Kukan da nake yi ya tsananta saboda na kasa hana kaina yin kukan a dalilin kalaman da yake ta jerowa wadanda ba masu dadin ji ba ne a wurina, don kuwa alama ne na yana cikin fushi mai yawa game da zaman nawa sai ya kara matsowa kusa dani yana cewa gaya wa Baba yau za ki koma dakinki Rabi sai muyi tafiyarmu ki koma dakinki kiyi zamanki ke kin san ina sonki fiye da komai a duniya, kin sani sarai kece mafi darajar abin da nake dashi a rayuwata. In kinyi abin da kika yin ne don ki horar dani ki nuna min matsayinki to na horu Rabi, na kuma kara jinjina al’amarinki tunda gashi da barinki gidan nima na kasa zama a cikinshi, rabon da inyi kwana bakwai ina zaune a gida har na manta Rabi, yau ina nanne gobe ina can, kiyi hakuri ki yafe min abin da nayi miki wanda yasa kika yanke wa kanki hukuncin yin nesa dani ba tare da kinyi tunanin abin da hakan zai iya jawo min ba, ganin da nayi Yaya Almu yana shirin durkusawa da guiwowinshi biyu a kasa don ya roke ni yasa nayi zunbur na mike daga kwanciyar tawa, na zauna a tsakiyar gadon ina rokonshi kar kayi min haka yaya Almu ba sai ka durkusa min ba zan dawo dakina, da sauri ya ce min yaushe?
Kan in ba shi amsa sai ya sake zuba min ido cikin natsuwa yana yi min wani irin matsanancin kallon da ya yi dalilin da nayi maza na jawo abin ruhuwana na rufe kirjina da ya zubawa ido, ciki ne dake Rabi? Nayi maza.na ce mishi wane irin ciki? Cikin lafiya? Ni mai haihuwa ce? Ya ce to kirjinki da ya cika haka fa? Ban taba ganin nonuwanki sunyi irin cikan da suka yi ba yau mu gani? Na bata ido na ce kaga me? Nayi maza na mike na shige bandaki nayi wanka har na fito yana zaune a wurin zaman jiran fitowana yake yi, me ya canzaki ki ka zama haka Rabi? Na ce zaman gaban iyaye na samu kwanciyar hankali da natsuwar da nake bukata, ban yarda ke ba Rabi dole akwai wani abin da ke tafiya wanda yasa Baban Tudu ya hakura ya huce fushin da ya zo da shi ya bar ki kike zaman gidan nan.
Na ce to koma dai menene ai kuma ba ciki bane tunda yaushe? Yaushe rabon ma da ace an yi wani abinnan? Kaima yanzu ai ba za ka so ace maka ni ina da wani abu ba in dai ba nema kake wata babbar magana ta taso ba, wuce shi nayi cikin hanzari na nufi dakin Umma Amarya, a can na karya na kuma yi zamana tare da ita, rannan a gidan yaya Almu ya wuni. sai dai ni kam ban yarda mun sake zama dashi a wuri daya ba.
Kwana biyu bayan nan ya sake dawowa gaban Umma yana magana da ita can komawa gidanshi ya ce Umma in zama da Lailatu ne bata so sai in canza wa Lailatun wani gida in kai ta wani wuri don itama dama tana yi min magana akan in Rabi zata dawo to in kai ta wani wuri ita in bar ta anan gidan na ce mata a’a wannan gidan ai don Rabi aka gina shi sai dai in ma raba sun zanyi ita in kai ta wani gidan.
