ni kuwa fa? Ina fadin haka Baba Talatu ta durkusa da guiwowinta biyu a kasa tana kuka na wuce naje na shige bandaki na zauna nayi kuka sai da na gaji sannan nayi wanka tare da alwala na fito.

Da daddare bayan yaya Almu ya tafi kai Lailatu da Rabi’atu asibiti saboda wai itama har da ita na daka naje na kira Baba Talatu a dakinsu ta biyo ni muka dawo wurina, na shaida mata abin da na shirya zan yi, cikin sanyin jiki ta kalle ni ta ce min amma da kararshi gida kika kai aka tsawatar mishi ina ganin da yafi, na ce ba zan iya ba ba zan je ina bata shi a gaban iyayenshi ba.

Tunda akayi haka na kama kaina sosai girki gida dai gaba daya na daina yi sai dai in sa masu aiki suyi, kullum kuma bana wani cewa ga wata rana ta girkin Lailatu yaya Almu kuma ko Kallon inda yake bana yi balle inje ina yi mishi wata magana in dai na ce mishi ina kwana ina gajiya to shi kenan sai kuma gobe. Cikin raina dai nasan abin da nake shiryawa.

Rannan bayan fitar Yaya Almu da rana sai nayi mishi waya na ce mishi lalura ta same ni yanzu zan fita, ban jira naji amsar shi ba don nasan cewa zai yi bai yarda ba, nayi maza kuma na kashe wayar nayi ficewata daga gidan naje na gama abin da zan yi na dawo sai na same shi a tsakar gida a tsaye cikin huci ina kika je? Nayi maza na bude jakata na debo mishi magunguna na nuna mishi na ce kada gwarzo da kurarrajin baki sun dame ni, ya kawar da kai daga magungunan yana fadin tun-tun-tuni da kika fita kina wurin sayen maganin kada gwarzo da kurjin baki? Na ce eh na shige dakina ban sake sauraronshi ba.

Wata guda bayan wannan loka cin ina kwance a dakina da daddare misalin sha biyu da rabi sai kawai naga yaya Almu ya shigo dakina alhalin girkin na Lailatu ne, na zuba mishi ido ina kallonshi cikin mamaki gashi kuma babu alamar walwala a fuskarshi, na zuba ido ina kallonshi cikin sauraro sai kawai naji ya ce min wai me kike nufi ne da wannan abin da kike yi min? Wai ni haihuwar nan wani ne yake ba da ita Rabi da zaki je kina yi min surkullen da ban san dalilinshi ba? Cikin natsuwa na kalle shi na ce mishi, me nayi maka? Ya ce kar ki ce min ba ki san komai ba don na riga an tabbatar da cewar ke kika yi kece kika yi abin da ki ka shiga tsakanina da Lailatu duk sanda zan kusance ta in rasa karfi saboda kina tsoron kar ta sake samun wani cikin, to akwai bakin ciki ne a tsakanina da ke?

Na zuba wa Yaya Almu ido ina kallonshi cikin kaduwa da kyar na iya buda bakina na ce mishi darajar aure dake tsakaninmu da kuma na iyayen da suka haife mu na yafe maka duk abin da kake yi mn na juya na gyara kwanciyata tare da cewar amma daga yau ka gama.

Washegari da safe yana wurin Lailatu ina jinta tana kuka shi kuma yana ta bata hakuri tare da yi mata alkawarin daukar mataka kan abin da ke faruwa, nasa makulli na kulle wurinaa na kira Tanbai na bata kudi na ce su raba na kuma kira Baba Talatu muka fice daga gidan.

Ina zamu uwardakina? Na ce mata ke dai zuba ido kawai ki gani Baba ta ce to.

Titin Sultan na kaimu na yi tafiya ta cikin layin dake tsakanin bishiyoyi banyi wata tafiya mai yawa ba na saki babban titin na koma kan wanda ya nemi yamma gaban wata katuwar katanga naje na tsaya nayi hon maigadi yazo ya bude min kofa na shige ciki, sai da ya rufe kofar ya biyo bayana muka gaisa sannan ya koma wurinshi nima na nufi cikin gidan sosai sai da naje muka gaisa da matar gidan dake zaune a boyis kwatas wacce ta maigidan ce sannan na dawo nasa makulli na bude asalin gidan muka shiga ciki ni da Baba Talatu ajiye jakata kawai nayi na shige wani daki mai bandaki nayi alwala nayi sallah raka’a biyu nayi addu’o’ina na shafa sannan na fito na samu Baba Talatu ita kadai a falo, tana zaune sai kalle-kalle take yi.

Na kalle ta nayi murmushi na ce gidan da na saya ne wannan Baba hannu biyu ta saka ta dafe kirjinta alamar kaduwa da mamaki na ce mata kishiya ce ta koro ki Baba sai ki ka zo kika yi renona a yau ke uwata ce duk inda zani tare dake zan tafi, tunda nima kishiyar ta koro ni yanzu sai kije ki debo mana ‘yan jikokinki guda biyu ki kawo mana su taya mu zaman gidan nan.