Umma ta ce kul ka ce zaka raba su su zauna tare ai ya ishe su suyi hakuri da juna kawai, kai kuma kayi kokarin yin adalci a tsakaninsu, shikenan. Yayi maza ya ce to Umma, to yaushe zata koma? Ta ce to bari in ga Alhaji anjima zan yi magana da shi ko zuwa gobe sai ka dawo ka ji yanda muka yi, ya ce a’a Umma ai wannan karon na riga na yankewa kaina hukuncin in yi ta zama a gidan nan in jira har zuwa lokacin da zaku yanke abin da ke tsakanina da Rabi, ku bani ita mu tafi ko kuma ku gaya min dalilin rike ta da kuka yi, ni ban taba ganin kun yiwa wani irin abin da kuka yi min ba Umma, ban kuma san dalilin da yasa ki ka yarda aka yi min hakan ba in wani laifi nayi miki ki yafe min, ya durkusa da guiwowinsa duka biyu a gabanta in har zaki juya min baya Umma to ai kenan na zama bani da kowa duniya ki yafe min Umma, nan da nan Umma ta soma share hawaye a idonta tana fadin ba ka yi min komai ba Lamido baka yi laifin komai ba Babangida to me zaka yi min? Me zai faru da har zaka yi tunanin wani abu zai shiga tsakanina da kai Babangida?
Ya sake dago ido a hankali ya kalle ta cikin natsuwa ya ce mata, to me yasa aka raba ni da matata kina kallo Umma? Ai kin fi kowa sanin ina sonta sabanin dake shiga tsakaninmu ai ba kiyayya ba ce yau da gobe ne kema kuma kin sha gaya min cewar zaman aure hakuri ne duk yanda aka kai da son juna in ba ayi hakuri ba zaman ba zai yiwu ba, kiji tausayina mana Umma ba fa na iya zama a gida sosai, ba na jin dadi ji nake tanfar nayi laifi 1yayena sun kwace matar da suka bani saboda ban iya rike ta ba.
Kafin Umman tasan abin da zata ce mishi sai ga Yaya Junaidu ya shigo da saurinshi kamar an aiko shi zo mana Mustapha dama Kaduna zan tafi don in ganka sai naji ance kana nan kazo
Yaya Almu ya mike suka fita, suna barin dakin na kalli Umma cikin sanyin jiki na ce mata Umma yau kuma fitsari a zaune nake yi nayi-nayi kuma in tsaida fitsarin na kasa, da sauri ta ce min fitsari Adawiyya ko dai haihuwa ce tazo? Tashi mu gani, na yi kokarin nmotsawa in yunkura in tashi na kasa janye kafata da na mike na sake kallonta cikin natsuwa na ce mata Umma masokiya ta rike min kafafuwana duka biyu ba zan iya tashi ba.
Nan da nan jikin Umma ya kama bari tana fadin watakila dai haihuwa ce tazo miki Adawiyya, Allah dai ya raba ku lafiya tana fadin hakan ta kama kuka, kuka sosai Umma ta kama yi ta kuma kasa hassala komai kukan da take yi din ya bani tausayi don nasan abin da take tunawa wanda kuma shi take tsoro, na kalle ta cikin natsuwa na ce mata kiyi hakuri Umma.
Umma Amarya ta shigo daidai lokacin da cikina yayi wani irin murdawa mai tsanan a firgice na kama salati ina ambaton sunayen Ubangiji da sauri Umma Amarya ta rike ni ta kaini wani daki dake kusa da na Ummana ta kwantar da ni kan wani gado wanda dama akanshi Nos din dake zuwa dubani take yi min awo, kiyi hakuri Adawiyyah kiyi hakuri yanzu Likita zai zo duba ki, don na ce a kira shi, tana maganar tana shafa ni bayana take shafawa tana kuma gaya min kalamai masu kwantar da hankali, zuwa can wani irin ciwo ya sake taso min mai tsananin rudarwa nayi matukar kidimcwa ina fadin waiyo Allah na waiyo Allah, ita kuwa Umma tanfar bata jin tausayin halin da nake ciki taki tabar ni in huta sai fadi take yi, yi nishi Adawiyyah yi nishi mai karfi ga kan yaro nan ya iso yi nishi mai karfi sosai nayi matukar dagewa da iyakacin karfin nawa nayi nishin da take cewa in yi cikin yardarm Ubangiji sai gashi a hannunta, yana ta faman kyara kuka ita kuwa bata kula ba sai tofa mishi addu’o’i take yi ta ko’ina, nan da nan kuma ta tauna dabino a bakinta ta diga mishi ruwan a nashi baki, sannan ta matso kaina tana nuna min shi kin ganshi Adawiyyah da namiji ne bari in mikawa Hajiya shi ta ganshi tana kai shi ta dawo kaina bata bar Nos ta taba ni ba sannu Adawiyyah sannu da kokari ke kam jarumar yarinya ce gaki kuma da hakuri har Umma ta gama abubuwan da zata yi min kalamai masu dadi na fatan alheri da addu’o’i iri-iri take yi min don haka har ta gama ban gundura da komai ba da kanta tayi min wanka ta riko ni ta dawo dani dakin Umma ta bani mai na shafa ta miko min doguwar riga mai laushi sabuwa na sanya bayan na sanya sabbin under wears ta bani tea nasha sannan ta ce wa Nos din to zo ki yi mata allura ta juya ta fita lokacin bata iya yin komai saboda tsananin tsorata da tayi.
Umma Amarya tana fita sai ga Baba ya shigo da saurinshi iko sai Allah uwata ikon Allah yau uwata ta haifar min kani sannu uwata sannu da kokari, kin ji wani abu yana yi miki ciwo ne? Na yi maza na ce mishi a’a Baba lafiyata kalau, ya mika wa Nos yaron ya ce mata gama kintsa shi sannan ya koma jikin Ummana ya zauna ya ce mata dubi nan ya nuna mata ni da dan yatsanshi ya ce mata uwata ta haihu lafiya ita da danta lafiyarsu kalau babu dalilin wannan kukan da kike yi ki kwantar da hankalinki babu abin da zai same ta wannan mafarki da kika yi ba komai ba ne dama na ce miki babu abin da zai same ta ita da cikinta sai alheri tsawon lokaci Baba yana rarrashinta na dago ido na kalle ta na ce mata Umma kiyi hakuri ki bar kuka ni lafiyata kalua taimake ni ki bani abin da zan ci don ji nake tamfar an sace min kayan cikina, da sauri Umma ta mike bari in sake hada miki tea, na yi maza na bata rai na ce tea kuma Umma tea me zai yi min? Ni tuwo za ki bani ko sakwara, ana cikin haka sai ga Yaya Almu ya shigo da saurinshi sallama yazo yi zai tafi gida, Umma tayi maza ta ce mishi to dan dakata min kadan Lamido ina zuwa, tayi maza ta dauki yaron ta danka mishi ta ce ungo wannan duba min shi tukuna kafin ka tafi, yana zubawa yaron ido ya nemi wuri ya zauna cikin sanyin jiki da natsuwa a hankali ya bude baki ya ce mata to da dai Rabi ta yarda da cewar da nayi tana da ciki sannan haihuwa wani abu ne mai sauki to da sai in ce Rabi ce ta haifar min shi Umma, don kuwa kama dani da Baba ya yi kinga kuwa kama da gidan nan yake yi inda so kuwa shi ne namu ai da nine na dace da haihuwar dan da zai yi kama da mahaifina Umma ba wani ne zai haifa ba.
Cikin natsuwa Umma ta ce mishi naka ne Lamido, Adawiyyarka ce ta haifar maka shi, tsawon lokaci yana zaune kanshi a sunkuye idanuwanshi akan yaron ko kifta su ba ya yi yana kuma sauraron abin da Umma ke gaya mishi na cewar ba a kwance maka matarka ba Babangida, an dai rike maka ita ce don ta samu kwanciyar hankali har ta haifar maka danka lafiya musamman da yake cikin nata mai lalura ne ko shi Yayan tudun da yazo kan maganarku rokon da Alhaji yayi mishi kenan na abar mishi ita ta haihu a gabanshi.