Baba Talatu ta zuba min ido cikin mamaki tana kallona, ke ki ka sayi gidan nan kika gyara shi haka uwardakina? Na ce mata eh Baba ko ba ki yarda ba ne? Ta yi maza ta ce a’a uwardakina ai ba ki da irin wannan wasan na dai kara jinjinawa al’amarinki ne nace mata tashi ma muje kiga wurin sosai na zaga da ita wurin na nuna mata ko’ina ta yaba cikin murna da addu’o’i masu dadin ji sai kuma naga ta fashe da kuka.

Nayi maza na tambaye ta dalili sai ta ce min to Babangida fa? Na kalle ta cikin sanyin jik na ce mata to yaya zanyi dashi Baba? Ba zan iya wannan zaman ba ai gara kawai muyi nesa da juna sai wajen yamma nayi wa Umma text a dalilin na kasa boye mata kaina don nasan zata shiga tsananin damuwa ina tura mata text dn kuma nayi maza na sake rufe wayata.

Ni da Baba Talatu muna zaune abinmu zamanmu gwanın dadi hankalinmu a kwance babu wata fitina girkinmu kawai muke yi muci1 sai muyi kallo in dare yayi mu kwanta da wuri saboda biyu da tabi nayi zamu farka ba kuma zamu sake kwanciya ba sai garı ya waye, bayan sallar asuba. Tun muna da kwana hudu a gidan Baba l’alatu ta sanya ni a gaba wai sai lalle na bude wayata da tata da na rufe don a san inda muke ai ko ba komai a yanzu tasan Yaya Almu ya gane kurenshi kan abubuwan da yake tayi min, nayi murmushi na ce Yaya Almu ai yanzu Lailatu da yarta ce damuwarshi ta ce wanc shi don dai kawai yana ganinki ne.

Baba Talatu tayi matukar kaduwa da ganin gidan da na mallaka na kuma gyara sannan na kawatashi da kayan alatu muna zaune da ita a bayan gidan cikin harabar dake baya shan iska muke yi ta kalle ni ta ce min, ni kuwa uwardakina yaya akayi ki ka samu ki ka mallaki wannan wuri haka? Nayi murmushi na ce komai nawa na sayar Baba har da sabuwar motar da Baba ya bani da duk kayan kwalliyata ko wannan sarkar dake jikina abin da yasa na barta don Umma ta ce min ta mahaifiyata ce na kuma hada da ajiyata ta tuntuni, Baba tayi murmushi addu’a kawai take yi ita kam ta gamsu ta yarda cewar wai ni din jaruma ce don rago baya iya yiwa kanshi maganin abin takaicin da ya dame shi.

Satinmu biyu cif a gidan rannan ina kwance a daki bayan na idar da sallar walaha sai kawai na mika hannu na dauko wayata dake ajiye kan mirrow nasa hannu na bude wayar nan da nan sai ga sakonni suna ta shigowa da sauri har wajen guda biyar, sakon da naga numbar Baba akai na fara budewa ga abin da na gani:

Anya uwata kin kyauta min wannan abin da kika yi?

Kafin in kai karshen sakon sai kawai ga wayar Yaya Junaidu ta shigo kasa bijire mata nayi don haka na dauke ta da sauri ya tambaye ni kina ina  ne Adawiyyah? Na gaya mishi na maida wayar na ajiye.

Awowi biyu bayan sai kawai naji wayar yaya Junaidu yana shaida min isowarshi kofar gida, nayi maza na ce wa maigadi ya bude mishi, banyi zaton ganınshi tare da wani ba don haka nace ya shigo falon sai kawai na ganshi tare da Baba. A kidime na durkusa a kasa ina. yi mishi sannu da zuwa, bai amsa ba sai ya ce min wuce mu tafi ban yi magana ba nayi maza na bi bayanshi zuwa cikin motar da suka zo a ciki, shima yaya Junaidu ya gama kalle gidan ya taso Baba Talatu a gaba suka zo suka shiga ya fara tuki, har muka isa gidan Yaya Almu babu wanda ya ce komai in ban da ni da nake ta faman kuka saboda na gane maidani zai yi.

Kai tsaye Baba ya tasa ni a gaba har cikin falona shi da Yaya Junaidu zuwan shi gidan Yaya Almu na farko kenan, da sauri yaya Almun ya fito yana yi mishi sannu da zuwa bai tanka mishi ba, ya kalle ni ya ce min nan nace miki ki zauna umarnin da na baki kenan, ya juya ya fita ya tafi.

Yaya Almu ya shigo yana min sannu da zuwa tare da tambayata inda na tafi? Ban tanka mishi ba na dai gane kawai hankula sun tashi saboda daga shi har Lailatun sun shiga cikin hankalinsu, banga su Tanbai ba ban kuma tambayi inda suke ba sai wata sabuwar mai aikin.

Dare na yi yaya Almu ya shigo don dama yana ta nuna zumudi da farin cikinshi kan dawowana, na ce mishi ba na dawo zama ba ne balle ayi rabon kwana dani, nazo sauraron hukuncin da Baba zai zartar ne a tsakaninmu. Fafur na ki sauraron komai daga Yaya Almu balle kuma wata Lailatu na ma daina ganin Rabi’atu in sa hannu in dauke ta balle ayi min wulakanci girki kuwa in nayi ni da Baba Talatu nake zubawa in bar saura anan mai so ya diba.

<< Wace Ce Ni? 42Wace Ce Ni? 44 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×