Shigowar da Umma Amarya tayi rike da foodflask mai wuri biyu a hannunta na dama ga kuma platc-plate a daya hannun nata yasa hankalina ya tashi daga sauraron zancen Umma da danta ya koma kan Umma Amarya da abincn da ta kawo min tuwon dawa ne miyar kukan da aka yi da naman kaji ga man shanu da yajin daddawa ya ji, Umma hada min miyar da tuwon kawai a wuri daya, ta yi murmushi saboda tasan ba dabi’ata ba ce yin hakan, na gama cinye tuwon da ta zuba min din na kalle ta na ce mata na koshi bari in shiga toilet in wanke hannuna bana son wankewa a nan a zaune ta ce to bari in rike ki don ba karfi ne dake ba, yaya AImu yana jin haka yayi maza ya ce bari in kaita Umma, ta debi kwanukanta ta fita shi kuma ya rike ni ya kai ni na gama abin da zan yi ya dawo dani sai da ya gyara min kwanciyar da nayi sannan ya kalle ni cikin natsuwa ya ce tausayinki ya kama ni Rabi, kin yi ta wahala ke kadai ban ma sani ba sannan a yau din nan da kike fama da nakuda na sanyaki a gaba ina gaya miki bakaken maganganu ki yafe min duk wani abin da nayi miki na kan gaya miki magana ne don in dan ji sanyin bacin raina saboda gani nake tanfar kin ki zama da ni ne ki ka gudu kika barni amma na rantse miki Rabi ranar da kika bar gidan nan aka neme ki aka rasa a zaune na kwana akan kujera zuwa yau kuma da safe ban samu jin dadin da na saba ji ba a tare dani, amma a yanzu da naga wannan mutumin na gane duk abubuwan da ake yi min din suna da dalili har kuma ga kyautar da Ubangiji yayi mana, Rabi sai naji bani da sauran matsala a tare dani na godewa Allah da ya rufa min asiri ya yaye mana mas’alar, Allah da ya bani haihuwa tare dake na gode mishi rayuwarmu na kuma gode mishi da ya azurta ni da dan da Ummana tayi ta zubar da hawaye don rashin samunshi.
Ya dago idanuwanshi a hankali ya kalle ni kafin ya ce min wannan dan na Umma ne Rabi nan gaba dai za ki haifar mana namu amma wannan nata ne ita da Baba da ma su suka yi renon cikin shi, nayi maza na ce mishi da Umma Amarya ma ya ce a’a Rabi Umma Amarya ai bata shiga lamarinmu tana jin kunya nayi murmushi na soma ba shi labarin abubuwa har dai daga karshe na ba shi labarin karbar haihuwar da tayi na kuma ce mishi to ko wannan kayan dake jikinmu ni dashi ai ita tazo dasu randa taje Umra, ya yi murmushin jin dadi ya ce to naji amma dai ba zan yarda kice su dukansu ukun ba sai dai kawai in kika kara haifo wani nan gaba sai ita Umma Amarya ta dauka, na ce mishi to shi kenan.
Haihuwar da na yi lafiya ta saukar da wani irin farin ciki da annashuwa mai yawa cikin zukatan yan uwa da abokan arziki, tun ma kuma ba iyayenmu ba ko da yake dai Umma ta boye komai ba za ka ganta kaga wani canji a yanayinta ba, ta dauki haihuwar kamar kowacce da aka saba yi, to amma kuma kowa yasan ta boye abin da ke ranta ne don kuwa dama ita mai barwa ranta al’amarinta ne na farin ciki ko bakin ciki ba kasafai takan baiyanar har kowa ya gane abin da take ciki ba.
Yaya Almu kuwa tun washe garin ranar da aka yi haihuwar ya fara azumi saboda wai ya taba viwa Ubangiji alkawarin duk sanda ya bani ciki to zai yi mishi azumi talatin don godiya sannan ya sake yin wasu talatin din in na haihu lafiya.